RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a Wa’azi
Muna farin ciki da muka sami sabuwar ƙasida da sabon littafi da za mu yi amfani da su wajen nazarin Littafi Mai Tsarki. Addu’armu ita ce, Jehobah ya albarkace mu yayin da muke ƙoƙarin taimakawa mutane da yawa su zo su bauta masa. (Mt 28:18-20; 1Ko 3:6-9) Yaya za mu yi amfani da su?
Da yake an tsara sabbin hanyoyin koyarwa a ƙasidar da kuma littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, ku bi waɗannan tsarin sa’ad da kuke shiri da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki.a
Ku karanta darasin, sa’an nan ku tattauna tambayoyin
Ku karanta nassosi da aka ambata “karanta” ko “ku karanta,” kuma ku taimaka wa ɗalibin ya fahimci darasin
Ku kalli kuma ku tattauna bidiyoyin ta wajen amfani da tambayoyin
Ku yi ƙoƙari ku gama darasi ɗaya a kowane lokaci da kuka soma nazari
Sa’ad da kuke wa’azi, ku ba da ƙasidar don ku san ko mutumin zai so ya ci gaba da yin nazari. (Ku duba akwati “Yadda Za Mu Ba da Ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a Haɗuwa ta Fari.”) Idan kun gama nazarin ƙasidar da ɗalibin, kuma yana so ya ci gaba da nazarin, sai ku ba shi littafin kuma ku soma a darasi na 4. Idan kun riga kun soma amfani da wani littafin nazari da wani ko wata, ku koma nazari da wannan sabon littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, kuma ku zaɓi wurin da ya dace ku soma a littafin.
KU KALLI BIDIYON NAN MARABA DA ZUWA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Me ɗalibai za su koya daga sabon littafin nan?
Me ya sa zai dace ka nuna wa sabbin ɗalibai wannan bidiyon?
Waɗanne maƙasudai ne za ka ƙarfafa ɗalibin ya kafa kuma ya cim ma?—Ka duba sashen nan “Abin Lura da Maƙasudai da Ke Kowane Sashe”
a ABIN LURA: Ko da yake ba dole ba ne ku tattauna sashen “Ka Bincika” sa’ad da kuke nazari, ka karanta ko ka kalli bidiyoyin yayin da kake shiri. Hakan zai sa ka san abin da zai ratsa zuciyar ɗalibinka kuma ya taimaka masa. Idan da waya ne kuke nazarin, za ku iya kallon bidiyoyin kai tsaye kuma ku karanta talifofin.
ABIN LURA DA MAƘASUDAI DA KE KOWANE SASHE |
|||
---|---|---|---|
DARUSSA |
ABIN LURA |
MAƘASUDAN ƊALIBI |
|
01-12 |
Ka yi la’akari da yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka da kuma yadda za ka san Mawallafinsa |
Ka ƙarfafa ɗalibin ya karanta Littafi Mai Tsarki, ya riƙa yin shiri don nazarin, kuma ya soma halartan taro |
|
13-33 |
Za mu koyi abin da Allah ya yi mana da kuma irin bauta da ke faranta ransa |
Ka taimaka wa ɗalibin ya san yadda zai riƙa gaya wa mutane abin da yake koya kuma ya zama mai shela |
|
34-47 |
Za mu koyi abin da Allah yake so masu bauta masa su yi |
Ka taimaka wa ɗalibin ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma |
|
48-60 |
Za mu koyi yadda Jehobah zai ci gaba da ƙaunarmu |
Ka koya wa ɗalibin ya san abin da ya dace da wanda bai dace ba, kuma ya kusaci Allah |