Ku Yi Amfani da Tsofaffin Mujallunmu da Kyau
Tsofaffin mujallunmu ba za su amfani kowa ba idan muka tara su a gida ko kuma muka zubar da su. Saboda haka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu rarraba wa mutane. Mujalla guda kawai tana iya sa mutum ya so saƙon Littafi Mai Tsarki har ya soma bauta wa Jehobah. (Rom. 10:13, 14) Shawarwarin da ke gaba za su iya taimaka mana mu yi amfani da tsofaffin mujallunmu da kyau.
Idan kuna wa’azi a yankin da ba kwa cika yi kuma kuka tarar da gidan da babu kowa, za ku iya barin mujalla a inda masu gidan za su gani idan suka dawo.
Idan kuna wa’azi a inda akwai jama’a, alal misali a tashar mota ko wuraren da mutane suke jiran mota ko kuma gidajen mai, za ku iya tambayar mutanen ko za su so a ba su abin da za su karanta, sa’an nan ku nuna musu kofi dabam-dabam na tsofaffin mujallu don su yi zaɓi.
A duk lokacin da za ku je wuraren kasuwanci ko asibitoci ko makamantansu a yankinku, ku je da tsofaffin mujallu kuma ku ajiye su a inda mutane za su iya gani su karanta. Amma kafin ku bar mujallu a wuraren da aka ambata a baya, zai dace ku karɓi izinin yin hakan. Idan kuka iske wasu tsofaffin mujallu a wurin, kada ku ƙara wasu a kai.
A lokacin da kuke shiri don ku koma ku ziyarci waɗanda kuka yi musu wa’azi, ku yi la’akari da yanayin kowannensu da kuma abin da yake sha’awa. Mutumin yana da iyali ne? Shi manomi ne? Yana jin daɗin tafiyar wurare ne? Ku bincika tsofaffin mujallun don ku ga ko akwai talifin da zai so karantawa, sa’an nan ku nuna masa sa’ad da kuka koma.
Idan akwai wanda kuke ziyartarsa sau da sau a gida amma ba kwa haɗuwa da shi, a duk lokacin da kuka same shi, ku nuna masa wasu tsofaffin mujallunmu da bai da su.