Tsarin Ayyuka na Makon 24 ga Satumba
MAKON 24 GA SATUMBA
Waƙa ta 45 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 243 sakin layi na 9 zuwa shafi na 246 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Daniyel 1-3 (minti 10)
Na 1: Daniyel 2:17-30 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Wasu Addu’o’i Wofi Ne?—td 3B (minti 5)
Na 3: Ta Yaya Za Mu Iya Guji Ɓata Ran Ruhu Mai Tsarki?—Afis. 4:30 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 130
Minti 30: “Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? (Sashe na 2)” Tambayoyi ana ba da amsoshi, an ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2010, shafi na 14. Ka yi ɗan gabatarwa da bayanin da ke sakin layi na farko, sai ka soma yi wa masu sauraro tambayoyin da aka yi a sakin layi na 12 zuwa 20 na talifin Hasumiyar Tsaro. Ka yi amfani da bayanin da ke sakin layi na biyu wajen kammalawa.
Waƙa ta 91 da Addu’a