Jehovah Yana Ƙyamar Cin Amana
“Ka da ku yi aikin cin amana kowane ɗaya da ɗan’uwansa.”—MALACHI 2:10, NW.
1. Menene Allah yake bukata a gare mu idan za mu samu rai madawwami?
KANA son rai madawwami? Idan ka gaskata da wannan bege da aka yi alkawarinsa a cikin Littafi Mai Tsarki, wataƙila ka ce: ‘Hakika kuwa.’ Amma idan kana son Allah ya yi maka tagomashi da rai marar ƙarewa cikin sabuwar duniyarsa, kana bukatar ka cika farillansa. (Mai-Wa’azi 12:13; Yohanna 17:3) Rashin hankali ne a bukaci mutane ajizai su yi haka? A’a, Jehovah ya yi furci mai ƙarfafawa: “Ni jinƙai ni ke biɗa, ba hadaya ba; sanin Allah kuma gāba da ƙonannun hadayu.” (Hosea 6:6) Saboda haka, har mutane masu yawan kurakure ma za su iya cika farillan Allah.
2. Ta yaya Isra’ilawa da yawa suka yi wa Jehovah aikin cin amana?
2 Duk da haka, ba duka ba ne suke so su yi nufin Jehovah. Hosea ya bayyana cewa har Isra’ilawa da yawa ma ba su yi haka ba. Al’ummarsu, sun yarda su yi alkawari, yarjejeniya, su yi biyayya da dokokin Allah. (Fitowa 24:1-8) Duk da haka, ba a jima ba suka fara ‘ƙetare wa’adinsu’ ta wajen taka dokokinsa. Saboda haka, Jehovah ya ce waɗannan Isra’ilawan sun yi masa “aikin cin amana.” (Hosea 6:7) Kuma haka mutane da yawa suka yi tun daga wannan lokaci. Jehovah yana ƙyamar cin amana, ko masa ko kuma wa waɗanda suke ƙaunarsa kuma suke bauta masa.
3. Wane bincike za a yi a wannan nazarin?
3 Hosea ba shi ne kawai annabi wanda ya nanata ra’ayin Allah game da cin amana ba, ra’ayin da muke bukatar mu ɗauka idan muna begen mu more rayuwar farin ciki. Daga talifi na baya, mun fara bincika saƙon annabci na Malachi, ya fara da sura na farko na littafinsa. Bari yanzu mu juya zuwa sura ta biyu ta wannan littafin mu ga yadda ra’ayin Allah game da cin amana ya samu nanaci. Ko da yake Malachi yana bi ne da yanayi da ya kasance tsakanin mutanen Allah shekaru da yawa bayan sun komo daga Babila, wannan sura ta biyu tana da ma’ana ƙwarai a gare mu a yau.
Firistoci Masu Laifi
4. Wane gargaɗi Jehovah ya yi wa firistocin?
4 Sura ta 2 ta fara ne da la’antar Jehovah a kan firistocin Yahudawa domin bauɗewa daga hanyarsa ta adalci. Idan ba su bi gargaɗinsa sun gyara hanyoyinsu ba, wahala mai tsanani babu shakka za ta zo. Ka lura da ayoyi biyu na fari: “Ku [firistoci], wannan doka dominku ce. In ba za ku ji ba, in kuwa ba za ku sa shi a rai ba, da za ku ɗaukaka sunana, in ji Ubangiji mai-runduna, sai in aike da la’anan a bisa kanku, in la’antadda albarkanku.” Da firistocin suna koyar da mutane dokokin Allah kuma suna kiyayewa, da albarka ta zama tasu. Amma domin sun yi banza da nufin Allah, la’ana ce za ta zo. Albarka ma da firist ya yi za ta juya ta zama la’ana.
5, 6. (a) Me ya sa firistocin ne musamman suke da laifi? (b) Yaya Jehovah ya furta ƙyamarsa ga firistocin?
5 Me ya sa firistocin ne musamman suke da laifi? Aya ta 7, ta ba mu cikakken bayani: “Ya kamata leɓunan [firist] su kiyayi ilimi, a kuwa nemi shari’a a bakinsa; gama shi manzon Ubangiji mai-runduna ne.” Fiye da shekara dubu a farko, dokokin Allah da aka bai wa Isra’ila ta wajen Musa suka ce firist ne yake da hakkin “koya ma ’ya’yan Isra’ila dukan farillai waɗanda Ubangiji ya faɗa.” (Leviticus 10:11) Abin baƙin ciki, wani lokaci, marubucin 2 Labarbaru 15:3 ya ba da rahoto: “Isra’ila sun daɗe sun rasa Allah mai-gaskiya, da [firist] mai-koyarwa, da shari’a.”
6 A zamanin Malachi, a ƙarni na biyar K.Z., yanayin firistoci duk ɗaya ne. Sun kasa koyar da Dokar Allah ga mutanen. Saboda haka waɗannan firistoci sun cancanci ya yi musu hisabi. Ka lura da magana da ƙarfafar murya da Jehovah ya yi game da su. Malachi 2:3 ta ce: “Zan . . . shafa turoso a bisa fuskokinku, turoson idodinku ke nan.” Lalle kuwa horo ne! Kashin dabbobi da aka yi hadayarsu ana ɗauka zuwa bayan zango a ƙona. (Leviticus 16:27) Amma sa’ad da Jehovah ya ce musu maimakon haka za a shafa kashin a fuskokinsu, ya nuna musu sarai cewa ya ƙi hadayu da kuma waɗanda suke miƙa su.
7. Me ya sa Jehovah ya yi fushi da masu koyar da Doka?
7 Ƙarnuka kafin zamanin Malachi, Jehovah ya gaya wa Lawiyawa su kula da mazauni kuma daga baya haikali da kuma hidimarta mai tsarki. Sune malamai a al’ummar Isra’ila. Cika wannan aikin yana nufin rai da kuma salama gare su da kuma al’ummar. (Litafin Lissafi 3:5-8) Amma Lawiyawan suka kawar da tsoron girmama Allah da suke da shi da farko. Saboda haka, Jehovah ya gaya musu: “Kun ratse daga hanya; kun sa mutane dayawa su yi tuntuɓe a wajen shari’a; kun ƙazantar da alkawarin Lawi . . . ba ku kiyaye tafarkokina ba.” (Malachi 2:8, 9) Ta wajen kasawarsu su koyar da gaskiya da kuma ta wajen misalinsu marar kyau, firistocin sun yaudari Isra’ilawa da yawa, ya dace da Jehovah ya yi fushi da su.
Ka Kiyaye Mizanan Allah
8. Yana da yawa ne a bukaci mutane su kiyaye mizanan Allah? Ka yi bayani.
8 Kada mu yi tunanin cewa waɗannan firistoci ya dace a tausaya musu kuma a yi musu gafara domin cewa mutane ne ajizai, kuma ba za a bukaci su kiyaye mizanan Allah ba. Gaskiyar ita ce, mutane za su iya kiyaye dokokin Allah, domin Jehovah ba ya bukatar abin da ba za su iya ba. Wataƙila wasu firistocin a can dā ɗin sun kiyaye mizanan Allah, babu shakka ma game da ɗaya wanda ya yi haka—Yesu, ‘babban firist.’ (Ibraniyawa 3:1) Game da shi za a iya cewa da gaske: “Shari’a ta gaskiya tana bakinsa, ba a kuwa iske rashin adalci a leɓunansa ba; ya tafi tare da ni cikin salama da adalci, har ya juyadda mutane dayawa ga barin mugunta.”—Malachi 2:6.
9. Su waye cikin aminci suke idar da gaskiyar a zamaninmu?
9 Idan aka gwada, fiye da ƙarni guda yanzu, ’yan’uwan Kristi shafaffu, waɗanda suke da begen zuwa sama, suna hidima ta “[tsarin firistoci] mai-tsarki, domin [su] miƙa hadayu masu-ruhaniya, abin karɓa ga Allah.” (1 Bitrus 2:5) Sun yi ja-gora wajen idar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki ga wasu. Kamar yadda ka koyi gaskiyar da suke koyarwa, ba ka gani daga abin da ka fahimta cewa dokar gaskiya tana bakinsu ba? Kuma sun juya mutane da yawa daga kuskure na addini, da yanzu da akwai miliyoyi a dukan duniya da suka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki waɗanda suke da begen rai madawwami. Waɗannan su ma suna da gatar koyar da dokar gaskiya har ga wasu miliyoyi.—Yohanna 10:16; Ru’ya ta Yohanna 7:9.
Dalilin Mai da Hankali
10. Me ya sa muke da dalilin mai da hankali?
10 Duk da haka, muna da dalilin mai da hankali. Za mu iya kuskura fahimta darussa da ke Malachi 2:1-9. Mu da kanmu muna mai da hankali saboda kar a iske rashin gaskiya a leɓunanmu? Alal misali, iyalinmu suna iya gaskata abin da muka ce? ’Yan’uwanmu na ruhaniya cikin ikilisiya kuma fa? Ba shi da wuya mu koyi halin tsara maganarmu saboda ya kasance daidai amma ta ruɗar da wasu. Ko kuma wani ya ƙara gishiri ko kuma ya ɓoye wasu ainihin batun kasuwanci. Jehovah ba zai fahimci haka ba ne? Kuma idan muna bin irin waɗannan hanyoyi, zai karɓi hadayar yabo daga bakinmu kuwa?
11. Su waye musamman suke bukatar su mai da hankali?
11 Ga waɗanda suke da gatar koyar da Kalmar Allah a ikilisiyoyi a yau, Malachi 2:7 ta kasance gargaɗi ne a gare su. Ta ce leɓunansu “su kiyayi ilimi, a kuwa nemi shari’a” kuma daga bakinsu. Hakki mai girma yana kan waɗanda suke irin wannan koyarwar, domin Yaƙub 3:1 ya nuna cewa za su “karɓi shari’a ma-fi girma.” Ko da yake za su koyar da ƙwazo da farin ciki, koyarwarsu dole ta kasance bisa rubutacciyar Kalmar Allah da kuma umurni da ya zo daga ƙungiyar Jehovah. A wannan hanyar za su zama waɗanda “za su iya su koya ma waɗansu.” Saboda haka, aka yi musu gargaɗi: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.”—2 Timothawus 2:2, 15.
12. Waɗanda suke koyarwa suna bukatar su fahimci menene?
12 Idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya jarabtuwa mu saka namu ra’ayin ko kuma abin da muka fi so cikin abin da muke koyarwa. Wannan zai kasance haɗari ne na musamman ga mutumin da ya dogara ga nasa kammalawa ko wannan ta saɓa wa abin da ƙungiyar Jehovah take koyarwa. Amma Malachi sura 2 ta nanata cewa ya kamata mu tsammaci masu koyarwa a ikilisiya su manne wa ilimi daga Allah, ba ga nasu ra’ayi ba, wanda zai iya sa tumaki su yi tuntuɓe. Yesu ya ce: “Dukan wanda za shi sa guda ɗaya a cikin ƙanƙananan na masu-bada gaskiya gare ni shi yi tuntuɓe, gwamma dai a gareshi a rataya ma wuyansa babban dutsen niƙa, a nutsadda shi cikin zurfin teku.”—Matta 18:6.
Auro Mara Bi
13, 14. Wace hanyar cin amana ce ɗaya da Malachi ya nanata?
13 Daga aya ta 10 zuwa gaba, Malachi sura 2 ta nanata cin amana ne kai tsaye. Malachi ya mai da hankali ne a kan abubuwa biyu da suke kawo haka, game da wannan ya yi ta amfani da wannan kalmomin “cin amana.” Da farko, ka lura cewa Malachi ya gabatar da gargaɗinsa ne da waɗannan tambayoyi: “Ba dukanmu da uba ɗaya ba? ba Allah ɗaya ya halicce mu ba? don menene mu ke aikin cin amana kowane ɗaya da ɗan’uwansa, muna tozartadda wa’adin ubanninmu?” Sai kuma a aya ta 11, ya daɗa cewa cin amana ta Isra’ila tozartadda ‘wuri mai-tsarki ne na Ubangiji.’ Menene suke yi da yake da tsanani haka? Ayar ta bayyana aiki ɗaya da ba daidai ba—sun “auro ’yar wani baƙon allah.”
14 Wato, wasu Isra’ilawa, waɗanda suke cikin al’ummar da ta keɓe kanta ga Jehovah, sun auri waɗanda ba sa bauta masa. Matanin ya taimaka mana mu fahimci abin da ya sa haka yake da muni. Aya ta 10 ta ce suna da uba ɗaya. Wannan ba ya nufin Yakubu (da aka sake masa suna Isra’ila), ko kuma Ibrahim ko ma Adamu ba. Malachi 1:6 ta nuna cewa Jehovah ne “uba ɗaya” ɗin. Al’ummar Isra’ila tana da dangantaka da shi, suna cikin alkawari da ya ɗauka da kakanninsu. Ɗaya daga cikin dokoki na wannan alkawarin shi ne: “Ba za ka yi surukuta da su ba; ’yarka ba za ka ba ɗansa ba, ba kuwa za ka ɗauka ma ɗanka ’yatasa ba.”—Kubawar Shari’a 7:3.
15. (a) Ta yaya wasu za su yi ƙoƙarin daidaita auren marar bi? (b) Ta yaya Jehovah ya bayyana ra’ayinsa game da batun aure?
15 Wasu a yau suna tunani cewa: ‘Kai, mutumin nan da na ke so babu kamarsa. Da shigewar lokaci, shi (ko ita) wataƙila zai karɓe bauta ta gaskiya.’ Irin wannan tunanin ya tabbatar da huraren gargaɗin cewa: “Zuciya ta fi kome rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irmiya 17:9) Ra’ayin Allah game da auren marasa bi ya bayyana a aya ta Malachi 2:12: “Ubangiji za ya yanke” dukan wanda ya yi hakan. Saboda haka, aka aririce Kiristoci su yi aure “sai dai cikin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 7:39) A cikin tsarin Kiristoci, ba a “yanke” mai bi domin ya auri marar bi. Duk da haka, idan marar bin ya kasance cikin rashin imaninsa ko nata, me zai faru da marar bin sa’ad da Allah ya kawo ƙarshen wannan zamanin ba da daɗewa ba?—Zabura 37:37, 38.
Wulaƙanta Abokiyar Aure
16, 17. Wace hanyar cin amana ce wasu suka bi?
16 Sai Malachi ya bincika hanyar cin amana ta biyu: wulaƙanta abokiyar aure musamman kashe aure ba dalili. Aya 14 ta sura 2 ta ce: “Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matarka ta ƙuruciya, wadda ka ci amanarta, ko da ta ke abokiyar zamanka, matar alkawarinka.” Ta wajen cin amanar matansu, magidanta Yahudawa suka sa aka “rufe” bagadin Jehovah “hawaye.” (Malachi 2:13) Waɗannan maza suna ta kashe aure a kan kowane irin laifi, suna shikan matansu na ƙuruciya yadda bai dace ba, wataƙila domin su auro ’yammata ƙanana ko kuma arna. Kuma lalatattun firistocin suka ƙyale wannan! Kuma, Malachi 2:16 ta ce: “Ina jin ƙyamar kisan aure, in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.” Daga baya, Yesu ya nuna cewa lalata ce kawai dalilin kashe aure da zai sa marar laifin ya iya sake yin aure.—Matta 19:9.
17 Ka yi tunani a kan kalmomin Malachi, ka ga yadda suka taɓa zuciya da kuma jin ya kamata a kyautata. Ya yi nuni da ‘abokiyar [aurenka] da kuma matar alkawarinka.’ Kowanne mutumin da hakan ya shafa, ya auri ’yar’uwa mai bi, Ba’isra’iliya, ya zaɓe ta ta zama abokiyarsa da yake ƙauna, sai mutuwa za ta raba su. Wannan wataƙila lokaci ne da shi da ita suke matasa, shigewar lokaci bai warware alkawari da suka yi ba, wato, suka yi aure.
18. A wace hanya ce gargaɗin Malachi game da cin amana ya shafe mu a yau?
18 Gargaɗi game da wannan al’amari yana da ƙarfi ma a yau. Abin baƙin ciki ne cewa wasu sun raina umurnin nan na Allah na yin aure sai cikin Ubangiji. Kuma abin nadama ne cewa wasu ba sa yin ƙoƙarin su ƙarfafa aurensu. Maimakon haka, suna so su ba da hujjoji ko kuma su yi ƙoƙarin gyara abin da Allah yake ƙyama wajen kashe aure da ba bisa Nassi ba domin su auri wata. Yin irin waɗannan abubuwa, suna “gajiyadda Ubangiji.” A zamanin Malachi, waɗanda suka ƙyale gargaɗin suna da ikon jin cewa Jehovah bai yi daidai a ra’ayinsa ba. Kamar suna cewa ne, “Ina Allah mai-shari’a?” Ji wannan mugun tunani! Kada mu faɗā cikin wannan tarko.—Malachi 2:17.
19. Ta yaya magidanta da mata za su samu ruhun Allah?
19 Akasarin haka, Malachi ya nuna cewa wasu magidanta a zamaninsa ba su ci amanar matansu ba. Suna da ‘sauran ruhu mai tsarki na Allah.’ (Aya ta 15) Abin farin ciki, ƙungiyar Allah a yau tana cike da irin waɗannan maza waɗanda suke ‘ba da girma ga matansu.’ (1 Bitrus 3:7) Ba sa wulaƙanta matansu a zahiri ko kuma da baki, ba sa nacewa ga jima’i mai ƙasƙantarwa ba, kuma ba sa raina matansu ta wajen neman wasu mata ko kuma ta wajen kallon hotunan tsirarun mata. Kuma an albarkaci ƙungiyar Jehovah ta wajen mata Kiristoci da yawa masu aminci waɗanda suke da aminci ga Allah da kuma dokokinsa. Dukan waɗannan mata da maza sun san abin da Allah yake ƙyama, kuma suna tunani da kuma aikata abubuwa cikin jituwa da haka. Ku ci gaba da zama kamarsu, kuna “biyayya ga Allah” shi masarauci kuna samun albarka ta wajen samun ruhunsa mai tsarki.—Ayukan Manzanni 5:29.
20. Wane lokaci ne ya yi kusa wa dukan ’yan Adam?
20 Ba da daɗewa ba, Jehovah zai yi wa dukan duniyar nan hukunci. Dole kowanne mutum ya ba da dalilin ayyukansa da kuma imaninsa gare shi. “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Romawa 14:12) Saboda haka, tambayar mai ban sha’awa a wannan lokacin ita ce: Waye zai tsira a ranar Jehovah? Talifi na uku kuma na ƙarshe na wannan jerin zai tattauna wannan jigon.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Domin wane dalili na musamman ne Jehovah ya la’anci firistoci a Isra’ila?
• Me ya sa mizanan Allah ba su fi ƙarfin mutane su kiyaye su ba?
• Me ya sa za mu mai da hankali a koyarwarmu a yau?
• Waɗanne ayyuka ne biyu musamman Jehovah ya haramta?
[Hoto a shafi na 21]
A zamanin Malachi an la’anci firistoci domin ba sa kiyaye hanyoyin Jehovah
[Hoto a shafi na 22]
Dole ne mu mai da hankali domin mu koyar da hanyoyin Jehovah, ba ma ɗaukaka namu ra’ayin ba
[Hotuna a shafi na 24]
Jehovah ya la’anci Isra’ilawa da suka saki matansu a kan ƙananan dalilai kuma suka auri matan arna
[Hoto a shafi na 24]
Kiristoci a yau suna daraja alkawarin aurensu