Bauta Da Za Ta Amfane Ka
“YA YI mani kyau in kusanci Allah” in ji mai zabura Asaph. Ya yi tunanin yin koyi da waɗanda ba su damu ba game da Allah domin su biɗi rayuwa na holewa. Amma sai Asaph ya yi la’akari da amfanin kusantar Allah kuma ya kammala da cewa ya fi masa kyau ya yi hakan. (Zabura 73:2, 3, 12, 28) Bauta ta gaskiya ta yi maka kyau ne a yau? Ta yaya za ta amfane ka?
Bauta wa Allah na gaskiya zai taimaka maka ka daina rayuwa na son kai. Domin an halicce mu cikin surar “Allah kuwa na ƙauna,” waɗanda suke biɗan nasu bukatu kawai ba za su taɓa farin ciki ba. (2 Korinthiyawa 13:11) Yesu ya koyar da muhimmiyar gaskiya game da halin ’yan adam sa’ad da ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Shi ya sa muke jin daɗi idan muka yi wa abokanmu da iyalinmu abubuwa. Amma za mu fi farin ciki idan muka yi abu domin Allah. Ya cancanci ƙaunarmu fiye da kowa. Mutane da yawa daga dukan yanayin rayuwa sun fahimci cewa bauta wa Allah ta yin abin da ya ce yana gamsarwa ƙwarai.—1 Yohanna 5:3.
Kasancewa da Manufa a Rayuwa
Bauta ta gaskiya tana da kyau domin tana sa ka kasance da manufa a rayuwa. Ka lura da yadda sau da yawa ana kwatanta farin ciki da samun wani abu mai amfani? Yawancin mutane suna da makasudi a rayuwa, wataƙila game da iyalinsu, abokai, kasuwanci, ko kuma nitshaɗi. Domin tsautsayi na rayuwa, waɗannan abubuwa sau da yawa ba sa sa su farin ciki. (Mai-Wa’azi 9:11) Amma, bauta ta gaskiya tana taimaka maka ka samu manufa a rayuwa, wadda za ta ci gaba da sa ka farin ciki ko sa’ad da wasu fasalolin rayuwa ba sa gamsarwa.
Bauta ta gaskiya ta ƙunshi sanin Jehobah da kuma bauta masa cikin aminci. Waɗanda suke bin bauta ta gaskiya suna kusantar Allah. (Mai-Wa’azi 12:13; Yohanna 4:23; Yaƙub 4:8) Kana iya tunanin cewa ba zai yiwu ba ka san Allah da kyau har ya zama abokinka. Ta wurin yin bimbini game da labarin sha’aninsa da mutane da kuma yin la’akari da abubuwan da ya halitta, za ka fahimci fannonin mutuntakarsa. (Romawa 1:20) Ƙari ga haka, ta wurin karanta Kalmar Allah, za ka fahimci abin da ya sa muke duniya, abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, yadda zai kawo ƙarshen wahala, kuma mafi muhimmanci yadda za ka sa hannu wajen cika nufin Allah. (Ishaya 43:10; 1 Korinthiyawa 3:9) Irin wannan fahimin zai motsa ra’ayinka na kasancewa da rai!
Zama Mutumin Kirki
Bauta ta gaskiya tana da kyau domin za ta taimake ka ka zama mutumin kirki. Yayin da kake yin bauta ta gaskiya, za ka koyi halin da zai sa ka yi dangantaka mai kyau da mutane. Za ka koyi halin kirki daga Allah da kuma Ɗansa, za ka riƙa faɗin gaskiya, za ka kuma zama wanda za a iya dogara da shi. (Afisawa 4:20–5:5) Idan ka san Allah da kyau da har ka ƙaunace shi, hakan zai motsa ka ka yi koyi da shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.”—Afisawa 5:1, 2.
Abin farin ciki ne ka kasance cikin mutanen da suke koyi da ƙaunar Allah. Hakika, bauta wa Allah na gaskiya ba abin da za ka yi kai kaɗai ba ne. Yana sa ka yi tarayya da mutane da suke ƙaunar abin da ke daidai da nagari. Hakika, mai yiwuwa ba za ka so addinin da aka tsara ba. Amma, kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, matsalar yawancin addinai ba don an tsara su ba ne, amma matsalar ita ce ba a tsara su ba yadda ya kamata kuma ba su da manufar da ta dace. Addinai da yawa da aka tsara ba sa cim ma manufa ta Kirista. Jehobah ne da kansa ya tsara mutanensa don manufa mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.” (1 Korinthiyawa 14:33) Kamar mutane da yawa, za ka ga cewa yin tarayya da rukunin Kiristoci da aka tsara zai daidaita tunaninka.
Bege don Nan Gaba
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana tsara masu bauta ta gaskiya domin su tsira wa ƙarshen wannan zamani kuma su gaji sabuwar duniya “inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 7:9-17) Bautar da za ta amfane ka za ta sa ka kasance da bege, da yake da muhimmanci don yin farin ciki. Wasu suna sa rai cewa duniya za ta yi kyau nan gaba idan aka sami gwamanati mai kyau, idan sun sami kasuwancin da zai kawo musu kuɗi, idan suna da koshin lafiya da kuma samun gamsuwa bayan sun yi murabus. Amma kaɗan ne cikin waɗannan abubuwa, idan ma akwai, da za su ba da begen farin ciki a nan gaba. A wata sassa kuma, manzo Bulus ya rubuta: “Muna da begenmu a kafe ga Allah mai-rai.”—1 Timothawus 4:10.
Idan ka yi bincike sosai, za ka samu masu bauta ta gaskiya. A duniyar yau da take a rarrabe, ƙauna da haɗin kai sun bambanta Shaidun Jehobah. Sun fito daga kusan kowace al’umma da yanayin rayuwa; duk da haka, suna da haɗin kai don suna ƙaunar juna da Jehobah. (Yohanna 13:35) Suna gayyatarka ka gano abin da suke morewa da kanka. Asaph ya rubuta: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah.”—Zabura 73:28.
[Hoto a shafi na 7]
Za ka iya zama abokin Allah