Cika Umurnan Jehovah Yana Ɗaukaka Shi
“Zan girmama shi da ban godiya.”—ZABURA 69:30.
1. (a) Me ya sa Jehovah ya cancanci a ɗaukaka shi? (b) Ta yaya za mu ɗaukaka shi da godiya?
JEHOVAH shi ne Mamallakin Dukan Sararin Samaniya, kuma Mahalicci. Saboda haka, sunansa da kuma nufinsa sun dace a ɗaukaka su. A ɗaukaka Jehovah tana nufin a daraja shi ƙwarai, a yaba masa da baki da kuma ta wurin ayyuka. Domin a yi haka da “ban godiya” yana bukatar mu riƙa godiya ko da yaushe domin abubuwa da yake yi da kuma abubuwa da zai yi a nan gaba. Halin da ya kamata mu kasance da shi an nuna a cikin Ru’ya ta Yohanna 4:11, inda halittun ruhu masu aminci suka ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Ta yaya muke ɗaukaka Jehovah? Ta wajen koyo game da shi da kuma yin abin da yake bukata a gare mu. Ya kamata mu ji kamar yadda mai Zabura ya ji sa’ad da ya ce: “Ka koya mini in aika nufinka; gama kai ne Allahna.”—Zabura 143:10.
2. Ta yaya Jehovah yake bi da waɗanda suke ɗaukaka shi, da kuma waɗanda ba sa yi?
2 Jehovah yana ɗaukan waɗanda suke ɗaukaka shi da tamani. Saboda haka shi “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Mecece ce ladar? Yesu ya ce cikin addu’a ga Ubansa na samaniya: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Hakika, waɗanda suke “girmama [Jehovah] da ban godiya” za su “gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) A wani ɓangare kuma, “mugu ba shi da lada.” (Misalai 24:20) Kuma a wannan kwanaki na ƙarshe, bukatar ɗaukaka Jehovah tana da gaggawa domin ba da daɗewa ba zai halaka miyagu ya ceci adalai. “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:17; Misalai 2:21, 22.
3. Me ya sa za mu saurari littafin Malachi?
3 Ana samun nufin Jehovah a cikin Littafi Mai Tsarki, domin “kowane nassi hurare daga wurin Allah” ne. (2 Timothawus 3:16) Wannan Kalmar Allah tana ɗauke da labarai da yawa na yadda Jehovah ya albarkaci waɗanda suka ɗaukaka shi da kuma abin da ya faru da waɗanda ba su yi ba. Ɗaya daga cikin labaran nan ya ƙunshi abin da ya faru a Isra’ila a zamanin annabi Malachi. A lokacin shekara ta 443 K.Z., sa’ad da Nehemiah yake gwamma na Yahuda, Malachi ya rubuta littafi da yake ɗauke da sunansa. Wannan littafi mai ƙarfi mai ban sha’awa yana ɗauke da bayani da annabce-annabce da aka “rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.” (1 Korinthiyawa 10:11) Sauraron kalmomin Malachi zai taimake mu mu yi shiri domin “ranan nan mai-girma mai-ban razana ta Ubangiji,” sa’ad da ya halaka wannan mugun zamani.—Malachi 4:5.
4. Waɗanne abubuwa ne guda shida suka ja hankalinmu a sura 1 na Malachi?
4 Ta yaya littafin Malachi da aka rubuta, fiye da shekara 2,400 da suka shige, zai taimake mu a wannan ƙarni na 21, mu yi shiri domin babbar rana mai ban razana ta Jehovah? Sura ta farko ta jawo hankalinmu ga aƙalla abubuwa shida masu muhimmanci wajen ɗaukaka Jehovah da godiya domin mu samu tagomashinsa da kuma rai madawwami: (1) Jehovah yana ƙaunar mutanensa. (2) Dole ne muna daraja abubuwa masu tsarki. (3) Jehovah yana son mu yi iyakacin ƙoƙarinmu wajensa. (4) Ƙauna ta rashin son kai ce take motsa bauta ta gaskiya, ba haɗama ba. (5) Karɓaɓɓiyar hidima ga Allah ba aiki ba ne kawai mai gajiyar da mutum. (6) Kowannenmu dole ne Allah ya yi masa hisabi. Saboda da haka, a cikin wannan talifi na farko cikin guda uku a kan littafin Malachi, bari mu bincika kowane cikin waɗannan batutuwa sa’ad da muke bincika Malachi sura ta 1.
Jehovah Yana Ƙaunar Mutanensa
5, 6. (a) Me ya sa Jehovah ya yi ƙaunar Yaƙub? (b) Idan muka yi koyi da amincin Yaƙub, menene za mu yi zatonsa?
5 Ƙaunar Jehovah ta bayyana sarai a ayoyi na farko na Malachi. Littafin ya fara ne da waɗannan kalmomin: “Jawabin maganar Ubangiji zuwa ga Isra’ila.” Bugu da ƙari, Allah ya ce: “Na ƙaunace ku.” Da ya ba da misali a wannan ayar, Jehovah ya ce: “Na ƙaunaci Yaƙub.” Yaƙub mutum ne mai bangaskiya ga Jehovah. Da shigewar lokaci, Jehovah ya canja sunan Yaƙub zuwa Isra’ila, shi kuma ya zama kakan al’ummar Isra’ila. Domin Yaƙub mutum ne mai bangaskiya ga Jehovah shi ya sa ya yi ƙaunarsa. A tsakanin mutane waɗanda suka nuna irin halin Yaƙub, Jehovah ya ƙaunace su su ma.—Malachi 1:1, 2.
6 Idan muna ƙaunar Jehovah kuma cikin aminci muka manne wa mutanensa, za mu samu ƙarfafa daga furcin da yake cikin 1 Samuila 12:22: “Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” Jehovah yana ƙaunar mutanensa kuma yana saka musu a ƙarshe da rai madawwami. Saboda haka mun karanta: “Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta; Ka zauna a cikin ƙasan, ka lizimci aminci. Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.” (Zabura 37:3, 4) Ƙaunarmu ga Jehovah ta ƙunshi abu na biyu da ya jawo hankalinmu a sura 1 na Malachi.
Ka Nuna Godiya ga Abubuwa Masu Tsarki
7. Me ya sa Jehovah ya ƙi Isuwa?
7 Kamar yadda muka karanta a Malachi 1:2, 3, bayan Jehovah ya ce, “Na ƙaunaci Yaƙub,” ya daɗa cewa, “Isuwa na ƙi.” Me ya kawo bambancin? Yaƙub ya ɗaukaka Jehovah, amma ɗan tagwayensa, Isuwa, bai yi haka ba. An kira Isuwa kuma Edom. A Malachi 1:4, an kira ƙasar Edom ƙasar mugunta, kuma mutanenta an ƙi su. Sunan nan Edom (ma’anarsa “Ja”) an bai wa Isuwa ne bayan ya sayar da gadōnsa na ɗan fari mai tamani ga Yaƙub domin jar miya. Farawa 25:34 ta ce: “Isuwa ya waƙala gadōnsa na haihuwa.” Manzo Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi su yi hankali “kada wani mai-fasikanci ya kasance, ko kuwa wani mara-ibada kamar Isuwa, wanda ya sayarda gadōnsa na ɗan fari saboda akushin abinci.”—Ibraniyawa 12:14-16.
8. Me ya sa Bulus ya kamanta Isuwa da fasiki?
8 Me ya sa Bulus ya haɗa abin da Isuwa ya yi da fasikanci? Domin kasancewa da irin halin Isuwa zai iya kai mutum ga ƙin nuna godiya ga abubuwa masu tsarki. Kuma wannan zai kai ga zunubi mai tsanani, kamar su fasikanci. Saboda haka, kowannenmu zai iya tambayar kansa: ‘Wani lokaci ana jaraba ni ne na sayar da gadōna na Kirista—rai madawwami—domin abu mai shigewa da sauri kamar jar miya? Ko ƙila ba da sanina ba ina ƙin abubuwa masu tsarki?’ Isuwa yana da rashin haƙuri wajen biyan muradinsa na jiki. Ya gaya wa Yakubu: “[Maza-maza], ka cishe ni da wannan jan dahuwa, ina roƙonka.” (Farawa 25:30) Abin baƙin ciki, wasu bayin Allah, a taƙaice sun ce: “Maza-maza! Me ya sa zan jira aure mai daraja?” Yin jima’i ko da menene sakamakonsa, ya zama musu jar miya.
9. Ta yaya za mu riƙe tsoron girmama Jehovah?
9 Kada mu taɓa ƙin abubuwa masu tsarki ta wajen nuna rashin daraja ga abubuwa masu tsarki, aminci, da kuma gadōnmu na ruhaniya. Maimakon mu zama kamar Isuwa, bari mu zama kamar Yaƙub mai aminci kuma mu riƙe tsoron girmama Allah mu nuna godiya ƙwarai ga abubuwa masu tsarki. Ta yaya za mu yi haka? Ta wajen mai da hankali mu cika umurnan Jehovah. Wannan ya kai ga abu na uku da aka fito da shi cikin Malachi sura 1. Menene wannan?
Ba wa Jehovah Abu Mafi Kyau
10. A wace hanya ce firistoci suka tozartadda teburin Jehovah?
10 Firistocin Yahuda da suka yi bauta a haikali a Urushalima a zamanin Malachi ba su ba da hadaya mafi kyau ba ga Jehovah. Malachi 1:6-8 suka ce: “Ɗa yana girmama ubansa, bawa kuma ubangijinsa; idan fa ni uba ne, ina girmana? idan kuma ni ubangiji ne, ina kwarjinina? in ji Ubangiji mai-runduna zuwa gareku, ku [firistoci] da ku ke rena sunana?” “A ina fa muka rena sunanka?” firistocin suka yi tambaya. “Kuna miƙa tozartaciyar gurasa a bisa bagadina,” in ji amsar Jehovah. “A ina fa muka tozartadda kai?” firistocin suka yi tambaya. Saboda haka Jehovah ya gaya musu: “Yayinda ku ke cewa, [tebur] na Ubangiji abin reni ne.” Waɗancan firistocin sun nuna sun raina teburin Jehovah a duk lokacin da suka miƙa hadaya mai aibi, suna cewa: “Ba mugun abu ba ne.”
11. (a) Menene Jehovah ya ce game da hadaya da ba a karɓa? (b) A wace hanya ce dukan mutanen suke da laifi?
11 Jehovah ya ba da shawara game da irin wannan hadaya da ba a karɓa: “Miƙa abin yanzu ga mai-mulkinka, a gani ko shi za ya ji daɗinka? za ya kuwa karɓe ka?” Ina, mai mulkinsu ba zai karɓi irin wannan kyauta ba. Yaya Mamallakin Dukan Sararin Samaniya zai karɓi irin wannan hadaya mai lahani! Kuma ba firistocin ba ne kawai suke da laifi. Hakika, suna raina Jehovah ta wajen miƙa hadayar. Amma dukan mutanen ne suke da laifi? Hakika! Su suke zaɓo waɗannan dabbobi makafi, guragu, da kuma marasa lafiya su kawo ga firistoci cewa su yi hadaya da su. Dubi irin zunubin nan!
12. Ta yaya ake taimakonmu mu bai wa Jehovah abu mafi kyau?
12 Bai wa Jehovah abu mafi kyau da za mu iya hanya ce da za mu nuna cewa muna ƙaunarsa da gaske. (Matta 22:37, 38) Ba kamar lalatattun firistoci na zamanin Malachi ba, ƙungiyar Jehovah a yau tana koyarwa da kyau daga Nassosi mu ɗaukaka Jehovah da godiya ta wajen cika umurnan Allah. Mai alaƙa da wannan shi ne batu na huɗu da za a iya ɗaukowa daga Malachi sura 1.
Ƙauna Take Motsa Bauta ta Gaskiya, Ba Haɗama Ba
13. Menene firistoci suke yi da ya nuna cewa haɗama ce take motsa su?
13 Firistocin zamanin Malachi suna da son kai, ba su da ƙauna, kuma suna da son kuɗi. Ta yaya muka san da haka? Malachi 1:10 ta ce: “Da fa da ko ɗaya a cikinku wanda za ya rufe ƙofofi, domin kada ku kunna wuta a bisa bagadina a banza! Ba na jin daɗinku, in ji Ubangiji mai-runduna, ba ni kuwa karɓan baiko daga hannunku ba.” Hakika, waɗannan firistoci masu haɗama suna bukatar kuɗi a kan hidima mafi sauƙi a haikali, suna son a biya su su rufe ƙofofi da kuma kunna wuta a kan bagadi! Babu mamaki da Jehovah bai ji daɗin baiko daga hannayensu ba!
14. Me ya sa za mu ce ƙauna ce take motsa Shaidun Jehovah?
14 Haɗama da kuma son kan firistoci masu zunubi na Urushalima ta dā na tunasar mana da cewa in ji Kalmar Allah, masu ƙyashi, ba za su gāji Mulkin Allah ba. (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Tunani a kan son jiki na waɗannan firistoci ya sake ƙara godiyarmu ga aikin wa’azi da Shaidun Jehovah suke yi. Mun ba da kai ne; kuma ba ma ba da farashi ga kowanne fasalin hidimarmu. A’a, “ba mu ɓata maganar Allah.” (2 Korinthiyawa 2:17) Kamar Bulus, kowannenmu zai iya cewa cikin gaskiya: “Na yi muku wa’azin bisharar Allah kyauta.” (2 Korinthiyawa 11:7) Ka lura cewa Bulus ya yi “bisharar Allah” da farin ciki. Wannan ya faɗi batu na biyar da aka jawo hankalinmu a kai a Malachi sura 1.
Hidima ga Allah Ba Aiki Ba ne Kawai Mai Gajiyarwa
15, 16. (a) Wane hali firistoci suke da shi game da miƙa hadaya? (b) Ta yaya Shaidun Jehovah suke ba da nasu hadaya?
15 Firistoci marasa bangaskiya a Urushalima ta dā suna jin miƙa hadaya aiki ne kawai mai gajiyarwa. Kaya ne a gare su. Kamar yadda aka lura a Malachi 1:13, Allah ya ce musu: “Kuma kun ce, Ga shi, wace irin fitina ke nan! kun kuwa hura masa hanci.” Waɗannan firistoci sun hura hanci ga abubuwa masu tsarki na Allah, ko kuma sun yi ƙyamarsu. Mu yi addu’a domin kada mu zama kamar su. Maimakon haka, bari mu nuna ruhun da yake cikin kalmomin 1 Yohanna 5:3: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”
16 Bari mu yi farin ciki wajen miƙa hadaya ta ruhaniya ga Allah, kuma kada mu ɗauki wannan kamar kaya ne mai nauyaya. Bari mu bi kalmomin annabci: “Ku ce ma [Jehovah], Ka kawarda dukan saɓo, ka karɓi abin da ke nagari; da hakanan za mu kawo hadayun leɓunanmu misalin bajimai.” (Hosea 14:2) Furcin nan “leɓunanmu misalin bajimai” yana nufin hadaya ta ruhaniya, kalmomin da muke furtawa wajen yabon Jehovah game da nufe-nufensa. Ibraniyawa 13:15 ta ce: “Ta wurin [Yesu Kristi] fa bari mu miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.” Muna farin ciki ƙwarai cewa hadayunmu na ruhaniya, ba kawai ayyuka ba ne, amma nuna ƙaunarmu ce da dukan zuciya ga Allahnmu! Wannan ya kai ga batu na shida da za a samu a Malachi sura 1.
Kowannenmu Dole ne Ya Ba da Lissafi
17, 18. (a) Me ya sa Jehovah ya la’anci “wanda ya ke” “mai-ha’inci”? (b) Menene waɗanda suke yin ha’inci ba su yi la’akari da shi ba?
17 Mutanen da suka rayu a zamanin Malachi sun ɗauki hakkin ayyukansu, mu ma haka. (Romawa 14:12; Galatiyawa 6:5) Saboda haka, Malachi 1:14 ta ce: “La’antace ne shi, mai-ha’inci, wanda ya ke da namiji [mara aibi] cikin garkensa, amma ya yi wa’adi, sa’annan ya yi ma Ubangiji hadaya da abu mai-aibi.” Mutumin da yake da garke ba dabba ɗaya yake da ita ba—a ce, tunkiya ɗaya kawai—da zai ce babu yadda zai iya zaɓe ba. Wajen zaɓen dabba domin hadaya, ba zai zaɓi makauniya, gurguwa, ko mara lafiya ba. Idan ya zaɓi wadda take da aibi, wannan zai nuna yana raina tsarin hadaya na Jehovah, domin mutumin da yake da garke zai iya zaɓen wadda ba ta da aibi!
18 Da kyakkyawan dalili ne, Jehovah ya la’anci mai-ha’inci, wanda yake da kyakkyawar dabba cikin garkensa amma ya kawo—mai wuyar kora—makauniya, gurguwa, ko kuma mara lafiya ga firist ya yi hadaya. Ba a ko ambato ba cewa firist ya karanta Doka a nuna cewa irin waɗannan dabbobi masu aibi, ba a karɓa ba ma. (Leviticus 22:17-20) Duk wani mutum mai hankali zai fahimci cewa ba zai yi kyau ba idan suka yi ƙoƙarin su ba wa mai mulkinsu irin wannan kyautar. Amma kuma, suna sha’ani da Mamallakin Dukan Halitta, Jehovah, wanda ya fi dukan wani gwamna. Malachi 1:14 ta faɗi batun a wannan hanyar: “Ni sarki ne babba, in ji Ubangiji mai-runduna; sunana kuma abin ban-razana ne a wurin al’ummai.”
19. Menene muke sauraro, kuma menene za mu riƙa yi?
19 Da yake mu amintattun bayin Allah ne, muna son mu ga ranar da dukan ’yan Adam za su tsoraci Babban Sarki, Jehovah. A wannan lokacin, “duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.” (Ishaya 11:9) Kafin nan, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu cika umurnan Jehovah, ta wajen yin koyi da mai Zabura wanda ya ce: “Zan girmama shi da ban godiya.” (Zabura 69:30) Domin mu cim ma wannan burin, Malachi yana da ƙarin gargaɗi da za su taimake mu. A talifofi biyu na gaba, bari mu mai da hankalinmu ga wasu ɓangarori na littafin Malachi.
Ka Tuna?
• Me ya sa za mu ɗaukaka Jehovah?
• Me ya sa Jehovah bai karɓi hadaya ba na firistoci a zamanin Malachi?
• Ta yaya muke ba Jehovah hadayar yabo?
• Menene ya kamata ya motsa bauta ta gaskiya?
[Hoto a shafi na 15]
Annabcin Malachi ya yi nuni ga zamaninmu ne
[Hoto a shafi na 16]
Isuwa bai yi ƙaunar abubuwa masu tsarki ba
[Hoto a shafi na 17]
Firistoci da mutanen sun ba da hadayu da ba a karɓa ba
[Hoto a shafi na 18]
A dukan duniya, Shaidun Jehovah suna ba da hadayar yabo kyauta