Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 10/1 pp. 21-25
  • Ƙauna Tana Ƙarfafa Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙauna Tana Ƙarfafa Gaba Gaɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ƙauna ta Allah Ce”
  • Sun Nuna Gaba Gaɗi da Ƙauna
  • Kada Ka Ƙyale Ƙaunarka ta Yi Sanyi
  • Fuskantar Gwaji da Gaba Gaɗi
  • Ƙauna Tana Taimakon Masu Zunubi Su Koma ga Jehobah
  • “Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Ba Ni Karfin Hali
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • “Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • ‘Ku Yi Ƙarfi Ku Yi Gaba Gaɗi!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 10/1 pp. 21-25

Ƙauna Tana Ƙarfafa Gaba Gaɗi

“Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo.”—2 TIMOTHAWUS 1:7.

1, 2. (a) Menene ƙauna za ta motsa mutum ya yi? (b) Me ya sa gaba gaɗin Yesu ya yi fice?

WANI ango da amaryarsa suna iyo da na’ura a gaɓar teku na Australiya. Suna kan fitowa sai babban kifi ya so ya cinye matar. Da jarumtaka, mutumin ya ture matarsa gefe kuma sai kifin ya cinye shi. Gwauruwar ta ce a lokacin jana’izar: “Ya ba da ransa domina.”

2 Hakika, ƙauna za ta iya motsa ’yan adam su nuna gaba gaɗi na musamman. Yesu Kristi ya ce: “Ba wanda ya ke da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, mutum shi bada ransa domin abokansa.” (Yohanna 15:13) Bayan kusan sa’o’i 24 da Yesu ya faɗi waɗannan kalmomin sai ya ba da ransa, ba don mutum ɗaya ba kawai, amma dukan ’yan adam. (Matta 20:28) Ƙari ga haka, Yesu bai ba da ransa farat ɗaya ta ayyukan jarumtaka ba. Ya sani tun da wuri cewa za a yi masa ba’a kuma a zalunce shi, a yanka masa hukunci da bai dace ba, kuma a kashe shi a kan gungumen azaba. Ya kuma shirya almajiransa don wannan, yana cewa: “Ga mu, muna tafiya zuwa Urushalima; za a bada Ɗan mutum ga hannun manyan malamai da marubuta; za su hukunta masa mutuwa, su bashe shi ga hannun Al’ummai: za su yi masa ba’a kuma, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kashe shi.”—Markus 10:33, 34.

3. Me ya sa Yesu yake da gaba gaɗi sosai?

3 Me ya sa Yesu ya kasance da gaba gaɗi da babu kamarsa? Bangaskiya da tsoron Allah sun taimake shi sosai. (Ibraniyawa 5:7; 12:2) Amma, mafi muhimmanci Yesu yana da gaba gaɗi don yana ƙaunar Allah da kuma ’yan’uwansa ’yan adam. (1 Yohanna 3:16) Idan muka kasance da irin wannan ƙauna tare da bangaskiya da tsoron Allah, mu ma za mu iya nuna irin gaba gaɗin da Kristi ya nuna. (Afisawa 5:2) Ta yaya za mu koyi irin wannan ƙaunar? Muna bukatar mu fahimci Tushenta.

“Ƙauna ta Allah Ce”

4. Me ya sa za a ce Jehobah ne Tushen ƙauna?

4 Jehobah ƙauna ne da kuma shi ne Tushenta. Manzo Yohanna ya rubuta: “Masoya, mu yi ƙaunar junanmu: gama ƙauna ta Allah ce; dukan wanda ya ke yin ƙauna an haife shi daga wurin Allah, ya san Allah kuma. Wanda ba ya yin ƙauna ba, ba ya san Allah ba; gama Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:7, 8) Saboda haka, mutum zai koyi ƙauna irin na Allah sa’ad da ya kusaci Jehobah ta wurin cikakken sani kuma ya aikata bisa wannan sani ta yin biyayya da dukan zuciyarsa.—Filibbiyawa 1:9; Yaƙub 4:8; 1 Yohanna 5:3.

5, 6. Menene ya taimaki mabiyan Yesu na farko su nuna irin ƙauna da Kristi ya nuna?

5 A addu’arsa ta ƙarshe da manzanninsa 11 masu aminci, Yesu ya nuna nasabar da ke tsakanin sanin Allah da kuma ƙauna, yana cewa: “Na kuma sanar masu da sunanka, zan kuma sanasda shi; domin wannan ƙauna wadda ka ƙaunace ni da ita ta zauna cikinsu, ni kuma a cikinsu.” (Yohanna 17:26) Yesu ya taimaki almajiransa su koyi irin ƙaunar da ke tsakaninsa da Ubansa, ya nuna musu ta kalma da misali abin da sunan Allah ke wakilta, wato, halayen Allah masu ban al’ajabi. Shi ya sa Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”—Yohanna 14:9, 10; 17:8.

6 Irin ƙaunar da Kristi ya nuna ɗiya ce ta ruhun Allah. (Galatiyawa 5:22) Sa’ad da aka aika wa Kiristoci na farko ruhu mai tsarki da aka yi musu alkawarinsa a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sun tuna abubuwa da yawa da Yesu ya koya musu kuma sun fahimci ma’anar Nassosi da kyau. Wannan fahimi mai zurfi babu shakka ya ƙarfafa ƙaunarsu ga Allah. (Yohanna 14:26; 15:26) Menene sakamakon? Ko da ya saka ransu cikin haɗari, sun yi wa’azin bishara da gaba gaɗi da kuma himma.—Ayukan Manzanni 5:28, 29.

Sun Nuna Gaba Gaɗi da Ƙauna

7. Menene Bulus da Barnaba suka jimre a tafiye tafiyensu na wa’azi tare?

7 Manzo Bulus ya rubuta: “Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo.” (2 Timothawus 1:7) Bulus yana magana don abin da ya fuskanta. Ka yi la’akari da abin da ya same shi da Barnaba sa’ad da suke tafiye tafiyen aikinsu na wa’azi tare. Sun yi wa’azi a birane da yawa, har da Antakiya, Ikoniya, da Listira. A kowane birni, wasu mutane sun zama masu bi, amma wasu sun zama masu hamayya. (Ayukan Manzanni 13:2, 14, 45, 50; 14:1, 5) A Listira taron ’yan banza da suka fusata sun jejjefi Bulus suna zato ya mutu! “Amma sa’anda masu-bi suka kewaye shi, ya tashi, ya shiga cikin birni; washegari ya fita tare da Barnaba, suka tafi Darba.”—Ayukan Manzanni 14:6, 19, 20.

8. Ta yaya gaba gaɗin Bulus da Barnaba ya nuna cewa suna ƙaunar mutanen sosai?

8 Bulus da Barnaba sun tsorata ne su daina wa’azi don an yi ƙoƙarin a kashe Bulus? Ko kaɗan! Bayan da “suka yi masu bi dayawa,” a Darba, maza biyun “suka koma Listra, da Ikoniya da Antakiya.” Me ya sa? Domin su ƙarfafa sababbi su kasance da ƙarfi cikin bangaskiya. Bulus da Barnaba sun gaya musu: “Sai ta wurin wahala dayawa za mu shiga mulkin Allah.” A bayyane yake cewa suna da gaba gaɗi don suna ƙaunar ‘ ’yan tumakin’ Kristi sosai. (Ayukan Manzanni 14:21-23; Yohanna 21:15-17) Bayan sun naɗa dattawa a kowace sabuwar ikilisiya da suka kafa, sai ’yan’uwa biyun suka yi addu’a kuma suka “danƙa su ga Ubangiji, wanda suka bada gaskiya gareshi.”

9. Ta yaya dattawa da ke Afisas suka aikata ga ƙaunar da Bulus ya nuna musu?

9 Kiristoci na farko da yawa sun ƙaunace Bulus sosai domin shi mutumi ne mai ƙauna da gaba gaɗi. Ka tuna abin da ya faru a wani taro da Bulus ya yi da dattawa da ke Afisas, inda ya yi shekara uku kuma ya fuskanci hamayya sosai. (Ayukan Manzanni 20:17-31) Bayan ya ƙarfafa su su yi kiwon garken Allah da aka ɗanka musu, Bulus ya ɗurkusa, su duka suka yi addu’a tare. “Duka suka yi kuka mai-zafi, suka fāɗa ma wuyan Bulus, suna sumbatasa, yawancin baƙinzuciya da su ke yi domin kalma ne wadda ya faɗi, cewa, ba za su ƙara ganin fuskatasa ba.” Waɗannan ’yan’uwan suna ƙaunar Bulus sosai! Hakika, sa’ad da lokaci ya zo da za su tafi, da kyar Bulus da abokan tafiyarsa suka “rabu” da su domin dattawan ba sa son su tafi.—Ayukan Manzanni 20:36–21:1.

10. Ta yaya Shaidun Jehobah na zamani suka nuna ƙauna ta gaba gaɗi ga juna?

10 A yau, ana ƙaunar masu kula masu ziyara, dattawan ikilisiya, da wasu da yawa sosai domin gaba gaɗi da suka nuna a madadin tumakin Jehobah. Alal misali, a ƙasashen da yaƙin basasa ya ragargaje ko kuma inda aka hana aikin wa’azi, masu kula masu ziyara da matansu sun sa rayuwarsu da ’yancinsu cikin haɗari don su ziyarci ikilisiyoyi. Hakanan ma, Shaidu da yawa sun sha wahala a wurin sarakuna abokan gaba da mabiyansu domin sun ƙi su ci amanar ’yan’uwansu Shaidu ko kuma su faɗi inda suke samun abinci na ruhaniya. An tsananta wa shaidu da yawa, an gana musu azaba, har ma an kashe su domin ba za su daina wa’azin bishara ba ko kuma su daina tarayya da ’yan’uwa masu bi a taron Kirista. (Ayukan Manzanni 5:28, 29; Ibraniyawa 10:24, 25) Bari mu yi koyi da bangaskiya da ƙauna irin ta waɗannan ’yan’uwa masu gaba gaɗi!—1 Tassalunikawa 1:6.

Kada Ka Ƙyale Ƙaunarka ta Yi Sanyi

11. A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan yake yaƙi na ruhaniya da bayin Jehobah, menene suke bukatar su yi?

11 Sa’ad da aka jefo da Shaiɗan zuwa duniya, ya ƙuduri aniya ya nuna fushinsa a kan bayin Jehobah domin suna “kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 17) Tsanantawa yana cikin dabarun da Iblis yake amfani da su. Sau da yawa, wannan dabara ba ta shafansu domin tana sa mutanen Allah su yi kurkusa da juna don ƙaunarsu kuma tana motsa da yawa cikinsu su kasance da himma ƙwarai. Sha’awar zunubi ne wata dabara da Shaiɗan yake amfani da ita. Don a tsayayya wa wannan dabara ana bukatar wani irin gaba gaɗi domin yaƙin game da sha’awoyi ne da ba su dace ba cikin zuciyarmu ‘mai rikici da kuma ciwuta.’—Irmiya 17:9; Yaƙub 1:14, 15.

12. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da “ruhun duniya” don ya raunana ƙaunarmu ga Allah?

12 “Ruhun duniya” wani makami ne mai iko sosai da Shaiɗan yake amfani da shi, wato, halinta ko motsawa, da ya saɓa wa ruhu mai tsarki na Allah. (1 Korinthiyawa 2:12) Ruhun duniya na ɗaukaka haɗama da abubuwan mallaka, wato, “sha’awar idanu.” (1 Yohanna 2:16; 1 Timothawus 6:9, 10) Ko da abubuwan mallaka da kuɗi suna da amfani, idan muna son su fiye da Allah, to, Shaiɗan ya yi nasara. “Iko” na ruhun duniya an yi su ne domin sha’awoyin jiki, dabararsa da ke cin gaba kamar iska take da ake sheƙa a ko’ina. Kada ka ƙyale ruhun duniya ya shafi zuciyarka!—Afisawa 2:2, 3; Misalai 4:23.

13. Ta yaya za a gwada gaba gaɗinmu na kasancewa da tsabtar ɗabi’a?

13 Amma, ana bukatar gaba gaɗi na tsabtar ɗabi’a don a tsayayya wa ruhun duniya kuma a ƙi ta. Alal misali, mutum na bukatar gaba gaɗi don ya tashi ya fita daga filin wasa ko kuma ya kashe kwamfuta ko talabijin sa’ad da ake abubuwa da ba su dace ba. Ana bukatar gaba gaɗi don a ƙi da matsi na tsara mai lahani kuma a daina tarayya da miyagu. Hakanan ma, muna bukatar gaba gaɗi don mu ɗaukaka dokokin Allah da ƙa’idodinsa sa’ad da abokan makaranta, abokan aiki, maƙwabta, ko kuma dangi suke mana ba’a.—1 Korinthiyawa 15:33; 1 Yohanna 5:19.

14. Menene ya kamata mu yi idan ruhun duniya ya shafe mu?

14 Shi ya sa yake da muhimmanci mu ƙarfafa ƙaunarmu ga Allah da kuma ’yan’uwanmu na ruhaniya. Ka ba da lokaci ka bincika muradinka da salon rayuwarka ka ga ko ruhun duniya yana shafanka a wata hanya. Idan ya shafe ka ko kaɗan ma, ka yi wa Jehobah addu’a ya ba ka gaba gaɗi don ka kawar da shi. Jehobah zai amsa roƙonka na gaske. (Zabura 51:17) Ƙari ga haka, ruhunsa ya fi na duniya ƙarfi.—1 Yohanna 4:4.

Fuskantar Gwaji da Gaba Gaɗi

15, 16. Ta yaya nuna ƙauna kamar Kristi take taimakonmu mu jimre da gwaji? Ka ba da misali.

15 Wasu wahaloli da bayin Jehobah suke jimrewa da shi sun ƙunshi sakamakon ajizanci da kuma tsufa da sau da yawa ke kawo ciwo, naƙasa, baƙin ciki, da sauransu. (Romawa 8:22) Ƙauna irin ta Kristi za ta taimake mu mu jimre da wannan gwaji. Ka yi la’akari da misalin Namangolwa, da aka yi renonta a iyalin Kirista a Zambiya. Namangolwa ta naƙasa sa’ad da take ’yar shekara biyu. Ta ce: “Yanayi na ya dame ni, ina tunani cewa kamani na zai tsoratar da mutane. Amma ’yan’uwana na ruhaniya sun taimake ni na kasance da ra’ayi dabam. Saboda haka, na daina damuwa game da yanayina, kuma ba da daɗewa ba na yi baftisma.”

16 Ko da yake Namangolwa tana da keken guragu, sau da yawa tana tafiya da hannayenta da kuma gwiwa sa’ad da take tafiya a hanya mai yashi. Duk da haka, tana hidimar majagaba na ɗan lokaci aƙalla wata biyu a kowace shekara. Wata mata ta yi kuka sa’ad da Namangolwa ta yi mata wa’azi. Me ya sa? Domin ta yi sha’awar bangaskiya da gaba gaɗin ’yar’uwarmu. Jehobah ya albarkaci Namangolwa, da yake biyar cikin ɗalibanta na Littafi Mai Tsarki sun yi baftisma, ɗaya dattijo ne a ikilisiyarsu. Ta ce, “sau da yawa ƙafafuna suna ciwo sosai, amma ba na barin wannan ya hana ni.” Wannan ’yar’uwa tana cikin Shaidu da yawa a dukan duniya da suka raunana a jiki amma suna himma sosai domin suna ƙaunar Allah da maƙwabtansu. Irin waɗannan muradi ne a gaban Jehobah!—Haggai 2:7.

17, 18. Menene ke taimakon mutane da yawa su jimre da ciwo da wasu gwaji? Ka ba da wasu misalai daga yankinku.

17 Ciwo mai tsanani zai iya sa mutum sanyin gwiwa da kuma baƙin ciki. Wani dattijo ya ce: “A rukunin nazarin littafi da nake halartar taro, wata ’yar’uwa tana da ciwon sukari da na ƙoda, wata tana da cutar daji, biyu suna da amosanin gaɓɓai mai tsanani, wata kuma tana ciwon da ke halaka garkuwan jiki da ciwon da ke sa jijiya, agara, da kuma tsoka zafi sosai. Wani lokaci suna yin sanyin gwiwa. Duk da haka, ba sa fasa taro sai lokacin da suke ciwo sosai ko kuma suna asibiti. Dukansu na fita hidimar fage a kai a kai. Suna tuna mini Bulus wanda ya ce: ‘Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.’ Ina sha’awar ƙaunarsu da gaba gaɗinsu. Yanayinsu ya sa su san ma’anar rayuwa da abin da ainihi ya fi muhimmanci.”—2 Korinthiyawa 12:10.

18 Idan kana fama da naƙasa, ciwo, ko wata matsala, ka “yi addu’a ba fasawa” ka sami taimako don kada ka zama wanda zai yi sanyin gwiwa. (1 Tassalunikawa 5:14, 17) Hakika, wani lokaci za ka yi baƙin ciki, amma ka yi ƙoƙari ka mai da hankali a kan abubuwa na ruhaniya masu ban ƙarfafa, musamman begenmu mai tamani na Mulki. Wata ’yar’uwa ta ce, “hidimar fage ne magani na.” Gaya wa wasu bishara na taimakonta ta kasance da ra’ayi mai kyau.

Ƙauna Tana Taimakon Masu Zunubi Su Koma ga Jehobah

19, 20. (a) Menene zai taimaki waɗanda suka yi zunubi su kasance da gaba gaɗi su koma ga Jehobah? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

19 Ba ya yi wa mutane da yawa da suka raunana a ruhaniya ko kuma suka yi zunubi sauƙi su koma ga Jehobah. Amma irin waɗannan za su sami gaba gaɗi da suke bukata idan suka tuba da gaske kuma suka sabonta ƙaunarsu ga Allah. Ka yi la’akari da Mario, da ke da zama a Amirka.a Mario ya bar ikilisiya ya zama mashayi kuma bayan shekara 20 aka saka shi a kurkuku. “Na soma tunani sosai game da rayuwata na nan gaba kuma na soma karanta Littafi Mai Tsarki kuma,” in ji Mario. “Da shigewar lokaci, na fahimci halayen Jehobah, musamman jinƙansa, da nake addu’a a kai a kai ya nuna mini. Bayan da aka sake ni daga kurkuku, na daina tarayya da abokai na na dā, na soma halartar taron Kirista, bayan haka aka mai da ni cikin ikilisiya. Ina girbe sakamakon abin da na yi a jikina, amma yanzu ina da bege mai ban al’ajabi. Ina gode wa Jehobah sosai don juyayinsa da gafara da ya yi mini.”—Zabura 103:9-13; 130:3, 4; Galatiyawa 6:7, 8.

20 Hakika, waɗanda suke cikin irin yanayin Mario za su yi iya ƙoƙarinsu su koma ga Jehobah. Amma ƙaunarsu ta wajen nazarin Littafi Mai Tsarki, addu’a, da yin bimbini zai ba su gaba gaɗi da ƙuduri da suke bukata. Bege na Mulki ya ƙarfafa Mario. Hakika, tare da ƙauna, da tsoron Allah, bege zai iya zama iko mai motsawa a rayuwarmu. A talifi na gaba za mu bincika wannan kyauta ta ruhaniya mai tamani sosai.

[Hasiya]

a An canja sunan.

Za Ka Iya Amsawa?

• Ta yaya ƙauna ta sa Yesu yake da gaba gaɗi na musamman?

• Ta yaya ƙaunar ’yan’uwansu ya sa Bulus da Barnaba su kasance da gaba gaɗi da babu na biyunsa?

• Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya kawar da ƙaunar Kirista?

• Idan muna ƙaunar Jehobah za mu kasance da gaba gaɗi mu jimre wane gwaji?

[Hoto a shafi na 23]

Da yake Bulus yana ƙaunar mutane wannan ya sa ya kasance da gaba gaɗi da yake bukata don ya jimre

[Hoto a shafi na 24]

Ana bukatar gaba gaɗi don a ɗaukaka mizanan Allah

[Hoto a shafi na 24]

Namangolwa Sututu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba