Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 8/1 pp. 7-11
  • “Ku Riƙa Auna Kanku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Riƙa Auna Kanku”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Jarraba Kanku Ku Gani, ko Har Yanzu Kuna Raye da Bangaskiya”
  • “Ku Riƙa Auna Kanku”
  • Ka Ƙaunaci Yin Nufin Allah
  • Ka Nace Bi Zuwa Kamala Don “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Gina Kanku Bisa Bangaskiyarku Maficin Tsarki”
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ka Ci Gaba da Koyar da Hankalinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Za Ka Iya ‘Bambance Nagarta Da Mugunta’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 8/1 pp. 7-11

“Ku Riƙa Auna Kanku”

“Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku.”—2 KORANTIYAWA 13:5.

1, 2. (a) Ta yaya rashin tabbaci game da imaninmu zai shafe mu? (b) Wane yanayi a Koranti ta ƙarni na farko mai yiwuwa ya sa wasu suka rasa hanyar da za su bi?

WANI mutum yana kan hanyarsa zuwa wata karkara, sai ya iso inda hanya ta rabu biyu. Da yake bai san wadda zai bi ba, sai ya tambayi masu wucewa amma suka ba shi bayani dabam dabam. Da yake ya rikice, bai ci gaba da tafiyarsa ba. Hakazalika, shakkar imaninmu za ta iya shafarmu. Za ta iya shafar yadda muke tsai da shawara, ta sa mu rasa hanyar da za mu bi.

2 Wani yanayi ya taso da ƙila ya shafi wasu mutane cikin ikilisiyar Kirista a Koranti na ƙarni na farko a Helas. “Mafifitan manzanni” suna tuhumar ikon manzo Bulus, suna cewa: “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.” (2 Korantiyawa 10:7-12; 11:5, 6) Mai yiwuwa irin wannan ra’ayin ya sa wasu a cikin ikilisiyar Koranti suka rasa hanyar da za su bi.

3, 4. Me ya sa za mu so gargaɗin da Bulus ya yi wa Korantiyawa?

3 Bulus ne ya kafa ikilisiya da ke Koranti a lokacin ziyararsa a shekara ta 50 A.Z. Ya zauna a Koranti “shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar da Maganar Allah a cikinsu.” Hakika, Korantiyawa “da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.” (Ayyukan Manzanni 18:5-11) Bulus ya damu sosai da ruhaniyar ’yan’uwansa da suke Koranti. Bugu da ƙari, Korantiyawa sun rubuta wa Bulus ya ba su shawara a kan wasu batutuwa. (1 Korantiyawa 7:1) Sai ya ba su shawara mai kyau.

4 Bulus ya rubuta: “Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku.” (2 Korantiyawa 13:5) Bin wannan gargaɗin da zai taimaki ’yan’uwa da suke Koranti su san hanyar da za su bi. Gargaɗin zai kāre mu ma a yau. To, ta yaya za mu bi shawarar Bulus? Ta yaya za mu jarraba kanmu mu gani ko muna raye da bangaskiya? Menene auna kanmu ya ƙunsa?

“Ku Jarraba Kanku Ku Gani, ko Har Yanzu Kuna Raye da Bangaskiya”

5, 6. Wane mizani muke da shi na gwada ko muna raye da bangaskiya, kuma me ya sa wannan ne mizani da ya dace?

5 Idan ana gwaji, dole ne ya kasance ana gwada mutum ko wani abu da kuma mizanin da ake bi a yi gwajin. A wannan batun, abin da ake gwadawa ba bangaskiya ba ce, wato, imaninmu. Mu ne ake gwadawa. Don a yi gwajin, muna da cikakken mizani. Waƙar da Dauda mai zabura ya rubuta ta ce: “Dokar Ubangiji cikakkiya ce, tana wartsakar da rai. Umarnan Ubangiji abin dogara ne, sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita. Ka’idodin Ubangiji daidai suke, waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi. Umarnan Ubangiji daidai suke, sukan ba da fahimi ga zuciya.” (Zabura 19:7, 8) Littafi Mai Tsarki na ɗauke da dokoki da ka’idodin Jehobah da kuma umarnansa da abin dogara ne. Saƙon da ke ciki ne mizani da ya dace don gwajin.

6 Manzo Bulus ya yi magana game da wannan saƙon da Allah ya hure, yana cewa: “Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufa tata.” (Ibraniyawa 4:12) Hakika, maganar Allah na iya gwada zuciyarmu, wato, irin mutane da muke a ciki. Ta yaya za mu yi amfani da wannan saƙo mai kaifi mai iko? Mai zabura ya faɗi yadda za a yi hakan. Ya rera: “Albarka ta tabbata ga mutumin da . . . yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, yana ta nazarinta dare da rana.” (Zabura 1:1, 2) Ana samun “shari’ar Allah” a cikin rubutacciyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Dole ne mu ji daɗin karanta Kalmar Jehobah. Hakika, dole ne mu keɓe lokacin karanta ta ko kuma yi bimbini a kai. Sa’ad da muke hakan ya kamata mu ƙyale abin da aka rubuta a ciki ya gwada mu.

7. Wace hanya ce ta musamman za mu gwada ko muna raye da bangaskiya?

7 Hanya ta musamman na gwada ko muna raye da bangaskiya ita ce karatu da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah cikin addu’a da kuma bincika yadda halinmu ya yi daidai da abin da muka koya. Ya kamata mu yi farin ciki cewa muna da taimako wajen fahimtar Kalmar Allah.

8. Ta yaya littattafan “amintaccen bawan nan mai hikima” ke taimakonmu mu gwada ko muna raye da bangaskiya?

8 Jehobah ya yi tanadin koyarwa da umurni ta wurin littattafai na “amintaccen bawan nan mai hikima” da suka bayyana Nassosi. (Matiyu 24:45) Alal misali, ka yi la’akari da akwati mai jigo “Tambayoyi don Bimbini” a ƙarshen yawancin babobi na littafin nan Ka Kusaci Jehovah.a Wannan fannin littafin ya ba da zarafi mai kyau don yin bimbini! Yawancin batutuwa da aka tattauna a cikin jaridunmu, Hasumiyar Tsaro da Awake!, suna taimako wajen gwada ko muna raye da bangaskiya. Wata mata Kirista ta yi magana game da talifofi a kan littafin Karin Magana da ke cikin Hasumiyar Tsaro na kwanan baya, ta ce: “Na iske waɗannan talifofi da ban taimako. Sun taimake ni na bincika ko furci na, halina, sun yi daidai da mizanai masu adalci na Jehobah.”

9, 10. Waɗanne tanadi na Jehobah za su taimake mu mu ci gaba da gwada ko muna raye da bangaskiya?

9 Ana yi mana ja-gora kuma ana ƙarfafa mu a taron ikilisiya, manyan taro da na gunduma. Waɗannan suna cikin tanadi na ruhaniya da Allah ya yi wa waɗanda Ishaya ya yi annabci game da su: “A kwanaki masu zuwa, dutse inda aka gina haikali zai zama mafi tsayi duka. Al’ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi. Jama’arsu za su ce, ‘Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, . . . za mu koyi abin da yake so mu yi, za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.’ ” (Ishaya 2:2, 3) Albarka ce mu sami irin wannan koyarwa game da hanyoyin Jehobah.

10 Wata hanya da za mu gwada kanmu ita ce ta gargaɗin waɗanda suka cancanta a ruhaniya, har da dattawan Kirista. Littafi Mai Tsarki ya ce game da su: “Ya ku ’yan’uwa, in an kama mutum yana cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi hanya da tawali’u, kowa na kula da kansa kada shi ma ya burmu.” (Galatiyawa 6:1) Ya kamata mu yi godiya don wannan tanadi na yi mana gyara!

11. Menene za mu yi idan muna so mu gwada ko muna raye da bangaskiya?

11 Littattafanmu, taron Kirista, dattawa—dukan waɗannan tanadi masu kyau ne daga Jehobah. Amma muna bukatar mu bincika kanmu don mu gwada ko muna raye da bangaskiya. Saboda haka sa’ad da muke karanta littattafanmu ko sauraron gargaɗi na Nassi, muna bukatar mu tambayi kanmu: “Wannan na kwatanta ni ne? Ina yin irin waɗannan abubuwa ne? Ina manne wa imani na Kirista kuwa? Halinmu game da bayanin da muka samu ta waɗannan tanadi na shafan yanayinmu na ruhaniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na’am da al’amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, . . . mutumin da ke na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome.” (1 Korantiyawa 2:14, 15) Shin bai kamata mu yi ƙoƙari mu kasance da ra’ayi na ruhaniya da ya dace game da abin muka karanta a littattafanmu, jaridu, da kuma abin da muke ji a taronmu da kuma wurin dattawa ba?

“Ku Riƙa Auna Kanku”

12. Menene auna kanmu ya ƙunsa?

12 Auna kanmu ya ƙunshi kimanta kanmu. Hakika, muna iya kasance cikin gaskiya, amma yaya ruhaniyarmu take? Auna kanmu ya ƙunshi nuna tabbaci cewa mun manyanta da kuma nuna tabbataciyar godiya don abubuwa na ruhaniya.

13. In ji Ibraniyawa 5:14, menene ke ba da tabbacin mun manyanta?

13 Ta yaya za mu auna kanmu mu san ko mu Kiristoci ne da suka manyanta? Manzo Bulus ya rubuta: “Abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Muna ba da tabbaci mun manyanta ta wajen koyar da hankalinmu. Yadda ɗan wasa zai gina wasu jijiyoyi cikin jikinsa ta wurin gwaji a kai a kai kafin ya iya wasan sosai, ya kamata mu koyar da hankalinmu ta wurin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

14, 15. Me ya sa ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi nazarin abubuwa masu wuya na Kalmar Allah?

14 Amma kafin mu koyar da hankalinmu, dole ne mu nemi sani. Nazari mai kyau na kanmu yana da muhimmanci don wannan. Idan muna nazari na kanmu a kai a kai—musamman abubuwa masu wuya na Kalmar Allah—muna kyautata hankalinmu ke nan. A dā, ana tattauna abubuwa masu wuya da yawa a Hasumiyar Tsaro. Menene muke yi sa’ad da muka ga talifofi da suka tattauna abubuwa masu wuya? Muna barin su ne domin suna ɗauke da abubuwa “masu wuyar fahimta”? (2 Bitrus 3:16) Maimakon yin hakan, ya kamata mu ƙara ƙoƙari mu fahimci abin da ake koyarwa.—Afisawa 3:18.

15 Idan yana mana wuya mu yi nazari na kanmu fa? Yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu koya jin daɗinta.b (1 Bitrus 2:2) Idan muna son mu manyanta, muna bukatar mu koya yadda ake samun amfani daga abinci mai ƙarfi, wato, abubuwa masu wuyan fahimta a Kalmar Allah. Idan ba haka ba, hankalinmu ba zai koyu ba. Amma, nuna tabbaci cewa mun manyanta ba ta wajen koyar da hankalinmu kaɗai ba ne. A ayyukanmu na kowace rana dole ne mu yi amfani da abin da muka koya daga nazari na kanmu.

16, 17. Wane gargaɗi almajiri Yakubu ya ba da game da zama “masu aikata magana”?

16 Ana ganin tabbacin irin mutane da muke a yadda muke nuna godiya don gaskiya—ayyukanmu na bangaskiya. Don ya kwatanta yadda za mu auna kanmu a wannan batun, almajiri Yakubu ya yi amfani da wannan misalin: “Ku zama masu aikata magana, ba masu ji kawai, kuna yaudara kanku ba. Don duk wanda yake mai jin maganar na kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba idonsa a madubi, don yakan dubi idonsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa. Amma duk mai duba cikakkiyar ka’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to, wannan shi za a yi wa albarka cikin abin da yake aikatawa.”—Yakubu 1:22-25.

17 Yakubu yana cewa: ‘Ka duba madubin kalmar Allah don ka auna kanka. Ka nace da yin haka, ka bincika kanka da taimakon abin da ka gani cikin kalmar Allah. Kada ka yi saurin mance abin da ka gani. Ka yi gyara da ake bukata.’ Wani lokaci zai yi wuya a bi wannan shawara.

18. Me ya sa bin gargaɗin Yakubu yake da wuya?

18 Alal misali, Bulus ya rubuta game da bukata na yin aikin wa’azin Mulki: “Da zuci mutum ke gaskatawa yā sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa ya sami ceto.” (Romawa 10:10) Yin shaida da baki don samun ceto na bukatar yin gyara da yawa. Aikin wa’azi na yi wa yawancinmu wuya. Zama masu shela da himma da kuma saka aikin a wuri na farko a rayuwarmu na bukatar ƙarin gyara da sadaukarwa. (Matiyu 6:33) Amma muddin muka zama masu aikata wannan aikin da Allah ya ba mu, muna farin ciki domin yana sa a yabi Jehobah. Saboda haka, mu masu shelar Mulki ne da himma kuwa?

19. Ayyukanmu na bangaskiya ya kamata su haɗa da menene?

19 Yaya ya kamata ayyukanmu na bangaskiya su kasance? Bulus ya ce: “Abin da kuka koya, kuka yi na’am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.” (Filibiyawa 4:9) Muna nuna irin mutane da muke ta yin abin da muka koya, abin da muka yi na’am da shi, abin da muka ji, kuma muka gani—nan ne keɓe kai na Kirista da almajiranci gabaki ɗaya ya kasance. “Ga hanyan nan, ku bi ta,” in ji Jehobah ta bakin annabi Ishaya.—Ishaya 30:21.

20. Waɗanne irin mutane ne albarka ga ikilisiya?

20 Maza da mata masu nazarin Kalmar Allah sosai, masu shelar bishara da himma, masu aminci sosai, da waɗanda suke tallafa wa Mulkin cikin aminci albarka ne sosai ga ikilisiya. Suna sa ikilisiya da suke ciki ta yi ƙarfi. Sun zama da ban taimako, musamman domin da akwai sababbi da yawa da za a kula da su. Idan mun tuna da shawarar Bulus mu ‘ci gaba da jarraba kanmu mu gani, ko har yanzu muna raye da bangaskiya, mu riƙa auna kanmu’ mu ma za mu yi tasiri mai kyau ga wasu.

Ka Ƙaunaci Yin Nufin Allah

21, 22. Ta yaya za mu yi farin ciki wajen yin nufin Allah?

21 Sarki Dauda na Isra’ila na dā ya rera: “Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah! Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.” (Zabura 40:8) Dauda yana farin ciki da yin nufin Allah. Me ya sa? Domin dokar Jehobah na cikin zuciyar Dauda. Dauda ya san hanyar da zai bi.

22 Idan muna riƙe koyarwar Allah a zuciyarmu, za mu san hanyar da za mu bi. Za mu yi farin cikin yin nufin Allah. Saboda haka, bari mu yi “fama” yayin da muke bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.—Luka 13:24.

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

b Don samun taimakon yadda za ka yi nazari, ka duba shafofi na 27-32 na littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, da Shaidun Jehobah suka wallafa.

Ka Tuna?

• Ta yaya za mu gwada ko muna raye da bangaskiya?

• Menene auna irin mutane da muke ya ƙunsa?

• Ta yaya za mu ba da tabbaci mu Kiristoci ne da suka manyanta?

• Ta yaya ayyukanmu na bangaskiya za su taimake mu mu gwada kanmu?

[Hoto a shafi na 9]

Ka san hanyar da ta fi kyau na gwada ko kana raye da bangaskiya?

[Hoto a shafi na 10]

Muna ba da tabbaci mu Kiristoci ne da suka manyanta ta wajen amfani da hankalinmu

[Hotuna a shafi na 11]

Muna ba da tabbacin irin mutane da muke idan ba ‘mu zama masu ji ne kawai mu mance ba, amma masu aikata magana’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba