Yadda Za a Yi Nazari da Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
1. Yaya aka tsara ƙasidar?
1 Kamar yadda aka ambata a Hidimarmu ta Mulki ta watan Yuli, ɗaya cikin kayan aikin da muke da shi don wa’azi shi ne ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Ba a yi ƙaulin yawancin nassosin ba don mutane su ji daɗin koyo kai tsaye daga Littafi Mai Tsarki. Ko da yake an tsara littattafanmu da yawa yadda mutum zai iya yin nazari da su shi kaɗai, amma an tsara wannan ƙasidar don a riƙa amfani da ita wajen koyar da wani. Saboda haka, idan mun ba wani ƙasidar, zai dace mu nuna masa yadda ake amfani da ita wajen yin nazari don ya ga muhimmancin sanin albishirin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.—Mat. 13:44.
2. Ta yaya za mu yi amfani da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a haɗuwa ta farko?
2 A Haɗuwa ta Farko: Za ka iya cewa: “Na ziyarce ka ne don mutane sun damu game da inda duniya za ta kai mu. Kana ganin abubuwa za su gyaru kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da albishirin da zai ba mu bege. Ga wasu cikin tambayoyin da Littafi Mai Tsarki ya ba da amsarsu.” Ka ba mutumin ƙasidar sai ka ce masa ya zaɓi tambayar da yake so a bayan ƙasidar. Bayan haka, ka nuna yadda ake nazari da ƙasidar ta wurin yin amfani da sakin layi na farko a ƙasidar. Wata hanya kuma ita ce ta wajen yi wa mutumin wata tambaya da ke ƙasidar, bayan haka, sai ka nuna yadda ƙasidar za ta taimaka masa ya sami amsar. Wasu masu shela suna nuna bidiyon da ke jw.org da ya yi magana a kan abin da suke tattaunawa.
3. Ka bayyana yadda za a yi nazari da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!
3 Yadda Za A Gudanar da Nazarin: (1) Ka karanta tambayoyin da ke saman sakin layin don ka taimaka wa mutumin ya mai da hankali ga darasin. (2) Ka karanta sakin layin. (3) Ka karanta nassosin da aka ce a karanta kuma ka yi wasu tambayoyin da za su sa mutumin ya ga amsar a cikin nassosin. (4) Idan akwai wani sakin layi, ka maimaita shawara ta 2 da 3 da aka ambata a baya. Idan akwai wani bidiyo da ya yi magana a kan tambayar, ka nuna wa maigidan idan ba ka riga ka yi hakan ba. (5) A ƙarshe, ka yi tambayar don ka tabbata cewa mutumin ya fahimci batun sosai.
4. Mene ne zai taimaka mana mu ƙware wajen yin amfani da wannan ƙasidar?
4 Ka san bayanan da ke cikin ƙasidar nan da kyau. Ka yi amfani da ita a kowane lokacin da ya dace. Kafin kowane nazari, ka yi tunani a kan ɗalibinka da yadda za ka taimaka masa ta wurin yin amfani da nassosin da ke darasin. (Mis. 15:28; A. M. 17:2, 3) Idan ka ƙware wajen yin amfani da ƙasidar nan sosai, za ka ji daɗin yin amfani da ita wajen taimaka wa mutane su san Jehobah!