Ka Nuna Ƙauna Da Daraja Ta Wurin Ƙame Bakinka
“Kowane ɗayanku ya ƙaunaci mata tasa kamar kansa, ita matar kuwa ta ladabta wa mijinta.”—AFISAWA 5:33.
1, 2. Wace tambaya ce mai muhimmanci ya kamata ma’aurata su yi wa kansu kuma me ya sa?
IDAN aka ba ka kyauta mai ɗauke da wannan rubutun: “Ka riƙe a hankali.” Yaya za ka riƙe wannan kyauta? Hakika za ka riƙe ta da hankali don kada ta lalace. Kyautan aure kuma fa?
2 Gwauruwa Naomi ’yar Isra’ila ta ce wa Orpah da Ruth: “Ubangiji shi yarda maku ku sami hutawa, kowace ɗayanku a cikin gidan mijinta.” (Ruth 1:3-9) Game da macen kirki Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gida da dukiya gādo ne daga wurin ubanni: amma mata mai-hankali daga wurin Ubangiji ce.” (Misalai 19:14) Idan kana da aure, ya kamata ka ɗauki matarka tamkar kyauta ce daga wurin Allah. Yaya ka ke riƙe kyautar da Allah ya ba ka?
3. Wane gargaɗi ne Bulus ya bayar da ya kamata mata da miji su yi amfani da shi?
3 Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci na ƙarni na farko, ya ce musu: “Kowane ɗayanku ya ƙaunaci mata tasa kamar kansa, ita matar kuwa ta ladabta wa mijinta.” (Afisawa 5:33) Ka yi la’akari da yadda mata da miji za su yi amfani da wannan gargaɗi ta wurin kame bakinsu.
Ka Mai da Hankali da “Mugunta”
4. Ta yaya ne magana za ta iya zama mai kyau ko marar kyau?
4 Yakubu marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce harshe abu ne mai “mugunta” kuma ‘cike yake da guba mai matarwa.’ (Yaƙub 3:8) Yakubu ya fahimci wannan gaskiya cewa: Harshe mai mugunta yana ɓarna. Babu shakka, ya fahimci yadda Littafin Misalai ya kwatanta magana da garaje da “sussukan takobi.” Akasarin haka, misalai ya ce: “Harshen mai-hikima lafiya ne.” (Misalai 12:18) Hakika, kalamai suna da ƙarfi. Za su iya ɓata wa mutum rai ko kuma su ƙarfafa shi. Wane amfani ne kalamanka suke da shi ga matarka? Idan ka yi wa matarka ko ki ka yi wa mijinki wannan tambayar, yaya kowannenku zai amsa?
5, 6. Me ya sa zai yi wa wasu wuya su kame bakinsu?
5 Idan magana ta ɓacin rai ta shiga tsakaninku, za ku iya sake yanayin ya zama da alheri. Hakika, zai yiwu idan kun ba da ƙwazo. Me ya sa? Domin mu ajizai ne. Ajizanci da muka gāda yana shafan tunaninmu da kuma yadda muke yi wa juna magana. Yaƙub ya ce: “Idan wani ba ya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne, mai-ikon sarrafa dukan jiki kuma.”—Yaƙub 3:2.
6 Ban da ajizancin mutane, irin iyalin da mutum ya yi girma a ciki yana shafan yadda yake magana. Wasu mutane sun yi girma a iyalai “masu-baƙar zuciya, . . . marasa-kamewa, masu-zafin hali.” (2 Timothawus 3:1-3) Sau da yawa, yaran da suka yi girma a cikin irin waɗannan iyalai suna nuna wannan hali idan sun manyanta. Hakika, ajizanci ko kuma yadda aka yi renon mutum ba hujja ba ne na yin baƙar magana. Idan muka fahimci haka, za su taimake mu mu fahimci abin da ya sa zai yi wa wasu wuya su kame bakinsu.
‘Ku Tuɓe Mugun Zance’
7. Menene Bitrus yake nufi sa’ad da ya aririci Kiristoci su “tuɓe . . . dukan mugun zance”?
7 Ko menene dalilin, yin muguwar magana tsakanin ma’aurata zai nuna cewa ba sa ƙauna da kuma daraja junansu. Don haka ne Bitrus ya aririce Kiristoci su “Tuɓe . . . dukan mugun zance.” (1 Bitrus 2:1) Kalmar Helenancin da aka fassara ta “mugun zance” tana nufin “baƙar magana.” Wadda ke nufin ‘yi wa mutane baƙar magana.’ Hakika, wannan ya kwatanta abin da muguwar magana take nufi.
8, 9. Menene zai faru idan mutum bai kame bakinsa ba, kuma me ya sa ya kamata ma’aurata su kauce wa yin haka?
8 Mai yiwuwa baƙar maganar ba za ta kasance gaskiya ba, amma ka yi la’akari da abin da zai faru idan miji ko mata ta ko ya yi wa ɗaya baƙar magana. Sa’ad da ya ce wa matarsa wawa, mai ƙin wuya, ko kuma ta ce masa mai son kai, irin waɗannan kalaman suna nuna wulakanci tsakanin ma’aurata! Hakika wannan zalunci ne. Idan kana ambata kurakuran matarka fa? Ba zai yi daidai ba ka ce “Kin ko ka cika makara” ko kuma “Ba ki ko ba ka taɓa saurara na ba.” Irin wannan furcin zai kawo ɓacin rai, wanda zai iya kai wa ga hargitsi.—Yaƙub 3:5.
9 Maganar da aka haɗa ta da baƙar magana za ta jawo damuwa, har ta kai ga matsala a cikin aure. Misalai 25:24 ta ce: “Gwamma a zauna cikin saƙo a kan bene, da a zauna cikin gida mai-yalwa tare da mace mai-tankiya.” Hakika, haka yake da miji mai-tankiya. A kwana a tashi, idan ma’aurata suka ci gaba da yin baƙar magana ga juna hakan za ta rushe dangantakarsu kuma za ta sa matar ko mijin ya ji ko ta ji ba a ƙaunarta ko kuma ma ba ta cancanci ƙauna ba. Babu shakka, yana da muhimmanci mu kame bakinmu. Amma ta yaya za mu yi haka?
‘Ka Kame Harshenka’
10. Me ya sa zai yi kyau mu kame harshenmu?
10 Yaƙub ya ce: “Amma harshe, babu mutum wanda ya ke da iko ya hore shi.” Duk da haka, kamar yadda mai hawan doki yake amfani da linzami ya sarrafa yadda dabbar take tafiya, ya kamata mu yi ƙoƙari mu kame harshenmu. “Idan kowane mutum yana aza kansa mai-addini ne, shi kuwa ba ya kame harshensa ba amma yana yaudara zuciyatasa, addinin wannan banza ne.” (Yaƙub 1:26; 3:2, 3) Waɗannan kalamai suna nuna cewa yadda ka ke amfani da harshenka, batu ne mai tsanani. Saboda wannan zai shafi dangantakarka da abokiyar aurenka, kuma musamman ma dangantakarka da Jehobah.—1 Bitrus 3:7.
11. Ta yaya ne mutum zai iya hana matsala ta kai ga hargitsi?
11 Idan ka kula da yadda ka ke yi wa matarka magana zai nuna kai mutum ne mai hikima. Idan matsala ta taso, ka yi ƙoƙari ka sasanta. Yi la’akari da abin da Farawa 27: 46–28:4 suka ce game da abin da ya faru a rayuwan Ishaƙu da matarsa Rifkatu. “Rifkatu ta ce ma Ishaƙu, na gaji da raina saboda ’yan mata na Heth: idan fa Yaƙubu ya yi aure cikin ’yan mata na Heth, irin waɗannan, ’yan mata na wannan ƙasa, me raina ya daɗa mini?” Babu alamar da ya nuna cewa Ishaku ya amsa mata da tsawa. Maimakon haka, Ishaku ya aiki ɗansu Yakubu ya je ya nemi mace mai tsoron Allah wadda za ta sa Rifkatu farin ciki. Idan saɓani ta taso tsakanin mata da miji, kada ka ce ke ce ki ka fara ko kai ne ka fara, saboda idan ka ce haka zai kawo saɓani da zai kai ga hargitsi. Misali, maimakon ki ce, “ba ka taɓa zama da ni ba!” zai fi kyau idan ki ka ce, “zan yi farin ciki idan muka ƙara ba wa junanmu lokaci mu zauna tare.” Ku mai da hankali ga matsalar maimakon mutumin da ya yi maganar. Ku guji neman mai gaskiya da marar gaskiya. Romawa 14:19 ta ce: “Mu bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama, da abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.”
Ka Kawar da ‘Ɗacin Zuciya, Hasala, da Fushi’
12. Idan muna son mu kame harshenmu, a kan me ya kamata mu yi addu’a, kuma me ya sa?
12 Hakika, kame harshe ba shi ne zai hana mu faɗin abin da muke so ba. Saboda, abin da ke fita daga bakinmu abu ne da muka yi tunani kafin mu faɗe sa. Yesu ya ce: “Mutum nagari daga cikin ajiya mai-kyau ta zuciyatasa ya kan fito da abin da ke mai-kyau; mugu kuwa daga cikin mugunyar ajiyatasa ya kan fito da abin da ke mugu: gama daga cikin yalwar zuciya bakinsa yake zance.” ( Luka 6:45) Saboda haka, idan kana so ka kame harshenka, sai ka yi addu’a kamar yadda Dauda ya yi: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina.”—Zabura 51:10.
13. Ta yaya ne ɗacin zuciya, da hasala, da fushi za su kai ga yin baƙar magana?
13 Bulus ya aririci Afisawa su kawar da baƙar magana da kuma abin da zai sa mutum ya ambaci waɗannan kalaman. Ya rubuta: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku, tare da dukan ƙeta.” (Afisawa 4:31) Ka lura cewa kafin ya ambaci “hargowa, da zage-zage,” Bulus ya ambaci “ɗacin zuciya, da hasala, da fushi.” Hakika, fushi ne ke jawo baƙar magana. Ka tambayi kanka: ‘Ina riƙe ɓacin zuciya da kuma fushi a cikin zuciyata? Ina da ‘saurin fushi’?’ (Misalai 29:22) Idan haka yake a gare ka, ka roƙi Allah ya taimake ka ka kawar da wannan hali kuma ka kame kanka don ka kauce wa yin saurin fushi. Zabura 4:4 ta ce: “Ku ji tsoro, kada kuwa ku yi zunubi: ku yi shawara da zuciyarku a bisa shimfiɗarku, ku yi shuru.” Idan an ɓata maka rai kuma ka ga ba za ka iya kame harshenka ba, ka bi gargaɗin da ke cikin Zabura 17:14: “Daina muhawwara, tun ba ta zama faɗa ba.” Ba tare da ɓata lokaci ba, ka kauce a wurin har sai zuciya ta huce.
14. Ta yaya ne nukura take shafan aure?
14 Ba shi da sauƙi mutum ya kauce wa fushi da hasala, musamman idan sun soma da abin da Bulus ya ƙira “ɗacin zuciya.” Kalmar Helenanci da Bulus ya yi amfani da ita tana nufin “fushin da ke sa mutum ya ƙi sasantawa” kuma ‘ƙeta ce da ba ta mance kuskuren da aka yi ba. A wani lokaci nukura takan sa mahani tsakanin mata da miji, wanda zai ci gaba har na tsawon lokaci. Wannan kuwa zai kawo ƙiyayya idan ba a sasanta matsalar ba. Amma fusata domin abin da ya riga ya wuce banza ne. Saboda ba za a iya sake abin da ya faru ba. Shi ya sa idan har ka gafarta wa wanda ya yi maka laifi, zai fi kyau ka mance da kome. Saboda ƙauna “ba ta yin nukura.”—1 Korinthiyawa 13:4, 5.
15. Menene zai taimakawa waɗanda suka saba yin baƙar magana su sake yadda suke magana?
15 Idan ka girma a cikin iyalin da aka saba yin baƙar magana fa? Za ka iya sake hali. Akwai wasu halaye a rayuwarka da ka riga ka ƙuduri aniyar ba za ka taɓa komawa gare su ba. A waɗanne wurare ne za ka kafa iyaka ga maganar da ke fita daga bakinka? Za ka iya daina magana kafin maganarka ta zama baƙar magana? Za ka so ka yi amfani da abin da Afisawa 4:29 ta ce: “Kada kowanne ruɓaɓɓen zance shi fita daga cikin bakinku.” Kana bukatar ka ‘tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa, ka yafa kuma sabon mutum, wanda a ke sabonta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa.’—Kolossiyawa 3:9, 10.
“Shawara” Tana da Muhimmanci
16. Me ya sa rashin yin magana yakan sa abokan aure su yi sanyin gwiwa?
16 Idan mata da miji suka daina yin magana da juna saboda sun yi fushi, wannan zai lalata dangantakarsu ne maimakon ya shirya su. Wannan ba zai yi wa ɗaya daga cikinsu horo ba, maimakon haka zai iya sa sanyin gwiwa. Kuma rashin magana da juna zai ƙara lalata abubuwa ne maimakon ya yi gyara. Kamar yadda wata mata ta ce, “da zarar mun fara magana kuma, ba za mu yi magana a kan matsalar ba.”
17. Me ya kamata Kiristoci da suke fuskantar matsala a cikin aurensu su yi?
17 Idan matsala a cikin aure ta ci gaba, ba shi da sauƙi. Misalai 15:22 ta ce: “Wurinda babu shawara, nufe nufe su kan warware: Amma cikin taron masu-shawara su kan tabbata.” Ya kamata ku zauna tare ku tattauna matsalar. Saboda haka, ku saurari abokan aurenku da zuciya ɗaya. Idan zai yiwu, ku yi magana da dattawa na cikin ikilisiyar Kirista. Suna da ilimi na Nassosi kuma sun saba da yin amfani da ƙa’idodi daga Littafi Mai Tsarki. Waɗannan mutane za su “zama kamar maɓoya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa.”—Ishaya 32:2.
Za Ka Iya Cin Nasara
18. Wace ɗawainiya ce aka kwatanta a Romawa 7:18-23?
18 Kame harshenmu sai da ɗawainiya. Haka nan ayyukanmu. Manzo Bulus ya kwatanta ƙalubalan da ya fuskanta sa’ad da ya ce: “Na sani a cikina, watau, cikin jikina, ba wani abin kirki ke zaune ba: gama nufi yana gareni, amma aika nagarta ba shi gareni ba. Gama nagarta da ni ke so in yi, ba na aikawa ba: amma mugunta da ba na so ba, ita ni ke aikawa. Amma idan abin da ba ni so, shi ni ke aikawa, ba ni ne mai-aikawa ba, amma zunubi da ke zaune.” Saboda muna ‘ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwanmu,’ shi ya sa muke amfani da harshenmu da kuma wasu gaɓaɓuwan jikinmu a hanyar da ba ta dace ba. (Romawa 7:18-23) Duk da haka, da taimakon Allah za mu kawar da wannan matsalar.
19, 20. Ta yaya ne mata da miji za su yi koyi da Yesu a wajen kame harshensu?
19 Bai kamata ana yin baƙar magana a dangantaka ta ƙauna da daraja ba. Ka yi tunanin gurbin da Yesu Kristi ya kafa. Sa’ad da Yesu ya ke tare da almajiransa, bai taɓa yi musu baƙar magana ba. A daren ƙarshe na rayuwarsa a duniya, sa’ad da manzaninsa suke musu tsakaninsu a kan ko wanene babbansu, Ɗan Allah bai yi musu magana da ɓacin rai ba. (Luka 22:24-27) Littafi Mai Tsarki ya yi wa “mazaje” gargaɗi “ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.”—Afisawa 5:25.
20 Me ya kamata mace ta yi? Ya kamata ta “ladabta wa mijinta.” (Afisawa 5:33, Littafi Mai Tsarki) Mace da take daraja mijinta ba za ta so ta yi masa baƙar magana ba. Bulus ya ce: “Ina so ku sani, kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu kamar yadda Yesu yake yi wa Allah. (Kolossiyawa 3:18) Ko da yake babu wani mutum ajizi da zai iya yin koyi da Yesu daidai, amma idan mata da maza suka yi ƙoƙari su “bi sawunsa” zai taimake su su daina yin amfani da harshensu a hanyar da bai dace ba.—1 Bitrus 2:21.
Menene Ka Koya?
• Ta yaya ne harshe marar kamuwa za ta iya rushe aure?
• Me ya sa harshe na da wuyan kamewa?
• Menene yake taimakonmu mu kame harshenmu?
• Me ya kamata ku yi idan kuna fuskantar matsala a cikin aure?
[Hoto a shafi na 10]
Dattawa suna ba da taimako daga cikin Littafi Mai Tsarki