Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Oktoba
“Mutane da yawa sun maimaita kalmomin da ke Addu’ar Ubangiji: ‘Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.’ Mene ne kake tsammani shi ne wannan Mulkin? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan aya ta Littafi Mai Tsarki ta ba da amsa.” Ka karanta Daniyel 2:44. Sai ka ba mai gidan kofi na Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba kuma ka karanta da kuma tattauna talifin da ke ƙarƙashin kan maganan da ke shafi na 8. Ka ba da mujallar, kuma ka shirya don koma ziyara don ka amsa tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Oktoba-Disamba
Ka nuna wa maigidan bangon mujallar, sai ka ce: “Yaya za ka amsa tambayar nan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. [Karanta 1 Yohanna 5:19.] Kamar yadda ayar nan ta nuna, “Shaitan” ne yake mulkin duniya. Amma wannan ya ta da wasu tambayoyi. Daga ina ne Iblis ya zo? Shin ya wanzu da gaske kuwa? Har tsawon shekara nawa ne Allah zai ƙyale shi ya yi sarauta? Wannan talifin da ya soma daga shafi na 3 ya nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.”
Awake! Oktoba
“Muna ziyararku a yau a matsayin masu hidima ga iyalai. Kana ganin mene ne ƙalubale mafi wuya da iyaye suke fuskanta a yau wajen renon yara? [Ka bari ya ba da amsa.] Iyaye da yawa suna neman shawara daga cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, kalaman nan na hikima suna taimakawa sa’ad da ake yi wa yara horo. [Karanta Afisawa 4:31.] Wannan mujallar ta nuna yadda shawarar Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka wa iyaye a lokacin da yaransu suke girma, daga jarirai zuwa ƙuruciya.”