Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 5/1 pp. 17-21
  • Makiyaya Waɗanda “Gurbi Ne Ga Garken”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Makiyaya Waɗanda “Gurbi Ne Ga Garken”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Ƙaunaci Garken da Kowace Tunkiya
  • Ku Ƙarfafa Farin Ciki da Kuma Salama ta Wajen Sadarwa
  • Ku Kasance Masu Tsawon Jimrewa da Kuma Alheri
  • Bangaskiya ce Ke Motsa Ayyuka Masu Kyau
  • Tawali’u na Bukatar Kamewa
  • Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 5/1 pp. 17-21

Makiyaya Waɗanda “Gurbi Ne Ga Garken”

“Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku . . . , da yardan rai . . . , kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.”—1 BITRUS 5:2, 3.

1, 2. (a) Wane gata ne Yesu ya ɗanka wa manzo Bitrus, me ya sa tabbacin Yesu ba kuskure ba ne? (b) Yaya Jehobah yake ji game da makiyaya da aka naɗa?

KAFIN Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Bitrus da almajirai shida suna karya kumallo da Yesu ya shirya a bakin Tekun Galili. Wannan ba lokaci ba ne na farko da Bitrus ya ga Yesu da aka ta da daga matattu, kuma babu shakka yana farin ciki cewa Yesu yana da rai. Amma mai yiwuwa Bitrus ya damu. Dalilin shi ne, ’yan kwanaki da suka shige, ya yi musun sanin Yesu a fili. (Luka 22:55-60; 24:34; Yohanna 18:25-27; 21:1-14) Yesu ya tsauta wa Bitrus da ya tuba don rashin bangaskiyarsa ne? A’a. Maimakon haka, Yesu ya ɗanka wa Bitrus gatar ciyar da kuma kiwon ‘tumakinsa.’ (Yohanna 21:15-17) Yadda labarin Littafi Mai Tsarki ya nuna game da tarihin ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko, Yesu bai yi kuskure ba da ya amince da Bitrus. Tare da sauran manzanni da dattawa a Urushalima, Bitrus ya yi kiwon ikilisiyar Kirista a lokacin gwaji mai tsanani da kuma samun ƙaruwa.—Ayukan Manzanni 1:15-26; 2:14; 15:6-9.

2 A yau ta wurin Yesu Kristi, Jehobah ya naɗa mutane da suka cancanci su yi hidimar makiyaya na ruhaniya don su ja-goranci tumakinsa a miyagun zamani na tarihin ’yan adam. (Afisawa 4:11, 12; 2 Timothawus 3:1) Kuskure ne a tabbata da irin waɗannan mazaje? Salama na ’yan’uwanci na Kirista a dukan duniya ya nuna cewa daidai ne a tabbata da su. Hakika, waɗannan makiyaya suna kuskure, yadda Bitrus ya yi. (Galatiyawa 2:11-14; Yaƙub 3:2) Duk da haka, Jehobah ya amince cewa za su kula da tumaki da “ya sayi da jinin [Ɗansa].” (Ayukan Manzanni 20:28) Jehobah yana ƙaunar waɗannan maza sosai, yana ɗaukansu da “bangirma ninki biyu.”—1 Timothawus 5:17.

3. Ta yaya makiyaya na ruhaniya suka kasance da halin son rai?

3 Ta yaya makiyaya na ruhaniya suka kasance da halin son taimako, kuma suka zama misalai ga garken? Kamar Bitrus da wasu makiyaya na ƙarni na farko, dattawa suna dogara ga ruhu mai tsarki na Allah, wanda ke ba su ƙarfi da suke bukata domin su cika hakkinsu. (2 Korinthiyawa 4:7) Ruhu mai tsarki na sa su nuna ’yar ruhu kamar, ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, da kamewa. (Galatiyawa 5:22, 23) Bari mu tattauna ainihin wurare da makiyaya za su nuna misali wajen nuna wannan ’yar ruhu yayin da suke kiwon garken da Allah ya ce su kula da su.

Ku Ƙaunaci Garken da Kowace Tunkiya

4, 5. (a) Ta yaya Jehobah da Yesu suke nuna ƙauna ga garken? (b) A waɗanne hanyoyi ne makiyaya na ruhaniya suke nuna ƙauna ga garken?

4 Ƙauna ce hali mafi muhimmanci da ruhun Allah yake sa mu kasance da shi. Jehobah yana nuna ƙaunarsa ga dukan garken sa’ad da yake ba su abinci na ruhaniya a yalwace. (Ishaya 65:13, 14; Matta 24:45-47) Amma ba abinci kawai yake ba su ba. Yana ƙaunar kowace tunkiya. (1 Bitrus 5:6, 7) Yesu ma yana ƙaunar garken. Ya ba da ransa dominsu, kuma ya san kowane da “sunansa.”—Yohanna 10:3, 14-16.

5 Makiyaya na ruhaniya suna koyi da Jehobah da Yesu. Suna nuna ƙauna ga dukan garken Allah ta wajen mai da hankali ga ‘koyar da’ ikilisiya. Jawabansu da ke bisa Littafi Mai Tsarki na taimako wajen ciyar da kuma kāre garken, kuma kowa na ganin aiki tuƙuru da suke yi. (1 Timothawus 4:13, 16) Ba a sanin lokacin da suke ba da wajen adana fayil na ikilisiya, rubuta wasiƙu, yin tsarin ayyuka da kuma kula da wasu abubuwa domin a tabbata cewa an yi taron ikilisiya da wasu ayyuka “da hankali bisa ga ƙa’ida kuma.” (1 Korinthiyawa 14:40) Yawancin mutanen ikilisiya ba sa ganin lokacin da ake waɗannan ayyuka kuma wataƙila ba sa cika sanin amfanin. Ayyuka ne da ake yi bisa ƙauna.—Galatiyawa 5:13.

6, 7. (a) Wace hanya ɗaya ce makiyaya za su san tumakin sosai? (b) Me ya sa wani lokaci yake da kyau mu gaya wa dattijo yadda muke ji?

6 Makiyaya na Kirista suna ƙoƙari su kula da kowane mutum cikin ikilisiya. (Filibbiyawa 2:4) Hanya ɗaya da makiyaya suke sanin kowane mutum sosai ita ce ta zuwan aikin wa’azi tare da su. Sau da yawa Yesu yana aikin wa’azi da mabiyansa kuma ya yi amfani da wannan lokacin ya ƙarfafa su. (Luka 8:1) Wani makiyayi Kirista da ya ƙware ya ce: “Na ga cewa hanya ɗaya mafi kyau da za a san ɗan’uwa ko ’yar’uwa kuma a ƙarfafa su ita ce ta fita hidimar fage da shi ko da ita.” Idan kwanan nan ba ka da zarafin fita wa’azi da ɗaya cikin dattawa, ka yi shirin yin hakan nan da nan.

7 Ƙauna ta motsa Yesu ya yi farin ciki da kuma baƙin ciki tare da mabiyansa. Alal misali, sa’ad da almajiransa 70 suka dawo daga aikin wa’azi suna farin ciki, Yesu “ya yi murna.” (Luka 10:17-21) Amma, sa’ad da ya ga yadda mutuwar Li’azaru ta shafi Maryamu da iyalinta da abokai, “Yesu ya yi kuka.” (Yohanna 11:33-35) Haka nan ma, makiyaya masu kula a yau suna damuwa da yadda tumakin suke ji. Ƙauna na motsa su su “yi farinzuciya tare da waɗanda ke farinzuciya” kuma su “yi kuka tare da masu-kuka.” (Romawa 12:15) Idan kana farin ciki ko baƙin ciki a rayuwarka, ka gaya wa makiyaya na Kirista yadda kake ji. Jin game da farin cikinka zai ƙarfafa su. (Romawa 1:11, 12) Sanin gwajin da kake fuskanta zai taimake su su ƙarfafa ka.—1 Tassalunikawa 1:6; 3:1-3.

8, 9. (a) Ta yaya wani dattijo ya nuna ƙauna ga matarsa? (b) Yaya muhimmancin makiyayi ya nuna ƙauna ga iyalinsa?

8 Ana ganin ƙaunar makiyayin ga garken a hanyar da yake bi da nasa iyalin. (1 Timothawus 3:1, 4) Idan yana da aure, yadda yake ƙauna da kuma daraja matarsa na kafa wa magidanta misali da za su yi koyi da shi. (Afisawa 5:25; 1 Bitrus 3:7) Ga abin da wata mata Kirista mai suna Linda ta faɗa. Mijinta ya yi hidima na mai kula fiye da shekara 20 kafin ya mutu. Ta ce: “Koyaushe mijina na taƙurewa wajen kula da ikilisiya. Amma ya sa na ji muna yi tare ne. Sau da yawa yana furta godiya da yadda nake tallafa masa, kuma muna zama tare mu shaƙata lokacin da ba ya aiki. Saboda haka, na ji ana ƙaunata kuma ba na jin haushi don lokacin da yake bayarwa wajen kula da ikilisiya.”

9 Idan makiyayi Kirista yana da yara, yadda yake horonsu cikin ƙauna da kuma yaba musu a kai a kai na kafa wa wasu iyaye misali da za su bi. (Afisawa 6:4) Hakika, ƙauna da yake nuna wa iyalinsa na ba da tabbaci cewa yana aikata daidai da abin da aka ɗanka masa ta wajen naɗa shi da ruhu mai tsarki.—1 Timothawus 3:4, 5.

Ku Ƙarfafa Farin Ciki da Kuma Salama ta Wajen Sadarwa

10. (a) Menene zai iya hana farin ciki da salama a cikin ikilisiya? (b) Wane batu ne yake son ya yi wa salama na ikilisiya na ƙarni na farko barazana, yaya aka warware wannan batun?

10 Ruhu mai tsarki zai iya sa zuciyar kowane Kirista ta kasance da farin ciki da kuma salama, tsakanin rukunin dattawa, da kuma cikin ikilisiya. Amma rashin sadarwa zai sa kada a kasance da farin ciki da salama. Sulemanu na dā ya lura: “Wurinda babu shawara, nufe nufe su kan warware.” (Misalai 15:22) A wata sassa kuma, sadarwa da aka yi da ladabi na kawo farin ciki da salama. Alal misali, sa’ad da batun kaciya yake son ya hana salama na ikilisiya na ƙarni na farko, hukumar mulki a Urushalima ta nemi ja-gorar ruhu mai tsarki. Sun furta ra’ayinsu dabam dabam game da batun. Bayan muhawwara mai kyau, suka tsai da shawara. Sa’ad da suka gaya wa ikilisiyoyin shawararsu, ’yan’uwan suka “yi murna saboda wannan gargaɗi.” (Ayukan Manzanni 15:6-23, 25, 31; 16:4, 5) Aka ƙarfafa farin ciki da salama.

11. Ta yaya dattawa za su ƙarfafa farin ciki da salama cikin ikilisiya?

11 Hakanan ma a yau, makiyaya suna ƙarfafa farin ciki da salama ta wajen sadarwa da waɗanda suke cikin ikilisiya da kyau. Sa’ad da matsaloli suke son su hana ikilisiya ta kasance da salama, suna taruwa kuma su faɗi ra’ayoyinsu. Suna sauraron kalaman ’yan’uwansu makiyaya cikin ladabi. (Misalai 13:10; 18:13) Bayan sun yi addu’a don ruhu mai tsarki, suna tsai da shawararsu bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma ja-gora da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya ba da cikin littattafansa. (Matta 24:45-47; 1 Korinthiyawa 4:6) Muddin rukunin dattawan sun tsai da shawara bisa Nassi, kowane dattijo yana bin ja-gorar ruhu mai tsarki ta wajen tallafa wa wannan shawara ko idan yawanci ba su yarda da ra’ayinsa ba. Irin wannan halin filako na kawo farin ciki da salama kuma yana kafa wa tumakin misali mai kyau a yadda za su bi Allah. (Mikah 6:8) Kana haɗa kai kuwa da shawarwari da ke bisa Littafi Mai Tsarki da makiyaya suka tsai da a cikin ikilisiya?

Ku Kasance Masu Tsawon Jimrewa da Kuma Alheri

12. Me ya sa Yesu yake bukatar ya kasance da tsawon jimrewa ya kuma yi alheri a sha’aninsa da manzannin?

12 Yesu ya kasance da tsawon jimrewa a sha’aninsa da manzanninsa, ya kuma yi musu alheri, duk da kasawarsu a kai a kai. Alal misali, a kai a kai Yesu ya yi ƙoƙari ya nanata musu abin da ya sa suke bukatar su kasance da tawali’u. (Matta 18:1-4; 20:25-27) Duk da haka, a daren Yesu na ƙarshe a duniya, bayan ya koya musu darasi na tawali’u ta wajen wanke ƙafafunsu “sai musu ya tashi tsakaninsu a kan kowanene babbansu.” (Luka 22:24; Yohanna 13:1-5) Yesu ya tsauta wa manzannin ne? A’a, ya sa su yi tunani ne, yana cewa: “Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abincin ba ne? Ga shi kuwa, ina cikinku kamar mai hidima.” (Luka 22:27) Daga baya tsawon jimrewa na Yesu da kuma alherinsa tare da misalinsa mai kyau ya motsa zukatan manzannin.

13, 14. Wane lokaci ne musamman makiyaya za su yi kirki?

13 Hakanan ma, makiyayi na ruhaniya yana iya yi wa mutum gargaɗi a kai a kai game da wata kasawa. Makiyayin na iya yin fushi da mutumin. Amma, idan ya tuna da nasa kasawa sa’ad da yake “tsawata wa malalata” zai iya kasance da tsawon jimrewa ya kuma yi wa ɗan’uwansa kirki.Ta yin hakan yana koyi da Yesu da Jehobah waɗanda suka nuna waɗannan halaye ga dukan Kiristoci har da makiyaya.—1 Tassalunikawa 5:14; Yaƙub 2:13.

14 Wani lokaci, makiyaya suna iya yi wa wanda ya yi zunubi mai tsanani gargaɗi sosai. Idan bai tuba ba, dole ne makiyayan su cire mai kuskuren daga cikin ikilisiya. (1 Korinthiyawa 5:11-13) Duk da haka, yadda za su bi da mutumin zai nuna cewa sun tsane zunubin, ba mutumin ba. (Yahuda 23) Idan makiyaya suka kasance da halin kirki zai yi wa ɗan’uwa da ya bijire sauƙi ya dawo garken daga baya.—Luka 15:11-24.

Bangaskiya ce Ke Motsa Ayyuka Masu Kyau

15. Wace hanya ɗaya ce makiyaya suke yin koyi da nagartan Jehobah, kuma menene ke motsa su su yi hakan?

15 “Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane” har da waɗanda ba sa godiya ga abin da yake musu. (Zabura 145:9; Matta 5:45) An fi ganin alherin Jehobah a yadda ya aika mutanensa su yi wa’azin “bishara kuwa ta mulki.” (Matta 24:14) Makiyaya suna nuna alherin Allah ta wajen yin ja-gora a wannan aikin wa’azi. Menene ke motsa su su yi aiki tuƙuru? Bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah da kuma alkawuransa.—Romawa 10:10, 13, 14.

16. Ta yaya makiyaya “suke aika nagarta zuwa ga dukan mutane?”

16 Ban da “aika nagarta zuwa ga dukan mutane” ta wurin wa’azi, makiyaya suna da hakkin aika nagarta musamman ga “waɗanda suke iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Hanya ɗaya da suke yin haka ita ce ta yin ziyara mai ƙarfafawa. Wani dattijo ya ce, “ina jin daɗin ziyarar kiwo, yana ba ni zarafin yaba wa ’yan’uwa don ƙoƙarce-ƙoƙarcensu kuma na taimake su su san cewa ana daraja aikinsu tuƙuru.” Wani lokaci, makiyaya na iya faɗan hanyoyi da mutum zai iya kyautata hidimarsa ga Jehobah. Ta yin haka, makiyaya masu hikima suna yin koyi da manzo Bulus. Ka yi la’akari da yadda ya yi wa ’yan’uwa a Tassalunika magana: “Muna kuwa amincewa ga Ubangiji a kanku, kuna yin abin da mu ke umurtanku, za ku yi kuma.” (2 Tassalunikawa 3:4) Irin wannan furci na tabbaci na motsa nufi mai kyau na tumakin kuma ya kasance da sauƙi su “yi biyayya da waɗanda ke shugabannan[s]u.” (Ibraniyawa 13:17) Idan an yi maka ziyara mai ƙarfafawa, ka yi godiya don irin wannan ziyara.

Tawali’u na Bukatar Kamewa

17. Wane darasi ne Bitrus ya koya daga Yesu?

17 Yesu mai tawali’u ne, har lokacin da aka ba shi haushi. (Matta 11:29) Sa’ad da aka ci amanarsa kuma aka kama shi, Yesu ya nuna tawali’u da kuma kamewa sosai. Bitrus mai aikata abu bisa motsin rai ya jawo takobi kuma ya rama. Amma Yesu ya tuna masa: “[Kana] tsammani ba ni da iko in roƙi Ubana, ko yanzu ma shi aiko mini rundunan mala’iku ya fi goma sha biyu?” (Matta 26:51-53; Yohanna 18:10) Bitrus ya koyi darasi mai kyau lokacin kuma daga baya ya tuna wa Kiristoci: “Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa,. . . sa’anda aka zage shi, ba ya mayarda zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba.”—1 Bitrus 2:21-23.

18, 19. (a) A wane yanayi ne musamman ya kamata makiyaya su nuna tawali’u da kamewa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a gaba?

18 Hakan nan ma, idan makiyaya suna so su yi nasara, dole ne su kasance masu tawali’u ko idan an bi da su yadda bai dace ba. Alal misali, wasu da suke ƙoƙari su taimaka musu a cikin ikilisiya ba za su aikata yadda ya dace ba. Idan mutum da yake bukatar taimako ya raunana ko kuma yana ciwo a ruhaniya, zai iya “magana da garaje kamar sussukan takobi” idan aka yi masa gargaɗi. (Misalai 12:18) Amma kamar Yesu, makiyaya ba sa rama baƙar magana ko kuma su yi ayyuka na ramako. Maimakon haka, suna kame kansu kuma su nuna juyayi, wanda zai iya zama albarka ga wanda yake bukatar taimako. (1 Bitrus 3:8, 9) Kana koyo daga misalin dattawa kuma ka nuna tawali’u da kamewa sa’ad da aka yi maka gargaɗi?

19 Babu shakka, Jehobah da Yesu suna godiya ga aiki tuƙuru da makiyaya dubbai da suke kula da garke a dukan duniya suke yi da son rai. Jehobah da Ɗansa suna kuma ƙaunar bayi masu hidima dubbai waɗanda suke tallafa wa dattawa wajen “yi wa tsarkaka hidima.” (Ibraniyawa 6:10) To, me ya sa wasu ’yan’uwa maza da suka yi baftisma suke jinkirin burin “aiki mai kyau”? (1 Timothawus 3:1) Kuma yaya Jehobah yake koyar da waɗanda ya naɗa makiyaya? Za mu bincika waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• A waɗanne hanyoyi ne makiyaya suke nuna ƙauna ga garken?

• Ta yaya duka a cikin ikilisiya za su ɗaukaka farin ciki da salama?

• Me ya sa makiyaya suke kame kansu kuma su yi kirki sa’ad da suke ba da gargaɗi?

• Ta yaya dattawa suke nuna nagarta da kuma bangaskiya?

[Hoto a shafi na 18]

Ƙauna ce ke motsa dattawa su yi wa ikilisiya hidima

[Hotuna a shafi na 18]

Suna kasancewa tare da iyalansu a wajen nishaɗi . . .

. . da kuma hidima

[Hoto a shafi na 20]

Sadarwa da kyau tsakanin dattawa na kawo farin ciki da salama a cikin ikilisiya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba