Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 10/1 pp. 11-15
  • “Ka Yi Murna Da Matar Kuruciyarka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Yi Murna Da Matar Kuruciyarka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Mai da Hankali da Zuciya Mai Rikici
  • “Mutum Mai-Hankali Yakan Hangi Masifa, Ya Ɓuya”
  • “Ka Zauna da Farin Ciki Tare da Mace Wadda Ka Ke Kaunatta”
  • A Lokacin “Wahala”
  • Babban Dalili
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Za A Iya Yin Nasara A Aure A Duniya Ta Yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Kasance Da Ra’ayi Mai Kyau Idan Kana Fuskantar Matsala A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 10/1 pp. 11-15

“Ka Yi Murna Da Matar Kuruciyarka”

“Ka yi murna da matar kurciyarka. . . Don me za ka jarabtu da karuwa?”—MISALAI 5:18, 20.

1, 2. Me ya sa aka ce soyayya tsakanin mata da miji abu ne mai kyau?

LITTAFI Mai Tsarki ba ya rufa-rufa a wajen magana game da jima’i. Misalai 5:18, 19 sun ce: “Maɓulɓularka ta zama mai-albarka: Ka yi murna da matar ƙuruciyarka. Kamar barewa ƙaunataciya da mariri mai-kyaun gani, bari mamanta su ishe ka kowane loto: Ka jarabtu da ƙaunarta kullayaumi.”

2 Furcin nan “maɓulɓularka” na nufin yin jima’i. Wannan kuwa abu ne mai kyau saboda soyayya tsakanin mata da miji kyauta ce daga wajen Allah. Wannan dangantakar tsakanin ma’aurata ne kawai. Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā marubucin Misalai, ya yi tambaya: “Gama don me za ka jarabtu da karuwa, ya ɗana, ka rungume ƙirjin baƙuwa?”—Misalai 5:20.

3. (a) Menene ya faru da aure masu yawa? (b) Yaya ne Allah ya ɗauki yin zina?

3 A ranar aurensu, mata da miji sukan yi alkawari za su ƙaunaci juna kuma su yi aminci da junansu. Duk da haka, aure da yawa sun rushe saboda zina. Bayan ya yi bincike wajen sau ashirin da biyar wani mai bincike ya ce: “Kashi 25 na mata da kashi 44 na maza sun taɓa yin zina.” Manzo Bulus ya ce: “Kada ku yaudaru; da masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza . . . ba za su gāji mulkin Allah ba.” (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Hakika haka yake. Dole ne Kiristoci na gaskiya su kauce wa yin zina, saboda mugun zunubi ne a gaban Allah. Me zai taimake mu mu sa ‘aure shi zama abin darajantuwa, kuma shi kasance mara-ƙazanta’?—Ibraniyawa 13:4.

Ka Mai da Hankali da Zuciya Mai Rikici

4. A waɗanne hanyoyi ne ma’aurata Kirista za su shiga cikin soyayya da waɗanda ba abokan aurensu ba da saninsu ba?

4 A irin wannan duniyar mai muguwar ɗabi’a da muke ciki, mutane da yawa suna da idanu ‘cike da zina, waɗanda ba su da iko su dena zunubi.’ (2 Bitrus 2:14) Da son ransu suna shiga soyayya da mazan da ba na su ba. A ƙasashe da yawa mata sun soma aikin ofis, kuma hakan ya ba su zarafin yin “soyayya a wajen aiki” da mazan da ba na su ba. Sai kuma a ɗakin hira na Intane wanda har mutane masu kunya ma sun soma soyayya ta wannan hanyar. Mutane da yawa sun faɗa cikin wannan hali ba tare da sanin cewa sun faɗa cikin tarko ba.

5, 6. Ta yaya ne wata Kirista ta shiga cikin mugun yanayi, kuma me muka koya?

5 Ka yi la’akari da wata Kirista da muka kira Maryamu, ta faɗa cikin wani yanayin da ya kusa kai ta ga yin zina. Maigidanta Mashaidin Jehobah ne, amma ba ya nuna wa iyalinsa ƙauna kamar yadda ya kamata. Maryamu ta tuna sa’ad da ta haɗu da wani abokin aikin maigidanta wasu shekaru da suka wuce. Mutumin yana da kirki, har daga baya ya nuna yana son addinin Maryamu. Maryamu ta ce: “Yana da kirki, ya bambanta da maigidana.” Ba da daɗewa ba Maryamu da abokin aikin maigidanta suka soma soyayya. Ta yi tunani, “Ban yi zina ba, kuma mutumin yana sha’awar sanin Littafi Mai Tsarki. Wataƙila zan iya taimaka masa.”

6 Maryamu ta dawo hankalinta kafin soyayyar ta kai ta ga yin zina. (Galatiyawa 5:19-21; Afisawa 4:19) Lamirinta ya fara damunta sai ta nemi ta gyara rayuwarta. Labarin Maryamu ya nuna cewa “zuciya ta fi komi rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irmiya 17:9) Littafi Mai Tsarki ya yi mana wannan gargaɗi: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa.” (Misalai 4:23) Ta yaya za mu iya yin hakan?

“Mutum Mai-Hankali Yakan Hangi Masifa, Ya Ɓuya”

7. Wace shawara ce da ke cikin Nassi ya kamata a bi, idan ana son a taimaka wa masu matsala a aure?

7 Manzo Bulus ya rubuta: “Wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.” (1 Korinthiyawa 10:12) Misalai 22:3 ta ce: “Mutum mai-hankali yakan hangi masifa, ya ɓuya.” Maimakon mu ce: “Ba abin da zai faru da ni,” zai yi kyau idan ka yi tunanin abubuwan da za su iya jefa ka cikin irin wannan matsalar. Alal misali, ka guji kasancewa kai kaɗai ne wadda take da damuwa a aurenta take zuwa wurinsa domin magance matsalar. (Misalai 11:14) Ka gaya mata cewa, tattauna matsalar aure da abokin aure ya fi, ko kuma da wata Kirista wadda take son aurenta ya yi nasara, ko kuma da dattawa. (Titus 2:3, 4) Dattawa na ikilisiyar Shaidun Jehobah suna ƙoƙari ta wannan hanya. Idan dattijo yana son ya yi magana da ’yar’uwa Kirista, ya yi magana da ita a fili, kamar a cikin Majami’ar Mulki.

8. Wane gargaɗi ne yake da kyau ga ma’aikata?

8 Ka lura da yanayi da zai iya kai wa ga soyayya a wajen aiki ko kuma a wani waje. Alal misali, idan ka ɗauki ƙarin lokaci kana aiki tare da wata, zai iya jawo gwaji. Ma’aurata maza ko mata, ku nuna da furcinku da halayenku cewa ba za ku yi soyayya da wadda ba abokiyar aurenku ba ce. Mai tsoron Allah, bai kamata ta jawo wa kanta mutane ta wurin yadda take sa tufafi da kuma kwalliya ba. (1 Timothawus 4:8; 6:11; 1 Bitrus 3:3, 4) Idan ka ajiye hoton matarka da na yaranka a wajen aikinka, hakan zai tuna maka da kuma wasu cewa kana son iyalinka. Kada ka yarda wasu su rinjaye ka.—Ayuba 31:1.

“Ka Zauna da Farin Ciki Tare da Mace Wadda Ka Ke Kaunatta”

9. Waɗanne abubuwa ne za su sa soyayya ta yi ƙarfi?

9 Kāre zuciyarmu yana bukatar fiye da guje wa mugun yanayi. Yin soyayya da wanda ba abokan aurenmu ba ne, yana nuna cewa maigida da matarsa ba sa mai da hankali ga bukatun juna. Zai iya yiwuwa cewa, maigidan ba ya kusa da matarsa ko kuma matar ba ta yin kusa da mijinta. Ba da daɗewa ba, a wajen aiki ko kuma a cikin ikilisiya za ku ga kamar wani yana da halin kirki da abokan aurenku ba su da shi. Bayan haka, sai ku soma soyayya mai ƙarfi. Waɗannan abubuwa da suka faru bi da bi suna nuna gaskiyar abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko.”—Yaƙub 1:14.

10. Ta yaya ne mata da miji za su sa soyayyarsu ta yi ƙarfi?

10 Maimakon ku je wajen wani wanda ba abokan aurenku ba ne, domin biyan bukatarku, ko don soyayya, dangantaka, ko kuma don ku jimre a lokacin yanayi mai tsanani, ya kamata mata da miji su yi ƙoƙari su gina dangantaka ta ƙauna da abokan aurensu. Ko yaya, ku zauna tare don ku kusaci juna. Ka tuna dalilin da ya sa ka soma soyayya. Ka tuna da yadda ka ke ji game da wadda ta zama abokiyar aurenka. Ka tuna da lokacin da ku ke farin ciki tare. Ka yi addu’a ga Allah game da damuwarka. Mai zabura Dauda ya roƙi Jehobah cewa: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina.” (Zabura 51:10) Ka ƙuduri aniyar za ka ‘zauna da farinciki tare da mace wadda ka ke ƙaunatta dukan kwanankinka masu-shuɗewa waɗanda Allah ya ba ka a duniya.’—Mai-Wa’azi 9:9.

11. Waɗanne abubuwa ne ilimi, hikima, da kuma fahimi suke yi a wajen ƙarfafa aure?

11 Ya kamata mu riƙa tuna cewa ilimi, hikima, da kuma fahimi suna da muhimmanci wajen ƙarfafa aure. Misalai 24:3, 4 sun ce: “Ta wurin hikima ake ginin gida: Ta wurin fahimi kuma ake kafassa: ta wurin ilimi kuma ana cika taskokinsa da dukan dukiya masu-tamani masu-daɗi.” Ƙauna, aminci, tsoron Allah da kuma bangaskiya, suna cikin abubuwa masu kyau da suke kawo farin ciki a gida. Kafin mu sami waɗannan abubuwa sai muna da sanin Allah. Ya kamata ma’aurata su zama ɗalibai masu himma na Nassosi. Menene muhimmancin hikima da fahimi? Kafin ka jimre wa matsalolin rayuwa na yau da gobe, ya kamata ka kasance mai hikima, wanda zai sa ka yi amfani da iliminka na Nassi. Mutum mai fahimi zai iya fahimtar ra’ayin matarsa. (Misalai 20:5) Ta wurin Sulemanu Jehobah ya ce: “Ɗana ka saurari hikimata: Ka karkata kunnenka ga fahimina.”—Misalai 5:1.

A Lokacin “Wahala”

12. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa ma’aurata suna fuskantar matsala?

12 Babu aure da ba a fuskantar matsala. Saboda Littafi Mai Tsarki ya ce mata da miji za su “sha wahala a cikin jiki.” (1 Korinthiyawa 7:28) Wani lokaci alhini, ciwo, tsanantawa da kuma waɗansu abubuwa za su iya jawo damuwa a cikin aure. Idan matsala ta taso, ya kamata ku nemi maganin matsalar tare ku ma’aurata masu aminci waɗanda suke faranta wa Jehobah rai.

13. A waɗanne wurare ne ya kamata mata da miji su binciki kansu?

13 Idan kuna fuskantar matsala a aure saboda yadda ku ke bi da juna, sai ku sa ƙwazo a wurin neman magance matsalar. Alal misali, wataƙila domin kuna yi wa juna baƙar magana ne ko da yaushe. (Misalai 12:18) Kamar yadda muka tattauna a talifi na baya, yin haka zai iya kawo matsala sosai. Karin magana na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma a zauna a cikin ƙasa mai-hamada, da a zauna tare da mace mai-tankiya mai-gunaguni.” (Misalai 21:19) Idan ke mace ce kina fuskantar matsala a aurenki, ki tambayi kanki, ‘Halina ne ya sa maigidana ba ya sha’awar zama tare da ni?’ Littafi Mai Tsarki ya ce wa magidanta: “Ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kolossiyawa 3:19) Idan kai maigida ne, ka tambayi kanka, ‘da gaske ne ba na ƙaunar matata kamar yadda ya kamata, shi ya sa take neman mai ƙaunar ta a waje?’ Hakika, babu hujjar da za ta sa a yi zina. Amma, tun da yake zai iya faruwa ya kamata a tattauna matsalar dalla-dalla.

14, 15. Me ya sa biɗan soyayya da wanda ba abokan aurenku ba ne, ba zai magance matsala a aurenku ba?

14 Biɗan soyayya da waɗanda ba abokan aurenku ba ne, ba zai magance matsalar da ku ke fuskanta ba. Ina ne irin wannan soyayya za ta kai ku? Wasu za su yi tunanin cewa, za ta kai su ga auren da ya fi na dā kyau. ‘Ballantana ma,’ ‘wannan mutum yana da halaye masu kyau da ni ke so a na miji.’ Amma irin wannan tunanin ba gaskiya ba ne, saboda duk wanda zai rabu da abokin aurensa ko kuma ya ba ka shawara ka rabu da na ka, ba ya ƙaunar tsarkakar aure. Saboda haka, ba shi da kyau mu yi tsammanin cewa irin wannan soyayya za ta kai ga aure da ya fi ta dā.

15 Maryamu da aka ambata da farko, ta yi tunani game da mugun sakamakon abin da ta yi, da yadda halinta zai sa ta, ko kuma wani ya rasa tagomashin Allah. (Galatiyawa 6:7) Ta ce: “Sa’ad da na soma tunanin son da ni ke yi wa abokin aikin maigidana, sai na fahimci cewa idan akwai zarafin da wannan mutum zai sami sanin gaskiya game Allah, ni ce ke hana shi. Mugun hali zai shafi kowannenmu kuma ya sa wasu su yi sanyin gwiwa!”—2 Korinthiyawa 6:3.

Babban Dalili

16. Menene wasu sakamakon lalata?

16 Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Gama leɓunan karuwa suna ɗiɗiga zuma, bakinta kuma ya fi mai sulɓi: Amma ƙarshenta da ɗaci ne kamar tafashiya, da kaifi kamar takobi mai-kaifi biyu.” (Misalai 5:3, 4) Sakamakon lalata ba shi da kyau kuma zai iya kai ga kisa. Waɗannan sun ƙunshi lamiri mai damuwa, cuta da ake ɗauka ta wajen jima’i, kuma zai bar abokan auren a cikin damuwa saboda rashin amincin ɗaya daga cikinsu. Hakika wannan dalili zai hana mu yin abin da zai sa mu yin zina.

17. Menene ainihin dalilin da ya sa ya kamata ma’aurata su riƙe aurensu?

17 Ainihin dalilin da ya sa zina ba ta da kyau shi ne, Jehobah wanda shi ne tushen aure kuma wanda ya ba mace da miji izini su yi jima’i, ya haramta yin zina. Annabi Malakai ya ce: “Zan zo kusa da ku domin shari’a; zan zama shaida mai-sauri a bisa . . . mazinata.” (Malachi 3:5) Game da abin da Jehobah yake gani, Misalai 5:12 ta ce: “Al’amuran mutum a gaban Ubangiji su ke, ya kan daidaita dukan tafarkunsa.” Hakika, “abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibraniyawa 4:13) Ainihin dalilin riƙe aure shi ne ko yaya ka yi zina a ɓoye, ko ba ka ɗauki cuta ba, ko kuma mutane ba su yi maka kallon banza ba, amma abin da ka yi ya lalata dangantakarka da Jehobah.

18, 19. Menene muka koya game da abin da Yusufu ya fuskanta a wajen matar Fotifa?

18 Misalin Yusufu, ɗan Yakubu uban iyali, ya nuna mana cewa son ya kasance da salama tare da Allah abu ne mai ƙarfi. Bayan ya sami tagomashi a idanun Fotifa, ma’aikacin Fir’auna, Yusufu ya sami matsayi a gidan Fotifa. Matar Fotifa ta lura cewa “Yusufu kyakyawa ne, murzaje kuma.” Kowace rana, tana ƙoƙari ta rinjayi Yusufu, amma ba ta ci nasara ba. Menene ya sa Yusufu ya kauce wa dukan gwajinta? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ya ƙi, ya kuwa ce ma matar ubangijinsa: Ga shi, ubangijina . . . ba ya kuwa hana ni komi sai ke, domin ke matatasa ce. Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah?”—Farawa 39:1-12.

19 Ko da yake Yusufu bai yi aure ba, ya tsarkaka ɗabi’arsa sa’ad da ya ƙi ya yi lalata da matar wani. Misalai 5:15 ta ce: “Ka ɗiba ruwa daga cikin kwadamin kanka, ka sha, ruwan daɗi kuma daga cikin rijiyar kanka.” Ka kiyaye yin soyayya da wadda ba abokiyar aurenka ba ce ba tare da saninka ba. Ka yi ƙoƙari ka sa ƙauna ta ƙarfafa aurenka, kuma ka yi ƙoƙari ka kawar da duk wata matsalar aure da ka ke fuskanta. Ko ta yaya, “Ka yi murna da matar ƙuruciyarka.”—Misalai 5:18.

Menene Ka Koya?

• Ta yaya ne Kiristoci za su shiga cikin soyayya ba tare da sun sani ba?

• Wane mataki ne ya kamata mutum ya ɗauka, don kada ya shiga cikin yin soyayya da wadda ba abokiyar aurensa ba?

• Menene ya kamata ma’aurata su yi idan suna fuskantar matsala?

• Menene ainihin dalilin da ya sa ya kamata ma’aurata su riƙe aurensu?

[Hoto a shafi na 12]

Abin baƙin ciki, wurin aiki zai iya zama wajen soyayya

[Hoto a shafi na 14]

‘Ta wurin ilimi kuma ana cika taskoki da dukan dukiya masu-daɗi’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba