Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Oktoba
“Muna tattaunawa da mutane game da batun addu’a. Ka taɓa tunani a kan abin da ya wajaba mu yi don Allah ya ji addu’armu?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa bangon bayan Hasumiyar Tsaro ta Satumba–Oktoba kuma ku tattauna tambaya ta biyu. Ka karanta sakin layi na farko a ƙarƙashin tambayar da kuma aƙalla nassi ɗaya cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallar kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na gaba.
Hasumiyar Tsaro Satumba–Oktoba
“Sa’ad da bala’i ya auku, mutane da yawa suna ganin kamar Allah ba ya kula da ’yan Adam kuma bai damu da wahala da suke sha ba. Shin ka taɓa yin irin wannan tunanin? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka yi la’akari da yadda Allah ya ji sa’ad da mutanensa Isra’ilawa suke shan wahala a dā. [Karanta Ishaya 63:9.] Babu shakka, za ka ji daɗin karanta talifin da ke shafuffuka na 12 da 13 a wannan mujallar.”
Awake! Oktoba
“Zan so in ji amsarka game da wannan tambayar: Shin zai yiwu mu kasance da wadar zuci idan ba mu da arziki sosai? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kan batun. [Karanta 1 Timotawus 6:8.] Wannan mujallar ta nuna yadda za mu iya kasancewa da ra’ayin da ya dace game da abin duniya kuma ta tattauna abubuwa masu muhimmanci guda uku da kuɗi ba zai iya saya ba.”