“Za Ka Fa Cika Da Murna Sarai”
“Za ka yi idi ga Ubangiji . . . za ka fa cika da murna sarai.”—KUBAWAR SHARI’A 16:15.
1. (a) Waɗanne batutuwa ne Shaiɗan ya tayar? (b) Menene Jehobah ya annabta bayan tawayen Adamu da Hauwa’u?
SHAIƊAN ya ta da batutuwa biyu masu muhimmanci sa’ad da ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi wa Mahaliccinsu zunubi. Na farko, ya ƙalubalanci gaskiyar da Jehobah ya faɗa da kuma ikonsa na yin sarauta. Na biyu, Shaiɗan ya yi hasashen cewa mutane za su bauta wa Allah ne kawai domin son kai. An bayyana wannan batun na biyu dalla-dalla a zamanin Ayuba. (Farawa 3:1-6; Ayuba 1:9, 10; 2:4, 5) Duk da haka, Jehobah ya ɗauki mataki nan da nan don ya daidaita batun. A lokacin da Adamu da Hauwa’u suke cikin lambun Adnin, Jehobah ya annabta yadda zai daidaita batun. Ya annabta zuwan “zuriya” wanda bayan an ƙuje diddigensa, shi kuma zai ragargaza kan Shaiɗan.—Farawa 3:15.
2. Wane ƙarin haske ne Jehobah ya ba da a kan yadda zai cika annabcin da ke Farawa 3:15?
2 Bayan wani ɗan lokaci, Jehobah ya ƙara ba da haske a kan wannan annabcin, wanda hakan ya tabbatar da cewa annabcin zai cika. Alal misali, Allah ya gaya wa Ibrahim cewa “zuriyar” zai bayyana daga cikin zuriyarsa. (Farawa 22:15-18) Jikan Ibrahim, Yakubu, ya zama uban ƙabilu 12 na Isra’ila. A shekara ta 1513 K.Z., sa’ad da waɗannan ƙabilun suka zama al’umma, Jehobah ya ba su dokoki da suka haɗa da bukukuwa masu yawa da za su dinga yi a kowace shekara. Manzo Bulus ya ce waɗannan bukukuwan “inuwar al’amuran da ke zuwa ne.” (Kolossiyawa 2:16, 17; Ibraniyawa 10:1) Suna ɗauke da ƙarin haske game da yadda nufin Jehobah zai cika a kan Zuriyar. Waɗannan bukukuwan na kawo farin ciki a Isra’ila. Ɗan tattauna su zai ƙarfafa bangaskiyarmu a cikar alkawuran Jehobah.
Zuriyar ta Bayyana
3. Wanene Zuriyar da aka yi alkawarinsa, kuma ta yaya aka ƙuje diddigensa?
3 Fiye da shekara 4,000 da Jehobah ya yi annabcin ne Zuriyar da aka yi alkawarinsa ya bayyana. Yesu ne zuriyar. (Galatiyawa 3:16) A matsayinsa na kamiltaccen mutum, Yesu ya kasance da aminci har mutuwa kuma ya tabbatar da cewa zargin da Shaiɗan ya yi duk ƙarya ne. Bugu da ƙari, tun da yake Yesu ba shi da aibi, mutuwarsa hadaya ce mai tamani sosai. Ta mutuwarsa, Yesu ya ceci ’ya’yan Adamu da Hauwa’u masu aminci daga zunubi da mutuwa. Mutuwar Yesu a kan gungume ita ce ‘ƙuje diddigen’ da aka yi alkawarin cewa za a yi wa Zuriyar.—Ibraniyawa 9:11-14.
4. Ta yaya aka alamta hadayar Yesu?
4 Yesu ya mutu a ranar 14 ga Nisan, a shekara ta 33, A.Z.a A Isra’ila, ranar 14 ga Nisan, rana ce ta farin ciki domin bikin Ƙetarewa. A wannan ranar a kowace shekara, iyalai suna cin abinci tare, wanda aka dafa da ƙaramar tunkiya marar naƙasa. Ta wannan hanyar, suna tuna matsayin jinin tunkiyar sa’ad da aka ceci ’ya’yan fari na Isra’ilawa a lokacin da mala’ika ya kashe ’ya’yan fari na Masarawa a ranar 14 ga Nisan, a shekara ta 1513 K.Z. (Fitowa 12:1-14) Tunkiyar Ƙetarewa tana alamtar Yesu, wanda manzo Bulus ya ce game da shi: “An yanke faskarmu, watau Kristi.” (1 Korinthiyawa 5:7) Kamar jinin tunkiyar bikin Ƙetarewa, jinin da Yesu ya zubar ya sa mutane masu yawa su sami ceto.—Yohanna 3:16, 36.
‘ ’Ya’yan Fari Daga Matattu’
5, 6. (a) A wane lokaci ne aka ta da Yesu daga matattu, kuma ta yaya aka alamta wannan aukuwar a cikin Doka? (b) Me ya sa tashin Yesu daga matattu ke da muhimmanci don cikar Farawa 3:15?
5 An ta da Yesu daga matattu a rana ta uku, don ya gabatar da tamanin hadayarsa ga Ubansa. (Ibraniyawa 9:24) An alamta tashinsa daga matattu a wani bikin. Ana soma Bikin Gurasa Marar Yisti a washegarin ranar 14 ga Nisan. A ranar 16 ga Nisan, Isra’ilawa suna kawo damin hatsin da suka fara girbe, wanda shi ne girbi na farko a Isra’ila domin firist ya kaɗa shi a gaban Jehobah. (Leviticus 23:6-14) Hakan ya dace domin a shekara ta 33 A.Z., a ranar 16 ga Nisan, Jehobah ya juyar da mugun ƙoƙarin da Shaiɗan yake yi na kashe “amintaccen mashaidi mai gaskiya” har abada! A ranar 16 ga Nisan, a shekara ta 33 A.Z., Jehobah ya ta da Yesu daga matattu kuma ya sami rai marar mutuwa.—Ru’ya ta Yohanna 3:14; 1 Bitrus 3:18.
6 Yesu ya zama “ ’ya’yan fari daga cikin waɗanda ke barci.” (1 Korinthiyawa 15:20) Yesu bai sake mutuwa ba, kamar waɗanda aka ta da daga matattu a dā. Maimakon haka, ya koma sama ya zauna a hannun damar Jehobah, a inda yake jira har sai an naɗa shi Sarkin Mulkin Jehobah na samaniya. (Zabura 110:1; Ayukan Manzanni 2:32, 33; Ibraniyawa 10:12, 13) Tun lokacin da aka naɗa shi Sarki, Yesu zai iya ƙuje kan babban maƙiyi, Shaiɗan, kuma ya halaka zuriyarsa har abada.—Ru’ya ta Yohanna 11:15, 18; 20:1-3, 10.
Zuriyar Ibrahim Sun Ƙaru
7. Menene Bikin Mako-Mako?
7 Yesu ne Zuriyar da aka yi alkawarinsa a cikin Adnin, kuma Jehobah zai yi amfani da shi wajen “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) Amma, sa’ad da Jehobah ya yi wa Ibrahim magana, ya nuna cewa “zuriyar” Ibrahim ta fi mutum ɗaya. Za su kasance “kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” (Farawa 22:17) An alamta bayyanuwar sauran “zuriyar” ta hanyar wani biki na farin ciki. Kwanaki hamsin bayan ranar 16 ga Nisan, Isra’ilawa suna yin Bikin Mako-Mako. Dokar ta ce: “Kwana hamsin ke nan za ku lissafta, har wāshegarin assabbat na bakwai; sa’annan za ku miƙa sabuwar hadaya ta gari kuma ga Ubangiji. Daga cikin mazaunanku za ku kawo dunƙule guda biyu na malelekuwa a bakin kashi biyu cikin goma na ephah: sai na gari mai-labshi, toyayye ne da yeast, su zama ’ya’yan fāri ga Ubangiji.”b—Leviticus 23:16, 17, 20.
8. Wane aukuwa na musamman ne ya faru a Fentakos ta shekara ta 33 A.Z.?
8 Sa’ad da Yesu yake duniya, ana kiran Bikin Mako-Mako Fentakos (kalmar Helenanci da ke nufin “na hamsin”). A ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z., Firist Mafi Girma, wato Yesu Kristi da aka ta da daga matattu, ya zuba ruhu mai tsarki a kan ƙaramin rukunin almajiransa su 120 da suka taru a Urushalima. Da haka, waɗannan almajiran sun zama shafaffun ’ya’yan Allah da kuma ’yan’uwan Yesu Kristi. (Romawa 8:15-17) Sun zama sabuwar al’umma, “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Daga ƙaramin adadi, wannan al’ummar za ta kai 144,000.—Ru’ya ta Yohanna 7:1-4.
9, 10. Ta yaya aka alamta ikilisiyar shafaffun Kiristoci a lokacin Fentakos?
9 Gurasa biyu da ake kaɗawa a gaban Jehobah a kowane Fentakos sune ke alamtar ikilisiyar shafaffun Kiristoci. Gurasar da aka sa wa yisti na nuna cewa har yanzu shafaffun Kiristoci suna da zunubin da muka gadā. Duk da haka, suna iya yin addu’a ga Jehobah domin fansar hadayar Yesu. (Romawa 5:1, 2) Me ya sa gurasar biyu ce kawai? Wataƙila hakan na nuna cewa shafaffun ’ya’yan Allah za su fito ne daga rukuni biyu, wato, Yahudawa da kuma ’yan Al’ummai.—Galatiyawa 3:26-29; Afisawa 2:13-18.
10 Gurasa biyu da ake yin hadaya da su a ranar Fentakos ana yin su ne da hatsin da aka fara girba. Daidai da wannan, ana kiran waɗannan Kiristoci da aka shafa da ruhu “yayan fari daga cikin halittattunsa.” (Yaƙub 1:18) Sune aka fara gafarta wa zunubansu bisa ga jinin da Yesu ya zubar, kuma hakan ya sa an ba su rai marar mutuwa a sama inda za su yi sarauta da Yesu a Mulkinsa. (1 Korinthiyawa 15:53; Filibbiyawa 3:20, 21; Ru’ya ta Yohanna 20:6) A wannan matsayin, nan ba da daɗewa ba za su “mallaka [al’ummai] kuma da sanda ta ƙarfe” kuma za su ga yadda za a ‘ƙuje Shaiɗan daga ƙarƙashin sawayensu.’ (Ru’ya ta Yohanna 2:27; Romawa 16:20) Manzo Yohanna ya ce: “Su ne sukan bi Ɗan rago inda ya tafi duka. Aka panshi waɗannan daga cikin mutane, su zama nunan fari ga Allah da Ɗan rago.”—Ru’ya ta Yohanna 14:4.
Ranar da Ke Alamtar Ceto
11, 12. (a) Menene ke faruwa a Ranar Kafara? (b) Wane amfani ne Isra’ila take samu daga hadayun Ranar Kafara?
11 A rana ta goma ta watan Ethanim (wadda ake kira Tishri)c, Isra’ila tana yin bikin da ke alamtar yadda hadayar fansa ta Yesu za ta amfana. A wannan ranar, duka al’ummar za ta taru don Ranar Kafara domin a yi hadaya a madadinsu don a gafarta musu zunubansu.—Leviticus 16:29, 30.
12 A Ranar Kafara, babban firist zai yanka ƙaramar tunkiya, kuma zai watsa jinin sau bakwai a gaban Akwati a wuri Mafi Tsarki, wanda yake wakiltar gabatar da jinin a gaban Jehobah. Za a yi wannan hadayar ne domin zunubin babban firist da kuma “gidansa,” mataimakin firistoci da kuma Lawiyawa. Bayan haka, babban firist zai ɗauki bunsurai biyu. Zai yanka guda domin hadayar zunubi don “jama’a.” Zai watsa jinin a gaban Akwati a wuri Mafi Tsarki. Bayan haka, babban firist zai saka hannunsa a kan ɗayan bunsurun kuma zai faɗi zunuban ’ya’yan Isra’ila. Daga bisani, zai saki bunsurun ya shiga daji don ya ɗauke zunuban al’ummar a alamance.—Leviticus 16:3-16, 21, 22.
13. Ta yaya ne abubuwan da ke faruwa a Ranar Kafara suke alamtar abin da Yesu ya yi?
13 Kamar yadda waɗannan aukuwa ke alamta, Babban Firist mafi girma, Yesu, ya yi amfani da jininsa mai tamani don a gafarta zunubai. Na farko, tamanin jininsa ta shafi “gida mai-ruhaniya,” na shafaffun Kiristoci 144,000, wanda hakan ya sa suka zama amintattu kuma suke more matsayi mai kyau a wurin Jehobah. (1 Bitrus 2:5; 1 Korinthiyawa 6:11) Hadayar bijimi ne ke alamtar hakan. Da haka, an buɗe musu damar samun gadōnsu na samaniya. Na biyu, tamanin jinin Yesu ya shafi miliyoyin mutanen da suka ba da gaskiya ga Kristi, kamar yadda hadayar bunsuru take nunawa. Za a albarkace su da rai na dindindin a nan duniya, gadōn da Adamu da Hauwa’u suka rasa. (Zabura 37:10, 11) Domin jinin da ya zubar, Yesu ya ɗauke zunuban ’yan adam, kamar yadda rayayyen bunsurun nan a alamance yake ɗauke zunuban Isra’ilawa zuwa cikin jeji.—Ishaya 53:4, 5.
Yin Farin Ciki a Gaban Jehobah
14, 15. Menene ke faruwa a lokacin Bikin Bukkoki, kuma menene hakan ke tuna wa Isra’ilawa?
14 Bayan Ranar Kafara, Isra’ilawa suna yin Bikin Bukkoki, wanda shi ne biki mafi daɗi a zamanin Yahudawa. (Leviticus 23:34-43) Ana yin bikin ne daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Ethanim kuma za a kammala shi da babban taro a ranar 22 na watan. Hakan na nuna cewa an gama girbi kuma lokaci ne na nuna godiya domin alherin Allah. Domin wannan dalilin, Jehobah ya umurci masu bikin: “Ubangiji Allahnka za ya albarkace ka cikin dukan anfaninka, da dukan aikin hannuwanka, za ka fa cika da murna sarai.” (Kubawar Shari’a 16:15) Wannan lokaci ne na farin ciki!
15 A lokacin wannan bikin, Isra’ilawa za su zauna ne a cikin bukkoki har kwana bakwai. Hakan na tuna musu cewa sun taɓa zama a cikin bukkoki a jeji. Bikin na ba su dama mai yawa na yin tunani a kan irin kula na uba da Jehobah yake yi musu. (Kubawar Shari’a 8:15, 16) Tun da dukansu, masu arziki da talakawa suna zaune ne a cikin bukkoki iri ɗaya, hakan na tuna wa Isra’ilawa cewa a wannan lokacin dukansu ɗaya ne.—Nehemiah 8:14-16.
16. Menene Bikin Bukkoki ke alamta?
16 Bikin Bukkoki biki ne na girbi, da kuma farin ciki, kuma yana alamtar farin cikin tara waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu Kristi. An soma wannan tarawar a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka shafa almajirai 120 na Yesu don su zama sashen “priesthood mai-tsarki.” Kamar yadda Isra’ilawa suka zauna a cikin bukkoki na ’yan kwanaki, shafaffu sun sani cewa su “baƙi masu-tafiya” ne a wannan duniyar marar ibada. Begensu na samaniya ne. (1 Bitrus 2:5, 11) Tara shafaffun Kiristoci ya soma kai wa ƙarshe a wannan “kwanaki na ƙarshe,” sa’ad da ake tara sauran 144,000.—2 Timothawus 3:1.
17, 18. (a) Menene ya nuna cewa ba shafaffun Kiristoci ba ne kaɗai za su amfana daga hadayar Yesu? (b) Su wanene a yau suke amfana daga Bikin Bukkoki na alama, kuma a wane lokaci ne wannan biki na farin ciki zai kai ƙarshensa?
17 Abu ne mai muhimmanci mu san cewa a lokacin da ake yin wannan bikin a dā, ana yin hadaya da bijimai 70. (Litafin Lissafi 29:12-34) Adadin nan 70, tana nufin 7 sau 10, adadin da a cikin Littafi Mai Tsarki tana alamtar kamiltawa a sama da duniya. Da haka, hadayar Yesu za ta amfane amintattun mutane da suka fito daga iyalai 70 na Nuhu. (Farawa 10:1-29) A cikin jituwa da wannan, a zamaninmu wannan tarawar ta haɗa da mutane daga dukan al’ummai da suka ba da gaskiya a Yesu kuma suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya.
18 Manzo Yohanna ya ga wannan tarawar ta zamani a wahayi. Da farko, ya ji sanarwar hatimce adadi na ƙarshe na mutane 144,000. Bayan haka, ya ga “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa,” suna a tsaye a gaban Jehobah da Yesu, riƙe “da ganyayen dabino cikin hannuwansu.” Waɗannan sun “fito daga cikin babban tsanani” zuwa cikin sabuwar duniya. Su ma baƙi ne a cikin wannan zamani, kuma suna sa rai da gabagaɗi su ga lokacin da “Ɗan rago . . . za ya zama makiyayinsu, za ya bishe su kuma wurin maɓulɓulan ruwaye na rai.” A wannan lokacin, “Allah kuma za ya share dukan hawaye daga idanunsu.” (Ru’ya ta Yohanna 7:1-10, 14-17) Bikin Bukkoki na alama zai kai ƙarshensa sa’ad da babban taro, da kuma waɗanda aka ta da daga matattu suka kamilta a ƙarshen Sarautar Kristi na Shekara Dubu.—Ru’ya ta Yohanna 20:5.
19. Ta yaya muka amfana daga tattauna bukukuwan da ake yi a Isra’ila?
19 Ya kamata mu “cika da murna sarai” yayin da muke yin bimbini a kan ma’anar bukukuwan Yahudawa na dā. Abin farin ciki ne mu tattauna cewa Jehobah ya ba da ƙarin haske a kan yadda annabcin da ya ba da a Adnin zai cika, kuma abin farin ciki ne mu shaida yadda yake cika a hankali a hankali. A yau, mun san cewa Zuriyar ya bayyana kuma an ƙuje shi a diddige. Yanzu ya zama Sarki a sama. Bugu da ƙari, yawancin mutanen 144,000 sun nuna amincinsu har mutuwa. Menene ya rage? A wane lokaci ne annabcin zai cika gabaki ɗaya? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Nisan ta yi daidai da watan Maris ko Afrilu a cikin kalandar mu ta zamani.
b A wannan hadayar da ake kaɗa gurasa mai yisti, a yawancin lokaci firist ɗin na riƙe gurasar a kan tafin hannunsa, zai ɗaga hannuwansa, kuma zai ɗinga kaɗa su. Wannan kaɗawar tana alamtar miƙa hadayar ga Jehobah.—Duba Insight on the Scriptures, na 2, shafi na 528, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
c Ethanim, ko Tishri, ta yi daidai da watan Satumba ko Oktoba a kalandar mu ta zamani.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene tunkiyar Ƙetarewa take alamta?
• Wane tattarawa ne Bikin Fentakos ke alamta?
• Waɗanne abubuwan da suka faru a Ranar Kafara ne suke nuni ga hanyar da hadayar fansa ta Yesu take amfana?
• Ta yaya ne Bikin Bukkoki yake alamtar tattarawar Kiristoci?
[Taswira a shafi nas 24, 25]
Aukuwa: Abin da Yake Alamta:
Ƙetarewa 14 ga Tunkiyar da aka Hadayar Yesu
Nisan yanka a ranar
Ƙetarewa
Bikin Gurasa 15 ga Assabaci
Marar Yisti Nisan
(15 zuwa
21 ga Nisan) 16 ga Hatsi da aka yi An ta da Yesu daga
Nisan hadaya da shi matattu
↑
Kwana 50
↓
Bikin Mako-Mako 6 ga Gurasa biyu da Yesu ya gabatar da
(Fentakos) Sivan aka yi hadaya shafaffun ’yan’uwansa
da su ga Jehobah
Ranar Kafara 10 ga Bijimi da Yesu ya gabatar da
Tishri bunsurai tamanin jininsa a
biyu da aka yi madadin duka
hadaya da su ’yan adam
Bikin Bukkoki 15 zuwa 21 Isra’ilawa sun Tattara shafaffu da
(Tarawa, ga Tishri zauna cikin “taro mai-girma”
Bukkoki) bukkoki da farin
ciki, suna murna
domin girbi,
bajimai 70 da
aka yi hadaya
da su
[Hotuna a shafi na 23]
Kamar jinin tunkiyar Ƙetarewa, jinin da Yesu ya zubar ya sa mutane masu yawa sun sami ceto
[Hotuna a shafi na 24]
Hatsi na farko da aka girbe wanda ake ba da hadayarsa a ranar 16 ga Nisan na alamtar tashin Yesu daga matattu
[Hotuna a shafi na 25]
Gurasa biyu da ake hadaya da su a ranar Fentakos na alamtar ikilisiyar shafaffun Kiristoci
[Hotuna a shafi na 26]
Bikin Bukkoki na alamtar farin cikin tattara shafaffu da kuma “taro mai-girma” daga dukan al’ummai