Waye Zai Tsira Wa Ranar Jehovah?
“Rana tana zuwa, tana ƙuna kamar tanderu.”—MALACHI 4:1.
1. Yaya Malachi ya kwatanta ƙarshen wannan mugun zamani?
ALLAH ya hure annabi Malachi ya rubuta annabci na abin mamaki da zai auku a nan gaba kaɗan. Waɗannan aukuwa sa shafi kowa a duniya. Malachi 4:1 ya annabta: “Ga shi, rana tana zuwa, tana ƙuna kamar tanderu; dukan masu-girman kai, da dukan waɗanda ke aikin mugunta, za su zama tattaka; ranan da ke zuwa kuma za ta ƙoƙone su, in ji Ubangiji mai runduna, har da ba za ta bar masu tushe ko reshe ba.” Yaya girman wannan halaka ta wannan zamanin za ta zama? Za ta kasance kamar an halaka tushen itace ne gabaki ɗaya, saboda itacen kada ya sake girma.
2. Ta yaya wasu nassosi suka kwatanta ranar Jehovah?
2 Kana iya tambaya, ‘Wace “rana” ce annabi Malachi yake annabtawa?’ Wannan ranar ce da aka faɗe ta a Ishaya 13:9, da ta ce: “Duba, ga ranar Ubangiji tana zuwa, mara-tausayi, da hasala da fushi mai-zafi; garin a maida ƙasa kango, a kuma halaka masu-zunubin da ke ciki, su ƙare.” Zephaniah 1:15 ya ba da wannan kwatanci: “Wannan rana ranar hasala ce, ranar wahala da ƙunci, ranar kaɗaici da risɓewa, ranar duhu da gama gira, ranar hadura masu-zurfi da duhu baƙi ƙirin.”
“Ƙunci Mai-Girma”
3. Mecece ce “ranar Ubangiji”?
3 A ainihin cikar annabcin Malachi “ranar Ubangiji” lokaci ne da Yesu ya kira “ƙunci mai-girma.” Yesu ya ce: “Sa’annan za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Matta 24:21) Ka yi tunanin ƙunci da duniya ta fuskanta musamman tun daga shekara ta 1914. (Matta 24:7-12) Yaƙin Duniya na II kawai ya ci rayuka wajen miliyan 50! Duk da haka, “ƙunci mai-girma” da yake zuwa zai mai da waɗannan matsaloli wasan yara. Wannan ƙunci mai-girma, a lokaci ɗaya da ranar Jehovah, zai ƙare a Armageddon, zai kawo ƙarshen wannan mugun zamani.—2 Timothawus 3:1-5, 13; Ru’ya ta Yohanna 7:14; 16:14, 16.
4. Sa’ad da ranar Jehovah ta kammala, menene zai kasance ya riga ya faru?
4 A ƙarshen wannan ranar Jehovah ɗin, za a halaka duniyar Shaiɗan da masu goyon bayanta. Wanda za a halaka da farko addinin ƙarya ne. Sai kuma fushin Jehovah ya faɗa wa tsarin siyasa da kuma na tattalin arziki na zamanin Shaiɗan. (Ru’ya ta Yohanna 17:12-14; 19:17, 18) Ezekiel ya annabta: “Za su jefarda azurfansu a cikin hanyoyin gari, zinariyarsu kuma za ta zama kamar abu mai-ƙazanta; azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya su cece su a ranar fushi na Ubangiji ba.” (Ezekiel 7:19) Game da wannan ranar Zephaniah 1:14 ta ce: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.” Domin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ranar Jehovah, ya kamata mu ƙudura niyyar mu yi aiki cikin jituwa da farillai masu adalci na Allah.
5. Menene waɗanda suke tsoron sunan Jehovah suke gani?
5 Bayan ya faɗi abin da ranar Jehovah za ta yi wa duniyar Shaiɗan, Malachi 4:2 ya ambata Jehovah yana cewa: “A gareku, ku da ke tsoron sunana, ranar adalci za ta fito da warkarwa cikin fukafukanta; za ku fita, ku yi tsalle tsalle kamar ’yan maruƙa na dangwali.” “Ranar adalci” Yesu Kristi ne. Shi ne “hasken duniya” a ruhaniya. (Yohanna 8:12) Yesu ya haskaka da warkarwa, na farko warkarwa na ruhaniya, wadda muke gani a yau, sai kuma cikakkiyar warkarwa na jiki a sabuwar duniyar. Kamar yadda Jehovah ya ce, waɗanda aka warkar za su “fita, su yi tsalle tsalle kamar ’yan maruƙa na dangwali,” da suke murna an sake su daga ɗauri.
6. Wane bikin nasara ne bayin Jehovah za su more?
6 Mutanen da suka yi banza da mizanan Jehovah fa? A Malachi 4:3 ya ce: “Za ku [watau, bayin Allah] tattake miyagu; gama za su zama toka daga ƙarƙashin tafin sawunku a ran da ni ke yin wannan, in ji Ubangiji mai-runduna.” Mutane masu bauta wa Allah ba za su saka hannu ba wajen halaka duniyar Shaiɗan. Maimakon haka, za a “tattake miyagu” an alamce ta wajen sa hannu a bikin babbar nasara da za ta biyo bayan ranar Jehovah. Babban biki ya biyo bayan halakar Fir’auna da rundunarsa a Jar Teku. (Fitowa 15:1-21) Hakanan ma, biki zai biyo bayan kawar da Shaiɗan da kuma duniyarsa. Masu aminci da suka tsira a ranar Jehovah za su yi ihun murna: “Mu yi murna, mu yi farinciki cikin cetonsa.” (Ishaya 25:9) Lalle zai kasance ɗaukaka sa’ad da aka kunita mulkin mallaka na Jehovah kuma aka tsabtace duniya domin rayuwa cikin salama!
Kiristendam Suna Yin Koyi da Isra’ila
7, 8. Ka kwatanta yanayin ruhaniyar Isra’ila a zamanin Malachi.
7 Waɗanda suke yanayi mai kyau da Jehovah, waɗanda suka bauta masa ne, da aka bambanta su da waɗanda ba su bauta masa ba. Ya kasance ɗaya da lokacin da Malachi ya rubuta littafinsa. A shekara ta 537 K.Z., raguwar Isra’ila an dawo da ita bayan shekara 70 na bauta a Babila. Duk da haka, bayan shekara ɗari, al’ummar da aka dawo da ita ta sake bauɗewa zuwa ridda da kuma mugunta. Yawancin mutanen suna raina sunan Jehovah; sun yi banza da dokokinsa na adalci; sun tozartar da haikalinsa ta wajen kawo makafin dabbobi, guragu; da kuma marasa lafiya domin hadaya, kuma suna sakin matansu na ƙuruciya.
8 Saboda haka, Jehovah ya gaya musu: “Zan zo kusa da ku domin shari’a; zan zama shaida mai-sauri a bisa masu-sihiri, da mazinata, da masu-rantsuwa da ƙarya, da waɗanda ke yi ma mai-aikin lada zalunci wajen zancen hakkinsa, suna aikin zalunci ga gwauruwa, da maraya, suna hana ma baƙo wajibinsa, ba su kuwa ji tsorona ba . . . gama ni Ubangiji ba mai-sakewa ba ne.” (Malachi 3:5, 6) Amma, Jehovah ya gayyace dukan waɗanda za su juyo daga munanan hanyoyinsa: “Ku juyo wurina, ni ma zan koma wurinku.”—Malachi 3:7.
9. Ta yaya annabcin Malachi ya samu cikarsa ta farko?
9 Waɗannan kalmomin sun samu cikarsu ta farko a ƙarni na farko A.Z. Raguwar Yahudawa suka bauta wa Jehovah kuma suka zama sashen sabuwar “al’umma” ta Kiristoci waɗanda ruhu ya shafa, wadda daga baya ta haɗa da mutanen Al’ummai. Amma yawancin Isra’ilawa na jiki sun ƙi Yesu. Saboda haka, Yesu ya gaya wa wannan al’ummar Isra’ila: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Matta 23:38; 1 Korinthiyawa 16:22) A shekara ta 70 A.Z., kamar yadda aka annabta a Malachi 4:1, “rana . . . [mai] ƙuna kamar tanderu” ta auko ma Isra’ilawa na jiki. Aka halaka Urushalima da haikalinta, kuma an ba da rahoto cewa fiye da mutane miliyan ɗaya suka rasa rayukansu domin rashin abinci, kokawar neman mulki, da kuma farmakin Romawa. Amma, waɗanda suka bauta wa Jehovah suka tsira daga wannan ƙuncin.—Markus 13:14-20.
10. A wace hanya ce mutane galiba da kuma limaman suka yi koyi da Isra’ila ta ƙarni na farko?
10 ’Yan Adam, musamman ma Kiristendam, ta yi koyi da al’ummar Isra’ila ta ƙarni na farko. Shugabanni da kuma mutane a cikin Kiristendam sun gwammace imani na addininsu maimakon gaskiya ta Allah da Yesu ya koyar. Limaman musamman suke da laifi. Sun ƙi su yi amfani da sunan Jehovah, sun cire shi ma a cikin nasu fassara dabam dabam na Littafi Mai Tsarki. Suna raina Jehovah da koyarwarsu da ba na nassosi ba, kamar su koyarwar arna ta azabtarwa cikin wutar jahannama, ta allah-uku-cikin ɗaya, kurwa marar mutuwa, da kuma ra’i na bayyanau. Saboda haka, sun yi wa Jehovah ƙwacen yabo da ya cancanta, kamar yadda firistocin zamanin Malachi suka yi.
11. Ta yaya addinai na duniya suka nuna wanda suke bauta wa da gaske?
11 Sa’ad da kwanaki na ƙarshe suka fara a shekara ta 1914, addinai na wannan duniya, da waɗanda suke da’awar su Kirista ne suka ja-gorance su, sun nuna wanda suke bauta wa da gaske. A lokacin yaƙe-yaƙen duniya biyu, sun ƙarfafa mabiyansu su je yaƙi domin bambancin ƙasa su kuma kashe har da mutanen nasu addinin. Kalmar Allah ta bambanta sarai tsakanin waɗanda suke yi wa Jehovah biyayya da kuma waɗanda ba su yi ba: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba. Gama jawabi ke nan da kuka ji tun daga farko, mu yi ƙaunar junanmu: ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shaiɗan, ya kashe ɗan’uwansa.”—1 Yohanna 3:10-12.
Cikar Annabci
12, 13. Waɗanne annabce-annabce ne bayin Allah suka cika a zamaninmu?
12 A ƙarshen Yaƙin Duniya na I a shekara ta 1918, bayin Jehovah sun ga cewa Allah ya la’anci Kiristendam tare da dukan addinan ƙarya na duniya. Daga lokacin zuwa gaba, aka fara kiran masu zukatan kirki: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi tarayya da zunubanta, kada ku sha rabon annobanta: gama zunubanta sun kawo har ga sama, Allah kuwa ya tuna da muguntanta.” (Ru’ya ta Yohanna 18:4, 5) Waɗanda suke da muradin su bauta wa Jehovah aka fara tsabtace su daga dukan raguwar addini na ƙarya kuma suka fara wa’azin bishara kuwa ta Mulki a dukan duniya, aikin da za a gama shi kafin ƙarshen wannan zamani ya zo.—Matta 24:14.
13 Wannan domin a cika annabcin da yake Malachi 4:5 ne, inda Jehovah ya ce: “Ku duba, zan aike muku annabi Iliya, kamin ranan nan mai-girma mai-ban razana ta Ubangiji ta zo.” Wannan annabcin ya samu cikarsa ta farko a ayyukan Yohanna Mai Baftisma, wanda yake hoton Iliya. Yohanna ya yi irin aikin Iliya a lokacin da ya yi wa Yahudawa da suka tuba daga zunubansu bisa Dokar alkawari baftisma. Mafi muhimmanci ma, Yohanna shi ne mai share fage wa Almasihu. Amma aikin Yohanna cikar farko ne na annabcin Malachi. Da Yesu ya ce Yohanna Iliya ne na biyu, wannan ya nuna ne cewa za a sake aiki irin na “Iliya” a nan gaba.—Matta 17:11, 12.
14. Wane aiki ne mai muhimmanci dole za a yi kafin wannan zamanin ya ƙare?
14 Annabcin Malachi ya nuna cewa wannan muhimmin aiki na Iliya za a yi shi kafin “ranan nan mai-girma mai-ban razana ta Ubangiji.” Wannan ranar za ta ƙare da yaƙin babbar rana ta Allah Mai Iko Duka da take gabatowa da gaggawa, a Armageddon. Wannan ya nuna cewa ƙarshen mugun zamani da kuma somawar Sarautar Alif na Mulkin Allah na samaniya ƙarƙashin Yesu Kristi da aka naɗa zai biyo bayan aiki da ya yi daidai da na Iliya. Kuma kamar yadda annabcin ya ce, kafin Jehovah ya halaka wannan mugun zamani, ajin Iliya na zamani, da miliyoyin ’yan’uwa Kiristoci da suke da begen zama a duniya, da ƙwazo suka maido da bauta mai tsarki, suna ɗaukaka sunan Jehovah, kuma suna koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki wa masu kama da tumaki.
Jehovah Ya Albarkaci Bayinsa
15. Ta yaya Jehovah yake tunawa da bayinsa?
15 Jehovah ya albarkaci waɗanda suke bauta masa. Malachi 3:16 ta ce: “Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu-tunawa da sunansa.” Daga Habila zuwa gaba, Allah yana rubuta a cikin littafi sunan waɗanda za a tuna da su don rai madawwami. Ga waɗannan Jehovah ya ce: “Ku kawo dukan zakka a cikin ma’aji, domin abinci ya samu a gidana, ku gwada ni hakanan yanzu, . . . ko ba zan buɗe muku sakatan sama ba, in zuba muku albarka, har da ba za a sami wurinda za a karɓa ba.”—Malachi 3:10.
16, 17. Ta yaya Jehovah ya albarkaci mutanensa da kuma aikinsu?
16 Hakika Jehovah ya yi wa waɗanda suke bauta masa albarka. Ta yaya? Hanya ɗaya ita ce ta ƙarin fahimtar nufe-nufensa. (Misalai 4:18; Daniel 12:10) Wata hanya kuma ita ce ta ba su amfani na ban mamaki a aikinsu na wa’azi. Mutane masu zukatan kirki sun haɗu da su wajen bauta ta gaskiya, kuma waɗannan sun zama “taro mai-girma, . . . daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna . . . suka tada murya da ƙarfi, suka ce, Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon kuma.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Kuma wannan taro mai-girma ya bayyana a hanya mai ban mamaki, kuma masu bauta wa Jehovah yanzu sun kai miliyan shida a ikilisiyoyi 93,000 a dukan duniya!
17 Albarkar Jehovah ta bayyana saboda Shaidun Jehovah suna buga littattafai da suke bisa Littafi Mai Tsarki da aka fi rarraba su a duk tarihi. A yanzu kowane wata ana buga Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! wajen miliyan 90; Hasumiyar Tsaro a harsuna 144, Awake! a harsuna 87. Littattafan nazarin Littafi Mai Tsarki Gaskiya mai bishe zuwa Rai Madauwami, da aka buga a shekarar 1968 (Hausa 1971), an rarraba fiye da miliyan 107 a harsuna 117. Kana Iya Rayuwa Har Abada A Duniya, da aka fito da shi a shekara ta 1982 (Hausa 1983), an rarraba fiye da miliyan 81 a harsuna 131. Littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada an fito da shi a shekara ta 1995, ya kai miliyan 85 a harsuna 154. Mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu?, da aka buga a shekara ta 1996, an riga an rarraba wajen miliyan 150 a cikin harsuna 244.
18. Me ya sa muke more ni’ima ta ruhaniya duk da hamayya?
18 Mun more wannan ni’ima ta ruhaniya duk da hamayya mai daɗewa daga duniyar Shaiɗan. Wannan ya nuna gaskiyar kalmomin da ke rubuce a Ishaya 54:17: “Babu alatun da aka halitta domin cutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi. Gadōn bayin Ubangiji ke nan, adalcinsu wanda shi ke daga wurina, in ji Ubangiji.” Yana da ban ƙarfafa ga bayin Jehovah su sani cewa Malachi 3:17 tana samun cikarsa na ainihi a kansu: “Za su zama nawa, in ji Ubangiji mai-runduna, a cikin wannan rana da ni ke yin ajiya mai-daraja ke nan.”
Bauta wa Jehovah da Farin Ciki
19. Ta yaya waɗanda suke bauta wa Jehovah suka bambanta daga waɗanda ba sa bauta masa?
19 Bambanci tsakanin amintattun bayin Jehovah daga waɗanda ke na duniyar Shaiɗan yana bayyana sarai kowacce rana. Malachi 3:18 ya annabta: “Za ku komo, ku rarrabe tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” Bambanci ɗaya daga cikin da yawa shi ne cewa waɗanda suke bauta wa Jehovah suna yin haka da farin ciki mai yawa. Dalili ɗaya cikinsu shi ne bege na ban sha’awa da suke da shi. Suna da cikakkiyar dogara ga Jehovah sa’ad da ya ce: “Sababbin sammai da sabuwar duniya ni ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa.”—Ishaya 65:17, 18; Zabura 37:10, 11, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.
20. Me ya sa mu mutane ne masu farin ciki?
20 Muna da tabbaci ga alkawuran Jehovah cewa mutanensa amintattu za su tsira a ranar Jehovah kuma a kawo su zuwa sabuwar duniya. (Zephaniah 2:3; Ru’ya ta Yohanna 7:13, 14) Ko da wasu za su mutu domin tsufa, ciwo, ko kuma haɗari kafin lokacin, Jehovah ya ce zai ta da su daga matattu kuma su samu damar rayuwa har abada. (Yohanna 5:28, 29; Titus 1:2) Ko da yake dukanmu muna da matsalolinmu da kuma damuwa, kamar yadda muke fuskantar wannan ranar Jehovah, muna da dalilan kasancewa mutane da suka fi farin ciki, a duniya.
Mecece Amsarka?
• Mecece “ranar Ubangiji”?
• Ta yaya addinai na duniya suka yi koyi da Isra’ila ta dā?
• Waɗanne annabce-annabce bayin Jehovah suke cikawa?
• Ta yaya Jehovah ya albarkaci mutanensa?
[Hoto a shafi na 27]
Urushalima ta ƙarni na farko ta ‘ƙone kamar tanderu’
[Hotuna a shafi na 29]
Jehovah yana yi wa waɗanda suke bauta masa tanadi
[Hotuna a shafi na 30]
Domin begensu mai ban sha’awa, bayin Jehovah suna farin ciki da gaske