Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? (Sashe na 1)
Sa’ad da matasa suke girma, dole ne su tsai da shawara masu muhimmanci. Littafi Mai Tsarki yana kama ne da taswirar da za ta taimaka wa matasa su san tafarkin da ya kamata su bi. (Mis. 3:5, 6) Idan matasa suka horar da lamirinsu bisa ga koyarwar Littafi Mai Tsarki, hakan zai zama ja-gora mai kyau da za ta taimaka musu wajen bin tafarki mai kyau. (Rom. 2:15) Yin bitar talifin da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2010, mai jigo: “Matasa, Me Za Ku Yi Da Rayuwarku?” zai taimaka wa matasa su tsai da shawarwari masu kyau. Ku duba ku ga ko za ku iya ba da amsoshin tambayoyin da ke sakin layi na 1-11 a cikin wannan talifi na nazari.
Don Allah ku ƙoƙarta ku karanta sauran sakin layin da ke wannan talifin kuma ku yi shiri don ku ba da amsoshin tambayoyin da za a tattauna a Taron Hidima na mako mai zuwa. Ku karanta warƙar nan mai jigo, Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? kuma ku kalli bidiyon nan Young People Ask—What Will I Do With My Life? Bidiyon nan tare da warƙar suna ɗauke da bayanai masu amfani sosai da za su taimaka wa matasa.