Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 2/15 pp. 10-14
  • “Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHAIDU MASU ƘARFIN ZUCIYA A MUGUWAR DUNIYA
  • SUN KASANCE DA BANGASKIYA DA ƘARFIN ZUCIYA
  • MATA DA SUKA BAUTA WA ALLAH DA ƘARFIN ZUCIYA
  • KALAMINMU ZA SU IYA SA MUTANE SU YI ƘARFIN ZUCIYA
  • ESTHER SARAUNIYA CE MAI ƘARFIN ZUCIYA
  • KA “YI ƘARFIN ZUCIYA”
  • “KA YI ƘARFIN HALI!”
  • “Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Ƙarfafa​—Jehobah Yana Tare da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kasancewa da Ƙarfin Zuciya Bai Fi Ƙarfinmu Ba
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • ‘Ku Yi Ƙarfi Ku Yi Gaba Gaɗi!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 2/15 pp. 10-14

“Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai”

“Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya ƙwarai . . . gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai.”—JOSH. 1:7-9.

MENE NE AMSARKA?

․․․․․

A waɗanne hanyoyi ne Anuhu da Nuhu suka nuna ƙarfin zuciya?

․․․․․

Ta yaya wasu mata a zamanin dā suka nuna misali na kasancewa da bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya?

․․․․․

Waɗanne misalan matasa da suka kasance da ƙarfin zuciya ne suka burge ka?

1, 2. (a) Mene ne ake bukata a wasu lokatai don a yi zaɓi mai kyau a rayuwa? (b) Mene ne za mu koya daga wannan talifin?

ƘARFIN zuciya ya bambanta da jin tsoro da rashin gaba gaɗi da kuma kumamanci. Za mu iya kwatanta mutum mai ƙarfin zuciya a matsayin mai ƙarfi da kuma gaba gaɗi. Amma a wasu lokatai, ana bukatar ƙarfin zuciya kawai domin a yi abin da yake da kyau a rayuwarmu ta yau da kullum.

2 Wasu mutane da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki sun kasance da gaba gaɗi sa’ad da suke fuskantar yanayi mai wuya. Wasu kuma sun kasance da ƙarfin zuciya a yanayin da bayin Jehobah gabaki ɗaya suke fuskanta kullum. Mene ne za mu iya koya daga misalan mutane da suka nuna ƙarfin zuciya da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu kasance da ƙarfin zuciya?

SHAIDU MASU ƘARFIN ZUCIYA A MUGUWAR DUNIYA

3. Wane annabci ne Anuhu ya yi game da miyagun mutane?

3 Mutanen da suka wanzu a duniya kafin Rigyawa ta zamanin Nuhu suna bukatar ƙarfin zuciya don su zama shaidun Jehobah. Duk da haka, Anuhu, mutum “na bakwai daga Adamu” ya idar da wannan saƙo na annabci: “Ku duba, ga Ubangiji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya hukumta shari’a bisa dukan mutane, domin shi kāda dukan masu-fajirci kuma a kan dukan ayyukansu na fajirci da suka yi cikin fajircinsu, da dukan maganganu na bātanci waɗanda masu-zunubi masu-fajirci suka ambace shi da su.” (Yahu. 14, 15) Anuhu ya yi magana kamar waɗannan abubuwa sun riga sun faru domin babu shakka wannan annabci zai cika. Kuma rigyawar ta halaka miyagun mutane.

4. Nuhu ya yi ‘tafiya da Allah’ duk da wane yanayi?

4 An yi Rigyawar a shekara ta 2370 K.Z., fiye da shekaru 650 bayan annabcin Anuhu. A wannan lokacin aka haifi Nuhu kuma ya samu iyali kuma ya gina jirgi tare da ’ya’yansa maza. Mugayen mala’iku sun canja jikinsu zuwa na ’yan Adam kuma suka auri kyawawan mata kuma suka haifa musu Ƙattai. Yawancin mutanen mugaye ne, kuma mugunta ta cika ko’ina a duniya. (Far. 6:1-5, 9, 11) Duk da irin wannan yanayin, Nuhu ya yi “tafiya tare da Allah” kuma ya yi wa’azi da gaba gaɗi a matsayin “mai-shelan adalci.” (Karanta 2 Bitrus 2:4, 5.) Muna bukatar nuna irin wannan gaba gaɗi a waɗannan kwanaki na ƙarshe.

SUN KASANCE DA BANGASKIYA DA ƘARFIN ZUCIYA

5. Ta yaya Musa ya kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi?

5 Musa ya nuna misali mai kyau na bangaskiya da ƙarfin zuciya. (Ibran. 11:24-27) Allah ya yi amfani da shi daga shekara ta 1513 zuwa 1473 K.Z., don ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar da kuma yi musu ja-gora a cikin jeji. Musa yana ganin ba zai iya wannan aikin ba, amma duk da haka ya yi aikin. (Fit. 6:12) Da shi da ƙanensa Haruna, sun bayyana a gaban azzalumi Fir’auna na ƙasar Masar a kai a kai. Kuma da gaba gaɗi sun sanar masa da Annoba Goma da Jehobah ya yi amfani da ita don ya kunyatar da allolin Masar kuma ya ceci mutanensa. (Fit., surori 7-12) Musa ya kasance da bangaskiya da gaba gaɗi domin Allah ya tallafa masa sosai, kamar yadda yake mana.—K. Sha 33:27.

6. Idan masu mulki suka tuhume mu, ta yaya za mu iya ba da shaida da gaba gaɗi?

6 Muna bukatar ƙarfin zuciya kamar Musa, gama Yesu ya ce: “A gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni, domin shaida garesu da Al’ummai kuma. Amma sa’anda sun bashe ku, kada hankalinku ya tashi a kan irin magana da za ku yi, ko kuwa abin da za ku faɗi: gama a cikin sa’an nan za a ba ku abin da za ku faɗi. Gama ba ku ne kuna faɗi ba, amma Ruhun Ubanku ne mai-faɗi a cikinku. Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al’ummai kuma. Lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin. Domin ba ku ne ke magana ba, Ruhun Ubanku ne ke magana ta bakinku.” (Mat. 10:18-20) Idan masu mulki suka tuhume mu, ruhun Jehobah zai taimaka mana mu ba da shaida da bangaskiya da gaba gaɗi cikin ladabi.—Karanta Luka 12:11, 12.

7. Me ya sa Joshua ya kasance da gaba gaɗi kuma ya yi nasara?

7 Yin nazarin Dokar Allah a kai a kai ne ya ƙarfafa bangaskiya da gaba gaɗin Joshua, wanda ya ɗauki matsayin Musa. A shekara ta 1473 K.Z., Isra’ila ta kasance a shirye don ta shiga Ƙasar Alkawari. Allah ya umurci Joshua: “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya ƙwarai.” Kuma Allah ya gaya wa Joshua cewa idan ya yi biyayya zai yi hikima kuma ya yi aikinsa da kyau. Allah ya gaya masa: “Kada ka tsorata, kada ka yi fargaba kuma: gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai dukan inda ka nufa.” (Josh. 1:7-9) Babu shakka, waɗannan kalmomin sun ƙarfafa Joshua! Kuma Allah ya kasance tare da shi, domin an gama mallakar yawancin wurare na Ƙasar Alkawari cikin shekara shida kawai, wato a shekara ta 1467 K.Z.

MATA DA SUKA BAUTA WA ALLAH DA ƘARFIN ZUCIYA

8. Mene ne muka koya daga bangaskiya da ƙarfin zuciya na Rahab?

8 A dā, mata da yawa sun kasance da ƙarfin zuciya a hidimarsu ga Jehobah. Alal misali, Rahab karuwa da ke Yariko ta kasance da bangaskiya ga Allah. Ta nuna gaba gaɗi sa’ad da ta ɓoye ’yan leƙen asiri biyu da Joshua ya aika, kuma sa’ad da sarkin ya turo mutane su nemo waɗannan ’yan leƙen asiri, ba ta faɗar musu inda suke ba. An cece ta da iyalinta sa’ad da Isra’ilawa suka ci birnin Yariko. Rahab ta daina karuwanci, ta soma bauta wa Jehobah da aminci kuma ta zama kakar Almasihu. (Josh. 2:1-6; 6:22, 23; Mat. 1:1, 5) An albarkace ta sosai don bangaskiya da kuma ƙarfin zuciyarta!

9. Ta yaya Deborah da Barak da Jael suka nuna ƙarfin zuciya?

9 Bayan rasuwar Joshua a misalin shekara ta 1450 K.Z., Allah ya naɗa mutane a matsayin alƙalai a Isra’ila. Wani Sarkin Kan’ana mai suna Jabin ya zalunci Isra’ilawa shekara 20, amma Allah ya sa annabiya Deborah ta gaya wa Alƙali Barak ya yaƙi wannan sarkin. Barak ya tara mutane 10,000 a Dutsen Tabor kuma ya kasance a shirye ya soma yaƙi da Sisera, shugaban sojojin Jabin, wanda ya shiga kwarin Kishon tare da sojojinsa da karusan yaƙi 900. Sa’ad da Isra’ilawa suka shiga cikin kwarin, Allah ya sa aka yi rigyawa farat ɗaya da ta sa bakin dāga ya cika da taɓo kuma hakan ya naƙasa karusan Kan’ana. Sojojin Barak suka ci yaƙin kuma “dukan rundunar yaƙin Sisera suka faɗi da kaifin takobi.” Sisera ya nemi mafaka a tanti Jael, amma ta kashe shi sa’ad da yake barci. Daidai da annabcin Deborah, Jael ce ta samu “darajar wannan” nasarar. Domin Deborah da Barak da Jael sun yi ƙarfin zuciya, Isra’ila “kuwa ta sami hutu shekara arba’in.” (Alƙa. 4:1-9, 14-22; 5:20, 21, 31) Maza da mata da yawa sun kasance da irin wannan bangaskiya da gaba gaɗi.

KALAMINMU ZA SU IYA SA MUTANE SU YI ƘARFIN ZUCIYA

10. Ta yaya muka sani cewa abin da muka faɗa zai iya sa wasu su yi ƙarfin zuciya?

10 Abin da muka faɗa yana iya taimaka wa masu bauta wa Jehobah su yi ƙarfin zuciya. A ƙarni na 11 K.Z., Sarki Dauda ya gaya wa ɗansa Sulemanu: “Ka yi ƙarfi, ka yi mazakuta, ka yi shi: kada ka ji tsoro, kada ka yi fargaba: gama Ubangiji Allah, Allahna ke nan, yana tare da kai, ba kuwa za shi tauye maka, ba za ya yashe ka ba, har an gama dukan aikin hidimar gidan Ubangiji.” (1 Laba. 28:20) Sulemanu ya kasance da gaba gaɗi kuma ya gina kyakkyawan haikalin Jehobah a Urushalima.

11. Ta yaya kalamin wata yarinya Ba’isra’iliya mai gaba gaɗi ya taimaki wani mutum?

11 A ƙarni na goma K.Z., kalamin wata yarinya Ba’isra’iliya mai gaba gaɗi ya kasance albarka ga wani kuturu. Suriyawa ne suka kama yarinyar kuma ta zama baiwar Naaman, shugaban sojojin mutanen Suriya, kuma shi kuturu ne. Da yake ta san game da mu’ujizoji da Jehobah ya yi ta wurin Elisha, sai ta gaya wa matar Naaman cewa annabin Allah zai warkar da mijinta idan zai je ya same shi a Isra’ila. Aka warkar da Naaman ta mu’ujiza sa’ad da ya je Isra’ila kuma ya zama mai bauta wa Jehobah. (2 Sar. 5:1-3, 10-17) Idan kai matashi ne mai ƙaunar Allah kamar wannan yarinyar, Allah zai ba ka gaba gaɗin yin wa’azi ga malamanka da abokan makarantarka da kuma wasu.

12. Ta yaya kalamin Sarki Hezekiya ya shafi talakawansa?

12 Zaɓan kalamin da ya dace zai iya sa mutum ya yi ƙarfin zuciya a lokacin wahala. Sa’ad da Assuriyawa suke son su kai wa Urushalima hari a ƙarni na takwas K.Z., Sarki Hezekiya ya gaya wa talakawansa: “Ku yi ƙarfi, ku yi mazakuta, kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba domin sarkin Assyria, ko domin babbar runduna da ke tare da shi; gama tare da mu akwai wanda ya fi nasa: tare da shi akwai iko na jiki, amma a garemu akwai Ubangiji, Allahnmu, mai-taimakonmu, wanda za ya yi yaƙi dominmu.” Ta yaya wannan kalamin ya shafi mutanen? “Jama’a kuwa suka dogara ga maganar Hezekiah.” (2 Laba. 32:7, 8) Irin wannan kalami na ƙarfafa zai taimaka mana da kuma wasu Kiristoci su kasance da gaba gaɗi sosai sa’ad da ake tsananta mana.

13. Me ya sa Obadiah bawan Sarki Ahab ya zama misali mai kyau na mai gaba gaɗi?

13 A wasu lokatai, muna nuna gaba gaɗi ta abin da ba mu faɗa ba. A ƙarni na goma K.Z., Obadiah bawan Sarki Ahab da gaba gaɗi ya ɓoye annabawa ɗari na Jehobah “hamsin hamsin, cikin wani kogon dutse,” don kada muguwar Sarauniya Jezebel ta kashe su. (1 Sar. 18:4) Kamar Obadiah mai jin tsoron Allah, bayin Jehobah da yawa a yau da gaba gaɗi sun kāre ’yan’uwansu Kiristoci ta wajen ƙin ba masu tsananta musu bayani game da su.

ESTHER SARAUNIYA CE MAI ƘARFIN ZUCIYA

14, 15. Ta yaya Sarauniya Esther ta nuna bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya kuma da wane sakamako?

14 Sarauniya Esther ta nuna bangaskiya sosai da kuma gaba gaɗi sa’ad da Haman mugu ya ƙulla ya kashe dukan Yahudawa da ke Fasiya a ƙarni na biyar K.Z. Shi ya sa suka yi makoki da kuma addu’a da dukan zuciyarsu! (Esther 4:1-3) Sarauniya Esther ta damu ƙwarai. Ɗan kawunta Mordekai, ya aika mata dokar da ta ba da izini cewa a kashe Yahudawa kuma ya umurce ta ta bayyana a gaban sarki ta roƙe shi ya taimaki mutanenta. Amma za a kashe duk wanda ya je gaban sarki ba tare da izini ba.—Esther 4:4-11.

15 Amma, Mordekai ya gaya wa Esther: ‘Idan kin yi shuru ceto zai zo daga wani wuri, wa ya sani ko domin wannan irin lokaci ne kin sami sarauta?’ Esther ta gaya wa Mordekai ya tara Yahudawa da ke Sushan don su yi azumi. Ta ce: “Da hakanan za ni wurin sarki, ko da shi ke ba bisa ga shari’a ba ne: idan kuwa na lalace, na lalace ke nan.” (Esther 4:12-17) Esther ta yi ƙarfin zuciya, kuma littafin da aka rubuta da sunanta ya nuna cewa Allah ya ceci mutanensa. A yau, Kiristoci shafaffu da ’yan’uwansu waɗansu tumaki suna nuna irin wannan ƙarfin zuciya sa’ad da suke fuskantar gwaji, kuma “mai-jin addu’a” yana tare da su a ko da yaushe.—Karanta Zabura 65:2; 118:6.

KA “YI ƘARFIN ZUCIYA”

16. Wane misali ne Yesu ya kafa wa matasa a ikilisiya?

16 A wani lokaci a ƙarni na farko A.Z., an samu Yesu ɗan shekara 12 a haikali, “yana zaune a tsakiyar malamai, yana jinsu, yana kuwa yi masu tambayoyi.” Bugu ga ƙari, “dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da magana da ya ke mayarwa.” (Luk 2:41-50) Ko da yake shi yaro ne, Yesu yana da bangaskiya da ƙarfin zuciya da ake bukata don ya yi wa tsofaffin malamai da suke haikali tambayoyi. Tunawa da misalin Yesu zai taimaka wa matasa a cikin ikilisiyar Kirista su yi amfani da zarafin da suka samu don su ‘amsa wa kowane mai-tambayarsu dalilin begensu.’—1 Bit. 3:15.

17. Me ya sa Yesu ya aririci almajiransa su “yi ƙarfin zuciya,” kuma me ya sa muke bukatar mu yi hakan?

17 Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku duba, sa’a tana zuwa, har ma ta zo, inda za ku warwatse, kowa zuwa nasa, za ku bar ni ni kaɗai: amma ba ni ɗaya ba ne, gama Uba yana tare da ni. Waɗannan abubuwa na faɗa maku domin a cikina ku sami salama. A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi [ƙarfin zuciya], na yi nasara da duniya.” (Yoh. 16:32, 33) Kamar mabiya na farko na Yesu, duniya ta tsane mu, amma ba za mu zama kamar mutanen duniya ba. Yin bimbini a kan tafarkin gaba gaɗi na Ɗan Allah zai sa mu kasance da ƙarfin zuciya mu ware kanmu daga wannan duniya. Ya yi nasara da duniya, mu ma za mu iya yin hakan.—Yoh. 17:16; Yaƙ. 1:27.

“KA YI ƘARFIN HALI!”

18, 19. Ta yaya manzo Bulus ya nuna bangaskiya da ƙarfin hali?

18 Manzo Bulus ya jimre da gwaje-gwaje da yawa. A wani lokaci, da Yahudawa da suke Urushalima sun kashe shi, amma sojojin Roma suka cece shi. Da dare, “Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.” (A. M. 23:11, Littafi Mai Tsarki) Bulus ya yi hakan.

19 Bulus bai ji tsoro ba sa’ad da ya tsauta wa “mafifitan manzanni” da suke son su ɓata ikilisiyar da ke Korinti. (2 Kor. 11:5; 12:11) Ba kamarsu ba, Bulus zai iya nuna cewa shi manzo na gaskiya ne domin dukan abubuwa da ya jimre, kamar zama a kurkuku da kuma dūka da tafiye-tafiye masu haɗari da wahaloli da yunwa da ƙishirwa da rashin barci da kuma alhini game da dukan ikilisiyoyi. (Karanta 2 Korintiyawa 11:23-28.) Misali mafi kyau na bangaskiya da ƙarfin hali na Bulus ya nuna cewa Allah ne ya ba shi ƙarfi!

20, 21. (a) Ka ba da misalin da ya nuna cewa dole ne mu kasance da ƙarfin zuciya. (b) A waɗanne yanayi ne muke bukatar mu nuna ƙarfin zuciya, kuma wane tabbaci za mu kasance da shi?

20 Ba dukan Kiristoci ba ne za su fuskanci tsanantawa mai tsanani ba. Amma dukanmu muna bukatar gaba gaɗi domin mu jimre da yanayi mai wuya a rayuwa. Alal misali, wani matashi a ƙasar Brazil yana cikin rukunin ’yan daba. Bayan ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ya ga cewa yana bukatar ya yi canje-canje, amma za a kashe duk wanda ya bar rukunin. Ya yi addu’a kuma ya yi amfani da nassosi don ya nuna wa shugaban dalilin da ya sa ba zai iya kasance cikin rukunin ba. An ƙyale matashin ya bar rukunin ba tare da yi masa horo ba, kuma ya zama Mashaidin Jehobah.

21 Ana bukatar ƙarfin zuciya don a yi wa’azin bishara. Matasa Kiristoci suna bukatar wannan halin idan suna son su kasance da aminci a makaranta. Muna bukatar ƙarfin zuciya don mu nemi izini daga wurin aiki don mu halarci dukan sashen taron gunduma da kuma sauransu. Amma, ko da wane irin ƙalubale ne muke fuskanta, Jehobah zai ji ‘addu’o’inmu na bangaskiya.’ (Yaƙ. 5:15) Kuma babu shakka, zai ba mu ruhunsa mai tsarki don mu ‘ƙarfafa, mu yi ƙarfin zuciya ƙwarai’!

[Hoto a shafi na 11]

Anuhu ya yi wa’azi da gaba gaɗi a cikin muguwar duniya

[Hoto a shafi na 12]

Jael tana da gaba gaɗi da kuma ƙarfi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba