Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/10 p. 2
  • Sabuwar Mujalla da Za a Ba Da!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sabuwar Mujalla da Za a Ba Da!
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za A Yi Amfani da Sabuwar Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Kana Yin Amfani da Waɗannan Ƙasidun?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Wata Hanya na Yin Amfani da Ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Yadda Za a Yi Nazari da Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 10/10 p. 2

Sabuwar Mujalla da Za a Ba Da!

1. Wace mujalla ce za mu ba da a watan Nuwamba, kuma mene ne manufar wannan mujallar?

1 A Taron Gundumarmu na “Ku Yi Tsaro!” wanda aka yi a shekara ta 2009/2010, an fito da sabuwar mujallar nan mai jigo Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? A watan Nuwamba, ikilisiyoyi a dukan duniya za su ba da mujallar a lokaci na farko. Ta yaya ne wannan mujallar za ta amfani mutane a yankinmu? Yawancin mutane, musamman waɗanda ba Kiristoci ba ne, ba su san Littafi Mai Tsarki sosai ba. Saboda haka, a shafi na 3 na mujallar an bayyana cewa an tsara ta don ta faɗa “ainihin abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.”

2. Ta yaya za mu iya gabatar da mujallar?

2 Yadda Za a Gabatar da Ita: Muna iya cewa: “Za mu so mu ji ra’ayinka a kan abin da wurin nan ya ce. [Karanta 2 Timotawus 3:16.] Mutane da yawa da muke tattaunawa da su sun amince da waɗannan kalaman, wasu kuma suna ji cewa Littafi Mai Tsarki, littafi mai kyau ne kawai. Mene ne ra’ayinka game da Littafi Mai Tsarki? [Ka bari ya ba da amsa.] Ko mene ne muka amince da shi, akwai dalilai masu kyau da ya kamata su motsa mu mu bincika Littafi Mai Tsarki da kanmu. [Ka karanta kalaman gabatarwar da ke saman shafi na 3.] Yayin da kake karanta taƙaitawar Littafi Mai Tsarki a wannan mujallar, za ka ga abu mai ƙayatarwa: Littafi Mai Tsarki yana da jigo ɗaya da kuma saƙo ɗaya.”

3. Wace gabatarwa ta biyu ce za mu iya yin amfani da ita, musamman a yankin da mutane da yawa ba Kiristoci ba ne?

3 Ga wata hanyar da za a iya gabatar da mujallar, musamman idan ana wa’azi a inda mutane da yawa ba Kiristoci ba ne: “Za mu so mu san ra’ayinka game da abin da aka ambata a wannan Nassin (ko kuma a wannan littafi mai tsarki). [Karanta Zabura 37:11.] Yaya kake gani duniya za ta kasance sa’ad da wannan annabci ya samu cikawa? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan misali ne na bege da tagomashi da mutane na dukan al’adu da imani za su iya samu daga Littafi Mai Tsarki.” Ka karanta sakin layi da ke saman shafi na 3, sai ka ba da mujallar.

4. Ta yaya za mu iya yin amfani da mujallar don mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

4 Ka Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki: Sa’ad da muka koma ziyara za mu iya tuna wa mai gidan abin da muka tattauna a kwanakin baya, sai mu yi bitar sakin layi ɗaya ko biyu a kan batun da muka tattauna, mu yi amfani da tambayoyin da ke ƙarshen sashen da suka dace. Ko kuma idan muna son mu gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a nan take, za mu iya karanta bangon mujallar, sai mu ba shi littafin, kuma mu tambaye shi ko wanne cikin jigon ya fi so, sai mu tattauna sakin layi ɗaya ko biyu na babin tare. Bari dukanmu mu sa hannu sosai wajen ba da mujallar nan a watan Nuwamba!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba