Ka Ci Gaba da Koyar da Hankalinka
ABIN farin ciki ne a ga ƙwararren mai wasan motsa jiki yana motsawa da sauri! Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su koyar da hankalinsu kamar yadda mai wasan motsa jiki yake koyar da kansa.
A wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, manzo Bulus ya rubuta: “Abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda [“ta yin amfani,” NW] hankalinsu [a zahiri, “gaɓaɓuwan hankalinmu”] ya horu yau da kullum, [kamar mai wasan motsa jiki] su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibran. 5:14; Littafi Mai Tsarki) Me ya sa Bulus ya ƙarfafa Kiristoci Ibraniyawa su koyar da hankalinsu kamar yadda ƙwararren mai wasan motsa jiki yake motsa gaɓaɓuwar jikinsa? Yaya za mu iya horar da hankalinmu?
Kuna Bukatan “Ku Zama Masu Koyarwa”
Sa’ad da yake bayyana matsayin Yesu na “babban firist bisa tabi’ar Malkisadaƙa,” Bulus ya rubuta: “Muna kuwa da abu da yawa da za mu faɗi a kansa [Yesu] masu-wuyan fassara kuma, da ya ke kun zama masu-nauyin ji. Gama lokacin da ya kamata, domin daɗewarku, ku zama masu-koyarwa, ku kuna bukata wani ya koya maku tussa na farkon zantattukan Allah; kun zama irin waɗanda ke bukatar madara, ba abinci mai-ƙarfi ba.”—Ibran. 5:10-12.
Babu shakka, wasu Kiristoci Yahudawa na ƙarni na farko ba su ƙara fahiminsu ba kuma sun ƙi ci gaba a ruhaniya. Alal misali, ya yi musu wuya su amince da ƙarin hasken da aka samu game da Doka da kuma kaciya. (A. M. 15:1, 2, 27-29; Gal. 2:11-14; 6:12, 13) Ya yi wa wasu wuya su daina ayyukan al’adu da suke da alaƙa da hutun Assabaci na mako-mako da kuma Ranar Kafara ta shekara-shekara. (Kol. 2:16, 17; Ibran. 9:1-14) Saboda haka, Bulus ya ƙarfafa su su horar da hankalinsu domin su iya rarrabe nagarta daga mugunta kuma ya gaya masu su “nace bi zuwa kamala.” (Ibran. 6:1, 2) Umurnin da ya ba da ya motsa wasu su yi tunani a kan yadda suke yin amfani da hankalinsu kuma wataƙila ya taimaka musu su samu ci gaba a ruhaniya. Mu kuma fa?
Ka Horar da Hankalinka
Ta yaya za mu horar da hankalinmu domin mu manyanta a ruhaniya? Ta wurin “yin amfani,” in ji Bulus. Kamar masu wasan motsa jiki, waɗanda ta wurin motsa jikinsu suna koyar da tsoka da kuma jikinsu su motsa a hanyoyi masu kyau da kuma masu wuya, muna bukatan mu horar da hankalinmu don mu iya rarrabe nagarta da mugunta.
“Wasa hankalinka shi ne abu mafi kyau da za ka iya yi wa ƙwaƙwalwanka,” in ji John Ratey, wanda farfesa ne na ilimin halayen taɓaɓɓu a Harvard Medical School. In ji Gene Cohen, darektan Cibiyar Tsufa, Lafiya da Halin ’Yan Adam a Jami’ar George Washington, “Sa’ad da muka wasa ƙwaƙwalwarmu da abubuwa masu wuya, kwayoyin halitta na ƙwaƙwalwa suna fito da sababbin jijiyoyi na samun saƙo, wanda hakan zai sa tsarin aiki na ƙwaƙwalwa ya ƙara yin aiki da kyau.”
Saboda haka, yana da kyau mu wasa hankalinmu kuma mu ƙara saninmu na Kalmar Allah. Ta yin hakan, za mu kasance a shirye mu yi “nufin nan na Allah mai-kyau.”—Rom. 12:1, 2.
Ka Yi Marmarin “Abinci Mai Tauri”
Idan muna sha’awar “nace bi zuwa kāmala,” muna bukatan mu yi wa kanmu wannan tambayar: ‘Ina samun ci gaba a fahimina na gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Wasu suna ganina a matsayin wanda ya manyanta a ruhaniya?’ Uwa tana farin cikin ciyar da jaririnta da madara da kuma abincin yara a lokacin da yake jariri. Amma ka yi tunanin yadda za ta ji idan shekaru sun shige kuma yaron ba ya cin abinci mai tauri. Hakazalika, muna farin cikin ganin mutumin da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ya samu ci gaba har ya keɓe kansa kuma ya yi baftisma. Idan mutumin ya kasa samun ci gaba a ruhaniya bayan haka kuma fa? Hakan zai sa mu baƙin ciki, ko ba haka ba? (1 Kor. 3:1-4) Malamin yana begen cewa a kwana a tashi sabon almajirin zai zama malami.
Yin amfani da hankalinmu wurin yin tunani a kan al’amura yana bukatan yin bimbini, kuma wannan ya ƙunshi ƙoƙartawa. (Zab. 1:1-3) Kada mu yarda abubuwan da ke raba hankali, kamar su kallon telibijin ko wasannin da muke so, waɗanda ba sa bukatan wasa hankali mai yawa, su hana mu yin bimbini a kan abubuwa masu amfani. Domin mu horar da hankalinmu, yana da muhimmanci mu koyi kuma mu gamsar da muradinmu na nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45-47) Ƙari ga tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu a kullum, yana da muhimmanci mu keɓe lokaci na Bauta ta Iyali da kuma nazari mai zurfi a kan darussa na Littafi Mai Tsarki.
Jeronimo, wani mai kula mai ziyara a ƙasar Mexico, ya ce yana nazarin kowanne fitowar Hasumiyar Tsaro da zarar ya karɓe su. Ya kuma keɓe lokaci na yin nazari tare da matarsa. Jeronimo ya ce, “A matsayin ma’aurata muna da al’adar karanta Littafi Mai Tsarki tare a kowace rana, kuma muna yin amfani da littattafan da za su taimaka mana kamar mujallar nan ‘See The Good Land.’” Wani Kirista mai suna Ronald ya ambata cewa a koyaushe yana bin tsarin karatun Littafi Mai Tsarki na ikilisiya. Ƙari ga haka, yana da wasu tsarin nazari ɗaya ko biyu na kai da zai kammala a cikin dogon lokaci. “Waɗannan tsare-tsaren suna sa ni in yi marmarin nazari na na gaba,” in ji Ronald.
Mu kuma fa? Muna keɓe isashen lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah? Muna koyar da hankalinmu da kuma samun fahimi wajen tsai da shawarwari daidai da ƙa’idodin Nassi? (Mis. 2:1-7) Bari ya zama makasudinmu mu zama Kiristoci da suka manyanta a ruhaniya, waɗanda aka albarkace su da sani da kuma hikima da waɗanda suka koyar da hankalinsu bisa ga rabewar nagarta da mugunta da suke da shi!
[Hoton da ke shafi na 23]
Muna koyar da hankalinmu ta wurin “yin amfani” da shi