Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/11 p. 2
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da Littattafanmu Yadda Ya Dace
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Mene ne Yanayinsa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 12/11 p. 2

Akwatin Tambaya

◼ Mene ne zai nuna ko za mu bar wa mutum littattafanmu?

Abin da ya fi muhimmanci da za mu yi la’akari da shi, shi ne ko mutumin yana son saƙonmu. Idan ya nuna yana son saƙonmu sosai, muna iya bar masa mujallu biyu ko ƙasida ɗaya ko littafi guda ko kuma wasu littattafai da muke bayarwa. Za mu yi hakan ko idan mun fahimci cewa ba shi da kuɗin da zai ba da gudummawa ga aiki na dukan duniya. (Ayu. 34:19; R. Yoh. 22:17) A wani ɓangare kuma, ba za mu bar littattafanmu masu tamani ga waɗanda ba su san amfaninsu ba.—Mat. 7:6.

Ta yaya maigida zai nuna yana son saƙonmu? Alama mai kyau ita ce kasancewa a shirye don ya tattauna da mu. Saurarawa sa’ad da muke magana da amsa tambayoyinmu da kuma furta ra’ayinsa ya nuna cewa yana bin abin da ake tattaunawa. Saurarawa sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana daraja Kalmar Allah. Sau da yawa, yana da kyau mu tambaye shi ko zai karanta littafin da muke bayarwa. Ya kamata masu shela su yi amfani da basira don su san ko mutumin yana son littattafanmu. Alal misali, sa’ad da muke wa’azi a kan titi, ba zai dace ba mu ba da mujallu da ƙasidu ko kuma littattafai ga kowa da ya wuce mu ba. Idan ba za mu iya sanin ko mutumin yana son littafin ba, zai fi kyau mu ba shi warƙa.

Haka nan ma, yawan littattafai da mai shela zai karɓa ya kamata ya dangana da abin da yake bukata don hidimarsa, ba bisa yawan gudummawar kuɗin da ya ba da ba. Gudummawar da ake ba da ba don biyan kuɗin littattafanmu ba amma don a tallafa wa dukan fannoni na aikin wa’azi da muke yi a dukan duniya. Ko muna da kuɗi ko a’a, nuna godiya zai motsa mu mu ba da gudummawa da dukan zuciyarmu don mu tallafa wa ayyukan Mulki. (Mar. 12:41-44; 2 Kor. 9:7) Hakan zai motsa mu mu karɓa littattafan da muke bukata kaɗai, ta hakan ba za mu riƙa ɓata dukiya na ƙungiyar Jehobah ba.

[Bayanin da ke shafi na 2]

Ya kamata masu shela su yi amfani da basira don su san ko mutumin yana son littattafanmu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba