Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 5/1 pp. 21-25
  • Kada Ka Raba Abin Da Allah Ya Haɗa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Raba Abin Da Allah Ya Haɗa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Magance Matsaloli
  • “Ku Ƙaunaci Matanku”
  • Ta Yaya Za Ka Kula da Matarka?
  • Menene Yake Nufi Ka Yi Tattalin Matarka?
  • Matan da Suke Bin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki
  • Muhimmancin Wa’adi
  • Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Mene ne Zai Sa Ma’aurata Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Magidanta Ku Yi Koyi Da Shugabancin Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 5/1 pp. 21-25

Kada Ka Raba Abin Da Allah Ya Haɗa

“Daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.”—MATTA 19:6.

1, 2. Me ya sa gaskiya ce kuma ya jitu da Nassi a ce ma’aurata za su fuskanci matsaloli a wasu lokatai?

ACE kana shirin yin wata doguwar tafiya da motarka. Kana ganin za ka iya fuskantar matsaloli a kan hanya? Zai zama wawanci idan mutum bai yi tunanin haka ba! Alal misali, kana iya haɗuwa da ruwa da iska, wanda hakan zai sa ka rage gudu kuma ka bi a hankali. A wani wurin kuma, motarka tana iya lalacewa wadda kai da kanka ba za ka iya gyarawa ba, hakan zai sa ka ajiye ta a gefen hanya kuma ka nemi taimako. Ya kamata irin waɗannan yanayin su sa ka kammala cewa ka yi kuskure da ka soma wannan tafiyar kuma hakan zai sa ka ajiye motar ka yi tafiyarka? A’a. Sa’ad da kake doguwar tafiya, za ka sa rai cewa matsaloli na iya faruwa kuma za ka nemi hanyar da ta dace ka magance su.

2 Haka yake da aure. Ba za a iya guje wa matsaloli ba, kuma zai zama wawanci idan waɗanda za su auri juna suka yi tunanin cewa matsala ba za ta taɓa faruwa ba. A 1 Korinthiyawa 7:28, Littafi Mai Tsarki ya faɗi dalla-dalla cewa maza da matansu za su “sha wahala a cikin jiki.” Me ya sa? Domin maza da matan ajizai ne, kuma muna zaune ne a “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1; Romawa 3:23) Saboda haka, har mata da mijin da suka dace da juna sosai kuma masu ruhaniya za su fuskanci matsaloli a wasu lokatai.

3. (a) Menene ra’ayin yawancin mutane a duniya game da aure? (b) Me ya sa Kiristoci suke iya ƙoƙarinsu su riƙe aure?

3 A wannan zamanin sa’ad da wasu ma’aurata suka fuskanci matsaloli, matakin da suke fara ɗaukawa shi ne kashe auren. A ƙasashe da yawa, kashe aure yana ƙaruwa sosai. Amma, Kiristoci na gaskiya suna magance matsaloli ne maimakon su kashe aurensu. Me ya sa? Domin sun ɗauki aure a matsayin kyauta ce mai tsarki daga Jehobah. Yesu ya ce game da ma’aurata: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Matta 19:6) Bin wannan mizanin ba a koyaushe ba ne yake da sauƙi. Alal misali, dangi da wasu mutane, har da wasu masu ba da shawara game da aure waɗanda ba su fahimci mizanan Littafi Mai Tsarki ba, a yawancin lokaci suna ba ma’aurata shawara cewa su rabu ko su kashe aure wanda hakan bai jitu da nassi ba.a Amma Kiristoci sun san cewa ya fi kyau a gyara kuma a riƙe aure fiye da a rushe shi da wuri. Hakika, ya fi muhimmanci mu ƙudurta cewa za mu yi abubuwa yadda Jehobah ya tsara, ba a kan shawarar wasu ba.—Misalai 14:12.

Magance Matsaloli

4, 5. (a) Waɗanne ƙalubale ne za a fuskanta a aure? (b) Me ya sa mizanan da ke cikin Kalmar Allah suke taimakawa sa’ad da aka samu matsaloli a aure?

4 Gaskiyar ita ce, kowane aure yana bukatar a mai da masa hankali a kai a kai. A yawancin lokaci, hakan zai ƙunshi warware ƙananan matsaloli. A wasu auren kuwa, za a iya samun matsaloli masu tsanani da za su iya ɓata dangantakar. A wasu lokatai, kuna iya neman taimako daga ƙwararren Kirista dattijo da ya yi aure. Waɗannan yanayin ba sa nufin cewa ba ku dace da juna ba. Amma suna nuna muhimmancin manne wa mizanan Littafi Mai Tsarki ne don magance matsaloli.

5 Domin shi ne ya halicci mutane kuma shi ne Tushen tsarin aure, Jehobah ya fi sanin abin da muke bukata don mu kasance da dangantaka mai kyau a aurenmu. Amma tambayar ita ce, Za mu saurari shawarar da ke cikin Kalmar Allah kuma mu bi ta? Za mu amfana idan muka yi haka. Jehobah ya gaya wa mutanensa na dā: “Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Ishaya 48:18) Bin ja-gorancin da aka tsara a cikin Littafi Mai Tsarki zai iya sa aure ya yi nasara. Bari mu fara tattauna shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba magidanta.

“Ku Ƙaunaci Matanku”

6. Wace shawara ce Nassi ya ba magidanta?

6 Wasiƙar manzo Bulus ga Afisawa tana ƙunshe da abubuwan da magidanta za su yi. Bulus ya rubuta: “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta; Hakanan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyarda shi ya kan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya; Duk da haka sai ku kuma kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”—Afisawa 5:25, 28, 29, 33.

7. (a) Menene ya kamata ya zama sashe mafi muhimmanci a ginshiƙin auren Kirista? (b) Ta yaya ne maza za su ci gaba da ƙaunar matansu?

7 Bulus bai tattauna duka matsalar da za ta iya tasowa tsakanin mata da mijinta ba. Maimakon haka, ya ambata ainihin yadda za a magance matsalar da za ta iya tasowa a aure ta wajen bayyana abin da ya kamata ya zama sashe mafi muhimmanci a ginshiƙin auren kowane Kirista, wato ƙauna. An ambaci ƙauna sau shida a ayoyin da ke baya. Ka lura cewa sa’ad da Bulus ya gaya wa maza: “Ku ƙaunaci matanku,” a rubutu na ainihi hakan na nufin su ci gaba da yin hakan. Babu shakka, Bulus ya fahimci cewa yana da sauƙi a soma soyayya da a ci gaba da yin soyayya. Hakan na faruwa musamman a wannan “kwanaki na ƙarshe,” domin yawancin mutane “masu-son kansu” ne kuma “masu-baƙar zuciya.” (2 Timothawus 3:1-3) Irin waɗannan halaye marar kyau suna kashe aure mai yawa a yau, amma mijin da yake ƙaunar matarsa ba zai ƙyale halayen son kai na wannan duniyar su shafi tunaninsa da ayyukansa ba.—Romawa 12:2.

Ta Yaya Za Ka Kula da Matarka?

8, 9. A waɗanne hanyoyi ne maigida Kirista yake kula da matarsa?

8 Idan kai Kirista ne magidanci, ta yaya za ka guje wa son kai kuma ka nuna ƙauna ta gaskiya ga matarka? A cikin kalamansa ga Afisawa da aka yi ƙauli a dā, Bulus ya ambata abubuwa biyu da kake bukatar ka yi, ka kula da matarka, kuma ka so ta yadda kake son jikinka. Ta yaya za ka iya kula da matarka? Hanya ɗaya ita ce, biyan bukatun matarka na zahiri. Bulus ya rubuta wa Timoti: “Amma idan wani ba ya yi tattalin nasa ba, balle na iyalinsa, ya musunci imani, gwamma marar-bangaskiya da shi.”—1 Timothawus 5:8.

9 Amma, ana bukatar fiye da yin tanadin abinci, sitira, da wurin kwana kawai. Me ya sa? Domin maigidan yana iya kasance mai ƙoƙari sosai wajen yin tanadin kayan da matarsa take bukata, amma sai ya kasa mai da mata hankali da kuma biyan bukatunta na motsin zuci da na ruhaniya. Biyan bukatunta a waɗannan hanyoyin suna da muhimmanci. Hakika, yawancin Kiristoci maza suna aiki tuƙuru wajen kula da batutuwan ikilisiya. Amma kasancewa da hakki mai yawa a ikilisiya ba ya nufin cewa maigida zai yi watsi da cika hakkin da Allah ya ba shi. (1 Timothawus 3:5, 12) A shekaru da suka shige, wannan mujallar ta yi kalaman da ke gaba a kan wannan batun: “Daidai da farillan Littafi Mai Tsarki, za a iya cewa ‘ana soma kiwo ne a gida.’ Idan dattijo ya yi watsi da iyalinsa, hakan na iya shafan gatarsa.”b Babu shakka, dole ne ka kula da matarka a zahiri, ka mai da mata hankali, kuma mafi muhimmanci, ka kula da bukatunta na ruhaniya.

Menene Yake Nufi Ka Yi Tattalin Matarka?

10. Ta yaya ne maigida zai yi tattalin matarsa?

10 Idan kana tattalin matarka, za ka kula da ita sosai domin kana ƙaunarta. Akwai hanyoyi da yawa da za ka iya yin haka. Na farko, ka ba matarka isashen lokaci. Idan ka yi watsi da matarka a wannan batun, tana iya daina ƙaunarka. Ka tuna cewa, abin da kake tunanin cewa matarka tana bukata a batun ba ta lokaci da kuma mai da mata hankali wataƙila ba abin da take bukata ba ke nan. Ba wai kawai za ka ce kana tattalin matarka ba. Matarka tana bukatar ta san cewa kana tattalinta ta ayyukanka. Bulus ya rubuta: “Kada kowa shi biɗa ma kansa, amma abin da za ya amfana maƙwabcinsa.” (1 Korinthiyawa 10:24) A matsayinka na maigida mai ƙauna, za ka so ka fahimci ainihin bukatun matarka.—Filibbiyawa 2:4.

11. Ta yaya ne yadda maigida ya bi da matarsa zai shafi dangantakarsa da Allah da kuma ikilisiya?

11 Wata hanyar kuma da za ka nuna cewa kana tattalin matarka ita ce bi da ita a hankali, ta wajen kalami da aikatawa. (Misalai 12:18) Bulus ya rubuta wa Kolosiyawa: “Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kolossiyawa 3:19) In ji wani littafi, ana iya fassara sashe na ƙarshe na furcin Bulus kamar “kada ka bi da ita kamar baiwa.” Maigidan da azzalumi ne a ɓoye ko a fili, ba ya nuna cewa yana tattalin matarsa. Idan ya bi da matarsa yadda bai kamata ba, hakan na iya shafan dangantakarsa da Allah. Manzo Bitrus ya rubuta wa magidanta: “Ku zauna da matayenku bisa ga sani, kuna bada girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi, da kuma masu-tarayyan gado na alherin rai: domin kada addu’oinku su hanu.”c—1 Bitrus 3:7.

12. Menene maigida Kirista zai koya daga yadda Yesu ya bi da ikilisiyar Kirista?

12 Kada ka yi tunani cewa matarka za ta ƙaunace ka haka kawai. Ka tabbatar mata cewa za ka ci gaba da ƙaunarta. Yesu ya kafa misali wa magidanta Kiristoci ta yadda ya bi da ikilisiyar Kirista. Har ma a lokacin da mabiyansa suka ci gaba da nuna halaye marar kyau, Yesu ya nuna masu halin kirki, ya kuma gafarta masu. Shi ya sa Yesu ya gaya wa mutane: “Ku zo gareni, . . . gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” (Matta 11:28, 29) Ta wajen koyi da Yesu, maigida Kirista zai bi da matarsa kamar yadda Yesu ya bi da ikilisiya. Mutumin da ke tattalin matarsa da gaske, kuma yana nuna haka a kalami da kuma halinsa, zai wartsakar da matarsa.

Matan da Suke Bin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki

13. Waɗanne ƙa’idodi da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne za su iya taimaka wa matan aure?

13 Littafi Mai Tsarki yana ƙunshe da ƙa’idodin da za su taimaka wa matan aure. Afisawa 5:22-24, 33 sun ce: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne, shi da kansa fa mai-ceton jiki ne. Amma kamar yadda ikilisiya take zaman biyayya ga Kristi, hakanan mataye su yi ga mazansu cikin dukan abu. . . . Matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”

14. Me ya sa ƙa’idar ba da kai da ke cikin Nassi ba wai yana rena mata ba ne?

14 Ka lura da nanacin da Bulus ya yi a kan ba da kai da kuma biyayya. An tuna wa matar aure ta ba da kanta ga mijinta. Hakan ya yi daidai da tsarin Allah. Duka halittun da ke sama da ƙasa suna ƙarƙashin wani ne. Har ma Yesu da kansa yana ƙarƙashin Jehobah Allah. (1 Korinthiyawa 11:3) Maigidan da ya nuna shugabancinsa a hanyar da ta dace zai sa matarsa ta ba da kanta a gare shi cikin sauƙi.

15. Waɗanne umurnai ga matan aure ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

15 Bulus ya ambata cewa mata “ta ga kwarjinin mijinta.” Ya kamata mata Kirista ta nuna “ruhu mai-ladabi mai-lafiya,” ba wai ta ƙalubalanci ikon maigidanta ko ta nemi ’yanci ba. (1 Bitrus 3:4) Matar aure mai tsoron Allah za ta yi aiki tuƙuru don ta kula da iyalinta kuma ta kawo ɗaukaka ga maigidanta. (Titus 2:4, 5) Za ta ƙoƙarta ta yi maganar kirki game da maigidanta kuma kada ta yi abin da zai sa wasu su raina shi. Kuma za ta yi aiki tuƙuru ta sa ya cim ma shawarwarinsa.—Misalai 14:1.

16. Menene matan aure Kirista za su iya koya daga misalan Saratu da Rifkatu?

16 Kasancewa da ladabi ba ya nufin cewa mace Kirista ba ta da nata ra’ayin ko kuwa tunaninta ba shi da muhimmanci. Mata na dā masu tsoron Allah, kamar su Saratu, da Rifkatu, sun bayyana damuwarsu game da wasu batutuwa, kuma labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya amince da abin da suka ce. (Farawa 21:8-12; 27:46–28:4) Matan aure Kiristoci suna iya bayyana ra’ayinsu. Amma, za su yi haka cikin biyayya, ba raini ba. Idan suka yi haka, za su ga cewa mazansu za su yi amfani da ra’ayinsu yadda ya kamata.

Muhimmancin Wa’adi

17, 18. Ta waɗanne hanyoyi ne magidanta da matan aure za su iya guje wa ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaiɗan don ya lalata dangantakarsu ta aure?

17 Aure wa’adi ne na dindindin. Saboda haka, ya kamata mata da miji su kasance da muradin sa aurensu ya yi nasara. Rashin tattaunawa da juna na iya jawo matsaloli kuma hakan ya yi tsanani. A yawancin lokaci, ma’aurata suna daina yi wa juna magana sa’ad da matsaloli suka taso, kuma hakan na jawo baƙin ciki. Wasu ma’aurata ma sukan nemi hanyar rusa dangantakarsu, wataƙila ta wajen yin tarayya da wani ko wata da ba abokin aurensu ba. Yesu ya yi gargaɗi: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.”—Matta 5:28.

18 Manzo Bulus ya gargaɗi dukan Kiristoci, tare da Kiristocin da suka yi aure: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afisawa 4:26, 27) Babban maƙiyinmu, Shaiɗan, yana ƙoƙarin ya yi amfani da saɓanin da Kiristoci za su iya samu. Kada ka bari ya yi nasara! Sa’ad da matsaloli suka taso, ka yi bincike a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ra’ayin Jehobah a kan batutuwan, kuma ka yi amfani da littattafan da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Ku tattauna saɓanin da kuka samu a natse. Ku yi amfani da abin da kuka sani game da ƙa’idodin Jehobah. (Yaƙub 1:22-25) Game da aurenku kuwa, ku kudurta cewa za ku ci gaba da bin Allah a matsayin ma’aurata, kuma kada ku yarda mutum ko wani abu ya raba abin da Allah ya haɗa!—Mikah 6:8.

[Hasiya]

a Ka dubi akwatin nan “Divorce and Separation” da ke cikin Awake! na 8 ga Fabrairu, 2002, shafi na 10, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

b Ka duba Hasumiyar Tsaro, 15 ga Mayu, 1989, shafi na 12 a Turanci.

c Don ya cancanci samun gata a ikilisiyar Kirista, mutum ba zai zama “mai saurin hannu ba,” wato, wanda ke bugun mutane a zahiri ko kuwa ya gaya masu baƙar magana. Shi ya sa Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1990, shafi na 25 ta ce: “Mutum ba zai cancanta ba idan ya nuna halin ibada a wani wuri amma azzalumi ne a gidansa.”—1 Timothawus 3:2-5, 12.

Ka Tuna?

• Me ya sa za a iya samun matsaloli a auren Kiristoci?

• Ta yaya ne maigida zai kula da matarsa kuma ya nuna cewa yana tattalinta?

• Menene matar aure za ta yi don ta nuna cewa tana daraja mijinta sosai?

• Ta yaya ne mata da miji za su iya ƙarfafa wa’adinsu?

[Hoto a shafi na 22]

Ya kamata maigida ya kula da matarsa sosai, ba a zahiri ba kawai amma a ruhaniya

[Hoto a shafi na 23]

Mutumin da ke tattalin matarsa zai sa ta sami wartsakewa

[Hoto a shafi na 25]

Matan aure Kiristoci suna faɗin ra’ayinsu a cikin tarbiyya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba