“Zan Karɓi Littattafanku Idan Kuka Karɓi Nawa”
Abin da wasu mutane da muke musu wa’azi suke faɗa ke nan. Ta yaya za mu ba su amsa cikin basira, tun da yake ba ma musanyar littattafanmu da littattafan addinai da suke yaɗa koyarwar ƙarya? (Rom. 1:25) Muna iya cewa: “Mun gode. Mene ne littafin ya faɗa a kan yadda za a iya magance matsalolin ’yan Adam? [Ku bari ya ba da amsa. Idan ya gaya muku cewa za ku sami amsar idan kuka karanta littafin, za ku iya gaya masa cewa kun bayyana masa abin da ke cikin littattafanku kafin kuka ba shi. Sai ku karanta ko kuma ku yi ƙaulin littafin Matta 6:9, 10.] Yesu ya ce Mulkin Allah zai sa a yi nufin Allah a duniya. Saboda haka, littattafan addini da nake karantawa su ne waɗanda ke tattauna batun Mulkin Allah. Bari in nuna maka wasu abubuwa da Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah zai yi.”