Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 6/1 pp. 22-27
  • Ceto, Ba Ta Wurin Aiki Ba Kawai, Amma Ta Wurin Alheri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ceto, Ba Ta Wurin Aiki Ba Kawai, Amma Ta Wurin Alheri
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Kowa na Mai da Ɗan’uwansa Ya Fi Shi”
  • “Ba Sai Ya Gwada Kansa da Wani Ba”
  • Ra’ayin da Ya Dace Game da Aikinmu
  • “Himmar Yin Kyakkyawan Aiki”
  • Ka Yi Wa’azi Game da Alherin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Nuna Godiya don Alherin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Kai ‘Wakili Na Alherin Allah’ Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kun Sami ‘Yanci Saboda Alherinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 6/1 pp. 22-27

Ceto, Ba Ta Wurin Aiki Ba Kawai, Amma Ta Wurin Alheri

“[An] cece ku saboda bangaskiya, . . . ba kuwa saboda aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.” —AFISAWA 2:8, 9.

1. Ta yaya Kiristoci suka bambanta daga galibin mutane game da abin da suka cim ma da kansu, kuma me ya sa?

MUTANE a yau suna fariya domin abubuwa da suka cim ma, kuma wani lokaci suna hanzarin yin gori da su. Amma Kiristoci sun bambanta. Suna guje wa nanata abin da suka cim ma, har da waɗanda suka shafi bauta ta gaskiya. Sa’ad da suke murna domin abin da mutanen Jehobah gaba ɗaya suka cim ma, sun rufe abin da suka cim ma da kansu. Sun fahimci cewa a hidimar Jehobah zuciyar kirki ta fi abin da mutum ya cim ma muhimmanci. Dukan wanda a ƙarshe aka ba shi kyautar rai madawwami ya samu ne ba domin abin da ya cim ma ba, amma domin bangaskiya da kuma alherin Allah.—Luka 17:10; Yahaya 3:16.

2, 3. Menene Bulus ya yi alfahari da shi, kuma don menene?

2 Manzo Bulus yana sane da wannan. Bayan ya yi addu’a sau uku domin ya sami sauƙi daga “ƙaya,” ya sami amsar Jehobah: “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Da ya karɓi shawarar Jehobah cikin tawali’u, Bulus ya ce: “Saboda haka sai ma in ƙara yin taƙama da raunanata, domin ikon Almasihu ya zauna tare da ni.” Halin tawali’u na Bulus shi ne abin da za mu so mu yi koyi da shi.—2 Korantiyawa 12:7-9.

3 Ko da yake Bulus ya yi fice wajen yin ayyukan Kirista, ya fahimci cewa nasararsa ba domin wani iyawarsa ba ne. Cikin filako, ya ce: “Ko da ya ke ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al’ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa.” (Afisawa 3:8) Babu fariya a nan, ko kuma adalcin kai. “Allah na gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali’u alheri.” (Yakubu 4:6; 1 Bitrus 5:5) Muna bin misalin Bulus kuwa, muna ɗaukan kanmu mafiya ƙanƙanta cikin ’yan’uwanmu?

“Kowa na Mai da Ɗan’uwansa Ya Fi Shi”

4. Me ya sa zai yi wuya ko da yaushe mu ɗauki wasu cewa sun fi mu?

4 Manzo Bulus ya yi wa Kiristoci gargaɗi: “Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa na mai da ɗan’uwansa ya fi shi.” (Filibiyawa 2:3) Wannan zai iya kasancewa ƙalubale, musamman ma idan muka kasance muna da iko. Wataƙila matsalar ta taso ne domin an rinjaye mu, da ra’ayin gāsa da ta yi yawa a duniya ta yau. Wataƙila, sa’ad da muke yara an koya mana mu yi gāsa, ko da ’yan’uwanmu a gida ko kuma da ’yan ajinmu a makaranta. Wataƙila an yi ta ariritarmu mu zama fitaccen ɗan wasa na makaranta ko kuma fitaccen ɗalibi. Hakika, yin iya ƙoƙarinmu a dukan wani abu mai kyau abin yabo ne. Amma kuma, Kiristoci suna yin haka ne ba domin su jawo hankali ga kansu ba, amma domin su amfana ne ƙwarai daga aiki kuma wataƙila domin su amfani wasu. Amma, kasancewa da niyar zama na ɗaya domin a yabi mutum yana iya kasancewa da haɗari. Ta yaya?

5. Idan aka ƙyale halin gāsa menene zai iya jawowa?

5 Idan aka ƙyale, halin gāsa ko kuma ɗaukaka kai zai iya sa mutum ya zama marar daraja wasu kuma mai girmankai. Wataƙila ya zama yana kishin iyawar wasu ko kuma gata da suke da shi. Karin Magana 28:22 ta ce: “Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.” Cikin girman kai zai ɗauki matsayin da ba a ba shi ba. Domin ya kāre abin da ya yi, sai ya fara gunaguni yana sūkan wasu—halaye da ya kamata Kiristoci su gujewa. (Yakubu 3:14-16) Ko yaya dai, yana kan hanyar koyar halin ni ne farko.

6. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi game da halin gāsa?

6 Saboda haka Littafi Mai Tsarki ya aririci Kiristoci: “Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.” (Galatiyawa 5:26) Manzo Yahaya ya yi magana game da wani Kirista wanda ya faɗa cikin irin wannan halin. “Na yi wa ikilisiya ’yar wasiƙa,” in ji Yahaya, “amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu. Saboda haka in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu.” Wannan yanayi ne na baƙin ciki a ce Kirista ya faɗa ciki!—3 Yahaya 9, 10.

7. Menene ya kamata Kirista ya guje wa a wajen aiki da ke cike da gāsa a duniya ta yau?

7 Hakika ba daidai ba ne a yi tunanin cewa Kirista zai iya ya guje wa dukan wani abin da ya shafi gāsa. Alal misali, aikinsa, yana iya ya ƙunshi gāsa wajen kasuwanci da mutane ko kuma da kamfanoni da suke ƙera abu iri ɗaya. Har a irin waɗannan yanayi ma, ya kamata Kirista ya yi kasuwancinsa da daraja, da ƙauna da kuma sanin ya kamata. Zai guje wa ayyukan taka doka ko kuma ayyuka da aka haramta, ya zama mutumin da aka sani da gāsa da hali irin na kare-ya-ci-kare. Kada ya ji cewa zama na ɗaya—a kowane irin abu—shi ya fi muhimmanci a rayuwa. Idan haka ya kasance wajen aiki, ai ya kamata ya fi haka wajen bauta!

“Ba Sai Ya Gwada Kansa da Wani Ba”

8, 9. (a) Me ya sa Kiristoci dattawa ba su da dalilin yin gāsa da juna? (b) Me ya sa abin da 1 Bitrus 4:10 ta ce ya shafi dukan bayin Allah?

8 Hali da ya kamata Kirista ya kasance da shi wajen bautarsa an kwatanta shi cikin waɗannan hurarrun kalmomi: “Kowa yā auna aikinsa ya gani, sa’an nan ne zai iya taƙama da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.” (Galatiyawa 6:4) Dattawan ikilisiya, sun sani cewa ba gāsa suke yi da juna ba, saboda haka suke ba da haɗin kai suke aiki tare. Suna farin ciki ga dukan wani gudummawa da kowane yake bayarwa domin jin daɗin ikilisiya. Da haka suke korar gāsa kuma suke kafa misali mai kyau na haɗin kai ga dukan ikilisiya.

9 Domin yawan shekaru, fahimi, da kuma iyawa, wasu dattawa za su fi wasu, ko kuma za su kasance suna da fahimi ƙwarai. Domin haka, hakkin dattawa ya bambanta a ƙungiyar Jehobah. Maimakon gwada wani da wani, sun tuna wannan gargaɗin: “Duk baiwar da mutum ya samu, yā yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan’uwansa, kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne.” (1 Bitrus 4:10) A gaskiya, wannan ya shafi dukan bayin Jehobah, domin duk sun sami kyauta ta cikakken sani kuma duka suna more gatar saka hannu cikin hidima ta Kirista.

10. A wace hanya ce kawai Jehobah zai karɓi bautarmu?

10 Hidimarmu ta bauta za ta faranta wa Jehobah idan muka yi ta cikin ƙauna da ibada, ba domin muna so mu ɗaukaka kanmu bisa wasu ba. Saboda haka yana da muhimmanci mu ɗauki ayyukanmu yadda ya kamata domin mu tallafa wa bauta ta gaskiya. Ko da yake babu wanda zai iya bincika dalilinmu, Jehobah “yana kuwa auna manufofi.” (Karin Magana 24:12; 1 Sama’ila 16:7) Saboda haka yana da muhimmanci mu tambayi kanmu lokaci lokaci, ‘Menene dalili na, na yin ayyukan bangaskiya?’—Zabura 24:3, 4; Matiyu 5:8.

Ra’ayin da Ya Dace Game da Aikinmu

11. Waɗanne tambayoyi ne game da ayyukanmu a hidima ya kamata mu yi la’akari da su?

11 Idan dalili yana da muhimmanci ƙwarai wajen samun yardar Jehobah, to, yaya ya kamata mu ɗauki aikinmu na bangaskiya? Idan muka yi aikinmu da zuciyar kirki, dole ne mu rubuta abin da muka yi da kuma yawansa? Waɗannan tambayoyi suna da muhimmanci tun da ba ma so mu saka adadi bisa ayyukan bangaskiya ko kuma samun rahoto mai kyau ya zama abin da ya fi damunmu a hidimarmu ta Kirista.

12, 13. (a) Waɗanne ’yan dalilai muke da su na adana rahoton hidimarmu ta fage? (b) Waɗanne dalilai muke da su na farin ciki sa’ad da muka ga rahoton ayyukan hidima gaba ɗaya?

12 Ka lura da abin da littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will ya ce: “Mabiyan Yesu Kristi na farko sun yi marmarin rahoton ci gaba na aikin wa’azi. (Markus 6:30) Ayyukan Manzanni littafi na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa da mutane 120 sa’ad da ruhu mai tsarki ya zubo kan almajirai a ranar Fentakos. Ba da daɗewa ba almajiran suka kai 3,000 sai kuma 5,000. . . . (Ayyukan Manzanni 1:15; 2:5-11, 41, 47; 4:4; 6:7) Lalle wannan labarin ƙaruwa ya ƙarfafa almajiran! Domin wannan dalili, Shaidun Jehobah a yau suke ƙoƙari su adana cikakken rahoton abin da aka cim ma a dukan duniya domin cika kalmomin Yesu: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Matiyu 24:14) Irin wannan rahoto yana ba da kwatancin abin da ake yi a duniya duka. Suna nuna wuraren da ake bukatar taimako da kuma irin littattafai da ake bukata da kuma yawansu domin a ci gaba da aikin wa’azi.

13 Saboda haka ba da rahoton ayyukanmu yana sa mu yi aikin wa’azinmu na Mulki da kyau. Ban da haka, ba ma samun ƙarfafa ne idan muka ji game da aiki da ’yan’uwanmu suke yi a wasu ɓangarorin duniya? Labarin faɗaɗa a dukan duniya yana ba mu farin ciki, kuma yana tabbatar mana da albarkar Jehobah. Kuma hakika yana kayatarwa cewa namu rahoto yana cikin waɗannan a dukan duniya! Namu ba shi da yawa idan aka gwada da na dukan duniya, amma Jehobah yana sane da shi. (Markus 12:42, 43) Ka tuna cewa idan ba tare da rahotonka ba, rahoto na dukan duniya ba zai cika ba.

14. Ban da wa’azi da koyarwa, menene kuma bautarmu ga Jehobah ta ƙunsa?

14 Hakika, yawancin dukan abin da Mashaidi ya yi domin cika hakkinsa na keɓaɓɓen bawa ga Jehobah ba ya bayyana a cikin rahoton. Alal misali, rahoton ba ya haɗawa da nazarin Littafi Mai Tsarki na kai, halarta da kuma yin kalami a taron Kirista, ayyuka a ikilisiya, da kuma taimako ga ’yan’uwa masu bi, da kuma tallafawa na kuɗi ga aikin wa’azin Mulki na dukan duniya da dai sauransu. Saboda haka, sa’ad da rahoto na hidimarmu ta fage take nata aiki wajen sa mu kasance da ƙwazo wajen wa’azi kuma mu guje wa sanyin gwiwa, dole ne mu ba ta matsayin da ya dace. Kada a ɗauki rahoton lasisi na tabbatar da samun rai madawwami.

“Himmar Yin Kyakkyawan Aiki”

15. Ko da yake ayyuka kawai ba za su cece mu ba, me ya sa suke da muhimmanci?

15 Babu shakka, ayyuka kawai ba za su cece mu ba, ko da yake suna da muhimmanci. Shi ya sa aka kira Kiristoci jama’a na musamman “su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki,” kuma abin da ya sa aka ƙarfafa su su ‘ta da juna a tsimi su yi ƙauna da aiki nagari.’ (Titus 2:14; Ibraniyawa 10:24) Bugu da ƙari, Yakubu marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.”—Yakubu 2:26.

16. Menene ya fi aiki muhimmanci, amma ga menene ya kamata mu mayar da hankali?

16 Ko da yake ayyukanmu suna da amfani, dalilin yin ayyukan ya fi ma muhimmanci. Saboda haka yana da muhimmanci lokaci lokaci mu riƙa bincika dalilanmu na yin aiki. Tun da babu mutumin da zai iya faɗin abin da ke zuciyar wasu, mu mai da hankali kada mu riƙa kushe wasu. “Kai wanene har da za ka ga laifin baran wani?” Aka yi mana tambaya, amsar kuma a bayyane take: “Ko dai ya tsaya ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne.” (Romawa 14:4) Jehobah Ubangijin kowa, da kuma alƙali da ya naɗa, Yesu Kristi, za su yi mana shari’a, ba bisa ayyukanmu ba kawai amma kuma bisa dalilin yin su, zarafin da muka samu, ƙaunarmu, da kuma ibadarmu. Jehobah ne kaɗai da kuma Yesu Kristi za su iya yi mana hukunci daidai bisa ko mun yi abin da aka umurci Kiristoci su yi, a kalmomin manzo Bulus: ‘Ka himmantu ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassarar Maganar gaskiya daidai.’—2 Timoti 2:15; 2 Bitrus 1:10; 3:14.

17. Sa’ad da muke fama mu yi iya ƙoƙarinmu, me ya sa za mu riƙa tuna Yakubu 3:17?

17 Jehobah mai sanin ya kamata ne game da abin da yake bukata a gare mu. Yakubu 3:17 ta ce: ‘Hikiman nan ta Sama, saliha ce.’ Ba zai kasance tafarkin hikima ba, da kuma na gamsuwa ta gaskiya, mu yi koyi da Jehobah a wannan hanyar? Saboda haka kada mu kafa wa kanmu ko kuma ga ’yan’uwanmu abin da ba za mu iya cim ma wa ba.

18. Menene za mu saurara idan muka kasance da daidaitaccen ra’ayi game da aikinmu da kuma alherin Jehobah?

18 Idan dai har muka ci gaba da kasancewa da daidaitaccen ra’ayi game da aikinmu na bangaskiya da kuma alherin Jehobah, za mu sami farin ciki da alama ce mai bambanta bayin Jehobah. (Ishaya 65:13, 14) Za mu yi farin ciki da albarkar da Jehobah yake ba wa mutanensa duka, ko da yaya iyakar abin da mu da kanmu za mu iya yi. Mu ci gaba cikin “addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah,” mu roƙi Allah ya taimake mu mu yi iyaka ƙoƙarinmu. Babu wata tantama kuma, “salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” (Filibiyawa 4:4-7) Hakika, za mu sami kwanciyar rai da ƙarfafa daga fahimtar cewa za a cece mu, ba ta wurin aiki ba kawai, amma ta wurin alherin Jehobah!

Za Ka Iya Ba da Bayanin Abin da Ya sa Kiristoci

• suke guje wa fariya game da abin da suka cim ma da kansu?

• suke guje wa yin gāsa?

• suke ba da rahoton hidimarsu ta fage?

• suke guje wa hukunta ’yan’uwansu Kiristoci?

[Hoto a shafi na 23]

‘Alheri na ya ishe ka’

[Hotuna a shafuffuka na 24, 25]

Dattawa suna farin ciki da gudummawa da kowanne yake bayarwa domin jin daɗin ikilisiya

[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]

Idan ba tare da rahoton ka ba rahoton dukan duniya ba zai cika ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba