Ka Ƙarfafa, Jehobah Yana Tare Da kai
‘Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya, Ubangiji Allahnka yana tare da kai.’—JOSH. 1:9.
1, 2. (a) Wane hali ne zai taimaka mana mu jimre da gwaje-gwaje? (b) Mece ce ma’anar bangaskiya? Ka kwatanta.
MUNA farin ciki don yin hidimar Jehobah. Duk da haka, muna fuskantar mawuyacin yanayi da gama gari ne. Muna kuma iya shan “wuya sabili da adalci.” (1 Bit. 3:14; 5:8, 9; 1 Kor. 10:13) Muna bukatar bangaskiya da gaba gaɗi don mu yi nasara.
2 Mece ce bangaskiya? Manzo Bulus ya ce: “Bangaskiya fa ainihin abin da mu ke begensa ne, tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.” (Ibran. 11:1) A Helenanci, ana yawan yin amfani da kalmomin nan “abin da muke begensa” a takardar sana’a kuma yana nuna garanti cewa mutum zai gāji abu a nan gaba. Hakazalika, muna da tabbaci cewa Allah zai cika dukan alkawuransa, kuma dukan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ce, har da abin “ba a gani ba tukuna.”
3, 4. (a) Mece ce ma’anar gaba gaɗi? (b) Me zai taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi da kuma bangaskiya?
3 Za a ce da mu masu gaba gaɗi, idan ba ma yin fargaba sa’ad da muke mawuyacin yanayi ko cikin kasada. Idan muna da gaba gaɗi, za mu kasance masu ƙarfi da ƙarfin zuciya da kuma jarumtaka.—Mar. 6:49, 50; 2 Tim. 1:7.
4 Gaba gaɗi da bangaskiya halaye ne masu kyau. Amma, muna iya ji cewa muna bukatar ƙarin bangaskiya da gaba gaɗi. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ɗimbin misalan bayin Allah da suka kasance da gaba gaɗi da kuma bangaskiya. Idan muna son mu kasance da waɗannan halayen, ya kamata mu yi la’akari da misalansu.
JEHOBAH YA KASANCE DA JOSHUA
5. Mene ne Joshua yake bukata don ya ja-goranci Isra’ilawa da kyau?
5 Bari mu yi la’akari da abin da ya faru shekaru 3,500 da suka shige. A lokacin, Musa ɗan shekara 120 ne, kuma shi ne yake wa Isra’ilawa ja-gora. Hakan ya faru shekara arba’in bayan Jehobah ya fitar da miliyoyin Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Sai Jehobah ya haura da shi Dutsen Nebo kuma ya nuna masa ƙasar Alkawari. Bayan hakan, sai Musa ya mutu. Joshua wanda yake “cike da ruhun hikima,” ya zama magajin Musa. (K. Sha 34:1-9) Isra’ilawa suna dab da shigan ƙasar Kan’ana. Joshua yana bukatar hikima daga wurin Allah don ya ja-gorance su da kyau. Yana kuma bukatar ya yi imani ga Jehobah kuma ya kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfi.—K. Sha 31:22, 23.
6. (a) Me ya sa muke bukatar gaba gaɗi, kamar yadda littafin Joshua 23:6 ya nuna? (b) Mene ne littafin Ayyukan Manzanni 4:18-20 da 5:29 suka koya mana?
6 Babu shakka, yadda Joshua ya kasance da hikima da gaba gaɗi da kuma bangaskiya a cikin shekaru da yawa da suka yaƙi Kan’aniyawa ya ƙarfafa Isra’ilawa. Ba don yaƙi kaɗai suke bukatar gaba gaɗi ba, amma don su yi biyayya ga Allah. Sa’ad da Joshua ya kusan mutuwa, ya ce wa Isra’ilawa: “Sai ku yi ƙarfin zuciya ƙwarai, ku kiyaye dukan abin da aka rubuta a cikin litafin shari’ar Musa, ku aika; domin kada ku ratse ko ga dama ko ga hagu.” (Josh. 23:6) Mu ma muna bukatar gaba gaɗi don mu riƙa yin biyayya ga Jehobah a kowane lokaci, musamman idan wani ya ce mu yi abin da ya saɓa wa nufin Allah. (Karanta Ayyukan Manzanni 4:18-20; 5:29.) Idan muka yi addu’a cewa Jehobah ya ja-gorance mu kuma muka dogara gare shi, zai saka mana da gaba gaɗi.
YADDA ZA MU YI NASARA
7. Mene ne Joshua yake bukatar ya yi don ya kasance da gaba gaɗi kuma ya yi nasara?
7 Idan muna son mu kasance masu gaba gaɗi, wajibi ne mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma mu aikata abin da muka koya. Abin da Jehobah ya umurci Joshua ya yi ke nan sa’ad da yake dab da zama magajin Musa. Ya ce: “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya ƙwarai, garin ka kiyaye ka aika bisa ga dukan shari’a, wadda Musa bawana ya umurce ka. . . . Wannan littafin shari’a ba za ya rabu da bakinka ba, amma za ka riƙa bincikensa dare da rana, domin ka kiyaye ka aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki: gama da hakanan za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara.” (Josh. 1:7, 8) Joshua ya yi nasara domin ya bi wannan umurnin. Idan mu ma muka yi hakan, za mu kasance da gaba gaɗi sosai kuma za mu yi nasara a hidimarmu ga Allah.
Jigonmu na 2013 shi ne: ‘Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, gama Jehobah Allahnka yana tare da kai.’—Joshua 1:9
8. Daga wace aya ce aka samo jigo na 2013, kuma yaya kake ganin zai taimake ka?
8 Bayan haka, sai Jehobah ya ce wa Joshua: “Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma; kada ka tsorata, kada ka yi fargaba kuma: gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai dukan inda ka nufa.” (Josh. 1:9) Jehobah yana tare da mu ma. Bai kamata mu yi fargaba ba, ko da wane irin gwaje-gwaje muke fuskanta. Kalmomin nan suna da ma’ana sosai a gare mu. Waɗanne kalmomi? ‘Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, gama Jehobah Allahnka yana tare da kai.’ Waɗannan kalmomin Joshua 1:9 ne jigonmu na shekara ta 2013. Babu shakka, waɗannan kalmomin da misalan mutanen da suka nuna bangaskiya da kuma gaba gaɗi za su ƙarfafa mu a watanni na gaba.
SUN YI ƘARFIN ZUCIYA
9. A waɗanne hanyoyi ne Rahab ta kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi?
9 Sa’ad da Joshua ya tura ’yan leƙen asiri biyu zuwa ƙasar Ka’ana, Rahab wadda karuwa ce ta ɓoye su kuma ta ruɗar da maƙiya da suka zo nemansu. Sa’ad da Isra’ilawa suka ci nasara a kan birnin Yariko, an ceci Rahab da danginta domin ta kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi. (Ibran. 11:30, 31; Yaƙ. 2:25) Rahab ta kuma daina karuwanci domin ta faranta wa Jehobah rai. Wasu ma da suka zama Kiristoci sun kasance da bangaskiya da gaba gaɗi kuma sun canja salon rayuwarsu domin su faranta wa Allah rai.
10. Me ya sa Ruth ta soma bauta wa Jehobah, kuma wane sakamako aka samu?
10 Bayan zamanin Joshua, akwai wata ’yar ƙasar Mowab mai suna Ruth da ta kāre bauta ta gaskiya. Wataƙila ta san Jehobah domin mijinta da ya rasu Ba’isra’ile ne. Surukarta Naomi ma tana zama a ƙasar Mowab, amma sai ta yanke shawara cewa za ta ƙaura zuwa garin Bai’talami a ƙasar Isra’ila. Sa’ad da take kan hanya, sai ta gaya wa Ruth cewa ta koma gida, amma ta ƙi. Ta ce: “Kada ki roƙe ni in rabu da ke, in kuma bar binki . . . danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.” (Ruth 1:16) Daga baya, sai Ruth ta auri wani dangin Naomi, mai suna Boaz. Sai ta yi juna biyu kuma ta haifi ɗa da ya zama kakan-kakannin Dauda da Yesu. Babu shakka, Jehobah ya saka wa waɗanda suke da bangaskiya da kuma gaba gaɗi.—Ruth 2:12; 4:17-22; Mat. 1:1-6.
BA SU JI TSORON MUTUWA BA
11. Ta yaya Jehoyada da matarsa suka kasance da gaba gaɗi, kuma mene ne suka cim ma?
11 Jehobah yana tare da waɗanda suke sa bukatun ’yan’uwansu gaba da nasu, kuma misalinsu yana ƙarfafa bangaskiyarmu da gaba gaɗinmu. Ka yi la’akari da misalin Babban Firist Jehoyada da matarsa Jehosheba. Bayan rasuwar Sarki Ahaziya, mahaifiyarsa Athaliah ta karkashe dukan ’ya’yan sarkin, amma ba ta samu kashe Jehoash ba kuma ta mai da kanta sarauniya. Amma, Jehoyada da matarsa Jehosheba sun ɓoye ɗan Ahaziya har shekara shida, duk da cewa yin hakan kasada ce. A shekara ta bakwai, sai Jehoyada ya naɗa Joash sarki kuma ya sa aka kashe Athaliah. (2 Sar. 11:1-16) Daga baya, Jehoyada ya taya Sarki Joash gyara haikalin Jehobah. Kuma sa’ad da Jehoyada ya rasu yayin da yake ɗan shekara 130, an binne shi tare da sarakuna “domin ya yi aikin nagarta cikin Isra’ila, zuwa ga Allah da gidansa kuma.” (2 Laba. 24:15, 16) Domin Jehoyada da matarsa sun kasance da gaba gaɗi, sun kāre ɗan da ya zama kakan-kakannin Yesu.
12. Ta yaya Ebed-melek ya kasance da gaba gaɗi?
12 Wani bawan Sarki Zedekiya mai suna Ebed-melek ya yi kasada don ya kāre Irmiya. Sarauniyar Yahuda ta yi wa sarkin ƙarya cewa Irmiya yana sa sojoji da kuma mutanen sanyin gwiwa. Sai sarkin ya ƙyale su su ci mutuncinsa. Suka jefa Irmiya cikin rami mai cike da laka, kuma suka bar shi a ciki don ya mutu. (Irm. 38:4-6) Sai Ebed-melek ya roƙi Sarki Zedekiya ya taimaki Irmiya. Abin da Ebed-melek ya yi kasada ce, domin mutane da yawa sun ƙi jinin Irmiya. Mene ne sarkin ya yi? Ya amince kuma ya gaya wa mutane 30 cewa su raka Ebed-melek, domin su ceto Irmiya. Jehobah ya yi wa Ebed-melek alkawari ta baƙin Irmiya cewa, ba zai mutu ba sa’ad da Babiloniyawa suka kawo wa Urushalima hari. (Irm. 39:15-18) Jehobah yana saka wa waɗanda suke kasancewa da gaba gaɗi don su yi nufinsa.
13. Ta yaya Ibraniyawa uku suka kasance da gaba gaɗi, kuma wane darassi za mu iya koya daga labarinsu?
13 Kusan shekara 600 kafin zamanin Yesu, Jehobah ya albarkaci wasu Ibraniyawa uku, domin sun kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Sarki Nebuchadnezzar ya tattara dukan manyan ƙasar Babila, kuma ya ce su bauta wa wata babbar gunkin zinariya da ya kafa. Amma, idan mutum ya ƙi bauta wa gunkin kuma fa? Za a saka shi cikin tanderu mai-wuta mai zafi ƙwarai kuma zai mutu. Sai Ibraniyawan suka gaya wa Sarkin cikin ladabi: “Allahnmu wanda mu ke bauta masa, yana da iko ya cece mu daga tanderu mai-wuta mai-zafi ƙwarai: za ya kuwa cece mu daga hannunka, ya sarki. Amma idan ba haka ba ne, a sanashe ka, ya sarki, ba za mu bauta ma allohinka ba, ba kuwa za mu yi sujada ga gumki na zinariya wanda ka kafa.” (Dan. 3:16-18) Littafin Daniyel 3:19-30 ya bayyana dalla-dalla yadda Jehobah ya cece su. Wataƙila ba za a yi mana barazana cewa za a jefa mu cikin tanderun wuta ba, amma a wasu lokatai, muna bauta wa Jehobah cikin mawuyacin yanayi sosai. Ko shakka babu, Jehobah zai saka mana da albarka idan muka kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi.
14. Kamar yadda littafin Daniyel sura ta 6 ta nuna, ta yaya Daniyel ya kasance da gaba gaɗi kuma da wane sakamako?
14 Maƙiyan Daniyel sun shawarci Sarki Darius cewa ya kafa sabuwar doka da za ta cutar da Daniyel. Suka ce wa sarkin: “Dukan wanda ya roƙi komi ga kowane allah, ko mutum, har kwana talatin, in ba a gareka ba, ya sarki, za a jefa shi cikin ramin zakuna.” Daniyel ya kasance da gaba gaɗi da kuma bangaskiya a wannan yanayin. Da zarar ya samu labari cewa sarki ya sa hannu a dokar, sai “ya shiga gidansa: (amma sakatunsa suna buɗe a cikin ɗakinsa zuwa wajen Urushalima:) ya durƙusa a bisa guwawunsa so uku kowace rana, ya yi addu’a, ya yi godiya a gaban Allahnsa, kamar yadda ya kan yi a dā.” (Dan. 6:6-10) A sakamako, aka jefa shi cikin ramin zakuna. Amma, Jehobah ya cece shi.—Dan. 6:16-23.
15. (a) Wane misalin bangaskiya da gaba gaɗi ne Akila da Biriskilla suka kafa? (b) Mene ne ma’anar kalmomin Yesu da ke Yohanna 13:34, kuma yaya Kiristoci da yawa suka bi wannan umurnin?
15 Littafi Mai Tsarki ya ce Akila da Biriskilla sun ‘miƙa wuyansu sabili da ran Bulus.’ (A. M. 18:2; Rom. 16:3, 4) Sun kasance da gaba gaɗi kuma sun yi abin da Yesu ya ce: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna.” (Yoh. 13:34) Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta bukaci mutum ya yi ƙaunar maƙwabcinsa kamar kansa. (Lev. 19:18) Amma, me ya sa Yesu ya ce wannan dokar “sabuwa” ce? Domin dokar ta umurce mu mu kasance a shirye mu ba da ranmu domin wasu, kamar yadda Yesu ya yi. Kiristoci da yawa sun nuna ƙauna ta wajen yin kasada da ransu domin su kāre ’yan’uwansu don kada maƙiyansu su lahanta su ko kuma kashe su.—Karanta 1 Yohanna 3:16.
16, 17. Ta yaya aka gwada bangaskiyar wasu Kiristoci a ƙarni na farko, da kuma a zamaninmu?
16 Kiristocin ƙarni na farko sun yi koyi da Yesu ta wajen bauta wa Jehobah kaɗai. (Mat. 4:8-10) Sun ƙi bauta wa Sarkin Roma ta wajen ƙona turaren wuta. (Ka duba hoto.) A cikin littafin da Daniel P. Mannix ya rubuta, ya ce ana yawan ajiye wuta da ke ci a filin wasa. Ya ce abin da kawai fursuna yake bukata ya yi shi ne, ya ɗan yayyafa turare a wutan kuma za a ba shi takarda a kuma sake shi. An bayyana wa fursunan cewa idan ya yi hakan, ba ya bauta wa sarkin. Sun ce idan ya yi hakan, ya amince ne kawai cewa sarkin allah ne. Duk da haka, Kiristoci ƙalilan ne suka amince da su.—In ji littafin nan Those About to Die.
17 A zamaninmu ma, an saka wasu Kiristoci a cikin kurkuku a ƙasar Jamus, kuma an ba su zarafi da yawa cewa za a sake su. Amma, me za su yi don a sake su? Suna bukata kurum su sa hannu a takarda cewa sun yi tir da Jehobah. Amma, mutane ƙalilan ne kawai suka sa hannu. A lokacin da ake yaƙi a ƙasar Ruwanda tsakanin ƙabilar Tutsi da Hutu, Shaidun Jehobah daga waɗannan ƙabilun ba su kashe juna ba. Maimakon haka, sun ɓoye su. Ana bukatar gaba gaɗi da bangaskiya don a yi hakan.
KADA KA MANTA CEWA JEHOBAH YANA TARE DA MU
18, 19. Waɗanne misalan mutanen da suka kasance da bangaskiya da gaba gaɗi da ke cikin Nassi ne za su taimaka mana sa’ad da muke wa’azi?
18 Yanzu, muna da gatan almajirtarwa da kuma yin wa’azi game da Mulkin Allah. Wannan ne aiki mafi girma da Allah ya taɓa ba bayinsa a duniya. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Muna matuƙar godiya don misalin da Yesu ya kafa mana. “Ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luk 8:1) Domin mu yi koyi da shi, muna bukatar bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Da taimakon Allah, za mu iya kasancewa da gaba gaɗi kamar Nuhu. Shi “mai-shelan adalci” ne a “duniya ta masu-fajirci,” wadda aka kusan halaka da rigyawa.—2 Bit. 2:4, 5.
19 Addu’a tana taimaka mana mu cika aikinmu na yin wa’azi. Sa’ad da ake tsananta wa wasu cikin almajiran Yesu, sun roƙe Allah ya ba su iko “su faɗi maganarsa da ƙarfin zuciya.” Kuma Allah ya amsa addu’arsu. (Karanta Ayyukan Manzanni 4:29-31.) Idan kana ɗan jin tsoron yin wa’azi gida-gida, ka yi addu’a don Allah ya cika ka da bangaskiya da kuma gaba gaɗi, kuma zai amsa addu’arka.—Karanta Zabura 66:19, 20.a
20. A matsayinmu na bayin Jehobah, wane taimako ne muke da shi?
20 Yin nufin Allah a wannan mugun zamanin ba cin tuwo ba ne. Amma, ba a bar mu kaɗai ba. Allah yana tare da mu. Ɗansa Yesu Kristi wanda shi ne shugaban ikilisiya ma yana tare da mu. Akwai Shaidun Jehobah sama da miliyan bakwai ma a faɗin duniya. Ya dace dukanmu mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya kuma mu yi wa’azin bishara. Jigonmu na shekara ta 2013 wanda ya ce: ‘Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, gama Jehobah Allahnka yana tare da kai’ zai taimaka mana mu yi hakan.—Josh. 1:9.
a Don ƙarin bayani game da gaba gaɗi, ka duba talifin nan “Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai” wanda ya fito a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2012.