Yadda Za A Yi Amfani da Ƙasidar Nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?
An Tsara Sabuwar Ƙasidar don Jawo Hankalin Ɗalibanmu Zuwa Ƙungiyar Jehobah
1. Waɗanne dalilai uku ne suka sa aka fitar da ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?
1 Kun soma amfani da sabuwar ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? kuwa? An tsara ta ne don (1) mu taimaka wa ɗalibanmu su san Shaidun Jehobah, (2) mu taimaka wa ɗalibanmu su san ayyukanmu, kuma (3) mu nuna musu yadda ake tafiyar da abubuwa a cikin ƙungiyar Jehobah. Ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? tana ɗauke da darasi guda a kowane shafi, wanda za a iya tattauna a cikin minti biyar zuwa goma kawai a ƙarshen nazari da ɗalibanmu.
2. Ku bayyana yadda aka tsara ƙasidar nan da kuma abubuwan da ke ciki.
2 Yadda Aka Tsara Ƙasidar: An tsara ƙasidar zuwa sassa uku, kuma kowane sashe yana bayyana wani abu dabam game da ƙungiyar Jehobah, kamar yadda aka nuna a baya. Kan maganar kowanne cikin darussa 28 tambaya ce, kuma ƙananan jigo da aka rubuta da baƙaƙen harufa sosai fiye da saura suna ba da amsar tambayar. An ɗauki hotuna daga ƙasashe fiye da 50 kuma an rubuta sunayen ƙasashen a jikin hotunan domin a nuna cewa muna wannan aikin a dukan duniya. Za a sami akwatunan nan “Ka Ƙara Bincike,” a cikin darussa da dama kuma suna ɗauke da shawarwari da za ku iya ƙarfafa ɗalibanku su bi.
3. Ta yaya za mu yi amfani da ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?
3 Yadda Za Ku Yi Amfani da Ƙasidar: Da farko, za ku iya nuna wa maigida tambayar da ta zama kan maganar darasin. Bayan haka, yayin da kuke karanta darasin tare, ku ja hankalinsa ga ƙananan jigon da aka rubuta da baƙaƙen harufa sosai. A ƙarshe, ku tattauna tambayoyin bita da ke ƙasan shafin. Za ku iya karanta darasi guda gaba ɗaya kafin ku tattauna shi ko kuma ku karanta da kuma tattauna darasi sakin layi bayan sakin layi. Za ku iya zaɓan Nassi da za ku karanta daga cikin waɗanda aka rubuta a wurin bisa ga yanayin. Kada ku manta ku tattauna hotunan da kuma bayanin da ke akwatunan nan “Ka Ƙara Bincike.” A yawancin lokatai, zai dace ku tattauna darussan bi da bi. Amma za ku iya tsallake darasi domin ku tattauna wani batun da ya dace da yanayin. Alal misali, idan ana gab da yin wani babban taro ko taron gunduma, za ku iya tsallake zuwa darasi na 11.
4. Me ya sa kake farin cikin samun wannan sabon kayan aiki?
4 Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, muna taimaka musu su san Ubanmu na sama. Amma, muna bukatar koya musu game da ƙungiyar Jehobah. (Mis. 6:20) Muna farin cikin samun wannan sabon kayan aiki da zai taimaka mana mu yi hakan cikin sauƙi, ko ba haka ba?