Kai ‘Wakili Na Alherin Allah’ Ne?
“Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatarda juna cikin bangirma.”—ROM. 12:10.
1. Wane tabbaci ne Kalmar Allah ta ba mu?
KALMAR ALLAH a kai a kai ta tabbatar da mu cewa Jehobah zai taimake mu sa’ad da muka yi sanyin gwiwa ko baƙin ciki. Alal misali, ka lura da waɗannan kalmomin masu ban ƙarfafa: “Ubangiji yana talafan dukan waɗanda su ke faɗuwa, yana tada dukan tanƙwararru.” “Yana warkadda masu-karyayyar zuciya, Yana ɗaure miyakunsu.” (Zab. 145:14; 147:3) Bugu da ƙari, Ubanmu na samaniya da kansa ya ce: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Isha. 41:13.
2. Ta yaya Jehobah yake tallafa wa bayinsa?
2 Amma, ta yaya ne Jehobah da ke sama inda ba za a iya ganinsa ba yake ‘riƙe hannunmu’? Ta yaya yake ‘tada mu tanƙwararru’ domin wahala? Jehobah Allah yana ba da irin wannan tallafin a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, yana ba mutanensa “mafificin girman iko” ta wurin ruhunsa mai tsarki. (2 Kor. 4:7; Yoh. 14:16, 17) Bayin Allah suna kuma jin cewa saƙo da ke cikin hurarriyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa su. (Ibran. 4:12) Da akwai wata hanya kuma da Jehobah yake ƙarfafa mu kuwa? Amsar tana cikin littafin Bitrus na Farko.
“Alherin Allah Iri Iri Masu-Yawa”
3. (a) Menene manzo Bitrus ya ce game da gwaje-gwaje? (b) Menene aka tattauna a sashe na ƙarshe ta wasiƙar farko na Bitrus?
3 Sa’ad da yake rubuta wa shafaffu ’yan’uwa masu bi, manzo Bitrus ya rubuta musu cewa suna da dalili mai kyau na yin farin ciki domin za su samu lada mai kyau. Sai ya daɗa: “Ko da an ga dalilin sa maku baƙinciki yanzu ’yan kwanaki da jarabobi dayawa.” (1 Bit. 1:1-6) Ka yi la’akari da kalmar nan “dayawa.” A yare na asali, Bitrus ya yi amfani da kalmar nan “iri iri” wadda aka kwatanta a sakin layin da ya gabata. Ta nuna cewa gwaje-gwaje za su kasance iri-iri. Amma, Bitrus bai ƙyale ’yan’uwansa su riƙa mamakin ko za su iya jimre irin waɗannan gwaje-gwaje iri-iri ba. Maimakon haka, Bitrus ya nuna cewa Kiristoci suna da tabbaci cewa Jehobah zai taimake su su jimre da kowane gwaji da suke fuskanta, ko da wane iri ne. An ba da wannan tabbacin a sashen wasiƙar Bitrus ta ƙarshe, inda manzon ya tattauna game da al’amuran da suka shafi “ƙarshen dukan abubuwa.”—1 Bit. 4:7.
4. Me ya sa kalaman da ke 1 Bitrus 4:10 suke ƙarfafa mu?
4 Bitrus ya ce: “Yayinda kowa ya karɓi baiko, kuna yi ma junanku hidima da shi, kamar nagargarun wakilai na alherin Allah iri iri masu-yawa.” (1 Bit. 4:10) A nan kuma Bitrus ya yi amfani da kalmar nan “iri iri.” Wato, yana cewa, ‘Gwaje gwaje suna zuwa ne a hanyoyi dabam dabam, amma kuma ana samun alherin Allah ma a hanyoyi masu yawa dabam dabam.’ Me ya sa wannan furcin yake da ban ƙarfafa? Hakan na nufin cewa ko da wane irin jarraba ce muke fuskanta, akwai alherin Allah da zai yi daidai da ita. Ka ga yadda Jehobah yake nuna mana alherinsa a furcin Bitrus? Yana yin hakan ne ta hanyar ’yan’uwanmu Kiristoci.
“Yi ma Junanku Hidima”
5. (a) Menene kowane Kirista zai yi? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka taso?
5 Sa’ad da yake magana ga dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista, Bitrus ya ce: “Gaba da kome kuma ku zama da ƙauna mai-huruwa zuwa ga junanku.” Sai ya daɗa: “Yayinda kowa ya karɓi baiko [“daidai gwargwado,” NW], kuna yi ma junanku hidima da shi.” (1 Bit. 4:8, 10) Saboda haka, dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna da hakkin ƙarfafa ’yan’uwa Kiristoci. An ba mu wani abu mai tamani na Jehobah, kuma mu ne ke da hakkin raba shi ga mutane. Menene wannan abin da aka ba mu? Bitrus ya ce “baiko” ne. Menene wannan baikon? Ta yaya za mu yi amfani da shi mu yi wa ‘juna hidima’?
6. Waɗanne baiwa ne aka ba Kiristoci?
6 Kalmar Allah ta ce: “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke.” (Yaƙ. 1:17) Hakika, dukan baiwar da Jehobah ya ba mutanensa alama ce ta alherinsa. Wata baiwa da ta fita dabam da Allah ya ba mu shi ne ruhu mai tsarki. Wannan baiwa yana sa mu koyi halaye kamar ƙauna, alheri, da kuma haƙuri. Irin waɗannan halayen suna motsa mu mu nuna wa ’yan’uwa masu bi cikakkiyar ƙauna kuma mu taimaka musu. Hikima ta gaskiya da kuma sani, suna cikin baiwar da muke samu ta hanyar ruhu mai tsarki. (1 Kor. 2:10-16; Gal. 5:22, 23) Hakika, dukan ƙarfin da muke da shi, iyawa, da kuma gwaninta duk baiwa ce da za mu iya amfani da su mu jawo yabo da ɗaukaka ga Ubanmu na samaniya. Allah ya ba kowannenmu hakkin yin amfani da iyawarmu da kuma halayenmu mu nuna alherin Allah ga ’yan’uwanmu masu bi.
Ta Yaya Za Mu ‘Yi Hidima da Shi’?
7. (a) Menene ma’anar furcin nan “daidai gwargwado”? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa?
7 Game da baiwar da muka samu, Bitrus ya ce: “Duk baiwar da mutum ya samu [“daidai gwargwado,” NW], yā yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan’uwansa.” Furcin nan “daidai gwargwado” ya nuna cewa halaye da iyawa za su bambanta sosai. Duk da haka, an umurci kowa ‘yā yi amfani da ita [wato, kowace baiwa da mutum yake da ita] ga kyautata wa ɗan’uwansa.’ Bugu da ƙari, furcin nan ‘yi amfani da ita . . . [a matsayin] amintaccen mai riƙon amana,’ umurni ne. Saboda haka, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina amfani da baiwar da aka ba ni don na ƙarfafa ’yan’uwana masu bi?’ (Gwada 1 Timothawus 5:9, 10.) ‘Ko kuwa ina amfani ne da baiwar da na samu daga Jehobah don kyautata wa kaina kawai, wataƙila don na sami arziki ko matsayi?’ (1 Kor. 4:7) Idan muka yi amfani da baiwarmu don “kyautata wa” juna, za mu faranta wa Jehobah rai.—Mis. 19:17; karanta Ibraniyawa 13:16.
8, 9. (a) Ta waɗanne hanyoyi ne Kiristoci a dukan duniya suke kyautata wa ’yan’uwa masu bi? (b) Ta yaya ne ’yan’uwa maza da mata da suke ikilisiyarku suke taimaka wa juna?
8 Kalmar Allah ta ambata hanyoyi dabam-dabam da Kiristoci na ƙarni na farko suka kyautata wa juna. (Karanta Romawa 15:25, 26; 2 Timothawus 1:16-18.) Hakazalika a yau, Kiristoci na gaskiya suna cika umurnin yin amfani da baiwarsu da dukan zuciyarsu domin ’yan’uwa masu bi. Yi la’akari da wasu hanyoyin da ake yin hakan.
9 ’Yan’uwa maza da yawa suna amfani da awoyi masu yawa suna shirya taro. A taro, sa’ad da suka furta bayanai masu muhimmanci na ruhaniya da suka samo a lokacin da suke nazarin Littafi Mai Tsarki, irin waɗannan kalaman da ke cike da hikima suna motsa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya su jimre. (1 Tim. 5:17) An san ’yan’uwa maza da mata masu yawa da suke daɗaɗa zuciyar ’yan’uwa masu bi da kuma tausaya musu. (Rom. 12:15) Wasu a kai a kai sukan ziyarci waɗanda suke baƙin ciki kuma su yi addu’a tare da su. (1 Tas. 5:14) Wasu kuma suna rubuta kalamai masu ƙarfafawa ga ’yan’uwa Kiristoci da suke fama da jarraba. Wasu kuwa suna taimaka wa naƙasassu su halarci taro a ikilisiya. Dubban Shaidu suna yin aikin kai agaji, ta wajen taimaka wa ’yan’uwa masu bi su sake gina gidajensu da suka rushe domin wasu bala’o’in da suka faru. Nuna ƙauna da kuma taimako da waɗannan ’yan’uwa maza da mata suke yi duk alamu ne na “alherin Allah iri iri.”—Karanta 1 Bitrus 4:11.
Wannene Ya Fi Muhimmanci?
10. (a) Bulus ya mai da hankali ne ga waɗanne ɓangarori biyu na hidimarsa ga Allah? (b) Ta yaya muke yin koyi da Bulus a yau?
10 An ba bayin Allah baiwar da za su yi amfani da ita su kyautata wa ’yan’uwansu masu bi kuma an ba su saƙon da za su gaya wa mutane. Manzo Bulus ya fahimci waɗannan ɓangarorin biyu na hidimarsa ga Jehobah. Ya rubuta wa ikilisiyar da ke Afisa game da “wakilcin alherin nan na Allah” da aka ba shi domin su amfana. (Afis. 3:2) Duk da haka, ya sake cewa: “Mun zama yardaddu ga Allah da za a sanya bishara a hannunmu.” (1 Tas. 2:4) Kamar Bulus, mu ma mun fahimci cewa an ba mu aikin yin hidima a matsayin masu wa’azin Mulkin Allah. Ta wajen yin aikin wa’azi sosai, muna koyi da misalin da Bulus ya kafa na mai yin wa’azin bishara da ƙwazo. (A. M. 20:20, 21; 1 Kor. 11:1) Mun san cewa yin wa’azin Mulki zai iya ceto rayuka. Hakazalika, muna bukatar mu ƙoƙarta mu yi koyi da Bulus ta wajen neman zarafin ba da “wani baiko mai-ruhaniya” ga ’yan’uwa masu bi.—Karanta Romawa 1:11, 12; 10:13-15.
11. Yaya ya kamata mu ɗauki ayyukanmu na yin wa’azi da kuma ƙarfafa ’yan’uwanmu?
11 Wannene ya fi muhimmanci a cikin waɗannan ayyuka guda biyu na Kirista? Yin irin wannan tambayar ya yi daidai da yin tambaya game da tsuntsu: Cikin fukafukansa biyu, wannene ya fi muhimmanci? Amsar a fili take. Tsuntsu yana bukatar ya yi amfani da fukafukansa guda biyu idan yana son ya tashi. Hakazalika, muna bukatar mu saka hannu a waɗannan fasalolin hidimarmu ga Allah idan muna son mu zama cikakkun Kiristoci. Saboda haka, maimakon mu ɗauki ayyukanmu na yin wa’azin bishara da kuma ƙarfafa ’yan’uwanmu masu bi a matsayin ayyuka dabam-dabam, ya kamata mu ɗauke su kamar yadda manzo Bitrus da Bulus suka ɗauke su, wato, ayyukan da ake yi tare. Ta wace hanya?
12. Ta yaya muke hidima a matsayin waɗanda Jehobah yake amfani da su?
12 A matsayinmu na masu wa’azi, muna amfani da kowanne irin salon koyarwa da muke da shi don mu taɓa zuciyar mutane da saƙo mai ƙarfafawa na Mulkin Allah. Ta haka, muna sa ran taimaka musu su zama almajiran Kristi. Muna kuma yin amfani da kowace iyawa da kuma baiwar da muke da su don daɗaɗa zukatan ’yan’uwanmu masu bi da kalamai masu ƙarfafawa da kuma ayyuka na taimako, abubuwan da alamu ne na alherin Allah. (Mis. 3:27; 12:25) Ta wannan hanyar, muna sa ran taimaka musu su ci gaba da kasancewa almajiran Kristi. A waɗannan ayyukan biyu, wato, yin wa’azi ga mutane da kuma “kyautata wa” juna, muna da gata mai ban al’ajabi na yin hidima a matsayin waɗanda Jehobah yake amfani da su.—Gal. 6:10.
Ku Yi “Ƙaunar ’Yan’uwa”
13. Menene zai faru idan muka daina “kyautata wa” juna?
13 Bulus ya umurci ’yan’uwansa masu bi: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatarda juna cikin bangirma.” (Rom. 12:10) Hakika, nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu zai motsa mu mu yi musu hidima da dukan zuciyarmu a matsayin masu riƙon amanar alherin Allah. Mun fahimci cewa idan Shaiɗan ya yi nasara wajen hana mu “kyautata wa” juna, zai raunana haɗin kanmu. (Kol. 3:14) Kuma rashin haɗin kai zai kai ga rashin ƙwazo a aikin wa’azi. Shaiɗan ya san cewa yana bukatar ya ji wa ɗaya daga cikin fukafukanmu rauni a alamance, don ya hana mu cika umurnin da aka ba mu.
14. Su wanene suke amfana daga “kyautata wa” juna da muke yi? Ka ba da misali.
14 “Kyautata wa” juna yana amfanar waɗanda suka sami alherin Allah da kuma waɗanda suka ba da shi. (Mis. 11:25) Alal misali, Ryan da Roni, ma’aurata ne da ke zaune a Illinois, a Amirka. Sa’ad da suka ji cewa guguwa da ake kira Katrina ta rugurguje ɗarurruwan gidajen Shaidu ’yan’uwansu, ƙaunar da suke yi wa ’yan’uwansu ta motsa su su bar aikin da suke yi, sun bayar da gidansu, kuma suka sayi kwancen mota wadda ake mai da wa gidan kwana, suka gyara ta, kuma suka yi tafiyar mil 900 zuwa Louisiana. Sun yi fiye da shekara guda a wannan wurin suna amfani da lokacinsu, ƙarfinsu, da kuma dukiyarsu don su taimaka wa ’yan’uwansu. “Saka hannu a aikin agaji ya jawo ni kusa ga Allah,” in ji Ryan, ɗan shekara 29. “Na ga yadda Jehobah yake kula da mutanensa.” Ryan ya daɗa: “Yin aiki tare da tsofaffin ’yan’uwa ya koya mini yadda zan kula da ’yan’uwa. Na kuma ga cewa mu matasa muna da aiki mai yawa da za mu yi a ƙungiyar Jehobah.” Roni, ’yar shekara 25 ta ce: “Ina farin ciki sosai domin na saka hannu wajen taimaka wa wasu. Ban taɓa irin wannan farin cikin ba a rayuwata. Na san cewa zan daɗe ina amfana daga wannan aikin mai ban sha’awa.”
15. Waɗanne dalilai muke da su na ci gaba da yin hidima a matsayin amintattu masu riƙon amanar alherin Allah?
15 Hakika, yin biyayya ga dokar Allah na yin wa’azin bishara da kuma ƙarfafa ’yan’uwa masu bi yana kawo albarka ga kowa. Waɗanda muka taimaka wa suna samun ƙarfafa a ruhaniya, yayin da muke samun farin cikin da masu bayarwa suke samu. (A. M. 20:35) Ikilisiya gabaki ɗaya tana samun farin ciki yayin da dukan waɗanda suke cikinta suke kula da juna. Bugu da ƙari, ƙauna da kula da muke nuna wa juna suna bayyana cewa mu Kiristoci ne na gaskiya. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:35) Fiye da komi, Jehobah, Ubanmu mai kula yana samun ɗaukaka yayin da muradinsa na ƙarfafa mabukata yake bayyanuwa a bayinsa na duniya. Muna da dalilai masu kyau na yin amfani da baiwarmu mu “kyautata wa [juna a matsayin] amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah”! Za ka ci gaba da yin haka?—Karanta Ibraniyawa 6:10.
Ka Tuna?
• A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake ƙarfafa bayinsa?
• Menene aka ba mu?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya kyautata wa ’yan’uwanmu masu bi?
• Menene zai motsa mu mu ci gaba da yin amfani da baiwarmu wajen “kyautata wa” juna?
[Hotunan da ke shafi na 13]
Kana amfani da ‘baiwarka’ ka yi wa wasu hidima ko kuwa ka kyautata wa kanka?
[Hotunan da ke shafi na 15]
Muna wa’azin bishara ga mutane kuma muna tallafa wa ’yan’uwa Kiristoci
[Hotunan da ke shafi na 16]
Masu kai agaji sun cancanci yabo domin halinsu na sadaukarwa