Matasa, Ku Zaɓi Ku Bauta Wa Jehobah
“Ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa.”—JOSHUA 24:15.
1, 2. Waɗanne irin baftisma ne marasa kyau aka yi a Kiristendom?
“KU BARI yara su zama Kiristoci sa’ad da suka isa sanin Kristi.” Wani marubuci mai suna Tertullian ne ya rubuta waɗannan kalaman a kusan ƙarshen ƙarni na biyu A.Z. Yana nuna rashin yardarsa a kan yi wa jarirai baftisma, abin da ya fara kahuwa a tsakanin Kiristoci ’yan ridda na zamaninsa. Don nuna rashin jituwa da Tertullian da kuma Littafi Mai Tsarki, Uba na Coci Augustine, ya bayyana cewa baftisma na kawar da zunubi na ainihi, kuma jarirai da suka mutu da ba a yi musu baftisma ba za su shiga wuta. Wannan imanin ya ɗaukaka yi wa jarirai baftisma nan da nan sa’ad da aka haife su.
2 Har yanzu yawancin cocin Kiristendom suna yi wa jarirai baftisma. Bugu da ƙari, duk cikin tarihi, masu sarauta da kuma shugabannin addinai na ƙasashen Kiristoci suna yi wa “arnan” da suka kamo baftisma ta dole. Amma yi wa jarirai baftisma da kuma yi wa manya baftisma ta dole ba sa cikin Littafi Mai Tsarki.
Babu Keɓe Kai Na Dole A Yau
3, 4. Menene zai taimaka wa yaran da iyayensu keɓaɓɓu ne su keɓe kansu da son rai?
3 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana ɗaukan yara ƙanana da tsarki ko da mutum ɗaya kawai cikin iyayensu ne Kirista mai aminci. (1 Korinthiyawa 7:14) Hakan na nufin cewa waɗannan yaran sun zama keɓaɓɓun bayin Jehobah? A’a. Amma yaran da iyayensu sun riga sun keɓe kansu ga Jehobah suna samun koyarwa da za ta iya su keɓe kansu da son rai ga Jehobah. Mai hikima Sarki Sulemanu ya rubuta: “Ɗana ka kiyaye umurnin ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yashe ta: . . . Sa’anda ka ke tafiya, za ta bishe ka: Sa’anda kana kwance, za ta tsare ka: Sa’anda ka falka za ta yi taɗi da kai. Gama umurninsu fitila ne, koyarwarsu kuma haske ce: tsautawar koyarwa tafarkin rai ne.”—Misalai 6:20-23.
4 Ja-gorar iyaye Kiristoci na iya kāre yara idan suka bi ta. Sulemanu ya daɗa cewa: “Ɗa mai-hikima yana faranta zuciyar ubansa: Amma jahilin ɗa yana nawaita zuciyar uwatasa.” “Ya ɗana, ka ji, ka yi hikima kuma, ka bida zuciyarka a cikin tafarkin.” (Misalai 10:1; 23:19) Hakika, don amfana daga koyarwa na iyaye, ku matasa kuna bukatar ku karɓi shawara, da horo da son rai. Ba a haife ku da hikima ba, amma kuna iya zama masu “hikima” kuma da son rai ku bi “tafarkin rai.”
Menene Gargaɗi?
5. Wace shawara ce Bulus ya ba yara da ubanni?
5 Manzo Bulus ya rubuta: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji: gama wannan daidai ne. Ka girmama ubanka da uwarka (ita ce doka ta fari tare da wa’adi), domin ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan. Ku ubanni kuma, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.”—Afisawa 6:1-4.
6, 7. Menene yin rainon yara cikin “gargaɗin” Jehobah ya ƙunsa, kuma me ya sa hakan baya nufin cewa iyaye suna tilastawa ’ya’yansu?
6 Iyaye Kiristoci suna rinjayar yaransu ne sa’ad da suka raine su “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa”? A’a. Wanene zai iya sūkan iyaye domin sun koya wa yaransu abin da ke da kyau? Ba a sukan waɗanda suke musun wanzuwar Allah domin sun koyar da ’ya’yansu cewa babu Allah. ’Yan Roma Katolika suna ganin cewa hakkinsu ne su koyar da yaransu a cikin imanin Katolika, kuma babu wanda ke sūkarsu domin suna ƙoƙarin yin haka. Hakazalika, kada a sūki Shaidun Jehobah domin suna daidaita hankulan yaransu sa’ad da suke renonsu, don su bi tunanin Jehobah game da gaskiya da mizanai na ɗabi’a.
7 In ji littafin nan Theological Dictionary of the New Testament, kalmar Helenanci ta ainihi da aka fassara ‘gargaɗi’ a Afisawa 6:4 tana nuni ne ga “yadda ake daidaita hankali, gyara abin da ba daidai ba, da kyautata hali na ruhaniya.” Idan yaro ya ƙi koyarwa na iyaye domin matsi na tsara, wato yana son ya yi abin da tsaransa ke yi fa? Wanene za a yi wa zargin matsi, iyayen ko kuwa abokan yaron? Idan abokansa suna matsawa yaron ya sha ƙwaya, ya yi maye, ko kuwa ya yi lalata, ya kamata a suki iyayen domin suna ƙoƙarin su daidaita tunanin yaronsu kuma su taimake shi ko ita ya ko ta gane sakamakon irin wannan mugun hali?
8. Menene ‘tabbatawar’ da Timoti ya yi ta ƙunsa?
8 Manzo Bulus ya rubuta wa matashi Timoti: “Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo, waɗanda ka tabbata da su kuma, ka sani wurin ko waɗannene ka koye su; tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki, waɗanda ke da iko su hikimtadda kai zuwa ceto ta wurin bangaskiya wadda ke cikin Kristi Yesu.” (2 Timothawus 3:14, 15) Tun sa’ad da Timoti yake yaro, uwarsa da kakarsa suka kafa masa tushe mai ƙarfi a bangaskiyarsa ga Allah bisa ga sani na Nassosi Masu Tsarki. (Ayukan Manzanni 16:1; 2 Timothawus 1:5) Daga baya, sa’ad da suka zama Kiristoci, ba su matsa wa Timoti ya gaskata ba, amma ya “tabbata da su” ta wajen rinjaya mai kyau na ilimin Nassi.
Jehobah Ya Gayyace Ka Ka Yi Zaɓe
9. (a) Ta yaya ne Jehobah ya daraja halittunsa, kuma don me? (b) Ta yaya ne Ɗan Allah makaɗaici ya nuna ikonsa na yin zaɓe?
9 Jehobah yana iya halittar mutane kamar ’yar tsana, ya tsara su su yi nufinsa kuma su kasa yin abin da ba ya so. Maimakon haka, ya ba su ikon yin zaɓi. Allahnmu yana son talakawa masu yardan rai. Yana son halittunsa, manya da ƙanana, su bauta masa domin ƙauna. Misali mafi kyau na biyayya ga nufin Allah shi ne Ɗansa makaɗaici, wanda Jehobah ya ce game da shi: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:17) Wannan Ɗan farin ya gaya wa Ubansa: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shariarka tana cikin zuciyata.”—Zabura 40:8; Ibraniyawa 10:9, 10.
10. Menene dalilin bauta wa Jehobah a yadda yake so?
10 Jehobah yana bukatar waɗanda suke bauta masa a ƙarƙashin ja-gorar Ɗansa su nuna irin wannan biyayya na son rai ga nufinsa. A hanyar annabci, mai zabura ya yi waƙa: “Mutanenka suna bada kansu hadaya da yardan rai cikin ranar ikonka: Cikin jamalin tsarki, daga cikin cikin safiya, kana riƙe da raɓar ƙuruciyarka.” (Zabura 110:3) Duka ƙungiyar Jehobah, sashe ta sama da ta duniya, suna aiki ne bisa biyayya ga nufin Allah.
11. Wane zaɓi ne aka sa a gaban matasan waɗanda mahaifansu keɓaɓɓu ne?
11 Saboda haka, ku matasa ya kamata ku fahimci cewa iyayenku ko Kiristoci dattawa da suke ikilisiyarku ba za su matsa muku ku yi baftisma ba. Muradin bautawa Jehobah zai fito ne daga zuciyarku. Joshua ya gaya wa Isra’ilawa: “Ku bauta masa [Jehobah] cikin sahihanci da cikin gaskiya . . . Ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa.” (Joshua 24:14-22) Hakazalika, dole ne ya zama cewa kai da kanka ne ka zaɓi ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka ba da ranka ga yin nufinsa.
Ka Ɗauki Hakkinka
12. (a) Ko da yake iyaye za su iya koyar da yaransu, amma menene ba za su iya yi musu ba? (b) A wane lokaci ne matashi zai ɗauki hakkin zaɓen da ya yi a gaban Jehobah?
12 Lokaci ya yi da amincin iyayenku ba zai kāre ku matasa ba. (1 Korinthiyawa 7:14) Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ga wanda ya san yin nagarta fa, ba ya aika ba, a gareshi zunubi ne.” (Yaƙub 4:17) Iyaye ba za su iya bauta wa Allah don ’ya’yansu ba, haka ma yara ba za su iya bauta wa Allah don iyayensu ba. (Ezekiel 18:20) Sa’ad da matasa suka koya game da Jehobah da nufe-nufensa, kuma sun isa su fahimci abin da suka koya kuma su soma dangantaka da shi, kana ganin Allah ba zai ɗauka cewa sun isa su yanke shawarar su bauta masa ba?
13. Waɗanne tambayoyi ne matasa marasa baftisma za su yi wa kansu?
13 Kai matashi ne marar baftisma wanda iyayenka da suka yi rainonka masu tsoron Allah ne, kana halartan taron Kirista kuma kana saka hannu a wa’azin bisharar Mulki? Idan haka ne, ka tambayi kanka: ‘Me ya sa nike yin wannan abin? Ina zuwa taro da aikin wa’azi ne kawai domin iyaye na suna son in yi haka, ko kuwa domin ina son in farantawa Jehobah rai?’ Ka tabbatar wa kanka abin da “Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma”?—Romawa 12:2.
Me Ya Sa Kake Jinkirin Yin Baftisma?
14. Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa bai kamata a yi jinkirin yin baftisma ba gaira ba dalili?
14 “Me za ya hana a yi mini baftisma?” Mutumin da ya yi wa Filip mai wa’azi wannan tambayar ya koyi cewa Yesu ne Almasihu. Mutumin habashan yana da ilimin Nassosi da ya sa ya fahimci cewa bai kamata ya ɓata lokaci ba wajen bayyana a fili cewa daga wannan lokacin zai bauta wa Jehobah a cikin ikilisiyar Kirista, kuma hakan ya sa shi farin ciki sosai. (Ayukan Manzanni 8:26-39) Hakazalika, wata mace mai suna Lidiya, wadda aka buɗe zuciyarta “ta lura da abin da Bulus yana faɗi,” nan da nan aka yi wa ita da iyalinta “baftisma.” (Ayukan Manzanni 16:14, 15) Haka kuma, yarin da ke Filibi ya saurari Bulus da Sila sa’ad da suka “faɗa masa maganar Allah” kuma “nan da nan aka yi masa baftisma, da dukan waɗanda ke nasa.” (Ayukan Manzanni 16:33) Saboda haka, idan kana da sani na Jehobah da manufofinsa, muraɗin gaskiya na yin nufinsa, da suna mai kyau a cikin ikilisiya kuma kana halartan taro a kai a kai kuma kana saka hannu a wa’azin bishara na Mulki, me zai sa ka dinga jinkirin yin baftisma?—Matta 28:19, 20.
15, 16. (a) Wane irin tunanin da bai da ce ba ne zai iya hana matasa yin baftisma? (b) Ta yaya ne keɓe kai da baftisma za su iya zama kāriya ga matasa?
15 Kana jinkirin ɗaukan wannan muhimmiyar mataki ne domin kana tsoron idan ka yi laifi za ka ɗauki hakkin laifinka? Idan haka ne, yi tunani game da wannan: Za ka ƙi karɓan lasisin tuƙi ne domin kana tsoron cewa wata rana za ka yi haɗari? A’a! Saboda haka, bai kamata ka yi jinkirin yin baftisma ba, idan ka cancanci yin haka. Hakika, za ka motsa ka yi iya ƙoƙarinka ka ƙi abin da ba shi da kyau idan ka keɓe ranka ga Jehobah kuma ka yarda ka yi nufinsa. (Filibbiyawa 4:13) Matasa, don Allah kada ku yi tunanin cewa idan ku ka yi jinkirin yin baftisma za ku iya kauce wa ɗaukan hakkinku. Idan kuka kai shekarar ɗaukan hakki, za ku ba da lissafi ga Jehobah a yadda kuka aikata ko kun yi baftisma ko ba ku yi ba.—Romawa 14:11, 12.
16 Yawancin Shaidu a dukan duniya sun ji cewa yanke shawarar da suka yi na yin baftisma sa’ad da suke matasa ya taimaka musu sosai. Yi la’akari da misalin wani Mashaidi ɗan shekara 23 da ke Yammacin Turai. Ya ce baftisma da ya yi yana ɗan shekara 13 ya motsa shi ya maida hankali kada “sha’awoyin ƙuruciya” su sha kansa. (2 Timothawus 2:22) Tun da farko, ya yanke shawarar zama mai hidima na cikakken lokaci. A yau, yana hidima da farin ciki a wani ofishin reshe na Shaidun Jehobah. Albarka mai yawa na jiran duka matasa, har da kai, da suka zaɓi yi wa Jehobah hidima.
17. A waɗanne hanyoyi ne ya kamata a “fahimci abin da ke nufin Ubangiji”?
17 Keɓewar kai da baftisma sune mafarin rayuwar da za mu yi muna la’akari da nufin Jehobah a dukan ayyukan da za mu yi. Cika keɓewarmu ya kunshi “rifta zarafi.” Ta yaya za mu iya yin haka? Ta wajen ɗaukan lokacin da muke yin amfani da su wajen biɗan abubuwa marar amfani kuma mu yi amfani da su wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki, mu halarci taro a kai a kai, kuma mu saka hannu yadda ya kamata a wa’azin “bishara kuwa ta mulki.” (Afisawa 5:15, 16; Matta 24:14) Keɓe kanmu ga Jehobah da kuma muraɗinmu na yin nufinsa zai shafi duka fasalolin rayuwarmu a hanya mai kyau, da kuma yadda muke hutawa, yadda muke ci da sha, da kuma irin waƙar da muke ji. Me ya sa ba za ka zaɓi irin walawa da za ka dawwama kana mora ba? Dubban Shaidu matasa masu farin ciki za su gaya maka cewa akwai hanyoyi masu kyau da za ka iya samun jin daɗi yayin da kake yin “nufin Ubangiji.”—Afisawa 5:17-19.
“Za Mu Tafi Tare da Ku”
18. Waɗanne tambayoyi ya kamata matasa su yi wa kansu?
18 Daga shekara ta 1513 K.Z., zuwa Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Jehobah yana da mutanen da ya tsara a duniya waɗanda ya zaɓa su bauta masa kuma su zama shaidunsa. (Ishaya 43:12) An haifi Isra’ilawa matasa a cikin wannan al’ummar. Tun Fentakos, Jehobah yana da sabuwar “al’umma” a duniya, wato Isra’ila ta ruhaniya, “jama’a daga cikinsu domin sunansa.” (1 Bitrus 2:9, 10; Ayukan Manzanni 15:14; Galatiyawa 6:16) Manzo Bulus ya faɗi cewa Kristi ya tsabtace wa kansa “jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.” (Titus 2:14) Ku matasa ne za ku yanke wa kanku shawarar inda za a iya samun waɗannan mutanen. Su waye ne a yau “alumma mai-adalci, mai-kiyaye gaskiya,” da suke rayuwa da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki, suke aikata a matsayin amintattun Shaidu ga Jehobah, kuma suke sanar da Mulkinsa wanda shi kaɗai ne begen ’yan adam? (Ishaya 26:2-4) Ka dubi cocin Kiristendom da kuma sauran addinai, kuma ka gwada halinsu da wanda Littafi Mai Tsarki ke bukata daga bayin Allah na gaskiya.
19. Menene miliyoyin mutane a duniya suka gaskata?
19 Miliyoyin mutane a dukan duniya, tare da matasa masu yawa, sun yarda cewa sauran shafaffun Shaidun Jehobah sune wannan “al’umma mai-adalci.” Sun gaya wa Isra’ila ta ruhaniya: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zechariah 8:23) Muna fata da kuma addu’a cewa ku matasa za ku yanke shawarar ku kasance a cikin mutanen Allah, da haka, ku “zaɓi rai,” wato rai madawwami a sabuwar duniya ta Jehobah.—Kubawar Shari’a 30:15-20; 2 Bitrus 3:11-13.
A Maimaitawa
• Menene gargaɗi ya ƙunsa?
• Wace irin hidima ce Jehobah ke so?
• Wane zaɓe ke gaban duka matasa da iyayensu keɓaɓɓu ne?
• Me ya sa bai kamata a dinga jinkirin yin baftisma ba gaira ba dalili ba?
[Hotuna a shafi na 26]
Wanene za ka saurara?
[Hoto a shafi na 28]
Ta yaya ne keɓe kai da baftisma za su iya zama kāriya a gare ka?
[Hoto a shafi na 29]
Me ya hana ka yin baftisma?