Yadda Za A Yi Amfani da Sabuwar Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
An Tsara ta Ne don Taimaka Mana a Koma Ziyara da Kuma Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki
1. Wace sabuwar ƙasida ce aka fitar a Taron Gunduma na “Ka Kiyaye Zuciyarka!” don taimaka mana a koma ziyara da kuma nazari da mutane?
1 A Taron Gunduma mai jigo “Ka Kiyaye Zuciyarka!” mun yi farin cikin samun sabuwar ƙasida da za ta taimake mu sa’ad da muka koma ziyara da kuma soma nazari da mutane. Ƙasidar Albishiri Daga Allah! za ta sauya wannan ƙasidar Menene Allah Yake Bukata a Garemu?, kuma kamar ɗayan, darussan da ke cikin ta ba su da tsawo, shi ya sa ƙasidun sun zo ɗaya da juna. Hakan ya sa zai kasance mana da sauƙi mu soma nazari da mutane a bakin ƙofa ta wajen amfani da wannan sabuwar ƙasidar. Ƙasidar Menene Allah Yake Bukata a Garemu? bai da sauƙin tattaunawa a wasu lokatai domin tana ɗauke da muhimman koyarwar Kirista da suke da wuya ɗalibanmu su bi, amma wannan sabuwar ƙasidar ta mai da hankali ga albishiri da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne kawai.—A. M. 15:35.
2. Me ya sa aka fitar da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!
2 Don me aka wallafa ta? ’Yan’uwa a dukan duniya sun daɗe suna tambaya ko za a fitar da wani littafi mai sauƙin ganewa da zai jawo hankalin mutane ga gaskiya kuma zai sa mutane su soma nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Mutanen da suke jin tsoron karanta babban littafi za su iya yarda mu yi nazari da su ta wajen amfani da ƙasida. Ƙari ga haka, yana da sauƙi a fassara ƙasida zuwa harsuna da yawa.
3. A wace hanya ce wannan ƙasidar ta bambanta da sauran littattafanmu na nazari?
3 Yadda Aka Tsara Ƙasidar: An tsara yawancin littattafanmu na nazari a hanyar da mutane za su iya karantawa da kansu kuma su fahimci gaskiya ba tare da ja-gorar ’yan’uwa ba. Amma wannan ƙasidar ba haka take ba. An wallafa ta a hanyar da ’yan’uwa ne za su riƙa amfani da ita wajen nazari da mutane. Saboda haka, idan muna ba da ƙasidar, zai dace mu tattauna sakin layi ɗaya ko biyu da masu gida nan tāke. Za a iya tattauna ƙasidar a bakin ƙofa ko a inda ake kasuwanci domin sakin layin ba su da tsawo. Za mu iya soma nazarin a kowane darasi, amma zai fi dacewa mu soma daga darasi na 1.
4. Ta yaya wannan ƙasidar za ta taimake mu mu yi koyarwa daga Littafi Mai Tsarki kai tsaye?
4 A cikin littattafanmu da yawa, ana samun amsoshin tambayoyi a cikin sakin layin. Amma a cikin wannan ƙasidar, yawancin amsoshin suna cikin Littafi Mai Tsarki ne. Yawancin mutane sun fi son su ga abin da muke koya musu a Littafi Mai Tsarki maimakon a littattafanmu. Saboda haka, ba a yi ƙaulin yawancin ayoyin da aka rubuta ba. Ya kamata a karanta su kai tsaye daga Littafi Mai Tsarki ne. Hakan zai sa ɗalibanmu su fahimci cewa abin da suke koya daga wurin Allah ne.—Isha. 54:13.
5. Me ya sa yake da muhimmanci mai gudanar da nazari ya yi shiri sosai kafin nazarin?
5 Wannan ƙasidar ba ta bayyana dukan ayoyin da ke cikinta ba. Me ya sa? An tsara ta ne don ta ƙarfafa ɗalibi ya riƙa yin tambayoyi kuma ya ba wa mai gudanar da nazarin damar yin koyarwa da kyau. Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu shirya abin da za mu tattauna kafin mu je. Abin lura: Kada ku yi magana da yawa. A gaskiya, muna jin daɗin bayyana Nassi. Amma ɗalibanmu za su fi amfana idan mun ba su damar bayyana ra’ayinsu a kan Nassin da suka karanta. Ta wajen yin tambayoyin da suka dace, za mu taimaka musu su fahimci ma’anar kowane nassi da kansu.—A. M. 17:2.
6. Ta yaya za mu yi amfani da ƙasidar nan: (a) a inda mutane ba su gaskata da Allah ko Littafi Mai Tsarki ba? (b) sa’ad da muke wa’azi gida-gida? (c) wajen soma nazari da mutane nan tāke? (d) sa’ad da muka koma mu ziyarci mutane?
6 Kamar sauran littattafai da ake amfani da su don nazari, za a iya ba da wannan ƙasidar a kowane lokaci, ko da ba ita ce ake ba da wa a watan ba. ’Yan’uwa da yawa za su ji daɗin yin amfani da ita don soma nazari nan take da mutane a bakin ƙofa. Ƙari ga haka, kamar yadda aka ambata a taron gunduma, yin amfani da wannan ƙasidar wajen tattaunawa da masu son saƙonmu “zai iya sa mu ji daɗin komawa mu ziyarce mutane sosai!”—Ku duba akwatunan da ke shafuffuka na 5-7.
7. Yaya za ku iya gudanar da nazari ta wajen amfani da wannan ƙasidar?
7 Yadda Za A Gudanar da Nazarin: Za mu iya soma tattaunawa ta wajen karanta tambaya da aka rubuta da harufa da suka yi baƙi sosai. Bayan haka ku karanta sakin layin da kuma Nassin da aka rubuta da rubutun tafiyar tsutsa. Ku yi tambayoyin da suka dace don maigidan ya fahimci ma’anar ayoyin. Sa’an nan kafin ku shiga sashe na gaba, ku gaya wa maigidan ya amsa tambayar da rubutunta ya yi baƙi fiye da saura, don ku tabbata cewa ya fahimci batun. A zuwanmu na farko-farko, za mu iya tattauna tambaya ɗaya-ɗaya kawai. Amma a hankali za mu iya tattauna darasi ɗaya a take.
8. Ta yaya za mu gabatar da Nassin da muke son mu karanta, kuma don me za mu yi hakan?
8 Nassin da aka rubuta “karanta” a gabansu ne suka ba da amsoshin ƙananan tambayoyi kai tsaye. Sa’ad da muke son mu karanta wani nassi, zai dace mu guji amfani da furuci kamar su, “Manzo Bulus ya rubuta” ko kuma, “Ka ga annabcin Irmiya.” Maigidan zai iya ɗauka cewa muna karanta kalamin mutane ne kawai. Zai fi dacewa mu ce, “Kalmar Allah ta ce” ko kuma, “Ka ga wani annabcin da Allah ya yi.”
9. Ya kamata mu karanta dukan ayoyin da ke cikin ƙasidar ne sa’ad da muke gudanar da nazari?
9 Ya kamata mu karanta dukan ayoyin da ke cikin ƙasidar ne ko kuma waɗanda aka rubuta “karanta” a gabansu kawai? Wannan ya dangana da yanayin ɗalibin ne. Dukan ayoyin da ke ƙasidar suna da ma’ana. Kowanne yana ɗauke da bayani da ya kamata a tattauna. Amma a wani lokaci za mu iya karanta Nassin da aka rubuta “karanta” a gabansa ne kawai domin wasu ɗalibanmu ba su da lokaci ko marmari, ko kuma ba su iya karatu ba.
10. A wane lokaci ne zai dace mu canja zuwa nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da mutane?
10 Lokacin da Ya Dace Mu Canja Zuwa Nazarin Littafin Nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?: Idan muka tattauna da ɗalibi sau da yawa kuma muddin mun soma nazari da shi a kai a kai, za mu iya ci gaba da nazarin ƙasidar har ƙarshe ko kuma mu canja zuwa nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ’Yan’uwa ne za su nuna sanin yakamata wajen zaɓan lokacin da ya dace su canja littafin. Bayan mun canja zuwa littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, dole ne mu soma nazarin daga farkon littafin? Ba lallai ba. Yanayin mutane ba ɗaya ba ne. Amma, yawancin ɗalibai za su amfana idan aka sake nazarin batutuwan dalla-dalla da su a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
11. Me ya sa ya kamata mu yi amfani da sabuwar ƙasidar nan da kyau?
11 A wannan duniyar da mutane ba sa samun albishiri, muna da babban gata na yaɗa wannan albishiri mai daɗi cewa Mulkin Allah yana sarauta kuma ba da jimawa ba, zai mai da duniya ta zama sabuwa, inda za a yi adalci! (Mat. 24:14; 2 Bit. 3:13) Mun tabbata cewa mutane da yawa da suka ji saƙon bisharar nan za su yarda da wannan hurarren furuci: “Duba! ga ƙafafun mai-kawo bishara, daɗin gani garesu bisa duwatsu! mai-shelan salama, yana kawo bishara ta alheri, mai-shelan ceto; yana ce ma Sihiyona, Allahnki yana mulki!” (Isha. 52:7) Bari mu yi amfani da wannan sabuwar ƙasida wajen taimaka wa mutanen da suke son wannan saƙon Mulki, albishiri daga Allah!
[Akwati a shafi na 5]
Inda Mutane Ba Su Gaskata da Allah ko Littafi Mai Tsarki Ba:
● A wasu wurare, masu shela sun gano cewa idan suka yi amfani da kalmomin nan “Allah” ko kuma “Littafi Mai Tsarki,” mutane ba sa cika son su ci gaba da tattaunawa da su. Idan haka ne yanayin yankinmu, zai dace mu tattauna abubuwan da suka shafe mutane a zuwanmu na farko, kamar batun gwamnati mai kyau, yadda iyalai za su sami shawara mai kyau da kuma abin da zai faru a nan gaba. Za mu iya gabatar da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! bayan mun tattauna da maigidan sau da yawa a kan yadda za mu san cewa Allah ya wanzu da kuma dalilin da ya sa za mu iya gaskata da Littafi Mai Tsarki.
[Akwati a shafi na 6]
Sa’ad da Muke Wa’azi Gida-gida:
● “Na zo ne don in nuna maka hanya mai sauƙi na sanin abin da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Kana ganin Allah zai kawar mana da wahala kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan ƙasidar ta nuna inda za a sami amsar wannan tambayar a cikin Littafi Mai Tsarki. [Ka ba shi ƙasidar kuma ku tattauna sakin layi na farko a darasi na ɗaya da kuma Irmiya 29:11.] Bisa ga abin da muka karanta, kana ganin Allah yana son mu ji daɗi a nan gaba kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Idan kana so, zan bar maka wannan ƙasida. Idan na dawo, za mu tattauna sakin layi na biyu don mu sami amsar wannan tambayar daga cikin Littafi Mai Tsarki: ‘Ta yaya Allah zai kawar da abubuwan da suke wahalar da ’yan Adam?’” Idan maigidan yana da lokaci a zuwanka na farko, za ka iya karanta da kuma tattauna sakin layi na biyu har da ayoyi ukun da aka rubuta a wurin. Ka gaya masa za ka dawo don ku ci gaba da tattauna tambaya ta biyu a darasin.
● “Mutane da yawa suna son yin addu’a musamman ma idan suna da damuwa. Kana yin addu’a a wasu lokatai kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Kana ganin Allah yana amsa dukan addu’o’i ne, ko akwai waɗanda ba ya amsawa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ina da wata ƙasida da ta nuna yadda za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyi a Littafi Mai Tsarki. [Ka miƙa masa ƙasidar kuma ku tattauna sakin layi na farko a darasi na 12 da kuma ayoyin da aka ce ku “karanta.”] Abin farin ciki ne cewa Allah yana son ya saurari addu’o’inmu, ko ba haka ba? Amma, idan muna so mu yi addu’a a hanya da ta jitu da nufin Allah, ya kamata mu san Allah sosai. [Ka buɗe darasi na 2 kuma ka nuna masa ƙananan jigon.] Idan kana so, zan bar maka wannan ƙasidar, kuma idan na dawo za mu tattauna amsoshin waɗannan tambayoyin daga cikin Littafi Mai Tsarki.”
● “Na zo ne domin yawancin mutane sun damu sosai da abin da zai faru a nan gaba. Kana ganin abubuwa za su canja kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa suna mamakin sanin cewa Littafi Mai Tsarki na ɗauke da albishiri da zai sa mu kasance da bege. Ga wasu tambayoyin da Littafi Mai Tsarki ya ba da amsarsu.” Ka ba shi ƙasidar, kuma ka ce ya zaɓi tambaya a bayan ƙasidar da yake so ku tattauna. Sai ka buɗe inda ya zaɓa kuma ka nuna masa yadda muke nazari. Ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambaya da ke gaba.
[Akwati a shafi na 7]
Ku Gwada Soma Nazari da Mutane Nan Tāke:
● “Na ɗan ziyarce ka ne don in nuna maka wata sabuwar hanya na yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Wannan ƙasidar tana da darussa 15 da ke nuna inda za ka samu amsoshin tambayoyi masu muhimmanci daga naka Littafi Mai Tsarki. [Ka nuna masa bangon gaba da kuma na baya.] Ka taɓa ƙoƙarin fahimtar wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki? [Ka bari ya ba da amsa.] Bari in nuna maka yadda darussan da ke wannan ƙasidar suke da sauƙin tattaunawa. [Ka tattauna sakin layi na farko da ke ƙarƙashin tambaya ta uku a darasi na 3, kuma ka karanta Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5. Idan zai yiwu, ka karanta sakin layi na gaba da ayoyin da ke wurin.] Idan kana so zan ba ka wannan ƙasidar. Muna so ka gwada nazarin Littafi Mai Tsarki ta wannan hanyar ko da sau ɗaya ne. Idan kana so, sai ka ci gaba. Idan na dawo, za mu tattauna darasi na farko, kuma ka lura cewa tsawonsa shafi ɗaya ne kawai.”
[Akwati a shafi na 7]
Ku Gabatar da Ƙasidar Sa’ad da Kuka Koma Ziyara:
● Idan muka koma don mu ziyarci wani da yake son saƙonmu, za mu iya cewa: “Na yi farin cikin sake ganin ka. Na kawo maka wannan ƙasidar da take ɗauke da amsoshin tambayoyi da yawa masu muhimmanci daga Littafi Mai Tsarki. [Ka ba shi ƙasidar, kuma ka gaya masa ya dubi bayan ƙasidar.] Wane kan magana ka fi so? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka buɗe darasin da ya zaɓa.] Bari in nuna maka yadda za a iya amfani da ƙasidar nan wajen samun amsoshi daga Littafi Mai Tsarki.” Ka nuna masa yadda ake yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta wurin tattauna sakin layi ɗaya ko biyu da kuma ayoyin da aka rubuta “karanta” a gaban su. Hanya mai sauƙi na yin nazari ke nan, ko ba haka ba? Ka bar masa ƙasidar kuma ka gaya masa za ka dawo don ku ci gaba da tattaunawa. Idan ka gama tattauna darasin da shi, za ka iya tattauna wani darasi dabam da ya zaɓa ko kuma ku soma nazarin ƙasidar daga farko.