Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? (Sashe na 2)
Littafin Mai Wa’azi 12:1 ta ƙarfafa matasa da waɗannan kalmomin: ‘Ku tuna da Mahaliccinku a cikin kwanakin ƙuruciyarku.’ Hakika, yin hidima a bautar Jehobah ita ce hanya mafi kyau ta yin rayuwa. Amma, kafin ku yi hidima a bautar Allah, wajibi ne ku zama waɗanda suka cancanta. Ta yaya za ku yi hakan? Mene ne yin hidima a bautar Allah ta ƙunsa? Za mu amsa waɗannan tambayoyin yanzu yayin da muke tattauna sauran sashen talifin da muka tattauna a makon da ya shige.
A wani lokaci, rashin lafiya, rashin kuɗi, da nauyin da mutum yake ɗauke da shi na iyali yana iya rage abin da zai iya cim ma. Amma duk da haka, dole ne dukan Kiristoci na gaskiya su bi wannan umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Jehobah yana so ku yi iya ƙoƙarinku don ku bauta masa yadda ya cancanta a duk wani halin da kuke ciki. Saboda haka, a duk yanayin da kuka sami kanku, ku sa bauta wa Jehobah ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarku. Ku kafa maƙasudai masu kyau da za ku iya cim ma a bautar Allah. Hakika, idan ‘kuka tuna da Mahaliccinku a cikin kwanakin ƙuruciyarku,’ za ku samu albarka har abada!