Ku Yi wa “Dukan Mutane” Wa’azi
1. Ta yaya masu shela suke kama da maƙeri da ya gwaninta?
1 Maƙeri da ya gwaninta yana da kayan aiki da yawa, kuma ya san lokacin da zai yi amfani da kowannensu da yadda zai yi hakan. Hakazalika, muna da kayan aiki dabam dabam da za su taimaka mana mu cika hidimarmu a matsayin masu shela. Alal misali, an wallafa ƙasidu da suka tattauna batutuwa dabam dabam don su taimaka mana mu yi wa’azi ga “dukan mutane.” (1 Kor. 9:22) ’Yar ciki da ke cikin wannan Hidimarmu Ta Mulki ta lissafa wasu cikin waɗannan ƙasidun, ta bayyana waɗanda aka wallafa wa ƙasidun da kuma yadda za a gabatar da su.
2. A wane lokaci ne zai dace mu yi amfani da ƙasidu a hidimarmu?
2 Lokacin da Za a Yi Amfani da Ƙasidu: Maƙeri zai yi amfani da kayan aiki a duk lokacin da ya dace. Hakazalika, za mu iya ba da ƙasida a duk lokacin da muke gani cewa zai amfane wani, ba a watanni da ake gabatar da su kawai ba. Alal misali, idan muna gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a watan, kuma muna wa’azi a yankin da mutane da ke wajen ba Kiristoci ba ne, zai dace mu ba da ƙasida da ta dace kuma mu gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? bayan mai-gidan ya nuna yana son saƙonmu.
3. Me ya sa ya kamata mu ƙware wajen yin amfani da kayan aikinmu na wa’azi?
3 Littafi Mai Tsarki ya yaba wa waɗanda suka gwaninta a aikinsu. (Mis. 22:29) Hakika, babu aikin da ya fi tsarkakkiyar ‘hidimar bishara’ muhimmanci a yau ba. (Rom. 15:16) Domin mu zama “ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gare shi” za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙware wajen yin amfani da kayan aikinmu.—2 Tim. 2:15.