Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?
1. A yaushe ne za mu soma nazarin ƙasidar Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? kuma ta yaya za mu amfana daga yin nazarinta?
1 A makon 28 ga watan Oktoba, za a soma nazarin ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. An tsara wannan sabuwar ƙasidar da aka fitar a Taron Gunduma na ‘Ka Kiyaye Zuciyarka!’ don a jawo hankalin ɗalibanmu zuwa ƙungiyar Jehobah. Yin nazarin wannan ƙasidar zai sa mu ƙara nuna godiya ga Jehobah don gatan kasancewa a cikin ƙungiyarsa kuma zai taimaka mana mu fahimci abubuwan da ke cikin ƙasidar sosai don mu iya yin amfani da ita da kyau sa’ad da muke wa’azi.—Zab. 48:13.
2. Wane tsari ne za a bi wajen yin nazarin wannan ƙasidar a ikilisiya?
2 Yadda Za a Yi Nazarinta: Zai dace mai gudanar da nazarin ya daidaita lokacinsa don a tattauna kowane darasi daidai wa daida. Zai gabatar da kowane darasi ta wajen karanta jigon darasin wanda tambaya ne. Sai ya gaya wa mai karatu ya karanta sakin layin da ke gabatar da darasin. Bayan haka mai gudanar da nazarin ya yi wa ’yan’uwa tambayar da ya shirya don wannan sakin layin. Sa’an nan, a karanta da kuma tattauna kowane sashe da aka soma rubutunsa da harufa da suka yi baƙi sosai. Bayan an karance sashen, mai gudanar da nazarin ya gaya wa ’yan’uwa su yi kalami a kan yadda sashen ya ba da amsar tambayar da ya zama jigon darasin. Ƙasidar tana ɗauke da hotuna da yawa da za a iya yin kalami a kansu. Ya kamata a karanta muhimman nassosin da ke ciki idan da lokaci. Bayan an gama nazarin darasi guda, mai gudanar da nazarin zai yi bitar darasin ta yin tambayoyi da ke ƙasan shafin kafin a soma nazarin darasi na gaba. Idan da akwatin “Ka Ƙara Bincike” a cikin darasin, ya sa mai karatun ya karanta akwatin kuma ya ba ’yan’uwa dama su faɗi yadda ɗalibansu za su iya amfana ta wajen bin wannan shawarar. Idan akwai lokaci, mai gudanar da nazarin yana iya yin amfani da jigon kowane darasi don ya yi bitar abin da aka tattauna bayan nazarin. Amma ba lallai sai mun bi wannan tsarin sa’ad da muke nazarin wannan ƙasidar da ɗalibanmu ba.
3. Me zai taimaka mana mu amfana sosai daga yin nazarin wannan ƙasidar?
3 Ku shirya da kyau kafin ku zo taro idan kuna son ku amfana sosai. Ku ƙoƙarta ku yi kalami. Sa’ad da ake nazarin, ku yi tunanin yadda ɗalibanku za su amfana. Bari nazarin wannan sabuwar ƙasidar ya sa mu ƙware wajen taimaka ma wasu su bi mu a yin nufin Allah don su ma su kasance da begen yin rayuwa har abada.—1 Yoh. 2:17.