Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Oktoba
“Mutane sun daɗe suna magana game da mala’iku. Kana ganin mala’iku halittu ne na gaske? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka duba abin da aka ce a nan.” Ka ba mutumin Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba, kuma ku tattauna ƙaramin jigo na farko da ke shafi na 16 tare, sa’an nan ka karanta aƙalla nassi ɗaya. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Oktoba-Disamba
Ka nuna wa maigidan kan magana da ke bangon Hasumiyar Tsaron kuma ka ce, “Mene ne ra’ayinka game da wannan tambayar: ‘Allah ya damu da mata kuwa?’ [Ka bari ya ba da amsa.] Dubi irin matsayin da mata suke da shi a gaban Allah. [Ka karanta 1 Bitrus 3:7.] Wannan mujallar tana ɗauke da bayani game da yadda Allah ya ɗauki mata.”
Awake! Oktoba
“Yawancin iyaye suna son ’ya’yansu su yi karatu sosai. Kana ganin cewa matasan da suke sauke karatu a yau za su iya jimre da ƙalubalen da za su fuskanta? [Ka bari ya ba da amsa.] Bari in nuna maka abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da muhimmancin samun ilimi tare da hikima. [Ka karanta Mai Wa’azi 7:12.] Wannan mujallar ta tattauna abubuwa guda biyar da za su taimaka wa yara su yi nasara a makaranta.”