Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 3 pp. 9-11
  • Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ZAƁIN MUTANE DA YAWA
  • WANE SAKAMAKO AKA SAMU?
  • Kowa Yana So Ya More Rayuwa a Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Yadda Za Ka More Rayuwa a Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Gabatarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • “Masu Tawali’u Za Su Gāji Kasan”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 3 pp. 9-11
Wata mata tana ba wata tsohuwa wurin zama a bas.

Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?

Mutane sun daɗe suna ganin cewa idan mutum yana da halin kirki, zai more rayuwa. Alal misali, mutanen gabas suna daraja abin da wani malamin falsafa mai suna Confucius (551-479 kafin haihuwar Yesu) ya faɗa cewa: “Abin da ba ka so a yi maka, kar ka yi ma wani.”a

ZAƁIN MUTANE DA YAWA

A yau ma, mutane da yawa sun gaskata cewa idan suka zama da halin kirki, za su more rayuwa. Suna iya ƙoƙari su daraja mutane, kuma su zama da hali mai kyau. Ba sa rigima don sun san iyakarsu, kuma ba sa yin abin da zai sa zuciyarsu ta dame su. Wata mata mai suna Linh daga ƙasar Vietnam ta ce: “Na yi imani cewa idan ina yin gaskiya a koyaushe, zan sami albarka.”

Matar har ila tana raba wa talakawa abinci.

Wasu suna ƙoƙarin su dinga yin abu mai kyau don abin da addininsu take koya musu ke nan. Wani mai suna Hsu-Yun da ke zama a ƙasar Taiwan ya ce: “An koya min cewa idan na yi abu mai kyau, zan ji daɗi bayan na mutu. Amma idan ban yi abu mai kyau yanzu ba, in na mutu zan sha azaba.”

WANE SAKAMAKO AKA SAMU?

Matar har ila tana raba wa talakawa abinci.

A gaskiya idan muna wa mutane kirki, za mu amfana a hanyoyi da dama. Amma akwai mutane da yawa a yau da suka yi ƙoƙari su yi wa mutane alheri, sai dai a ƙarshe sun ga cewa wasu ba sa kyautata musu. Wata mai suna Shiu Ping daga Hong Kong ta ce: “Abin da ya faru a rayuwata ya koya min cewa ba a koyaushe yin alheri yake sa mutum ya sami albarka a rayuwa ba. Na yi iya ƙoƙari in kula da iyalina kuma in yi alheri, duk da haka na yi fama da matsaloli a aurena. A ƙarshe, maigidana ya yasar da mu.”

Mutane da yawa kuma sun lura cewa ba dukan masu addini suke da halin kirki ba. Wata mata mai suna Etsuko daga Japan ta ce: “Na shiga wani addini, har na zama mai ja-gorar ayyukan matasa. Amma na yi mamaki sosai da na ga irin lalata da gwagwarmayar neman matsayi da kuma sata kuɗi da suke yi.”

“Na yi iya ƙoƙari in kula da iyalina kuma in yi alheri, duk da haka na yi fama da matsaloli a aurena. A ƙarshe, maigidana ya yasar da mu.”​—SHIU PING, DAGA HONG KONG

Wasu masu bin addini tsakani da Allah sun yi bakin ciki sosai da suka ga cewa munanan abubuwa suna faruwa da su, duk da alherin da suke yi. Abin da ya faru ke nan da wata mai suna Van daga ƙasar Vietnam. Ta ce: “Na yi ta sayan ’ya’yan itace da furanni da abinci ina kai in ajiye ma kakannina da suka mutu. Na yi zaton cewa hakan zai sa rayuwata ta yi albarka. Amma duk da ayyukan kirki da ibada da na yi shekaru da yawa ina yi, maigidana ya kamu da wata muguwar cuta. ’Yata ma da ta je karatu a ƙasar waje ta rasu tana ’yar shekara ashirin.”

ABIN DA YA SA HALIN KIRKI KAWAI BAI ISA BA

Yana da kyau mutum ya zama mai halin kirki, amma hakan ba lallai shi ne zai sa ya more rayuwa a nan gaba ba. Me ya sa muke ce hakan? Ga abin da Nassosi Masu Tsarki suka ce.

BA KOWA BA NE YAKE DA HALIN KIRKI

“Wawa ɗaya yakan lalatar da yawan ayyuka masu kyau.”​—MAI-WA’AZI 9:18.

Ko da kana ƙoƙari ka yi abin da ya dace, abubuwa marasa kyau da wasu suke yi za su iya jefa ka cikin matsala. Alal misali, idan akwai cuta da ke yaɗuwa, hukuma za ta iya cewa mutane su riƙa ba da tazara ko su yi wasu abubuwa don su kāre kansu. Idan kai ka bi shawarar, amma mutanen da ke kewaye da kai sun ƙi bi, halinsu zai iya sa kai da kake kiyayewa ka kamu da cutar.

ABIN DA KAKE GANIN YA DACE MAI YIWUWA BA HAKA BA NE

“A ganin mutum, akwai hanyar da take daidai, amma ƙarshenta mutuwa ce.”​—KARIN MAGANA 14:12.

Akwai mutane da yawa da suka ta yin wasu abubuwa suna ganin abu mai kyau suke yi, amma daga baya sun gano cewa abubuwan nan ba su dace ba. Ko da yake da kyakkyawar niyya suka yi abubuwan nan, sun yi fama da mugun sakamako don abin da suka yi bai dace ba.

BA MU SAN GOBE BA

“Ba ku ma san me zai faru gobe ba.”​—YAKUB 4:14.

Ko da mutum mai kirki ne, zai iya rasa ransa babu zato. Alal misali, akwai mutane da yawa da suka rasu garin taimaka ma waɗanda suke fama da cutar korona. Akwai wata mata kuma mai suna Liting daga ƙasar China da ta rasa mahaifinta sanadiyyar hatsarin mota. Ta ce: “Ban taɓa tsammanin irin wannan mugun abu zai sami mutum mai kirki haka ba. Mahaifina ba rago ba ne, yana da sauƙin kai kuma yana yin gaskiya. Sai ga shi, shi ne kaɗai ya rasu a hatsarin.”

Idan zama mai kirki ba zai iya ba mutum tabbaci cewa zai ji daɗin rayuwa ba, to mene ne zai yi hakan? Don mu sami amsar, muna bukatar shawara daga wurin wani mai hikima, wanda zai gaya mana abin da ya sa rayuwa ta zama yadda take a yau, da kuma abin da za mu yi don mu more rayuwa a nan gaba. A ina za mu samu irin wannan shawarar?

a Don ka sami ƙarin bayani a kan koyarwar Confucius, ka duba littafin nan Mankind’s Search for God babi na 7, sakin layi na 31-35, Shaidun Jehobah ne suka wallafa littafin kuma za ka iya samunsa a dandalinmu na www.pr418.com.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba