Tsarin Ayyuka na Makon 17 ga Satumba
MAKON 17 GA SATUMBA
Waƙa ta 49 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 240 zuwa 242 sakin layi na 8 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ezekiyel 46-48 (minti 10)
Na 1: Ezekiyel 48:1-14 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Mu Kasance da Gaskiya a Dukan Abu—Afis. 4:25, 28; 5:1 (minti 5)
Na 3: Addu’o’in da Allah Ke Amsawa—td 3A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 64
Minti 30: “Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?—(Sashe na 1)” Tambayoyi ana ba da amsoshi, an ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2010, shafi na 12. Ka yi ɗan gabatarwa da bayanin da ke sakin layi na farko, sai ka soma yi wa masu sauraro tambayoyin da aka yi a sakin layi na 1 zuwa 11 da ke talifin Hasumiyar Tsaro. Ka yi amfani da bayanin da ke sakin layi na biyu wajen kammalawa.
Waƙa ta 88 da Addu’a