Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 2/1 pp. 7-11
  • Ka Koyar Da Ainihin Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koyar Da Ainihin Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Ya Damu da Mu Kuwa?
  • Me Ya Sa Muke Wanzuwa?
  • Menene Yake Faruwa da Mu Sa’ad da Muka Mutu?
  • Sabon Littafin da za Mu Yi Amfani da Shi
  • Ka Yi Godiya Don Gatanka Mai Tamani
  • Za Ka So Ka San Amsoshin Wadannan Tambayoyin?
    Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?
  • Mece ce Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Taimaka Wa Mutane Su Yi Biyayya Da Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 2/1 pp. 7-11

Ka Koyar Da Ainihin Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa

“Ku almajirtadda dukkan al’ummai, . . . kuna koya musu.”—MATTA 28:19, 20.

1. Menene za a iya cewa game da yaɗuwar Littafi Mai Tsarki?

KALMAR JEHOBAH, Littafi Mai Tsarki tana cikin tsofaffin littattafai kuma ta fi kowane littafi yaɗuwa a duniya. An fassara rabinta cikin harsuna fiye da 2,300. Fiye da kashi 90 na mutanen duniya suna da ita a harshensu.

2, 3. (a) Menene ya jawo ruɗani game da koyarwar Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

2 Miliyoyin mutane suna karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana. Wasu sun karance shi sau da yawa. Rukunin addinai da yawa suna da’awar cewa koyarwarsu ta fito ne daga Littafi Mai Tsarki, amma sun ƙi yin biyayya da abin da yake koyarwa. Abin da ya daɗa ruɗanin shi ne rashin jituwar da ke tsakanin waɗanda suke cikin addini ɗaya. Wasu suna shakka game da asalin Littafi Mai Tsarki da kuma amfaninta. Mutane da yawa suna ɗaukansa littafi ne mai tsarki da ake amfani da shi sa’ad da suka lashe takobi ko kuma rantsuwa don su faɗi gaskiya a kotu.

3 Hakika, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da kalmar Allah mai iko, ko kuma saƙo domin mutane. (Ibraniyawa 4:12) Shi ya sa mu Shaidun Jehobah muke so mutane su koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Muna farin cikin yin biyayya ga dokar da Yesu ya ba wa mabiyansa sa’ad da ya ce: “Ku je ku almajirtadda dukkan al’ummai, . . . kuna koya musu.” (Matta 28:19, 20) A hidimarmu ga jama’a, muna saduwa da mutanen da suke damuwa domin ruɗanin da ke cikin addini a duniya ta yau. Suna so su san gaskiya game da Mahaliccinmu, kuma su koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ma’anar rayuwa. Bari mu bincika tambayoyi uku da suke damun mutane. Za mu bincika abin da malaman addinai suka ce cikin kuskure, da kuma abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa a kan kowanne. Tambayoyin su ne: (1) Allah ya damu da mu kuwa? (2) Me ya sa muke wanzuwa? (3) Me ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

Allah Ya Damu da Mu Kuwa?

4, 5. Me ya sa mutane suke tunanin cewa Allah ba ya damuwa da mu?

4 Bari mu fara da tambaya ta fari, Allah ya damu da mu kuwa? Abin baƙin ciki, mutane da yawa suna tsammanin cewa amsar wannan tambayar a’a ce. Me ya sa suka ce haka? Dalili ɗaya shi ne domin duniya ta cika da ƙiyayya, yaƙi, da kuma wahala. Mutane da yawa sun yi tunani cewa: ‘Idan Allah ya damu da mu, hakika zai hana waɗannan munanan abubuwa faruwa.’

5 Wani dalili kuma da ya sa mutane suke ganin cewa Allah ba ya damuwa shi ne abubuwan da malaman addinai suke faɗa. Menene malaman addinai suke cewa sa’ad da bala’i ta faɗa wa mutane? Sa’ad da wata mata ta yi rashin ’ya’yanta biyu ƙanana a haɗarin mota, malaminta na addini ya ce: “Nufin Allah ne. Allah yana bukatar ƙarin mala’iku biyu.” Sa’ad da malaman addinai suka furta irin waɗannan kalamai, hakika suna ɗora wa Allah alhakin munanan abubuwan da ke faruwa ne. Duk da haka, almajiri Yaƙub ya rubuta: “Kada kowa sa’anda ya jarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” (Yaƙub 1:13) Jehobah Allah ba ya jawo munanan abubuwa. Hakika, “daɗai Allah shi yi mugunta.”—Ayuba 34:10.

6. Wanene tushen mugunta da kuma wahalar da ke faruwa a cikin duniya?

6 To me ya sa ake mugunta da wahala haka sosai? Wani dalili shi ne, ’yan adam sun ƙi sarautar Allah, ba sa son su yi biyayya da dokokinsa da kuma mizanansa. Domin haka, ’yan adam sun miƙa kai da son ransu ga abokin gaban Allah, Shaiɗan Iblis domin “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Sanin wannan ya bayyana mana dalilin da ya sa miyagun abubuwa suke faruwa. Shaiɗan mugu ne, maƙiyi, mayaudari da kuma maƙetacci. Saboda haka dole ne duniya ta nuna irin halin sarkinta. Dalilin da ya sa ke nan wahala ta yi yawa!

7. Waɗanne dalilai ne suka sa mutane suke fuskantar wahala?

7 Wani dalili da ya sa ake wahala shi ne ajizancin ’yan adam. Mutane masu zunubi suna kokawar neman iko, kuma irin wannan kokawar sau da yawa tana kawo yaƙe-yaƙe, danniya, da wahala. Kamar yadda Mai-Wa’azi 8:9 ta ce: “Mutum ya sami iko bisa wani.” Har yanzu kuma wani dalilin da ya sa ake wahala shi ne “sa’a, da tsautsayi.” (Mai Hadishi 9:11, L.M.T) Sau da yawa, mutane suna faɗawa masifa ne domin sun kasance a wani wuri a lokacin da bai dace ba.

8, 9. Ta yaya muka sani cewa Jehobah ya damu da mu?

8 Abin farin ciki ne mu fahimci cewa ba Allah ba ne yake haddasa wahala. Amma Allah ya damu kuwa da abin da yake faruwa a rayuwarmu? Amsar ita ce e! Hakika mun sani cewa Jehobah ya damu da mu, domin hurarriyar Kalmarsa ta gaya mana dalilin da ya sa ya ƙyale mutane su bi mummunar tafarki. Dalilin Allah ya shafi batu biyu: na ikon mallakarsa da kuma amincin mutane. Saboda shi ne Mahalicci maɗaukaki, bai wajaba ba Jehobah ya gaya mana dalilin da ya sa ya ƙyale wahala. Duk da haka, ya gaya mana domin ya damu da mu.

9 Ka yi la’akari da ƙarin tabbacin da ya nuna cewa Allah ya damu da mu. Abin ya “ɓata masa zuciya” sa’ad da muguntar mutane ta cika duniya a zamanin Nuhu. (Farawa 6:5, 6) Abin yana damun shi kuwa a yau? Ƙwarai kuwa, domin Allah ba ya sakewa. (Malachi 3:6) Allah ya ƙi jinin rashin adalci kuma ba ya son ganin mutane suna shan wahala. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa ba da daɗewa ba Allah zai kawar da wahalar da mulkin mutane ta jawo a ƙarƙashin rinjayar Iblis. Wannan ba tabbaci ba ne ba cewa Allah ya damu da mu?

10. Yaya ne Jehobah yake ji game da wahalar da mutane suke sha?

10 Saboda haka, shugabannin addinai ba sa faɗin gaskiya game da Allah sa’ad da suka ce masifu da muke fuskanta nufin Allah ne. Gaskiyar ita ce, Jehobah yana ɗokin kawar da wahalar ’yan adam. 1 Bitrus 5:7 ta ce: “Yana kula da ku.” Wannan shi ne ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa!

Me Ya Sa Muke Wanzuwa?

11. Menene addinai suke koyarwa game da rayuwar mutane a duniya?

11 Bari mu tattauna tambaya ta biyu da mutane da yawa suke mamaki a kai, Me ya sa muke wanzuwa? Addinai na duniya sau da yawa suna koyar da cewa mutum yana duniya ne kawai na ɗan lokaci. A gare su duniya ba ta wuce wurin jira ba kawai a kan hanyar zuwa wani wuri. Wasu malaman addinai suna koyar da cewa, wata rana Allah zai halaka duniya. Domin irin wannan koyarwar, mutane da yawa sun ƙuduri aniyar samun abin da za su samu sa’ad da za su iya tun da mutuwa ce kawai take jiransu. Menene ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da dalilin da ya sa muke wanzuwa?

12-14. Menene Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da nufin Allah ga duniya da mutane?

12 Allah yana da manufa mai ban sha’awa ga duniya da kuma ’yan adam. Ya “halicce ta ba wofi ba” amma “domin wurin zama.” (Ishaya 45:18) Bugu da ƙari, Jehobah ya “kafa tussan duniya, Domin kada ta jijjigu har abada.” (Zabura 104:5) Koyan nufin Allah ga duniya da kuma ’yan adam zai iya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa muke duniya.

13 A Farawa sura 1 da 2 mun koyi cewa Jehobah ya shirya duniya domin mutane su zauna a ciki. Bayan da ya gama halittar duniya, ya tabbata cewa kome ya yi “kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Allah ya saka mata da miji na farko, wato Adamu da Hauwa’u a cikin kyakkyawan lambu kuma ya cika shi da kyawawan abinci. Ya ce masu: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya.” Za su haifi ’ya’ya kamilai, su faɗaɗa lambun zuwa dukan duniya, kuma za su yi iko cikin ƙauna bisa dabbobi.—Farawa 1:26-28.

14 Nufin Jehobah shi ne kamiltattun iyali ta ’yan adam su rayu har abada a duniya. Kalmar Allah ta ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Hakika, an halicci ’yan adam su yi rayuwa har abada a cikin Aljanna a duniya. Wannan shi ne nufin Allah, kuma shi ne ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa!

Menene Yake Faruwa da Mu Sa’ad da Muka Mutu?

15. Menene addinai na duniya suke koyarwa game da abin da yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

15 Bari yanzu mu tattauna tambaya ta uku da ta dami mutane da yawa: Menene yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu? Yawancin addinai na duniya suna koyar da cewa da wani abu a cikin mutum da yake ci gaba da rayuwa bayan jiki ya mutu. Wasu rukunin addinai har yanzu suna manne wa ra’ayin cewa Allah yana hukunta miyagu cikin wutar jahannama. Amma hakan gaskiya ne? Menene ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da mutuwa?

16, 17. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da yanayin matattu?

16 Kalmar Allah ta ce: “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba, ba su kuwa da sauran lada.” Tun da matattu “ba su san komi ba,” ba sa ji, ba sa gani, ba sa yin magana, ko tunani. Ba sa iya karɓan ladan aiki. Ta yaya za su yi hakan, tun da ba su san kome ba? Ba za su iya wani aiki ba! Bugu da ƙari, “ƙaunarsu duk da ƙiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun ƙare,” saboda ba za su iya nuna motsin zuciya ba.—Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10.

17 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batu ba shi da wuya kuma ya fita sarai, matattu ba sa rayuwa a wani wuri. Babu abin da yake barin jikinmu bayan mutum ya mutu ko kuwa a haifi mutum da ya riga ya mutu a wani wuri, kamar yadda waɗanda suka yarda da sake haifan matattu suka yi imani da shi. Za mu iya ba da misali da wannan: Rai da muke morewa tana kama da wutar kyandir. Sa’ad da aka kashe wutar ba ta tafiya ko’ina. Hakika ta daina wanzuwa.

18. Menene ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai iya kammalawa sa’ad da ya koyi cewa matattu ba su san komi ba?

18 Ka yi tunanin ma’anar wannan misali mai sauƙi amma mai ɗauke da hakikanin gaskiya. Da zarar ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya koyi cewa matattu ba su san komi ba, zai iya kammala cewa magabtansa a lokacin da suke raye ba za su iya damunsa ba. Ya kamata ya fahimci cewa waɗanda yake ƙauna da suka mutu ba sa iya jin magana, ba sa gani, ba sa yin magana, ko kuma tunani. Saboda haka, ba zai yiwu su riƙa shan azaba ba da kewa a wurin jira ko kuma a wutar jahannama. Amma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah zai ta da matattu da ya tuna da su. Wannan bege ne mai ban sha’awa!—Yohanna 5:28, 29.

Sabon Littafin da za Mu Yi Amfani da Shi

19, 20. Wane hakki ne mu Kiristoci muke da shi, kuma wane littafi ne na Littafi Mai Tsarki aka shirya da za mu yi amfani da shi a hidimarmu?

19 Tambayoyi uku ne kawai muka bincika daga cikin waɗanda suke damun mutane da yawa. A kowace tambaya mun ga cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar na kai tsaye ne babu rufa-rufa. Abin farin ciki ne mu gaya wa mutane da suke so su san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa! Amma akwai wasu tambayoyi masu muhimmanci da mutane masu zuciyar kirki suke bukatar amsoshi masu gamsarwa. Mu Kiristoci muna da hakkin taimaka wa mutane su samu amsoshi ga irin waɗannan tambayoyi.

20 Ƙalubalen da muke fuskanta shi ne mu koyar da Littafi Mai Tsarki ta hanya mai sauƙi kuma mai motsa zuciya. Don mu fuskanci wannan ƙalubalen, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya shirya wani littafin da za mu yi amfani da shi a hidimarmu ta Kirista. (Matta 24:45-47) Jigon littafin nan mai shafuffuka 224, shi ne Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

21, 22. Waɗanne abubuwa ne na musamman wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa yake ɗauke da shi?

21 Wannan littafin da aka fito da shi a Taron Gunduma na “Biyayya Ta Ibada” na shekara ta 2005 zuwa 2006, ya ƙunshi abubuwa da yawa. Alal misali, akwai shafuffuka biyar na farko da aka tsara domin su taimake mu mu fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Za ka ga cewa hotuna da kuma nassosin da ke gabatarwa ba su da wuyan tattaunawa. Kana iya kuma yin amfani da abubuwa da suke cikin wannan sashen ka nuna wa ɗalibin yadda zai iya samun surori da ayoyi na Littafi Mai Tsarki.

22 Rubutun yana da sauƙi kuma ya fita sarai. An yi ƙoƙari sosai don ya motsa zuciyar ɗalibin kuma ya faɗi ra’ayinsa inda hakan zai yiwu. A kowane babi akwai tambayoyin gabatarwa da kuma akwati mai jigo “Abin da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa.” Wannan akwatin yana ɗauke da amsoshi na tambayoyin gabatarwa. A wannan littafin an yi amfani da hotuna masu kyau da ɗan rubutu da ake yi don a bayyana su da kuma kwatanci don a taimaki ɗalibin ya fahimci sabon batun. Ko da yake ainihin mahallin littafin yana da sauƙi, yana da rataye da za ka iya bincika batutuwa 14 masu muhimmanci dalla-dalla, idan ɗalibin yana bukatar ƙarin bayani.

23. Wace shawara ce aka ba da game da yadda za a yi amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa a nazarin Littafi Mai Tsarki?

23 An tsara wannan littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ya taimake mu mu koyar da mutane musu ilimi da marasa ilimin da kuma waɗanda suke addinai dabam dabam. Idan ka lura cewa ɗalibin ba shi da ilimin Littafi Mai Tsarki, zai ɗauki fiye da sashen nazari ɗaya kafin ku kammala babi ɗaya. Kada ka yi saurin gama babin, amma ka yi ƙoƙari ka motsa zuciyar ɗalibin. Idan bai gane kwatancin da aka rubuta a littafin ba, ka bayyana kwatancin ko kuma ka ba da wani kwatanci dabam. Ka shirya sosai, ka yi iya ƙoƙarinka ka yi amfani da littafin sosai, kuma ka roƙi Allah ya taimake ka ka “rarrabe kalmar gaskiya sosai.”—2 Timothawus 2:15.

Ka Yi Godiya Don Gatanka Mai Tamani

24, 25. Wane gata ne mai tamani Jehobah ya ba mutanensa?

24 Jehobah ya ba mutanensa gata mai tamani. Ya ƙyale mu mu koyi gaskiya game da shi. Kada mu yi wasa da wannan gatan! Ban da haka ma, Allah ya sa an bayyana nufe-nufensa ga masu tawali’u kuma ya ɓoye su ga masu fahariya. Game da wannan, Yesu ya ce: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Matta 11:25) Ɗaukaka ce mai girma mu kasance tsakanin waɗanda suke da tawali’u da suke bauta wa Jehobah Mamallakin Duka Halitta.

25 Jehobah ya ba mu gatar koya wa mutane game da shi. Ka tuna cewa wasu suna yaɗa ƙarya game da shi. Saboda haka, mutane da yawa ba su fahimci Jehobah da kyau ba, suna tunanin cewa ba ya damuwa da su kuma ba ya tausayi. Kana son ka gyara wannan ra’ayi? Kana so mutane masu zuciyar kirki a ko’ina su fahimci gaskiya game da Allah? To, ka nuna biyayyarka ta ibada, ta wajen saka hannu a wa’azi da kuma koya wa mutane abin da Nassi ya ce game da batutuwa masu muhimmanci! Masu neman gaskiya suna bukatar su san ainihi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

Menene Amsoshinka?

• Ta yaya muka sani cewa Allah ya damu da mu?

• Me ya sa muke wanzuwa a duniya?

• Me ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

• Waɗanne abubuwa ne da ke cikin littafi nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa suka amfane ka?

[Hotuna a shafi na 8]

Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa wahala za ta ƙare

[Inda aka Daukos]

Yarinyar da ke sama: © Bruno Morandi/age fotostock; a hagu, mata: AP Photo/Gemunu Amarasinghe; a gefen dama a ƙasa, ’yan gudun hijira: © Sven Torfinn/Panos Pictures

[Hoto a shafi na 9]

Mutane masu adalci za su rayu har abada a Aljanna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba