Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Tarihi na Biyu
SULEMANU ne sarkin Isra’ila sa’ad da aka soma rubuta littafin Tarihi na Biyu na Littafi Mai Tsarki. An kammala littafin ne da waɗannan kalaman na Sarkin Farisa Sairus ga Yahudawan da ke zaman bauta a Babila: “[Jehobah] ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda ke na mutanensa da ke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.” (2 Tarihi 36:23) Ezra firist ne ya kammala littafin a shekara ta 460 K.Z., littafin ya ba da tarihin shekara 500, wato daga shekara ta 1037 K.Z., zuwa 537 K.Z.
Umurnin da Sairus ya bayar ya ba Yahudawa damar komawa Urushalima don su sake kafa bauta ga Jehobah. Daɗewar da suka yi a zaman bauta a Babila ya shafe su sosai. Yahudawan da suka koma daga bauta ba su san tarihin ƙasarsu ba. Littafin Tarihi na Biyu ya ba su labarin abubuwan da suka auku a lokacin sarakunan Isra’ila. Labarin yana da muhimmanci a gare mu domin ya taƙaita albarkar da ake samu idan aka yi biyayya ga Allah na gaskiya da kuma sakamakon rashin yi masa biyayya.
SARKI YA GINA WA JEHOBAH GIDA
(2 Tarihi 1:1–9:31)
Jehobah ya ba Sarki Sulemanu abin da ya roƙa, wato, hikima da fahimi, tare da arziki da ɗaukaka. Sarkin ya gina wa Jehobah gida mai martaba a Urushalima, kuma mutanen “suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu.” (2 Tarihi 7:10) Kuma Sulemanu “ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.”—2 Tarihi 9:22.
Bayan ya yi sarauta na shekara 40 a Isra’ila, Sulemanu ‘ya rasu aka binne shi tare da kakanninsa, kuma Rehobowam ɗansa shi ya gāje shi.’ (2 Tarihi 9:31) Ezra bai rubuta game da yadda Sulemanu ya bar bauta ta gaskiya ba. Kurakuran sarkin da aka ambata kawai sune yadda ya tara dawakai daga ƙasar Masar da kuma ɗiyar Fir’auna da ya aura. Marubucin ya rubuta labarai masu kyau ne kawai.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:14—Me ya sa zuriyar maƙerin da aka kwatanta a nan ya bambanta da wanda yake 1 Sarakuna 7:14? Littafin Sarakuna na Ɗaya ya kira mahaifiyar masassaƙin “wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu” domin ta auri ɗan kabilar. Amma ainihi, ita ’yar kabilar Dan ce. Bayan mutuwar mijinta, ta auri mutumin Taya kuma ta haifar masa maƙerin.
2:18; 8:10—Waɗannan ayoyin sun ambata cewa adadin shugabanni da suke lura da aikin da ake yi 3,600 ne da kuma 250, amma in ji 1 Sarakuna 5:16; 9:23, su 3,300 ne da kuma 550. Me ya sa adadin suka bambanta? Kamar an sami bambancin ne domin yadda aka rarraba shugabannin. Wataƙila littafin Tarihi na Biyu ya bambanta shugabanni 3,600 waɗanda ba Isra’ilawa ba ne da kuma 250 waɗanda Isra’ilawa ne, kuma littafin Sarakuna na Ɗaya ya bambanta shugabanni 3,300 da suke lura da aikin daga manyan shugabanni su 550 masu lura da aiki. Ko da yaya, dukan adadin waɗanda suka yi shugabanci ɗaya ne 3,850.
4:2-4—Me ya sa aka yi amfani da alamar bijimai wajen ginin kwatarniya? A cikin Nassosi, bijimai alama ce ta ƙarfi. (Ezekiyel 1:10; Wahayin Yahaya 4:6, 7) Siffofin bijimai ya dace domin ‘kwatarniyar’ tana bisa bijimai 12 na azurfa, wadda ke da nauyin tan 30. Yin siffofin bijimai domin wannan manufar bai karya doka ta biyu ba, wadda ta hana bauta wa siffofi.—Fitowa 20:4, 5.
4:5—Yaya girman kwatarniyar? Idan aka cika ta, kwatarniyar za ta iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa, ko kuwa galan 17,400. Amma, yawan ruwan da za a iya zubawa a ciki shi ne kashi biyu cikin uku na kwatarniyar. 1 Sarakuna 7:26 ta ce: “Takan ci garwa dubu biyu.”
5:4, 5, 10—Wane kayan ɗaki ne aka ɗauko daga mazauni kuma aka saka cikin haikalin da Sulemanu ya gina? Abin da kawai aka ɗauko daga cikin alfarwar sujada aka saka cikin haikalin Sulemanu shi ne Akwatin Alkawari. Bayan an gama gina haikalin, an ɗauki mazaunin daga Gibeyon kuma an ajiye shi a Urushalima.—2 Tarihi 1:3, 4.
Darussa Dominmu:
1:11, 12. Roƙon da Sulemanu ya yi ya tabbatar wa Jehobah cewa samun hikima da fahimi shi ne muradin sarkin. Addu’armu ga Jehobah na nuna abin da ke zuciyarmu. Hikima ce mu bincika abin da muke roƙo.
6:4. Godiya ga ƙauna ta alheri na Jehobah ya kamata ya motsa mu mu ɗaukaka Jehobah, wato mu ɗaukaka shi cikin ƙauna da godiya.
6:18-21. Ko da yake babu ginin da zai iya ɗaukan Allah, ana bauta wa Jehobah ne a haikalin. A yau, Majami’un Mulki na Shaidun Jehobah sune inda ake bauta ta gaskiya a kowane yanki.
6:19, 22, 32. Jehobah yana sauraron addu’ar kowa, daga sarki har ƙananan mutanen da suke ƙasar, har ma baƙo wanda ya zo gare shi cikin gaskiya.a—Zabura 65:2.
SARAKUNA NA ZURIYAR DAUDA
(2 Tarihi 10:1–36:23)
Haɗaɗɗiyar Masarautar Isra’ila ta rabu gida biyu, wato masarautar ƙabilu goma na arewa da kuma masarautar ƙabilu biyu na Yahuza da Biliyaminu. Firistoci da Lawiyawan Isra’ila sun ɗora amincinsu ga alkawari na Mulki ba ƙabilanci ba, kuma sun goyi bayan ɗan Sulemanu, Rehobowam. Bayan shekara 30 da gama ginin, an sace dukan kayakin da ke cikin haikalin.
Cikin sarakuna 19 da suka yi mulki bayan Rehobowam, 5 sun kasance da aminci, 3 sun fara da aminci amma daga baya suka zama marasa aminci, ɗaya cikinsu ya tuba daga mummunar tafarkin da ya bi. Sauran sarakunan kuwa sun aikata mugunta a gaban Jehobah.b An nanata ayyukan sarakuna biyar da suka dogara da Jehobah. Labaran hidimomin haikalin da Hezekiya ya maido da kuma shirin Idin Ƙetarewa da Yosiya ya yi, babu shakka, sun ƙarfafa Yahudawan da suke son a sake kafa bautar Jehobah a Urushalima.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
13:5—Menene ma’anar furcin nan “alkawarin gishiri”? Domin yadda, gishiri yake kāre abubuwa, gishiri ya zama alamar ƙarƙo ne da kuma abin da ba ya canjawa. Saboda haka, “alkawarin gishiri” na nufin yarjejeniyar da ba ta canjawa.
14:2-5; 15:17—Sarki Asa ya kawar da dukan “masujadan” kuwa? A bayyane yake cewa bai yi haka ba. Wataƙila Asa ya kawar da masujadan da ake bautar ƙarya ne kawai, amma bai kawar da masujada inda mutane suke bauta wa Jehobah ba. Wataƙila kuma, an sake gina masujadan ne a ƙarshen mulkin Asa. Waɗanda ɗansa Yehoshafat ya kawar da su. Hakika, har ma a lokacin sarautar Yehoshafat, ba a kawar da duka masujadan gabaki ɗaya ba.—2 Tarihi 17:5, 6; 20:31-33.
15:9; 34:6—Menene matsayin ƙabilar Saminu sa’ad da masarautar Isra’ila ta rabe biyu? Da yake yawancin gadōnta na cikin yankin Yahuza, ƙabilar Saminu tana cikin ƙasar Yahuza da Biliyaminu. (Joshuwa 19:1) Amma game da addini da siyasa kuwa, ƙabilar tana tare ne da masarauta ta arewa. (1 Sarakuna 11:30-33; 12:20-24) Saboda haka aka haɗa Saminu a masarautar ƙabilu goma na arewa.
16:13, 14—An kona gawar Asa ce? A’a, “babbar wuta [da suka hura] don su darajanta shi,” ba wai yana nufin cewa an ƙona gawar Asa ba ne, amma yana nufin turaren da aka ƙona.
35:3—Daga ina Yosiya ya sa aka ɗauki tsattsarkan Akwati zuwa cikin haikali? Littafi Mai Tsarki bai faɗi ko wani cikin mugayen sarakuna ne ya cire shi ba, ko kuwa Yosiya ne ya sake wa akwatin wuri domin a adana shi saboda gagarumin aiki da ake yi a haikalin. Inda aka yi magana kawai game da Akwatin bayan zamanin Sulemanu shi ne sa’ad da Yosiya ya maido shi cikin haikali.
Darussa Dominmu:
13:13-18; 14:11, 12; 32:9-23. Wannan ya koya mana muhimmancin dogara ga Jehobah!
16:1-5, 7; 18:1-3, 28-32; 21:4-6; 22:10-12; 28:16-22. Yin tarayya da baƙi ko kuwa waɗanda ba masu bi ba ne na kawo sakamako marar kyau. Hikima ce mu ƙi tarayya da duniya.—Yahaya 17:14, 16; Yakubu 4:4.
16:7-12; 26:16-21; 32:25, 26. Fahariya ta sa Sarki Asa ya aikata abin da bai dace ba a ƙarshen rayuwarsa. Fahariya ta kai ga faɗuwar Azariya. Hezekiya ya yi wauta ya kuma nuna fahariya sa’ad da ya nuna wa ’yan saƙon Babila dukiyarsa. (Ishaya 39:1-7) Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa, “girmankai jagora ne zuwa ga halaka, fariya kuwa zuwa ga fāɗuwa.”—Karin Magana 16:18.
16:9. Jehobah yana taimakon waɗanda suka dogara a gare shi da zuciya ɗaya, kuma yana ɗokin yin amfani da ikonsa dominsu.
18:12, 13, 23, 24, 27. Kamar Mikaiya, ya kamata mu kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfin hali a wajen yin magana game da Jehobah da kuma nufe nufensa.
19:1-3. Jehobah yana neman abu mai kyau a gare mu har ma a lokacin da muka ba shi haushi.
20:1-28. Muna da tabbacin cewa Jehobah zai yarda mu same shi idan muka nemi ja-gora a wurinsa cikin tawali’u.—Karin Magana 15:29.
20:17. Domin mu ‘ga nasarar Ubangiji,’ muna bukatar mu “jā daga” ta wajen tallafa wa Mulkin Allah sosai. Maimakon mu ɗauki mataki da kanmu, muna bukatar mu “jā daga” wato, mu dogara ga Jehobah.
24:17-19; 25:14. Bautar gumaka ta zama tarko ga Yowash da kuma ɗansa Amaziya. A yau, bautar gumaka na iya rinjayarmu, musamman idan ta zo a wani fasali na ɓoye, wato, kwaɗayi ko kuwa kishin ƙasa.—Kolosiyawa 3:5; Wahayin Yahaya 13:4.
32:6, 7. Muna bukatar mu kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfin hali yayin da muka “yi ɗamara da dukan makamai na Allah” kuma muka ci gaba da yaƙi na ruhaniya.—Afisawa 6:11-18.
33:2-9, 12, 13, 15, 16. Mutum na nuna tuba ta gaskiya sa’ad da ya guji tafarki marar kyau da yake bi, ya kuma ƙudurta aniya cewa zai ci gaba da yin abin da ke da kyau. Idan da tuba ta gaskiya, har ma mutumin da ya aikata mugunta kamar Sarki Manassa zai iya samun tagomashin Jehobah.
34:1-3. Duk wani yanayi marar kyau na yaranta bai kamata ya hana mu sanin Allah da kuma bauta masa ba. Wataƙila daga wajen kakansa Manassa da ya tuba ne Yosiya ya samu tasiri mai kyau sa’ad da yake ɗan yaro. Ko da wane irin tasiri ne mai kyau Yosiya ya samu, hakan ya kawo sakamako mai kyau. Mu ma muna iya yin haka.
36:15-17. Jehobah yana da haƙuri da tausayi. Amma fa, tausayinsa da kuma haƙurinsa suna da iyaka. Dole ne mutane su saurari aikin wa’azi na Mulki idan za su tsira sa’ad da Jehobah zai kawo ƙarshen wannan mugun zamanin.
36:17, 22, 23. Maganar Jehobah a kowane lokaci tana kasancewa gaskiya.—1 Sarakuna 9:7, 8; Irmiya 25:9-11.
Littafi ya Motsa Shi ya Aikata
“Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama’ar Isra’ila ke da ita, ya sa dukan waɗanda ke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu,” in ji 2 Tarihi 34:33. Menene ya motsa Yosiya ya yi haka? Sa’ad da Shafan magatakarda ya kai wa Sarki Yosiya littafin Shari’ar Jehobah da suka gano, sarkin ya sa a karanta masa littafin. Abin da sarkin ya ji ya motsa shi ya ɗaukaka bauta ta gaskiya a dukan rayuwarsa.
Karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta zai iya shafanmu sosai. Yin bimbini a kan labaran sarakuna ta zuriyar Dauda zai ƙarfafa mu mu bi misalan waɗanda suka dogara ga Jehobah kuma mu guje wa halayen waɗanda suka ƙi yin haka. Littafin Tarihi na Biyu ya motsa mu mu bauta wa Allah shi kaɗai kuma mu kasance da aminci. Hakika, saƙonsa rayayyiya ce kuma mai ƙarfin aiki.—Ibraniyawa 4:12.
[Hasiya]
a Domin tambayoyi game da keɓe haikalin da kuma wasu darussa daga addu’ar Sulemanu a wannan ranar, duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2005, shafuffuka na 28-31 na Turanci.
b Domin samun cikakken jerin sunayen sarakunan Yahuza, duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2005, shafi na 12.
[Hoto a shafi na 28]
Ka san dalilin da ya sa siffar bijimai ya dace da inda kwatarniyar take?
[Hotuna a shafi na 31]
Ko da yake bai sami cikakken taimako ba sa’ad da yake ɗan yaro, Yosiya ya girma kuma ya amince da Jehobah