Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 3/1 pp. 21-26
  • Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Koyi da Yesu da Kuma Ikilisiyarsa
  • Ku Ci Gaba da Zama da Su
  • “Rashin Ƙarfi” a Wace Hanya?
  • A Iyali Mai Addinai Dabam Dabam
  • “Hali”
  • Shawara Mai Kyau ta Littafi Mai Tsarki
  • Magidanta Ku Yi Koyi Da Shugabancin Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Kada Ka Raba Abin Da Allah Ya Haɗa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Mata Ku Yi Wa Mazanku Ladabi Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 3/1 pp. 21-26

Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata

“Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa. Ku maza, ku ƙaunaci matanku.”—Afisawa 5:22, 25.

1. Wane ra’ayi ne ya dace game da aure?

YESU ya ce Allah ne ya haɗa mata da miji cikin aure su zama “jiki guda.” (Matiyu 19:5, 6) Ya ƙunshi mutane biyu masu mutuntaka dabam dabam su koyi son abu ɗaya kuma su yi aiki tare don su cim ma makasudinsu. Aure gami ne na dindindin, ba yarjejeniya ta ɗan lokaci da za a daina haka kawai ba. A ƙasashe da yawa ba shi da wuya a kashe aure, amma a ra’ayin Kirista nasaba na aure yana da tsarki. Za a kashe aure ne domin dalili mai tsanani.—Matiyu 19:9.

2. (a) Wane taimako ne ma’aurata suke da shi? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu yi nasara a aurenmu?

2 Wata mai ba da shawara game da aure ta ce: “Za a yi nasara cikin aure idan ma’aurata sun ci gaba da yin gyara sa’ad da suke fuskantar sababbin batutuwa. Su bi da matsaloli da ke tasowa, kuma su yi amfani da abubuwa da zai taimake su a kowanne yanayi na rayuwa.” Waɗannan abubuwa sun haɗa da gargaɗi na Littafi Mai Tsarki ga ma’aurata Kirista, da kuma goyon baya na ’yan’uwa Kiristoci, da nasaba ta kurkusa da Jehobah ta yin addu’a. Aure mai nasara na jimre wa matsaloli, kuma na sa mata da miji farin ciki kuma su sami gamsuwa cikin aurensu. Mafi muhimmanci, yana ɗaukaka Jehobah Allah, Tushen aure.—Farawa 2:18, 21-24; 1 Korantiyawa 10:31; Afisawa 3:15; 1 Tasalonikawa 5:17.

Ku Yi Koyi da Yesu da Kuma Ikilisiyarsa

3. (a) Wane darasi na musamman ke cikin gargaɗin Bulus ga ma’aurata. (b) Wane misali mai kyau Yesu ya kafa?

3 Manzo Bulus ya ba wa ma’aurata Kiristoci gargaɗi mai kyau shekaru dubu biyu da suka shige, ya rubuta: “Kamar yadda ikilisiya ke bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali. Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikilisiya, har ya ba da kansa dominta.” (Afisawa 5:24, 25) Wannan kwatanci ne mai kyau sosai! Mata Kiristoci da suke biyayya ga mazansu cikin tawali’u suna koyi da ikilisiya ta wajen fahimta da kuma kiyaye ƙa’ida na shugabanci. Maza masu bi da suka ci gaba da ƙaunar matansu ko da daɗi ko ba daɗi, suna nuna cewa suna bin misalin yadda Kristi ke ƙaunar ikilisiya da kuma kula da ita.

4. Ta yaya maza za su bi misalin Yesu?

4 Kiristoci maza ne shugaban iyalansu, amma su ma Yesu ne shugabansu. (1 Korantiyawa 11:3) Saboda haka, yadda Yesu yake kula da ikilisiyarsa haka maza za su kula da iyalansu a ruhaniya da kuma a zahiri ko wannan zai bukaci sadaukar da kai. Suna sa zaman lafiyar iyalansu a kan gaba da abin da suke so. Yesu ya ce: “Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu.” (Matiyu 7:12) Wannan ƙa’ida tana da amfani musamman cikin aure. Bulus ya nuna wannan sa’ad da ya ce: “Maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. . . . Ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa.” (Afisawa 5:28, 29) Ya kamata miji ya rene kuma yi wa matansa tattali yadda yake yi wa jikinsa.

5. Ta yaya mata za su yi koyi da ikilisiyar Kirista?

5 Mata da suke bauta wa Allah suna bin misalin ikilisiyar Kirista. Sa’ad da Yesu yake duniya, mabiyansa sun bar ayyukansu suka bi shi da farin ciki. Bayan mutuwarsa sun ci gaba da yi masa biyayya. Fiye da shekaru 2,000 da suka shige, ikilisiyar Kirista ta gaske ta ci gaba da yi wa Yesu biyayya kuma tana bin shugabancinsa a dukan abubuwa. Hakanan ma mata Kirista ba za su rena mazansu ba ko kuma su nemi su rage muhimmancin tsarin Nassi na shugabanci cikin aure. Maimakon haka, za su taimaka wa mazansu kuma su yi musu biyayya. Za su haɗa kai da mazansu kuma su ƙarfafa su. Sa’ad da mata da miji suka yi hakan cikin ƙauna, za su yi nasara cikin aurensu kuma su yi farin ciki a dangantakarsu.

Ku Ci Gaba da Zama da Su

6. Wane gargaɗi ne Bitrus ya yi wa maza, me ya sa yake da muhimmanci?

6 Manzo Bitrus shi ma ya gargaɗi ma’aurata, kalmominsa musamman ga maza ne. Ya ce: “Hakanan kuma ku mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi, da kuma masu-tarayyan gādo na alherin rai: domin kada addu’o’inku su hanu.” (1 Bitrus 3:7; Litafi Mai-Tsarki) An bayyana muhimmancin gargaɗin Bitrus a kalmomin ƙarshe na ayar. Idan miji bai girmama matarsa ba, zai shafi dangantakarsa da Jehobah. Ba zai amsa addu’arsa ba.

7. Ta yaya ya kamata namiji ya girmama matarsa?

7 To, ta yaya maza za su girmama matansu? Mutum ya girmama matarsa na nufin ya bi da ita cikin ƙauna, daraja, da ɗaukaka. Mutane da yawa za su ga bai kamata a bi da mata hakan nan ba. Wani Bahelene da ya malanta ya rubuta: “Mata ba su da iko a dokar Roma. Bisa dokar ikonta daidai yake da na yaro. . . . Tana biyayya da mijinta a kome, ba ta da ’yancin magana.” Wannan ya bambanta da koyarwar Kirista! Maigida Kirista na girmama matarsa, uwar yaransa. Yana sha’ani da ita bisa ƙa’idodin Kirista, ba yadda yake ji ba. Ƙari ga haka, yana zama da ita “bisa ga sani” ya tuna cewa ta fi rashin ƙarfi.

“Rashin Ƙarfi” a Wace Hanya?

8, 9. A waɗanne hanyoyi ne mata suke daidai da maza?

8 Da ya ce mata sun “fi rashin ƙarfi” Bitrus ba ya nufin cewa maza sun fi mata ilimi ko kuma ruhaniya. Hakika, maza Kiristoci da yawa suna da gata cikin ikilisiya da mata ba za su taɓa samu ba, kuma mata za su yi wa mazansu biyayya. (1 Korantiyawa 14:35; 1 Timoti 2:12) Duk da haka, ana bukatar kowa, maza da mata su kasance da bangaskiya, su yi jimiri kuma su bi mizanan ɗabi’a mai girma. Yadda Bitrus ya ce, mata da maza “masu-tarayyan gādo na alherin rai” ne. Matsayin dukansu ɗaya ne a gaban Jehobah Allah in ya zo ga samun ceto. (Galatiyawa 3:28) Bitrus ya gaya wa Kiristoci shafaffu na ƙarni na farko. Shi ya sa, kalmominsa ya tuna wa maza Kiristoci cewa da yake su “abokan gādo kuma da Almasihu” ne, da su da matansu suna da bege ɗaya na zuwa sama. (Romawa 8:17) Wata rana, dukansu za su yi hidima na firistoci da sarakuna tare a Mulkin Allah na samaniya!—Wahayin Yahaya 5:10.

9 Mata Kiristoci shafaffu suna da matsayi ɗaya da mazansu shafaffu Kiristoci. Bisa ƙa’ida haka yake da waɗanda suke da bege na zama a duniya. Maza da mata na “ƙasaitaccen taro” sun wanke rigunansu suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Maza da mata suna sa hannu wajen yabon Jehobah a dukan duniya “dare da rana.” (Wahayin Yahaya 7:9, 10, 14, 15) Maza da mata suna jira su more “ ’yancin nan na ɗaukaka na ’ya’yan Allah,” sa’ad da za su yi farin cikin “rai wanda yake na hakika.” (Romawa 8:21; 1 Timoti 6:19) Ko su shafaffu ne ko kuwa waɗansu tumaki, dukan Kiristoci suna bauta wa Jehobah tare, su “garke guda” ne a ƙarƙashin ‘makiyayi guda.’ (Yahaya 10:16) Wannan dalili ne na musamman da ya sa mata da miji Kiristoci za su girmama juna!

10. A wane azanci ne mace ta “fi rashin ƙarfi”?

10 To, a wace hanya ce mace ta fi rashin ƙarfi? Bitrus yana magana ne cewa mata ƙanana ne kuma ba su da ƙarfi kamar maza. Ƙari ga haka, a yanayinmu na ajizanci, gatar ɗaukan ciki da kuma haihuwa na shafan ƙarfin mace. Mata da suke cikin shekarun haihuwa suna iya kasancewa da damuwa dabam dabam kuma a kai a kai. Suna bukatar a kula da su da kyau kuma a yi la’akari da su sa’ad da suke jimre wa damuwa ko kuma gajiya na haihuwa. Namiji da ke girmama matarsa, da ya fahimci goyon baya da take bukata, zai sa su yi nasara cikin aurensu.

A Iyali Mai Addinai Dabam Dabam

11. Me ya sa za a yi nasara cikin aure ko idan mata da miji suna bin addinai dabam dabam?

11 Idan ma’aurata suna bin addinai dabam dabam fa, mai yiwuwa ɗaya cikinsu ya karɓi gaskiya ta Kirista bayan sun yi aure kuma ɗayan bai karɓa ba. Za a iya yin nasara a irin wannan auren kuwa? Labarai sun nuna cewa da yawa sun yi nasara. Mata da miji da suke bin addinai dabam dabam har ila za su yi nasara cikin aurensu kuma ya kasance mai jimrewa kuma ya sa su farin ciki. Ballantana ma, a gaban Jehobah auren har ila na bisa ƙa’ida; su har ila “jiki guda” ne. Saboda haka, an gargaɗi ma’aurata Kirista su zauna da abokin aurensu marar bi idan ya yarda za su zauna tare. Idan suna da yara, za su amfana daga amincin mahaifiya Kirista.—1 Korantiyawa 7:12-14.

12, 13. Ta bin gargaɗin Bitrus, ta yaya mata Kiristoci za su taimaki mazansu marasa bi?

12 Bitrus ya ba da gargaɗi mai kyau ga mata Kiristoci da suke zama cikin iyali mai addinai dabam dabam. Maza Kiristoci da suke irin wannan yanayi su ma za su yi amfani da gargaɗin. Bitrus ya rubuta: “Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yā shawo kansu, ba tare da wata magana ba, don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.”—1 Bitrus 3:1, 2.

13 Idan mace za ta iya bayyana wa mijinta imaninta cikin basira, wannan yana da kyau. Idan ba ya son ya saurara fa? Wannan zaɓensa ne. Har ila ba za ta fid da rai ba, da yake halin Kirista mai kyau yana ba da shaida. Maza da yawa da dā ba sa son imanin matansu ko kuma suna hamayya da su sun zama waɗanda “aka ƙaddara wa samun rai madawwami” bayan sun ga hali mai kyau na matansu. (Ayyukan Manzanni 13:48) Ko idan miji bai bi gaskiya ta Kirista ba, halin matarsa na iya burge shi, kuma wannan zai ƙarfafa auren. Wani mutum da matarsa Mashaidiyar Jehobah ce ya ce ba zai iya bin mizananmu mai girma ba. Duk da haka ya ce shi “mutum mai farin ciki ne mai mata da ke da kyakkyawan hali.” Ya yabi matarsa da Shaidu ’yan’uwanta a wasiƙa cikin wata jarida.

14. Ta yaya maza za su taimaki matansu da ba masu bi ba?

14 Maza Kiristoci da suka yi amfani da ƙa’idodin kalmomin Bitrus su ma sun shawo kan matansu ta halinsu. Mata marasa bi sun lura cewa mazansu sun soma kula da hakkinsu, ba sa ɓad da kuɗi ta shan taba, shan giya, da yin caca kuma ba sa zancen banza. Wasu cikin irin waɗannan mata sun sadu da waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista. Ƙaunar ’yan’uwanci na Kirista ta burge su, kuma abin da suka lura da shi tsakanin ’yan’uwan ya sa su so bauta wa Jehobah.—1 Korantiyawa 14:24, 25.

“Hali”

15, 16. Mace Kirista za ta nuna wane irin hali ne da zai iya shawo kan mijinta marar bi?

15 Wane irin hali ne zai shawo kan namiji? Hakika, hali ne da mata Kirista suke nunawa. Bitrus ya ce: “Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa, sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dusashewa na tawali’u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah. Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu, kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma ’ya’yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.”—1 Bitrus 3:3-6.

16 Bitrus ya gargaɗi mace Kirista kada ta mai da hankali ga ado na waje kawai. Maimakon haka, mijin zai lura da yadda koyarwar Littafi Mai Tsarki ke shafan halinta. Halinta zai sa shi ya lura cewa tana da sabon hali. Wataƙila zai ga bambanci da halin da matarsa take da shi dā. (Afisawa 4:22-24) Babu shakka zai iske ‘tawali’unta da natsuwa’ da ban sha’awa da kuma wartsakarwa. Irin wannan halin yana faranta wa mijin kuma “wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.”—Kolosiyawa 3:12.

17. Ta yaya Saratu ta zama misali mai kyau ga mata Kirista?

17 An ambata misalin Saratu. Mata Kirista za su yi koyi da ita ko mazansu masu bi ne ko marasa bi. Babu shakka Saratu ta yi na’am cewa Ibrahim shugabanta ne. Har a zuciyarta, ta kira shi ‘shugabana.’ (Farawa 18:12) Duk da haka, wannan bai rage darajarta ba. A bayane yake cewa ita mace ce mai ruhaniya sosai domin bangaskiyarta ga Jehobah. Hakika, tana cikin “taron shaidu masu ɗumbun yawa” da misalinsu na bangaskiya ya kamata ya motsa mu mu “yi tseren nan da ke gabanmu tare da jimiri.” (Ibraniyawa 11:11; 12:1) Ba reni ba ne mace Kirista ta zama kamar Saratu.

18. Waɗanne ƙa’idodi za a yi amfani da su cikin iyali mai addinai dabam dabam?

18 Har ila mijin ne shugaba a cikin iyali mai addinai dabam dabam. Idan shi ne mai bi zai yi la’akari da imanin matarsa ba tare da yin shirka ba. Idan matar ce mai bi, ita ma ba za ta yi shirka ba. (Ayyukan Manzanni 5:29) Amma, za ta yi biyayya da shugabancin mijinta. Za ta daraja matsayinsa kuma ta kasance cikin “shari’ar . . . mijin.”—Romawa 7:2; Litafi Mai-Tsarki.

Shawara Mai Kyau ta Littafi Mai Tsarki

19. Waɗanne matsi suke damun gami na aure, ta yaya za a yi tsayayya wa irin wannan matsi?

19 A yau, abubuwa da yawa na iya lalata gami na aure. Wasu maza ba sa kula da hakkinsu. Wasu mata ba sa na’am da shugabancin mijinsu. A wasu aure-aure ana zaluntar mata. Ƙari ga haka, alhinin kuɗi, ajizanci, da ruhun duniya na lalata game da ɗabi’a zai iya gwada amincin Kirista. Duk da haka, maza da mata Kirista da suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna samun albarkar Jehobah, ko yaya yanayinsu yake. Yanayin zai fi kyau idan ma mutum ɗaya ne yake bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki cikin aure, da a ce ba wanda yake yin hakan. Ƙari ga haka, Jehobah yana ƙaunar bayinsa da kuma tallafa wa waɗanda suka kasance da aminci ga wa’adi na aurensu har a yanayi mai wuya. Ba zai manta da amincinsu ba.—Zabura 18:25; Ibraniyawa 6:10; 1 Bitrus 3:12.

20. Wane gargaɗi ne Bitrus ya yi wa dukan Kiristoci?

20 Bayan ya yi wa ma’aurata gargaɗi, manzo Bitrus ya kammala da kalmomi masu ƙarfafa. Ya ce: “Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar ’yan’uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali’u. Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.” (1 Bitrus 3:8, 9) Wannan gargaɗi ne mai kyau ga dukanmu, musamman ga ma’aurata!

Ka Tuna?

• Ta yaya maza Kiristoci suke yin koyi da Yesu?

• Ta yaya mata Kiristoci suke yin koyi da ikilisiya?

• Ta yaya maza za su girmama matansu?

• Wane tafarki da ya fi kyau mace Kirista da mijinta ba mai bi ba za ta ɗauka?

[Hoto a shafi na 22]

Maigida Kirista na ƙaunar matarsa yana kuma kula da ita

Mace Kirista na daraja da kuma ɗaukaka mijinta

[Hoto a shafi na 23]

Bisa ga koyarwar Kirista maigida na bukatar ya girmama matarsa, ba kamar dokar Roma ba

[Hoto a shafi na 24]

Maza da mata na “ƙasaitaccen taro” na jiran rai madawwami a cikin Aljanna

[Hoto a shafi na 26]

Saratu ta ɗauki Ibrahim a matsayin ubangijinta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba