Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 8/1 pp. 22-26
  • Jehobah Mai ‘Sakamako Ne Ga Masu Nemansa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Mai ‘Sakamako Ne Ga Masu Nemansa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalan Jimiri na Zamanin Dā
  • Mutanen Jehobah na “Ainihi”
  • Jehobah “Mai Sakamako” Ne
  • Ka Mai da Hankali da ‘Kissoshin’ Shaiɗan
  • Jehobah “Ya Fi” Zuciyarmu
  • “Kyakkyawan Rawani” Kuma “Kambin Sarauta”
  • Jehobah Yana Sāka wa Wadanda Suke Bidarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Waye Zai Tsira Wa Ranar Jehovah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Jehovah Yana Kula Da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 8/1 pp. 22-26

Jehobah Mai ‘Sakamako Ne Ga Masu Nemansa’

“Duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.”—IBRANIYAWA 11:6.

1, 2. Me ya sa wasu bayin Jehobah suke fama da yanayi marar daɗi?

“NI MASHAIDIYAR Jehobah ce na kusan shekara 30, amma ban taɓa jin cewa na cancanci a kira ni haka ba,” in ji Barbara.a “Ko da yake na yi hidimar majagaba kuma na more wasu gata na musamman, babu ɗaya cikinsu da ya sa na gaskata a zuciyata cewa na cancanta.” Keith ya furta haka. “Wani lokaci ina jin ban cancanta ba domin bayin Jehobah suna da dalilai masu yawa na farin ciki, amma ba ni da farin ciki,” in ji shi. “Wannan ya sa na fara jin ina da laifi, kuma wannan ya tsananta al’amari.”

2 Da yawa cikin bayin Jehobah, na dā da na yanzu, sun yi kokawa da irin wannan yanayi. Kai ma kana jin haka wani lokaci? Wataƙila matsala wata bayan wata sun dame ka, sa’ad da ’yan’uwanka Kiristoci kuma kamar suna more rayuwa, suna farin ciki suna walawa. Domin haka, sai ka ji cewa ba ka da yardar Jehobah kuma ba ya lura da kai. Kada ka yi tunanin haka cikin hanzari. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci: “[Jehobah] ba ya ƙyale matalauta, ko ya ƙi kulawa da wahalarsu, ba ya rabuwa da su, amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.” (Zabura 22:24) Waɗannan kalmomin annabci game da Almasihu sun nuna cewa Jehobah yana sauraron bayinsa masu aminci kuma yana ba su lada.

3. Me ya sa ba mu kuɓuta ba daga matsi na wannan zamani?

3 Babu wanda zai kuɓuce wa matsi na wannan zamanin, har mutanen Jehobah ma ba su kuɓuta ba. Muna raye ne a duniya da babban magabcin Jehobah, Shaiɗan Iblis yake mallaka. (2 Korantiyawa 4:4; 1 Yahaya 5:19) Maimakon kāre su cikin mu’ujiza, bayin Jehobah ne ainihi abin fako na Shaiɗan. (Ayuba 1:7-12; Wahayin Yahaya 2:10) Saboda haka, har sai lokacin da Allah ya kafa ya cika, kafin nan, dole ne mu “jure wa wahala” kuma mu “nace da addu’a,” da tabbacin cewa Jehobah yana kulawa da mu. (Romawa 12:12) Kada mu yi tunanin cewa Allahnmu Jehobah ba ya ƙaunarmu!

Misalan Jimiri na Zamanin Dā

4. Ka ba da misalin wasu bayin Jehobah masu aminci da suka jimre wa yanayi masu wuya.

4 Da yawa cikin bayin Jehobah na dā sun jimre wa yanayi masu wuya. Alal misali, Hannatu ta yi “baƙin ciki ƙwarai” domin ba ta sami haihuwa ba, yanayin da a ganinta daidai yake da Allah ya mance da ita. (1 Sama’ila 1:9-11) Sa’ad da Sarauniya Yezebel mai kisa take neman Iliya, ya tsorata ya yi wa Jehobah addu’a: “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi rai na gama ban fi kakannina ba.” (1 Sarakuna 19:4) Manzo Bulus hakika ya fuskanci nauyin ajizancinsa sa’ad da ya ce: “In na so yin abin da ke daidai, sai in ga mugunta tare da ni.” Ya daɗa cewa: “Kaitona!”—Romawa 7:21-24.

5. (a) Ta yaya aka yi wa Hannatu, Iliya, da kuma Bulus albarka? (b) Ta yaya Kalmar Allah za ta sanyaya mana zuciya idan muna fama da rashin jin daɗi?

5 Hakika, mun sani cewa Hannatu, Iliya, da kuma Bulus dukansu sun jimre a wajen bauta wa Jehobah, kuma ya albarkace su ƙwarai. (1 Sama’ila 1:20; 2:21; 1 Sarakuna 19:5-18; 2 Timoti 4:8) Duk da haka, sun yi kokawa da ire-iren motsin zuciya na mutane, waɗanda suka haɗa da baƙin ciki, fid da rai, da tsoro. Saboda haka, kada ya zame mana abin mamaki idan wani lokaci muka kasance da yanayi marar daɗi. To, me za ka yi idan damuwa ta rayuwa ta sa ka yi mamaki ko da gaske Jehobah yana ƙaunarka? Kalmar Allah za ta iya sanyaya maka zuciya. Alal misali, a talifi da ya gabata, mun tattauna furcin Yesu cewa Jehobah ya ƙidaye “gashin kanku.” (Matiyu 10:30) Waɗannan kalmomi masu ba da ƙarfafa sun nuna cewa yana kula ƙwarai da kowane bawansa. Ka tuna kuma kwatancin Yesu game da gwara. Idan babu ko ɗaya daga cikin gwara da za ta faɗi ƙasa ba tare da sanin Jehobah ba, me ya sa zai rufe idanunsa ga wahalarka?

6. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai kasance tushen sanyaya zuciya ga waɗanda suke fama da rashin jin daɗi?

6 Shin yana yiwuwa kuma mu mutane ajizai mu kasance da muhimmanci a gaban Mahalicci mai iko duka Jehobah Allah? E! Hakika, da ayoyi masu yawa na Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar mana da haka. Idan muka riƙa tuna wannan, za mu maimaita kalmomin mai Zabura wanda ya ce: “Sa’ad da nake alhini, ina cikin damuwa, ka ta’azantar da ni, ka sa in yi murna.” (Zabura 94:19) Bari mu bincika wasu cikin waɗannan kalmomin ta’aziyya daga Kalmar Allah da za su taimake mu mu fahimci cewa Allah yana ɗaukanmu da muhimmanci kuma zai yi mana albarka idan muka ci gaba da yin nufinsa.

Mutanen Jehobah na “Ainihi”

7. Wane annabci ne mai ƙarfafawa Jehobah ya bayar ta bakin Malakai ga al’umma marar aminci?

7 Mummunan yanayi ya kasance a tsakanin Yahudawa a ƙarni na biyar K.Z. Firistoci suna karɓan dabbobi da ba su dace ba kuma suna yin hadaya da su a bagadin Jehobah. Alƙalai suna nuna son kai. Sihiri, ƙarya, da kuma zina sun zama ruwan dare. (Malakai 1:8; 2:9; 3:5) Ga wannan al’umma marar aminci, Malakai ya furta annabci mai ban mamaki. Bayan wani lokaci, Jehobah zai mai da jama’arsa ta sami yardarsa. Mun karanta: “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, za su zama mutanena na ainihi, a ranar da na aikata. Zan ji ƙansu kamar yadda mahaifi yakan ji ƙan ɗansa wanda ke masa hidima.”—Malakai 3:17.

8. Me ya sa za a iya cewa Malakai 3:17 ta shafi ƙasaitaccen taro?

8 Annabcin Malakai ya sami cika ta zamani a kan Kiristoci da aka shafa da ruhu, waɗanda suka kasance al’umma ta ruhu mai mutum 144,000. Wannan al’umma hakika ita ce mutanen “ainihi” ko kuma “jama’ar mallakar” Jehobah. (1 Bitrus 2:9) Annabcin Malakai kuma abin ƙarfafa ne ga “ƙasaitaccen taro,” waɗanda suke “tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, saye da fararen riguna.” (Wahayin Yahaya 7:4, 9) Waɗannan suka kasance cikin garke guda da shafaffu, a ƙarƙashin Makiyayi guda, Yesu Kristi.—Yahaya 10:16.

9. Me ya sa mutanen Jehobah suke da ‘muhimmanci’ a gare shi?

9 Yaya Jehobah yake ɗaukan waɗanda suka zaɓi su bauta masa? Kamar yadda aka lura a Malakai 3:17, yana ɗaukansu kamar yadda uba mai ƙauna yake ɗaukan ɗansa. Ka kuma lura da kalmomin yabo da ya yi amfani da su wajen kwatanta mutanensa, “ainihin mutanena.” Wasu fassara sun yi amfani da wannan furci “nawa,” “mallaka ta mai tamani,” da kuma “dukiyata.” Me ya sa Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke bauta masa haka da muhimmanci? Domin shi Allah ne mai godiya. (Ibraniyawa 6:10) Yana kusantar waɗanda suke bauta masa da zuciyarsu kuma yana ɗaukansu da muhimmanci.

10. Me ya sa Jehobah yake kāre mutanensa?

10 Za ka iya tuna da wani abu da ka mallaka da kake ɗauka da muhimmanci? Ba ka ɗaukan mataki ne ka kāre shi? Haka Jehobah yake yi da abinsa mai ‘muhimmanci.’ Hakika, ba ya kāre mutanensa daga dukan gwaji da masifu na rayuwa. (Mai Hadishi 9:11) Amma babu shakka cewa Jehobah zai iya kuma zai kāre bayinsa masu aminci a ruhaniya. Yana ba su ƙarfi da suke bukata domin su jimre wa gwaji. (1 Korantiyawa 10:13) Saboda haka, Musa ya gaya wa Isra’ilawa mutanen Allah a dā: “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, . . . gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.” (Maimaitawar Shari’a 31:6) Jehobah yana yi wa mutanensa albarka. Suna da ‘muhimmanci’ a gare shi.

Jehobah “Mai Sakamako” Ne

11, 12. Ta yaya fahimtar Jehobah cewa shi mai yin sakamako ne zai taimake mu mu yi kokawa da shakka?

11 Wani tabbaci kuma cewa Jehobah yana ɗaukan bayinsa da muhimmanci shi ne cewa yana yi musu albarka. Ya gaya wa Isra’ilawa: “Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.” (Malakai 3:10) A ƙarshe, Jehobah zai albarkaci bayinsa da rai madawwami. (Yahaya 5:24; Wahayin Yahaya 21:4) Wannan albarka da ta fi gaban a gwada, ta bayyana yawan ƙauna da kuma karimcin Jehobah. Kuma ta nuna cewa da gaske yana ɗaukan waɗanda suka zaɓi su bauta masa da muhimmanci. Koyon ɗaukan Jehobah cewa mai karimci ne zai taimake mu mu yi kokawa da shakka game da matsayinmu a gaban Allah. Hakika, Jehobah ya aririce mu mu ɗauke shi mai yin Sakamako! Bulus ya rubuta: “Duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.”—Ibraniyawa 11:6.

12 Hakika muna bauta wa Jehobah ne domin muna ƙaunarsa, ba domin ya yi alkawarin zai yi mana albarka ba. Duk da haka, sa rai cewa zai yi mana albarka ba laifi ba ne kuma ba son kai ba ne. (Kolosiyawa 3:23, 24) Domin ƙaunarsu da kuma muhimmancin da yake ɗaukansu da shi, Jehobah ya ɗauki zarafin ya yi wa waɗanda suke biɗansa albarka.

13. Me ya sa tanadin fansa tabbaci ne mai girma na ƙaunar Jehobah a garemu?

13 Tabbacin girman martaban mutane a idanun Jehobah shi ne tanadin da ya yi na fansa. Manzo Yahaya ya rubuta: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.” (Yahaya 3:16) Tanadin hadayar fansa na Yesu Kristi bai jitu da ra’ayin cewa ba mu da mutunci a idanun Allah ba. Hakika, tun da har Jehobah ya ba da ran Ɗansa Makaɗaici, yana ƙaunarmu ƙwarai.

14. Menene ya nuna yadda Bulus ya ɗauki fansa?

14 Saboda haka, idan rashin jin daɗi ya dame ka, ka yi bimbini bisa fansa. Hakika, ka ɗauki wannan tanadi daga Jehobah domin kai ne. Abin da manzo Bulus ya yi ke nan. Ka tuna cewa ya ce: “Kaitona!” Amma ya ci gaba da cewa: “Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu,” wanda, in ji Bulus, ‘ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.’ (Romawa 7:24, 25; Galatiyawa 2:20) Da ya faɗi haka, ba ɗaga kai Bulus yake yi ba. Yana da tabbaci ne kawai cewa Jehobah yana ɗaukansa da muhimmanci. Kamar Bulus, kai ma ya kamata ka koyi ka ɗauki fansar kyauta ce dominka daga wurin Allah. Jehobah ba Mai ceto ba ne kawai mai iko amma kuma Mai yin sakamako ne mai ƙauna.

Ka Mai da Hankali da ‘Kissoshin’ Shaiɗan

15-17. (a) Ta yaya Iblis yake amfani da yanayin rashin jin daɗi? (b) Wane ƙarfafa za mu samu daga abin da Ayuba ya fuskanta?

15 Duk da haka, zai yi maka wuya ka gaskata cewa hurarrun kalmomin ta’aziyya da suke Kalmar Allah sun shafe ka. Kana iya jin cewa wannan lada na rayuwa har abada a sabuwar duniya ta Allah aba ce da wasu za su iya samu, amma kai ba ka cancanci samu ba. Idan haka kake ji to me ya kamata ka yi?

16 Babu shakka ka san gargaɗin Bulus ga Afisawa: “Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dage gāba da kissoshin Iblis.” (Afisawa 6:11) Sa’ad da muka yi tunanin dabarun Shaiɗan, abubuwa kamar su son abin duniya da lalata za su faɗo mana zuciya babu wuya. Irin waɗannan jaraba sun zarge mutanen Allah na dā da na zamani. Amma, bai kamata mu manta da wata dabarar Shaiɗan ba, wato, ƙoƙarinsa ya huɗubantar da mutane cewa Allah Jehobah ba ya ƙaunarsu.

17 Shaiɗan yana da basira wajen yin amfani da irin wannan yanayi ya yi ƙoƙarin juya mutane daga Allah. Ka tuna kalmomin Bildad ga Ayuba: “Akwai wanda ya isa ya zama adali, ko mai tsarki a gaban Allah? Hasken wata ba haske ba ne a gare shi, ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa. To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah?” (Ayuba 25:4-6; Yahaya 8:44) Ka yi tunanin yadda waɗannan kalmomi za su kasance da kashe jiki? Saboda haka, kada ka ƙyale Shaiɗan ya kashe maka jiki. Hakika, ka fahimci dabarun Shaiɗan domin ka kasance da gaba gaɗin yin kokawa ƙwarai domin yin abin da yake da kyau. (2 Korantiyawa 2:11) Ko da yake an yi wa Ayuba gyara, Jehobah ya albarkaci jimirinsa ta wajen mai da masa ninki biyu na dukan abin da ya yi asararsa.—Ayuba 42:10.

Jehobah “Ya Fi” Zuciyarmu

18, 19. Ta yaya ne Allah ya ‘fi zuciyarmu,’ kuma a wace hanya ce ya ‘san kome’?

18 Gaskiya ne yana da wuya a fid da mutuwar zuci musamman ma idan ta yi jijiya. Duk da haka, ruhun Jehobah zai taimake ka sannu a hankali ka “rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah.” (2 Korantiyawa 10:4, 5) Sa’ad da rashin jin daɗi ya nemi ya mamaye ka, ka yi bimbini bisa kalmomin manzo Yahaya: “Ta haka za mu tabbata mu na gaskiya ne, har kuma mu amince wa kanmu gaban Allah, duk sa’ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome.”—1 Yahaya 3:19, 20.

19 Me ake nufi da furcin nan ‘Allah ya fi zuciyarmu’? Wani lokaci zuciyarmu za ta ba mu laifi, musamman ma sa’ad da muka fahimci ajizancinmu da kurakuranmu. Ko kuma zai iya kasancewa domin tushenmu, muna iya yawan tunanin abin da babu daɗi game da kanmu, kamar da a ce ba abin da za mu yi da Jehobah zai karɓa. Kalmomin manzo Yahaya sun tabbatar mana cewa Jehobah ya fi zuciyarmu! Yana ganin muhimmancinmu fiye da kurakuranmu. Kuma ya san abin da ke zuciyarmu. Dauda ya rubuta: “Ubangiji ya san abin da aka yi mu da shi, yakan tuna, da ƙura aka yi mu. (Zabura 103:14) Hakika, Jehobah ya san mu fiye da yadda maka san kanmu!

“Kyakkyawan Rawani” Kuma “Kambin Sarauta”

20. Menene annabcin dawowa na Ishaya ya nuna game da yadda Jehobah yake ɗaukan bayinsa?

20 Ta bakin annabi Ishaya, Jehobah ya bai wa jama’arsa ta dā begen dawowa. Sa’ad da aka kwashe su bauta a Babila, wannan sanyayar zuciya da kuma tabbaci ne waɗannan suke bukata! Saurarar lokacin da za su komo ƙasarsu, Jehobah ya ce: “Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji, wato kambin sarauta mai daraja gare shi.” (Ishaya 62:3) Da waɗannan kalmomi, Jehobah ya lulluɓe mutanen da daraja da ɗaukaka. Haka ya yi da al’ummarsa ta Isra’ila ta ruhaniya a yau. Kamar dai ya ɗaga su sama ne domin kowa ya gani ya yi sha’awa.

21. Ta yaya za ka tabbata cewa Jehobah zai albarkaci jimirinka na aminci?

21 Ko da yake wannan annabci ya sami ainihin cikarsa a kan shafaffu, ya kwatanta darajar da Jehobah ya ba dukan waɗanda suke bauta masa. Saboda haka, idan muna da shakka, mu tuna cewa ko da yake mu ajizai ne, muna da muhimmanci kamar “kyakkyawan rawani” da kuma “kambin sarauta” ga Jehobah. Saboda haka ka ci gaba da faranta masa rai ta wajen yin iya ƙoƙarinka ka yi nufinsa. (Karin Magana 27:11) Ta wajen yin haka, za ka iya tabbata cewa Jehobah zai albarkaci jimirinka na aminci!

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

Ka Tuna?

• Su waye suke da ‘muhimmanci’ ga Jehobah?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu ɗauki Jehobah Mai sakamako ne?

• Waɗanne ‘kissoshin’ Shaiɗan ya kamata mu mai da hankali a kai?

• A wace hanya ce Allah ya ‘fi zuciyarmu’?

[Hotuna a shafi na 22]

Bulus

Iliya

Hannatu

[Hoto a shafi na 24]

Kalmar Allah tana ɗauke da kalmomin ta’aziyya masu yawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba