Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 10/1 pp. 22-27
  • Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zaɓan Rayuwa Mai Kyau
  • Yin Shiri Don Nan Gaba
  • Matsalolin Makarantun Gaba da Sakandare
  • Menene Wasu Zaɓin da Za a Iya Yi?
  • Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 10/1 pp. 22-27

Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?

“Ku yabe shi ku samari da ’yan mata! . . . Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji.”—ZABURA 148:12, 13.

1. Waɗanne damuwa ne iyaye suke nunawa game da ’ya’yansu?

DUKAN iyaye, suna damuwa domin rayuwar ’ya’yansu ta nan gaba. Tun daga lokacin da aka haifi jariri, ko kuwa kafin a haife shi, iyaye sukan soma damuwa da lafiyarsa. Zai kasance lafiyayye kuwa? Zai girma yadda ya kamata? Yayin da yaron ke girma, damuwan na ƙaruwa. Galibi, iyaye suna son ’ya’yansu su sami abubuwa masu kyau.—1 Sama’ila 1:11, 27, 28; Zabura 127:3-5.

2. Me ya sa iyaye da yawa a yau suke son ’ya’yansu su more rayuwa mai kyau sa’ad da suka girma?

2 A yau, ba shi da sauƙi iyaye su yi wa ’ya’yansu tanadin abubuwa masu kyau. Iyaye masu yawa sun fuskanci lokatai masu wuya irinsu lokatan yaƙe-yaƙe, rikicin siyasa, tattalin arziki, wahala, da sauransu. Hakika, iyaye ba sa son ’ya’yansu su fuskanci irin waɗannan matsalolin. A ƙasashe masu arziki, iyaye suna iya ganin yaran abokansu da na ’yan’uwansu suna ci gaba a sana’o’i masu girma kuma suna jin daɗin rayuwa. Da haka, suna ganin cewa tilas ne su yi dukan abin da ya kamata domin ’ya’yansu su more rayuwa, wato rayuwa mai kyau sa’ad da suka girma.—Mai Hadishi 3:13.

Zaɓan Rayuwa Mai Kyau

3. Wane zaɓi ne Kiristoci suka yi?

3 Don su mabiyan Yesu Kristi ne, Kiristoci sun zaɓi su ba da rayuwarsu ga Jehobah. Sun bi kalaman Yesu: “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki [gungumensa] kowace rana, yā bi ni.” (Luka 9:23; 14:27) Hakika, rayuwar Kirista ta ƙunshi ba da kai. Amma, ba rayuwa ba ce ta talauci da wahala. Akasarin haka, rayuwa ce ta farin ciki da gamsuwa, domin ta ƙunshi bayarwa, kuma kamar yadda Yesu ya ce, “bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35.

4. Menene Yesu ya umurci mabiyansa su biɗa?

4 Mutane a zamanin Yesu suna zaune ne a cikin yanayi mai wuya. Ƙari ga neman abin rayuwa, suna jimre wa matsananciyar mulkin Romawa da kuma nauyin da addinin zamaninsu suka ɗora musu. (Matiyu 23:2-4) Duk da haka, yawancin waɗanda suka saurari Yesu, cikin farin ciki sun yi watsi da biɗan abin kai, har da sana’o’i, kuma suka zama mabiyansa. (Matiyu 4:18-22; 9:9; Kolosiyawa 4:14) Waɗannan almajiran sun yi kasada ce da rayuwansu? Ka yi la’akari da kalaman Yesu: “Kowa ya bar gidaje, ko ’yan’uwa mata, ko ’yan’uwa maza, ko uwa, ko uba, ko ’ya’ya ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.” (Matiyu 19:29) Yesu ya tabbatar wa mabiyansa cewa Ubansa na sama ya san bukatunsu. Saboda haka, ya umurce su: “Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.”—Matiyu 6:31-33.

5. Yaya ne wasu iyaye suke ji game da tabbacin da Yesu ya bayar cewa Allah zai kula da bayinsa?

5 Abubuwa ba su bambanta ba a yau. Jehobah ya san bukatunmu, kuma waɗanda suka mai da al’amuran Mulki abu na farko a rayuwarsu, musamman waɗanda suke yin hidima na cikakken lokaci, suna da tabbacin cewa zai kula da su. (Malakai 3:6, 16; 1 Bitrus 5:7) Wasu iyaye ba su da tabbaci da wannan batun. A wata sassa, za su so su ga ’ya’yansu na samun cin gaba a hidimar Jehobah, wataƙila, bayan wani lokaci su soma hidima na cikakken lokaci. A wani ɓangaren kuma, idan suka yi la’akari da yanayin tattalin arziki da aiki a duniya ta yau, za su ji cewa ya kamata ’ya’yansu su fara samun ilimi mai kyau tukuna, domin su sami aiki mai kyau, ko kuwa domin su sami wani abin da za su dangana a kai. Irin waɗannan iyayen suna ganin cewa ya dace ’ya’yansu su sami ƙarin ilimi.

Yin Shiri Don Nan Gaba

6. Ta yaya ne aka yi amfani da kalmar nan “ƙarin ilimi” a wannan talifin?

6 Tsarin ilimi ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Alal misali, a Nijeriya, mutum na zuwa makaranta na shekara 12. Bayan haka, ɗalibin na iya zuwa jami’a ko kwaleji ya yi shekara huɗu ko fiye da haka, a inda zai sami digiri na farko ko kuwa ilimin gaba da digiri a magani, shari’a, injiniya, da sauransu. Irin wannan ilimi na makarantar gaba da sakandare ne ake nufi da “ƙarin ilimi” da aka yi amfani da ita a cikin wannan talifin. A wata sassa kuma, akwai makarantun koyan aikin hannu, waɗanda ba sa ɗaukan lokaci kuma ana ba da takardar shaida ko kuwa difiloma na aikin hannu ko kuwa hidima.

7. Waɗanne ƙalubale ne ɗalibai suke fuskanta a manyan makarantu?

7 Abin da ya zama sananne a yau shi ne cewa, manyan makarantu ko kuwa sakandare suna shirya ɗalibansu domin ƙaro ilimi. Saboda haka, yawancin manyan makarantu suna mai da hankali ne a kan darussan da za su sa ɗalibansu su ci jarabawar shiga fitacciyar jami’a, maimakon darussan da za su sanya ɗaliban su sami aikin yi. Ɗaliban manyan makarantu a yau suna ƙarƙashin matsi daga malamansu, mashawarta, da ’yan’uwansu ɗalibai domin su shiga makaranta ta gaba da sakandare mai kyau, inda za su iya samun digirori masu kyau da za su sa su sami aiki a inda ake biyan kuɗi sosai.

8. Waɗanne zaɓi iyaye Kiristoci suke fuskanta?

8 Menene ya kamata iyaye Kiristoci su yi? Hakika, iyaye suna son ’ya’yansu su sami nasara a makaranta kuma su koyi aikin da za su kula da kansu da shi a nan gaba. (Karin Magana 22:29) Amma ya kamata su ƙyale ruhun gasa na duniya da yin nasara su shafi ’ya’yansu ne? Waɗanne irin makasudai ne suke sakawa a gaban ’ya’yansu, ta wajen kalma ko kuwa misali? Wasu iyaye suna aiki tuƙuru su tara kuɗi domin su aika ’ya’yansu makarantu na gaba da sakandare idan lokacin yin haka ya kai. Wasu har karɓan bashi suke yi domin wannan manufa. Matsalolin da ake fuskanta domin wannan shawarar, ba su misaltuwa da kuɗin da za a kashe. Waɗanne matsaloli ne ake fuskanta a makarantun gaba da sakandare?—Luka 14:28-33.

Matsalolin Makarantun Gaba da Sakandare

9. Menene za a iya cewa game da kuɗin da ake kashewa a kan makarantu na gaba da sakandare a yau?

9 Idan muka yi tunanin matsaloli, mukan yi tunanin yawan kuɗin da za mu kashe. A wasu ƙasashe, gwamnati ce ke ɗaukan nauyin waɗanda suke makaranta ta gaba da sakandare kuma ɗaliban da suka cancanta ba sa biyan kuɗin makaranta. A yawancin wurare, makarantu na gaba da sakandare suna da tsada. Talifin wata jarida na New York Times ta ce: “An ɗauki makaranta na gaba da sakandare abin da ke ba mutum dama. Amma yanzu ya zama abin da ke nuna tazarar da ke tsakanin masu hannu da shuni da talakawa.” A wata sassa, makarantu na gaba da sakandare sun zama na masu kuɗi da mutane masu rinjaya, waɗanda suke sanya ’ya’yansu a makarantun domin su tabbata cewa su ma sun zama masu kuɗi da kuma masu rinjaya na zamani. Ya kamata iyaye Kiristoci su zaɓi irin wannan makasudin wa yaransu?—Filibiyawa 3:7, 8; Yakubu 4:4.

10. Ta yaya ne ƙaro ilimi ke da nasaba ta kusa da ɗaukaka wannan zamanin?

10 Har ma inda makarantun gaba da sakandare kyauta ne, ana iya samun wasu matsaloli tattare da ita. Alal misali, Jaridar The Wall Street ta ce a kudu maso gabas na ƙasar Asiya, gwamnatin tana “gudanar da makarantu masu tsarin dala domin ta ɗaukaka ɗalibai mafi ilimi zuwa makarantu masu martaba.” “Makarantu masu martaba” na nufin shiga fitattun jami’o’i na duniya, kamar su, jami’ar Oxford da Kambridge da ke Ingila, makarantun Ivy League da ke Amirka, da sauransu. Me ya sa gwamnatin ta yi tanadin irin wannan tsarin mai girma? Rahoton ya ce, “domin ta ɗaukaka tattalin arzikinta.” Ƙaro ilimi na iya zama kyauta, amma abin da ɗaliban za su biya shi ne rayuwarsu da za ta shagala wajen ɗaukaka wannan zamanin. Tun da yake irin wannan hanyar rayuwar ce ake bi a wannan duniyar, ya kamata iyaye Kiristoci su ƙyale yaransu su bi ta?—Yahaya 15:19; 1 Yahaya 2:15-17.

11. Menene rahoto ya nuna game da yin maye da kuma lalata tsakanin ɗalibai na jami’a?

11 Wani abu kuma da za mu yi la’akari da shi, shi ne mahalli. Mummunar hali ya zama ruwan dare a harabar jami’a da kwaleji, kamar su shan ƙwayoyi, barasa, lalata, zamba, da sauransu. Ka yi la’akari da shan barasa. Sa’ad da take ba da rahoto game da shan barasa mai yawa domin buguwa, mujallar New Scientist ta ce: “Kusan kashi 44 na [ɗaliban jami’o’i a Amirka] suna shan barasa domin kawai su bugu aƙalla sau ɗaya a sati biyu.” Irin wannan matsalar ta zama ruwan dare tsakanin matasa a Ostereliya, Britaniya, Rasha, da wasu wurare. Idan aka zo batun lalata kuwa, abin da ke faruwa tsakanin ɗalibai shi ne “kwanan gida,” wadda rahoton Newsweek ta “kira saduwa sau ɗaya, wanda ya haɗa da yin sumba ko lalata, tsakanin idon sani waɗanda ba su da ra’ayin yi wa juna magana bayan haka.” Bincike ya nuna cewa daga kashi 60 zuwa 80 na ɗalibai ne suke irin wannan abin. “Idan kai ɗalibi ne da bai taɓu ba,” in ji wata mai bincike, “ya kamata ka yi haka.”—1 Korantiyawa 5:11; 6:9, 10.

12. Waɗanne matsi ne ɗalibai na makarantun gaba da sakandare suke fuskanta?

12 Ƙari ga mahalli marar kyau, akwai kuma matsi na aikin makaranta da jarabawa. Hakika, ɗalibai suna bukatan su yi karatu da kuma aikin da aka ba su na gida idan suna son su ci jarabawa. Wasu kuma suna yin aiki na ɗan lokaci yayin da suke zuwa makaranta. Dukan waɗannan abubuwa suna ɗaukan yawancin lokacinsu da kuma ƙarfinsu. Cikin dukan waɗannan, wane lokaci ne aka rage wa ayyuka na ruhaniya? Sa’ad da matsin ya yi yawa, menene za su ƙyale? Al’amuran Mulki za su zama abu na farko, ko kuwa za a yi watsi da su? (Matiyu 6:33) Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi Kiristoci: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.” (Afisawa 5:15, 16) Abin baƙin ciki ne cewa wasu sun yi watsi da imaninsu domin sun ba da kansu ga bukatun lokacinsu da ƙarfinsu ko kuwa domin sun saka hannu a ayyuka da ba na nassi ba a makarantu na gaba da sakandare!

13. Waɗanne tambayoyi ne iyaye Kiristoci ya kamata su yi la’akari da su?

13 Ba a gidaje na makarantu na gaba da sakandare kaɗai ba ne ake lalata, halaye marasa kyau, da kuma matsi. Yawancin matasa na duniya suna ɗaukan waɗannan abubuwan sashe na ilimi, kuma suna ganin hakan ya dace. Ya kamata iyaye Kiristoci su ƙyale ’ya’yansu su shiga irin wannan mahalli har na shekara huɗu ko fiye da haka? (Karin Magana 22:3; 2 Timoti 2:22) Haɗarin da matasan za su fuskanta ya kai amfanin da za su samu kuwa? Mafi muhimmanci, menene matasan suka koya cewa ya kamata ya zama abu na farko a rayuwarsu?a (Filibiyawa 1:10; 1 Tasalonikawa 5:21) Dole ne iyaye su yi tunani kuma su yi addu’a sosai game da waɗannan tambayoyin, da kuma haɗarin aika ’ya’yansu zuwa wata makaranta a wani gari ko wata ƙasa.

Menene Wasu Zaɓin da Za a Iya Yi?

14, 15. (a) Duk da ra’ayin da ya zama ruwan dare, wace shawara na Littafi Mai Tsarki ne ya shafe mu a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne matasa za su iya tambayar kansu?

14 Ra’ayin da ya zama ruwan dare a yau shi ne, idan matasa suna son su yi nasara, dole ne su je makarantar gaba da sakandare. Amma, maimakon bin ra’ayin mutane, Kalmar Allah ta gargaɗi Kiristoci: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (Romawa 12:2) Menene nufin Allah ga mutanensa matasa da tsofaffi, a wannan zamani na ƙarshe? Bulus ya yi gargaɗi ga Timoti: “Ka natsu cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.” Waɗannan kalmomin sun shafi dukanmu a yau.—2 Timoti 4:5.

15 Maimakon mu nitse cikin ruhun mallaka abin duniyar nan, muna bukatar ‘mu natsu,’ wato, mu kasance da hankalinmu na ruhaniya. Idan kai matashi ne, ka tambayi kanka: ‘Ina iyaka ƙoƙari na kuwa in ‘cika hidimata,’ domin in zama ƙwararren mai hidima na Kalmar Allah? Menene makasudai na wajen son in “cika” hidimata sosai? Na yi tunanin soma hidima ta cikakken lokaci kuwa?’ Waɗannan tambayoyi ne masu muhimmanci, musamman idan ka ga wasu matasa da suke biɗan abubuwan sonkai, wato, “manyan abubuwa” da suke tunanin cewa za su sa su zama masu arziki a nan gaba. (Irmiya 45:5) Saboda haka, ya kamata iyaye Kiristoci su yi wa ’ya’yansu tanadi na mahalli na ruhaniya da kuma koyarwa da ta dace tun suna ƙanana.—Karin Magana 22:6; Mai Hadishi 12:1; 2 Timoti 3:14, 15.

16. Ta yaya ne iyaye Kiristoci za su iya yi wa ’ya’yansu tanadi mai kyau na mahalli na ruhaniya?

16 “Innarmu ba kowa take ƙyale mu mu yi tarayya da shi ba,” in ji wani matashi wanda shi ne babba cikin yara maza uku a wani iyali, wadda innarsu take hidima na cikakken lokaci na shekaru da yawa. “Ba ma tarayya da ’yan makarantarmu, sai dai waɗanda suke cikin ikilisiya kuma suke da hali mai kyau na ruhaniya. Kuma tana gayyatar waɗanda suke cikin hidima na cikakken lokaci a kai a kai, wato, masu wa’azi na ƙasashen waje, masu tafiya masu ziyara, masu hidima a Bethel, da kuma majagaba zuwa gidanmu don tarayya. Saurarar labaransu da kuma farin cikin da suke samu, ya taimake mu wajen sa muradinmu ya zama na yin hidima na cikakken lokaci.” Abin farin ciki ne cewa a yau, dukan yaran uku suna hidima na cikakken lokaci, ɗaya na hidima a Bethel, ɗaya ya halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima, kuma ɗayan yana majagaba!

17. Wane ja-gora ne iyaye za su iya ba ’ya’yansu game da darussan da za su zaɓa a makaranta da kuma aikin da za su yi? (Dubi akwati da ke shafi na 25.)

17 Ƙari ga yi wa yara tanadi mai kyau na mahalli na ruhaniya, yana da muhimmanci tun da wuri-wuri, iyaye su ba da ja-gorar da ta dace game da darussan da ’ya’yansu za su zaɓa da kuma makasudansu na aiki. Wani matashi da ke hidima a Bethel ya ce: “Iyayena sun yi hidimar majagaba kafin su auri juna kuma sun ci gaba bayan haka, kuma sun yi iyaka ƙoƙarinsu su saka wannan ruhun na majagaba ga dukan iyalin. Duk lokacin da muke zaɓan darussa a makaranta ko kuwa sa’ad da muke yanke shawara da zai shafi rayuwarmu a nan gaba, suna ƙarfafa mu mu yi zaɓin da zai ba mu damar samun aiki na ɗan lokaci kuma mu yi hidimar majagaba.” Maimakon zaɓan darussan da za su kai ga neman ƙarin ilimi a makaranta ta gaba da sakandare, ya kamata iyaye da ’ya’yansu su tattauna game da darussan da za su amfana wajen biɗan ayyukan Allah.b

18. Waɗanne ayyuka ne matasa suke iya yi?

18 Bincike ya nuna cewa a yawancin ƙasashe, ana bukatar mutane masu aikin hannu da kuma waɗanda za su yi hidima, ba waɗanda suka kammala makaranta ta gaba da sakandare ba. Jaridar nan USA Today (Amirka a Yau) ta ba da rahoto cewa, “a shekaru masu zuwa kashi 70 na ma’aikata ba za su bukaci digiri na shekara huɗu na makarantar gaba da sakandare ba, amma na shekaru biyu a ƙaramin kwaleji ko kuwa satifiket na aikin hannu.” Yawancin irin makarantun nan suna koyar da ayyuka na ofis, makaniken mota, gyaran kwamfuta, gyaran fanfo, yin kitso, da sauransu. Waɗannan ayyuka ne kuwa masu muhimmanci? Ƙwarai kuwa! Wasu na iya tunanin cewa waɗannan ba ayyuka ba ne masu muhimmanci, amma suna ba da abin biyan bukata da kuma sauƙaƙa da waɗanda suke son yin hidima ga Jehobah suke bukata.—2 Tasalonikawa 3:8.

19. Wace hanya ce ta fi kyau wajen samun rayuwa mafi kyau da wadatar zuciya?

19 “Ku samari da ’yan mata,” in ji Littafi Mai Tsarki, “su yabi sunan Ubangiji, sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma, ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!” (Zabura 148:12, 13) Idan aka gwada da matsayi da kuma ɗaukaka da duniya ke ba da wa, yin hidima ta cikakken lokaci ga Jehobah ita ce hanyar rayuwa mafi kyau, mai ba da farin ciki da kuma wadatar zuciya. Ka sanya tabbacin da Littafi Mai Tsarki ya ba da a zuciya: “Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.”—Karin Magana 10:22.

[Hasiya]

a Game da labarin waɗanda suka daraja ilimi na tsarin Allah fiye da ilimi na manyan jami’o’i, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 1982, shafuffuka na 3-6; 15 ga Afrilu, 1979, shafuffuka na 5-10; Awake! 8 ga Yuni, 1978, shafi na 15; da kuma 8 ga Agusta, 1974, shafuffuka na 3-7 na Turanci.

b Dubi Awake! 8 ga Oktoba, 1998, “In Search of a Secure Life,” (“Neman Rayuwa Mai Kyau”) shafuffuka na 4-6, da kuma 8 ga Mayu, 1989, “What Career Should I Choose?” (Wane Aiki ne Zan Zaɓa?) shafuffuka na 12-14 na Turanci.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ga menene Kiristoci suka dogara domin rayuwa mai kyau a nan gaba?

• Waɗanne ƙalubale ne iyaye Kiristoci suke fuskanta game da rayuwar ’ya’yansu a nan gaba?

• Menene ya kamata a yi la’akari da shi sa’ad da ake gwada fa’idodi da kuma rashin muhimmancin ƙaro ilimi?

• Ta yaya ne Iyaye za su iya taimaka wa ’ya’yansu su biɗi hidimar Jehobah?

[Akwati a shafi na 25]

Menene Amfanin Ƙarin Ilimi?

Yawancin mutanen da ke shiga makaranta na gaba da sakandare suna son samun digiri ne da zai sa su sami aikin da zai ba su kuɗi. Amma, rahoton gwamnati ya nuna cewa, kusan kashi 25 na waɗanda suka je makarantar gaba da sakandare ne kawai suke samun digiri tsakanin shekara shida. Duk da haka, digiri na ba da tabbaci ne cewa za a sami aiki mai kyau? Yi la’akari da abin da wani bincike da nazari da aka yi ba da daɗewa ta ce.

“Babu tabbacin cewa zuwa jami’ar Harvard ko kuwa Duke zai sa a sami aiki mai kyau da kuma albashi mai tsoka. . . . Kamfanoni ba su da sani sosai game da matasa masu neman aiki. Digiri daga jami’a yana iya burgewa. Amma, abu mafi muhimmanci shi ne, abin da mutum ya iya da kuma wanda bai iya ba ake lura.”—Newsweek, 1 ga Nuwamba, 1999.

“Ko da yake ana bukatar gwanaye a wurin aiki a yau fiye da dā . . . , gwanintar da ake bukata domin waɗannan ayyukan sune na sanannun manyan makaranta, wato, lissafi, iya karatu, da kuma iya rubutu kamar na waɗanda suke aji uku na sakandare . . . , ba na makarantar gaba da sakandare ba. . . . Ɗalibai ba sa bukatar su je kwaleji kafin su sami aiki mai kyau, amma ya kamata su gwanance a aikinsu kamar waɗanda suka je jami’a.”—American Educator, Spring 2004.

“Yawancin makarantu na gaba da sakandare ba sa tunani game da yanayin duniya sa’ad da suke koyar da ɗalibansu domin su sami aikin yi sa’ad da suka kammala karatunsu. Makarantun koyan sana’a . . . suna samun ƙaruwa. Sun sami ƙaruwa na kashi 48 na masu shiga makarantar daga shekara ta 1996 zuwa 2000. . . . Amma, difloma na makarantar gaba da sakandare masu tsada kuma masu ɗaukan lokaci, sun zama abubuwa marasa amfani fiye da dā.”—Time, 24 ga Janairu, 2005.

“Wani bincike a Amirka daga Sashen Ƙwadago ya ba da tabbaci cewa a shekara ta 2005 kashi ɗaya cikin uku na waɗanda suka kammala karatunsu a makarantar gaba da sakandare na shekara huɗu ne ba za su sami aikin da ya yi daidai da digirin da suka yi ba.”—The Futurist, Yuli/Agusta 2000.

Domin dukan waɗannan abubuwan, ƙarin malamai suna shakkar darajar ƙaro ilimi a yau. Rahoton Futurist ta furta wannan baƙin cikin: “Muna koya wa mutane makasudai marasa kyau.” Akasarin haka, yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah: “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi. Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa da suke bugowa zuwa gāɓa.”—Ishaya 48:17, 18.

[Hoto a shafi na 22]

Sun yi watsi da biɗar abin kansu suka bi Yesu

[Hoto a shafi na 27]

Iyaye Kiristoci suna yi wa ’ya’yansu tanadin mahalli mai kyau na ruhaniya tun suna ƙanana

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba