Tsarin Ayyuka na Makon 1 ga Oktoba
MAKON 1 GA OKTOBA
Waƙa ta 103 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 247 zuwa shafi 249 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Daniyel 4-6 (minti 10)
Na 1: Daniyel 4:18-28 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Bai Kamata Kiristoci na Gaske Su Saka Hannu a Sihiri Ba (minti 5)
Na 3: Ba Bisa Kadara Mutum Yake Ba—td 25A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 80
Minti 5: Yadda Za Mu Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Ranar Asabar ta Farko. Ta wajen yin amfani da gabatarwar da ke wannan shafin, ka sa a gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta farko a watan Oktoba. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su saka hannu a yin hakan.
Minti 15: Mene Ne Muka Cim Ma a Bara? Jawabin da mai kula da hidima zai ba da. Ka yi bitar aikin wa’azi da ikilisiya ta yi a shekarar hidima da ta gabata, ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da aka cim ma, ka kuma yaba wa ’yan’uwa a inda ya kamata. Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da za su iya ba da labarai masu daɗi game da wa’azin da suka yi bara. Ka ambata sashen hidima ɗaya ko biyu da ’yan’uwa a cikin ikilisiya za su iya ingantawa a shekara mai zuwa, kuma ka ba da shawarwari masu kyau da za su taimaka musu su cim ma hakan.
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Oktoba. Tattaunawa. Ka ɗauki sakan 30 zuwa minti ɗaya ka tattauna dalilan da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Ta wajen yin amfani da jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro da kuma talifofi na farko, ka sa masu sauraro su faɗi tambayar da za su yi, wadda za ta jawo hankalin mutane, sa’an nan su faɗi nassin da za su karanta. Ka yi hakan ma da jigon da ke bangon gaba na Awake! da kuma wani talifi a ɗaya daga cikin mujallun idan da sauran lokaci. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowace mujallar.
Waƙa ta 85 da Addu’a