Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 3 pp. 6-8
  • Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ZUWA JAMI’A MUTANE SUKA SA A GABA
  • WANE SAKAMAKO AKA SAMU?
  • Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kowa Yana So Ya More Rayuwa a Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Yadda Za Ka More Rayuwa a Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 3 pp. 6-8
’Yan mata biyu ’yan jami’a za su aji.

Neman Kuɗi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

Mutane da yawa suna ganin idan suka yi karatu sosai kuma suka yi kuɗi, rayuwarsu za ta yi kyau. A nasu ra’ayin, idan mutum ya je jami’a ya dawo, zai zama ƙwararren ma’aikaci kuma zai taimaka wa iyalinsa da ƙasarsa sosai. Ƙari ga haka, suna ganin idan mutum ya yi karatu sosai, zai sami babban aiki. Kuma in yana samun kuɗi, zai more rayuwa.

ZUWA JAMI’A MUTANE SUKA SA A GABA

Wani mutum mai suna Zhang Chen daga ƙasar China ya ce: “Na ɗauka cewa zuwa jami’a ne zai sa in rabu da talauci. Kuma cewa idan na sami babban aiki, kome zai tafi sumul a rayuwata.”

Mutane da yawa suna zuwa manyan makarantu, wasu har suna zuwa makaranta a ƙasashen waje garin neman ilimi don su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Annobar korona ce ta sa waɗanda suke zuwa karatu a ƙasashen waje suka ragu kwanan nan. Wani rahoto da Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci-gaba (OECD) ta bayar a 2012 ya ce: “Fiye da rabin mutanen da suke zuwa karatu a ƙasashen waje, daga Asiya suke.”

Iyaye da dama sukan yi aiki tukuru don yaransu su samu su je karatu a ƙasar waje. Wani mai suna Qixiang, daga ƙasar Taiwan ya ce: “Iyayena ba masu kuɗi ba ne, amma sai da suka yi iya ƙoƙari suka tura dukanmu ’ya’yansu huɗu mu je jami’a a Amirka.” Sai da iyayensa suka ci bashi kafin suka iya yin hakan kuma abin da mutane da yawa suke yi ke nan.

WANE SAKAMAKO AKA SAMU?

Daya daga cikin matan tana zaune a gaban kwamfuta a gajiye da dare.

Mutane da yawa sun je babbar makaranta kuma sun sami kuɗi, duk da haka ba sa jin daɗin rayuwa

Ilimi yakan taimaka wa mutane a wasu hanyoyi, amma mutane da yawa da suka yi karatun ba sa samun abin da suke nema. Alal misali, akwai mutanen da suka yi iya ƙoƙari kuma suka ci bashi don su je babbar makaranta, amma a ƙarshe sun kāsa samun aikin da suke so. Wata ’yar jarida mai suna Rachel Mui a ƙasar Singapore ta ce: “Adadin waɗanda suka sauke karatu daga jami’a ba tare da samun aiki ba, sai daɗa karuwa yake yi.” Wani mai digirin digirgir mai suna Jianjie, daga ƙasar Taiwan ya ce: “Rashin aiki yana tilasta wa mutane da yawa su karɓi aikin da bai shafi abin da suka karanta a jami’a ba.”

Waɗanda suka sami irin aikin da suke so ma, rayuwa ba ta musu daɗi yadda suka zata ba. Alal misali, da wani mai suna Niran ya gama karatu a Turai kuma ya dawo ƙasar Thailand, ya ce: “Digiri da na samu ya sa na sami babban aikin da nake nema. Amma aikin yana bukatar kuzari da lokaci sosai. A ƙarshe an sallami yawancin ma’aikantan kamfanin har da ni. A nan ne na gano cewa, ba wani babban aiki da zai ba mutum tabbacin cewa zai ji daɗin rayuwa.”

Wasu suna da kuɗin kuma ana ganin kamar suna jin daɗin rayuwa. Duk da haka, suna fama da rashin lafiya da matsaloli a iyalinsu, kuma suna tsoro kar su rasa kuɗin da suke da shi. Alal misali, wani mai suna Katsutoshi daga Japan ya ce: “A dā ni mai kuɗi ne sosai, duk da haka rayuwa ba ta min daɗi ba domin mutane da yawa sun yi kishin abin da nake da shi, kuma sun yi ta wulaƙanta ni.” Wata mai suna Lam da take zama a Vietnam ta ce: “Na ga mutane da yawa da suka yi ƙoƙari su sami aiki mai kyau don su more rayuwa, amma hakan bai sa sun more rayuwar ba. Kuɗi yana ƙara wa mutum damuwa, ya sa shi rashin lafiya da kuma baƙin ciki.”

ABIN DA YA SA NEMAN KUƊI DA ILIMI BA SU ISA BA

Hakika mutane suna bukatar su ɗan yi makaranta kuma su sami kuɗi. Hakan zai taimaka musu su iya kula da kansu da kuma iyalansu. Amma kuɗi da ilimi ba su ne za su sa mutum ya more rayuwa a nan gaba ba. Me ya sa muka ce hakan? Ga abin da Nassosi Masu Tsarki suka ce.

BA A KULLUM NE ZUWA JAMI’A YAKE SA MUTUM YA YI NASARA BA

“Ba kullum mai saurin gudu shi ne mai cin tsere ba, . . . ba kullum mai basira shi ne mai samun dukiya ba, ba kullum mai iyawa shi ne mai samun farin jini ba. Amma lokaci da sa’a sukan same kowannensu.”​—MAI-WA’AZI 9:11.

Ko da mutum ya yi karatu sosai, babu tabbas cewa kome zai tafi sumul a rayuwarsa domin akwai abubuwa da dama da za su iya shafansa. Kome ilimin mutum, idan tattalin arziki ya taɓarɓare ko ana tashin hankali a inda yake ko ana nuna masa bambanci, zai yi masa wuya ya sami abin da yake nema.

MUTUM ZAI IYA YIN HASARA

“Kada ka gajiyar da kanka garin neman dukiya, ka yi amfani da hikimarka ka kauce. Sa’ad da ka kafa ido a kanta, za ta shuɗe. Ba shakka takan yi fikafikai ta tashi a sama kamar gaggafa.”​—KARIN MAGANA 23:​4, 5.

Kuɗi zai iya kāre mutum amma zai iya rasa su babu zato. Faɗuwar tattalin arziki da bala’i kamar su girgizar ƙasa da ambaliyar ruwa da wutar daji da kuma mahaukaciyar guguwa za su iya sa mutum ya rasa kome a dare ɗaya.

KUƊI NA TATTARE DA MATSALOLI

“Ƙoshin mai arziki yakan hana shi barci saboda damuwar yawan arzikinsa.”​—MAI-WA’AZI 5:12.

Wani mai suna Franklin da ke zama a Hong Kong ya shaida hakan. Ya yi karatu sosai, ya sami babban aiki har ya zama manaja. Amma ya ce: “Yawan aiki da nake yi ya soma shafan lafiyata. Yawan tunani ya bi ya hana ni barci.” A kwana a tashi, ya ga cewa aikin ba na yi ba ne. Ya ƙara da cewa: “Na soma tambayar kaina, me ya sa nake irin wannan aikin? Na bi na rasa abin da mutum zai yi don ya ji daɗin rayuwa.”

“Kada ka gajiyar da kanka garin neman dukiya.”​—KARIN MAGANA 23:4

Akwai mutane da yawa da ra’ayinsu ya zo ɗaya da na Franklin, sun ga cewa neman ilimi da kuɗi ba shi ne zai sa su more rayuwa ba. Don haka, maimakon su sunkuya neman abin duniya, wasu suna iya ƙoƙarinsu su zama mutanen kirki, suna yi wa mutane alheri. A nasu ra’ayin, abin da zai sa su ji daɗin rayuwa ke nan. Amma idan mutum ya zama mutumin kirki, shi ke nan zai more rayuwa? Za a ba da amsar a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba