Mene ne Yanayinsa?
Ya dace a yi irin wannan tambaya game da kowane littafin da muke son mu ba mutane. Kowane littafin da ya kalmasa kuma kalan ya canja kuma an ɓata shi ko ya yage zai ɓata sunan ƙungiyarmu kuma zai janye hankalin mai gidan daga saƙo mai kyau da ke ceton rai da ke cikin littafin.
Ta yaya za mu iya sa littattafanmu ya kasance da tsabta? Mutane da yawa sun ga yana da ban taimako su tsara jakarsu na wa’azi don su ajiye abubuwa iri ɗaya tare. Alal misali, suna da gefen saka littattafai da kuma na mujallu da ƙasidu, har da na warƙoƙi da kuma sauransu. Bayan kowane tattaunawa, sai su mai da Littafi Mai Tsarki da kuma kowane littafi cikin jakarsu na wa’azi a hankali don kada ya lalace kome. Wasu masu shela suna ajiye littattafansu a cikin fayil ko kuma jakar leda. Ko da mene ne muke amfani da shi, bai kamata mu ba wani dalilin ganin laifi da hidimarmu don mun ba su littafin da ya lalace.—2 Kor. 6:3.