Mata Ku Yi Wa Mazanku Ladabi Sosai
“Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku.”—AFISAWA 5:22.
1. Me ya sa yake da wuya a yi ladabi ga maigida?
AƘASASHE da yawa idan mace da na miji suna yin aure, amaryar tana yin alkawari cewa za ta ga kwarjinin mijinta. Amma, yadda magidanta da yawa suke bi da matansu ne zai nuna ko zai yi wuya ko ba zai yi wuya ba a cika wannan alkawari. Duk da haka, an soma aure da kyau. Allah ya ɗauki haƙarƙarin Adamu, mutum na farko, ya yi mace. Adamu ya furta: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.”—Farawa 2:19-23.
2. Ta yaya ne hakkin mata da kuma halinsu game da aure ya canja a kwanan bayan nan?
2 Duk da wannan farawa mai kyau, an kafa tsarin da ake kira ’yanci na mata wato wanda zai sa mata su samu ’yanci daga ikon maza a shekara ta 1960 a Amirka. A wannan lokacin kafin a kafa tsarin za ka ƙirga maza 300 da suka rabu da iyalansu kafin ka sami mace guda da ta rabu da iyalinta, amma a ƙarshen shekara ta 1969 abubuwa sun canza, za ka sami maza 100 da suka rabu da iyalansu kafin ka samu mace guda da ta rabu da maigidanta. Amma yanzu mata suna zage-zage, suna shan giya, suna shan taba, kuma suna yin lalata kamar yadda maza suke yi. Saboda haka, mata sun fi farin ciki ne yanzu? A’a. A wasu ƙasashe, kusan rabin mutanen da suka yi aure sun kashe aurensu daga baya. Ƙoƙarin da mata suka yi don su gyara aurensu ya sa abubuwa sun gyaru ne ko kuwa sun ƙara lalacewa?—2 Timothawus 3:1-5.
3. Menene ainihin matsalar da take shafan aure?
3 Menene ainihin matsalar? Matsalar ta soma ne tun lokacin da wani mala’ika ɗan tawaye ya rinjayi Hauwa’u, wato “tsohon macijin, wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 1 Timothawus 2:13, 14) Shaiɗan ya raina abin da Allah ya koyar. Alal misali, Iblis ya sa aure ya zama kamar abu ne da yake hana mutane su yi abin da suke so kuma abu ne mai wuya. Da yake shi ne sarkin duniya ya tsara labarin ƙarya da yake kawo wa ta hanyar labarai na duniya, domin ya sa umurnin Allah ya kasance marar kyau kuma ya zama tsohon yayi. (2 Korinthiyawa 4:3, 4) Idan muka yi la’akari da zuciya ɗaya abin da Allah ya ce game da hakkin mace a aure, za mu fahimci cewa Kalmar Allah tana da amfani.
Gargaɗi ga Waɗanda Suka Yi Aure
4, 5. (a) Me ya sa ya kamata mace ta mai da hankali sosai kafin ta yarda ta aure wani? (b) Menene ya kamata mace ta yi kafin ta yarda ta aure wani?
4 Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi. Ya ce a wannan duniyar da Iblis yake mulkinta, har waɗanda suka yi nasara a aure za su sha “wahala.” Ko da yake aure shiri ne daga Allah, Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi ma’aurata. Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce game da matar da mijinta ya mutu kuma tana da ’yancin ta sake wani aure: “Amma ta fi farin ciki idan ta zauna haka.” Yesu ya ƙarfafa rashin aure ga “wanda ya ke da iko shi karɓi wannan shi karɓa.” Duk da haka, wanda yake so ya yi aure, ya yi shi a “cikin Ubangiji,” wato ya ko ta auri mai bauta wa Allah da ya ko ta yi baftisma.—1 Korinthiyawa 7:28, 36-40; Matta 19:10-12.
5 Dalilin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi mace ta lura da wanda take so ta aura, shi ne: “Mace wadda ta ke da miji a daure ta ke ga mijin bisa ga shari’a.” Idan ya mutu ne ko kuma an kashe auren ne za ta ‘saku daga shari’arsa.’ (Romawa 7:2, 3) Gani na farko yana iya sa a so mutum, amma ba shi ba ne zai kawo farin ciki a aure ba. Saboda haka, ya kamata mace da ba ta yi aure ba ta tambayi kanta, ‘Ina shirye na kasance a ƙarƙashin ikon wannan mutumin?’ Ya kamata ta yi wannan tambayar kafin ta yi aure, ba bayan ta yi aure ba.
6. Wace shawara ce yau ya kamata mace ta tsai da, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
6 A yawancin wurare, mace tana da ’yancin ta yarda ko ta ƙi wanda ya zo mata da batun aure. Duk da haka, yin zaɓe mai kyau zai iya zama abu mafi wuya da mace za ta yi, tun da muradinta da dangantaka na kud da kud da kuma ƙauna da ake nunawa a aure zai iya kasancewa da ƙarfi. Wani marubuci ya ce: “Idan muna so mu yi wani abu, ko a batun aure ne ko muna so mu hau wani dutse mai tsawo, idan ba mu mai da hankali za mu zato komi daidai ne kuma mu saurari shawara da muke so mu ji ne kawai.” Idan mai hawan dutse bai yi tunani ba sosai kafin ya hau babban dutse, hakan na iya sa ya rasa ransa, haka nan ma idan mutum ya zaɓi abokin aure wanda bai dace ba zai kasance da lahani.
7. Wanene gargaɗi ne mai kyau aka ba da game da neman abokin aure?
7 Ya kamata mace ta yi la’akari da abin da kasancewa a ƙarƙashin shari’ar mutumin da ya ce zai aure ta ya ƙunsa. A shekaru da suka wuce, wata ’yar Indiya ta ce: “Iyayenmu sun fi mu da shekaru kuma da hikima, kuma ba za a iya ruɗinsu da sauri ba kamar mu . . . Zan iya yin kuskure nan da nan.” Taimakon iyaye da kuma wasu mutane yana da muhimmanci. Wani mai ba da shawara ya gargaɗi matasa su san iyayen wanda ko wadda suke son su aura kuma su lura da halinsa ko halinta sa’ad suke tare da iyayensu da kuma sauran mutanen iyalinsu.
Yadda Yesu Ya Nuna Biyayya
8, 9. (a) Ta yaya ne Yesu ya ɗauki yi wa Allah biyayya? (b) Wane amfani ne za a iya samu idan aka yi biyayya?
8 Ko da yake yin biyayya zai iya kasancewa da wuya, mata suna iya ɗaukansa abu ne mai daraja, kamar yadda Yesu ya yi. Ko da yake biyayyarsa ga Allah ta haɗa da wahala, har ga mutuwa a kan gungumen azaba, ya yi farin cikin yin biyayya ga Allah. (Luka 22:41-44; Ibraniyawa 5:7, 8; 12:3) Ya kamata mata su bi misalin Yesu, gama Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Saboda haka, ba sai mace ta yi aure ba ne kawai take ƙarƙashin shugabancin na miji.
9 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa matan da suka yi aure ko marasa aure, su yi biyayya ga shugabancin maza da suke kula da ikilisiyar Kirista. (1 Timothawus 2:12, 13; Ibraniyawa 13:17) Idan mata suka bi ja-gorar Allah, za su kafa misali ga mala’iku da suke cikin tsarin ƙungiyar Allah. (1 Korinthiyawa 11:8-10) Bugu da ƙari, ta misalinsu da kuma shawara masu kyau, matan da suka manyanta za su iya koya wa ƙananan mata su yi ‘biyayya ga mazansu.’—Titus 2:3-5.
10. Ta yaya ne Yesu ya kafa misali game da biyayya?
10 Yesu ya fahimci muhimmancin yin biyayya da ta dace. Akwai lokacin da ya ce wa manzo Bitrus ya biya haraji ga masu mulki ’yan adam, har ya ba Bitrus kuɗin harajin da ya biya. Bulus ya rubuta: “Ku yi biyayya ga kowanne hukunci na mutane sabili da Ubangiji.” (1 Bitrus 2:13; Matta 17:24-27) Game da fitaccen misali na biyayya da Yesu ya yi, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane; da aka iske shi cikin kamanin mutum, ya ƙasƙantadda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa.”—Filibbiyawa 2:5-8.
11. Me ya sa Bitrus ya ƙarfafa mata su yi biyayya har ga mazansu da ba masu bi ba ne?
11 Sa’ad da yake ƙarfafa Kiristoci su yi biyayya ga masu mulki matsananta, marasa adalci na wannan duniya, Bitrus ya bayyana: “Gama zuwa wannan aka kiraye ku: gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bitrus 2:21) Bayan ya kwatanta yadda Yesu ya sha wahala da kuma yadda ya jimre, Bitrus ya ƙarfafa matan da mazansu ba masu bi ba ne, ya ce: “Hakanan, ku mata kuma, ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.”—1 Bitrus 3:1, 2.
12. Menene sakamakon biyayya da Yesu ya yi?
12 Waɗansu suna ganin cewa kumamanci ne mutum ya yi biyayya sa’ad da ake yi masa ba’a kuma ana zaginsa. Amma, Yesu bai ɗauke shi haka ba. Bitrus ya rubuta cewa: “Sa’ad da aka zage shi, ba ya mayarda zagi ba; sa’ad da ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba.” (1 Bitrus 2:23) Wasu da suka ga sa’ad da Yesu ya sha wahala sun zama masu bi, har da wani ɓarawon da ke kan gungumen azaba kusa da Yesu da kuma jarumi da ya ga lokacin da aka kashe shi. (Matta 27:38-44, 54; Markus 15:39; Luka 23:39-43) Haka nan ma, Bitrus ya nuna cewa wasu maza marasa bi har da waɗanda suke tsananta wa matansu a dā za su zama Kirista bayan sun lura da yadda matansu suke yin biyayya. Muna ganin hakan yana faruwa a yau.
Yadda Mata Za Su Shawo Kan Mazansu
13, 14. Ta yaya ne biyayya ga maza marasa bi ya kawo sakamako mai kyau?
13 Mata da suka zama masu bi sun shawo kan mazansu saboda halinsu na Kirista. A wani taro na gunduma na Shaidun Jehobah, wani maigida ya ce game da matarsa: “Yadda na bi da ita ya nuna cewa ni azzalumi ne. Duk da haka, ta yi ma ni ladabi sosai. Ba ta taɓa raina ni ba. Ba ta tilasta mini in bi imanin ta ba. Tana kula da ni cikin ƙauna. Idan za ta tafi taro, tana shirya mini abinci kuma ta yi aikace-aikacen gida kafin lokacin ya yi. Halinta ya soma sa ni sha’awar sanin Littafi Mai Tsarki. Ga shi na zama mashaidi!” Hakika, ya “rinjayu banda magana” saboda halin matarsa.
14 Kamar yadda Bitrus ya nanata, ba yawan maganar mace ba ce, amma abin da take yi ne zai kawo sakamako mai kyau. An ga cewa wannan gaskiya ce ta halin wata mata da ta koyi gaskiya daga Littafi Mai Tsarki kuma ta ƙudurta za ta je taron Kirista. Maigidanta ya ce, “Agnes, idan ki ka fita ta wannan ƙofar, kada ki dawo.” Saboda haka ba ta fita ta “wannan ƙofar” sai ta fita ta wata ƙofar dabam. A wata ranar taro, ya yi mata barazana: “Idan ki ka dawo ba za ki same ni ba.” Hakika, ba ta same shi ba, ya tafi har na kwana uku. Sa’ad da ya dawo, sai ta tambaye shi da ladabi: “Za ka so ka ci abinci?” Agnes ba ta daina bauta wa Jehobah ba. Daga baya maigidanta ya yarda zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ya keɓe kansa ga Allah, yanzu ya zama mai kula wanda yake da hakki da yawa.
15. Wane “ado” ne aka ce Kiristoci mata su yi?
15 Manzo Bitrus ya faɗi wani abu da mata da aka ambata a baya suka nuna, wato “ado,” amma wannan ba mai da hankali ga “kitson gashi” ko kuma “yafa tufafi masu ƙawa” ba ne. Maimakon haka, Bitrus ya ce: “Adonku ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya, abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.” Ana ganin irin wannan halin ta yadda take magana da kuma halin kirki maimakon zagi ko kuma yawan bukatar abubuwa. Ta yin hakan, mace Kirista tana wa maigidanta biyayya.—1 Bitrus 3:3, 4.
Misalai da Za a Yi Koyi da Su
16. Ta yaya ne Saratu ta zama misali mai kyau ga Kiristoci mata?
16 Bitrus ya rubuta: “Tsarkakan mata kuma na dā, waɗanda suna kafa bege ga Allah, suka yi ma kansu ado, suna zaman biyayya ga mazajensu.” (1 Bitrus 3:5) Waɗannan sun fahimci cewa faranta wa Jehobah rai ta wurin biyayya ga umurninsa zai kawo farin ciki a iyali da kuma ladar rai har abada. Bitrus ya faɗi cewa Saratu, matar Ibrahim kyakkyawa, “ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta.” Saratu ta taimaki maigidanta mai tsoron Allah, wanda Allah ya aika zuwa wata ƙasa mai nisa. Ta rabu da jin daɗin rayuwa kuma ta sadakar da ranta. (Farawa 12:1, 10-13) Bitrus ya yaba wa Saratu saboda misalinta mai kyau, ya ce: “Ku ne kuwa ’ya’yanta yanzu, idan kuna aika nagarta, ba ku cikin tsoro ga kowane abin firgitawa.”—1 Bitrus 3:6.
17. Me ya sa mai yiwuwa Bitrus yana maganar Abigail ne ga Kiristoci mata?
17 Abigail wata mata ce da ba ta jin tsoro kuma ta dogara ga Allah, mai yiwuwa Bitrus yana magana ne game da ita. Ita “macen mai-fahimi ce,” amma maigidanta Nabal “mutumin mai-tankiya ne mai-munanan ayuka.” Sa’ad da Nabal ya ƙi ya taimaki Dauda da mutanensa, sai suka shirya za su kashe Nabal da iyalansa. Amma Abigail ta ɗauki mataki ta ceci iyalinta. Ta ɗauki abinci a kan jaki ta je ta tare Dauda da mayaƙansa a hanya. Da ta ga Dauda, sai ta sauka daga kan jakinta, ta durƙusa ta roƙe shi kada ya yi saurin aikata abin da yake son ya yi. Abin da Abigail ta ce ya motsa Dauda sosai. “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni!” ya ce, “mai-albarka ce hikimarki.”—1 Samuila 25:2-33.
18. Idan wani wanda ba mijin su ba ne ya ce yana son su, wane misali ne ya kamata mata su tuna kuma me ya sa?
18 Wani misali mai kyau ga mata shi ne na ’yar Shulem da ta kasance da aminci ga makiyayi da ta yi alkawari za ta aura. Ƙaunar da take yi masa ya ci gaba duk da soyayyar da sarkin yake nuna mata. Sa’ad da take furta ƙaunarta ga makiyayin, ta ce: “Sa ni kamar hatimi a bisa zuciyarki, kamar hatimi a hannunki: gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa; . . . Ruwa mai-yawa ba shi da iko shi ɓice ƙauna, rigyawa ba ta da iko ta dulmaye ta.” (Waƙar Waƙoƙi 8:6, 7) Bari duka ’yan mata da suka yarda za su aure wani su kasance da aminci ga mazansu kuma su yi masu ladabi sosai.
Ƙarin Umurni na Allah
19, 20. (a) Wane dalili ne ya sa ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu? (b) Wane misali ne mai kyau aka kafa wa matan aure?
19 A ƙarshe, ka yi la’akari da nassi na jigonmu: “Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku.” (Afisawa 5:22) Me ya sa yin biyayya yake da muhimmanci? Sura ta gaba ta ce, “miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne.” Saboda haka, an aririce mata: “Kamar yadda ikilisiya take zaman biyayya ga Kristi, hakanan mataye su yi ga mazansu cikin dukan abu.”—Afisawa 5:23, 24, 33.
20 Don su yi biyayya ga wannan umurni, ya kamata mata su yi nazari kuma su bi misalin ikilisiyar Kirista na mabiya shafaffu. Don Allah ku karanta 2 Korinthiyawa 11:23-28 kuma ku yi koyi da abin da wani ɗan ikilisiyar wato manzo Bulus ya jimre cikin aminci ga Shugabansa, Yesu Kristi. Kamar Bulus, ya kamata mata da kuma sauran ’yan ikilisiya su kasance da aminci ga Yesu. Mata suna nuna haka ta wurin yin biyayya ga mazansu.
21. Menene zai ƙarfafa mata su ci gaba da yin biyayya ga mazansu?
21 Ko da yake mata da yawa ba sa son yin biyayya, mace mai hikima za ta yi la’akari da amfanin yin biyayya. Alal misali, idan maigidan marar bi ne, idan ta yi masa biyayya bisa ga al’amuran da ba su kauce wa dokokin Allah ba ko kuma ka’idodinsa, za ta samu ladar ta ‘ceci mijinta.’ (1 Korinthiyawa 7:13, 16) Bugu da ƙari, za ta yi farin cikin fahimtar cewa Jehobah Allah ya yi na’am da abin da ta yi kuma zai albarkace ta saboda ta bi misalin ƙaunataccen Ɗansa.
Ka Tuna?
• Me ya sa yake da wuya mace ta yi wa maigidanta ladabi?
• Me ya sa yin na’am da batun aure ba a bin wasa ba ne?
• Ta yaya ne Yesu ya zama misali ga mata, kuma menene amfanin bin misalinsa?
[Hoto a shafi na 13]
Me ya sa yin tunani kafin a yi na’am da batun aure yake da muhimmanci?
[Hoto a shafi na 15]
Menene mata za su koya daga misalin Abigail na cikin Littafi Mai Tsarki?