Ka Taimaka Wa Mutane Su Yi Biyayya Da Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
“Na cikin ƙasa mai-kyau, su ne waɗanda sun ji magana cikin zuciya mai-gaskiya mai-kyau, daga baya su kan riƙe ta, da haƙuri kuma suna bada amfani.”—LUKA 8:15.
1, 2. (a) Menene ya sa aka tsara littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? (b) A shekaru na baya bayan nan, ta yaya ne Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen mutanensa don su almajirantar?
“WANNAN littafin yana da sauƙi. Ɗalibai na suna son sa. Ni ma ina son sa. Wannan littafin ya sa muna iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki a bakin ƙofar mutane.” In ji wata mai hidima na cikkaken lokaci na Shaidun Jehobah game da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a Wani tsoho mai shelar Mulki ya ce game da wannan littafin, “A shekaru 50 da ni ke hidima, na samu gatar taimaka wa mutane da yawa su san Jehobah. Amma wannan littafin fitacce ne. Hotuna da kuma kwatancin da ke cikinsa suna da kyau.” Ra’ayinka ke nan game da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? An tsara wannan littafin don ya taimake ka ka cika umurnin Yesu: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—Matta 28:19, 20.
2 Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki don ganin Shaidunsa fiye da miliyan shida da dari shida suna yin biyayya ga umurnin da Yesu ya yi game da almajirantarwa. (Misalai 27:11) Jehobah yana yi masu albarka saboda ƙoƙarin da suke yi. Alal misali, a shekara ta 2005, an yi shelar bishara a ƙasashe 235, kuma an yi nazarin Littafi Mai Tsarki na gida fiye da 6,061,500. A sakamakon haka, mutane da yawa sun ‘karɓi maganar Allah, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah.’ (1 Tassalunikawa 2:13) Shekaru biyu da suka wuce, sababbin almajirai fiye da rabin miliyan ne suka sa rayuwarsu ta jitu da mizanan Jehobah kuma suka keɓe kansu ga Allah.
3. Waɗanne tambayoyi ne game da amfanin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa za mu bincika a wannan talifin?
3 Ka shaida farin cikin yin nazari da wani a kwanan nan? A duniya duka, har yanzu akwai mutane masu “zuciya mai-gaskiya mai-kyau” waɗanda bayan sun ji maganar Allah suka “riƙe ta, da haƙuri kuma suna bada amfani.” (Luka 8:11-15) Bari mu bincika yadda za ka iya yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa a wurin aikin almajirantarwa. Za mu tattauna tambayoyi uku: (1) Ta yaya za ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki? (2) Wace hanyoyin koyarwa ce ta dace? (3) Ta yaya za ka taimaki mutum ya zama malamin rubutacciyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki?
Yadda Za Ka Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Wani
4. Me ya sa wasu suke jinkirin yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma ta yaya za ka iya taimakonsu su daina irin wannan tunanin?
4 Za ka ƙi idan aka ce ka tsallaka rafi mai faɗi da kafa. Amma za ka so ka tsallaka idan aka saka maka abin da zai taimake ka ka tsallake. Hakazalika, mutum da ya taƙure zai yi jinkirin nazarin Littafi Mai Tsarki. Mai gidan zai ga kamar nazarin zai ɗauki lokaci da kuma aiki tuƙuru. Ta yaya za ka taimake shi ya daina irin wannan tunanin? Bayan kun ɗan tattauna, za ka iya yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa ka soma nazarin Kalmar Allah kullum da mai gidan. Idan ka shirya da kyau, kowane komawa ziyara zai taimaki mutumin ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah.
5. Me ya sa ya kamata ka karanta littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
5 Amma, kafin ka taimaki wani ya amfana daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa, ya kamata ka fahimci littafin sosai. Ka karanta littafin daga farko zuwa ƙarshe kuwa? A lokacin da suka ɗauki hutu daga wajen aiki, wasu ma’aurata sun ɗauki littafin nan sa’ad suka je hutawa a wajen rafi. Sa’ad da wata mata da take sayar da kaya a wajen ta zo kusa da su, ta lura da jigon wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ta gaya wa ma’auratan cewa ta yi addu’a ga Allah ya ba ta amsar wannan tambayar ɗazu. Ma’auratan suka ba matar wannan littafin. Ka taɓa samun “zarafi” na sake karanta wannan littafin kuwa, sa’ad da kake jiran wani ko kuma a lokacin da kake hutawa a wajen aiki ko kuma a makaranta? (Afisawa 5:15, 16) Idan ka yi haka, za ka saba da wannan littafin na nazarin Littafi Mai Tsarki kuma za ka nemi zarafi ka yi magana da wasu game da abin da yake cikinsa.
6, 7. Ta yaya za ka iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
6 Idan za ka ba da littafin a hidimar fage, ka yi amfani da kwatanci da nassosi, da kuma tambayoyi da ke shafofi na 4, 5, da 6. Alal misali, za ka iya soma tattaunawa da wannan tambayar, “Duk da matsalolin da mutane suke fuskanta a yau, a ina ne za su iya samun tabbatacciyar ja-gora?” Bayan ka saurari amsar mutumin, sai ka karanta 2 Timothawus 3:16, 17, kuma ka bayyana cewa Littafi Mai Tsarki ya faɗi yadda za a magance matsalolin ’yan adam. Sai ka jawo hankalin mai gidan zuwa shafi na 4 da na 5, kuma ka yi tambaya: “Cikin yanayin da ke waɗannan shafuffuka, wannene ya fi damunka? Idan mai gidan ya nuna ɗaya, ka sa shi ya riƙe littafin sa’ad da kake karanta abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun. Sai, ka karanta shafi na 6, ka tambayi mai gidan, “Cikin tambayoyi shida da ke ƙasan wannan shafin, waccece za ka so ka san amsarta?” Idan mai gidan ya nuna ɗaya, ka nuna masa babin da ya amsa wannan tambayar, ka bar masa littafin, ka yi tabbatacciyar shiri ka dawo don ka amsa tambayar.
7 Wannan gwaji da aka nuna zai ɗauki kusan minti biyar ne kawai kafin a kammala shi. A cikin waɗannan ’yan mintocin za ka fahimci abin da ke damun mai gidan, za ka karanta kuma ka bayyana nassosi biyu, kuma ka yi tambaya da za ka amsa idan ka koma ziyara. Ɗan tattaunawar da ka yi da mai gidan wataƙila shi ne magana mai ban ƙarfafa da aka yi masa da daɗewa. A sakamakon haka, mutumin da yake taƙure zai ƙosa ya kasance tare da kai sa’ad da kake koya masa ya bi hanyar da za ta taimake shi ya samu ‘rai.’ (Matta 7:14) A hankali, sa’ad da marmarin mai gidan ta ƙaru, sai ka ƙara tsawon lokacin da kuke yin nazari. Kana iya yin haka ta wajen samun wurin zama don ku yi nazari mai tsawo.
Hanyoyin Koyarwa da Suka Fi Kyau
8, 9. (a) Ta yaya za ka iya shirya ɗalibinka da ke nazarin Littafi Mai Tsarki ya tsayayya wa gwajin da zai iya fuskanta? (b) A ina ne za a sami kayayyakin da ba sa cin wuta don a ƙarfafa bangaskiya?
8 Da zarar mutum ya soma yin biyayya da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, zai fuskanci gwaji da za su iya hana shi samun ci gaba. Manzo Bulus ya ce: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12) Bulus ya kwatanta wannan gwajin da wuta da za ta ƙone kayan gini marar kyau kuma ta ƙyale zinariya, azurfa, da kuma duwatsu masu daraja wanda ba sa cin wuta. (1 Korinthiyawa 3:10-13; 1 Bitrus 1:6, 7) Don ka taimaki ɗalibinka da yake nazarin Littafi Mai Tsarki ya samu halayen da yake bukata don ya tsayayya wa gwajin da zai fuskanta, ya kamata ka taimake shi ya kasance mai ƙarfi a ruhaniya.
9 Mai zabura ya kwatanta “kalmomin Ubangiji” da “azurfa da an gwada cikin tanderu a ƙasa, Wadda an tsarkake har so bakwai.” (Zabura 12:6) Hakika, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da kayayyaki masu daraja da za su iya taimaka a ƙarfafa bangaskiya. (Zabura 19:7-11; Misalai 2:1-6) Kuma littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa ya nuna maka yadda za ka ƙware wajen yin amfani da Nassosi.
10. Ta yaya za ka jawo hankalin ɗalibi zuwa Littafi Mai Tsarki?
10 A lokacin nazari, ka jawo ra’ayin ɗalibin ga nassosin da aka ambata a kowane babin da kuke tattaunawa. Ka yi amfani da tambayoyi don ka taimaki ɗalibin ya fahimci muhimman nassosi kuma ya yi amfani da su a rayuwarsa. Ka mai da hankali kada ka gaya ma shi abin da zai yi. Maimakon haka, ka bi misalan Yesu. Sa’ad da wani masanin Attaurat ya yi wa Yesu tambaya, Yesu ya amsa: “Mi ke a rubuce cikin Attaurat? Yaya ka ke karantawa?” Mutumin ya ba da amsarsa daga cikin Nassosi, kuma Yesu ya taimake shi ya fahimci yadda mizanin ya shafe shi. Yesu ya yi amfani da kwatanci kuma ya taimaki mutumin ya fahimci yadda koyarwar za ta shafe shi. (Luka 10:25-37) Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa yana ɗauke da kwatanci masu sauƙi sosai da za ka iya amfani da su ka taimaki ɗalibi ya yi amfani da Nassosi.
11. Menene yawan abin da ya kamata ku tattauna a kowane zama ɗaya na nazari?
11 Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa ya yi amfani da kalamai masu sauƙi don bayyana Kalmar Allah kamar yadda Yesu ya bayyana abubuwa masu wuyar fahimta da kalamai masu sauƙi. (Matta 7:28, 29) Ka bi misalinsa. Ka yi bayani dalla-dalla, mai sauƙin fahimta, daidai, kuma cikakke. Kada ka yi nazarin abubuwa masu yawa. Maimakon haka, ka bari yanayin ɗalibin da iyawarsa su nuna yawan sakin layin da ya kamata a yi nazarinsa a zama ɗaya. Yesu ya fahimci kasawar almajiransa shi ya sa bai cika su da bayani mai yawa ba fiye da wanda suke bukata a lokacin.—Yohanna 16:12.
12. Ta yaya za a yi amfani da ratayen?
12 Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa yana ɗauke da rataye da ya ƙunshi batutuwa 14. Bisa ga abin da ɗalibin yake bukata, malamin zai san yadda zai yi amfani da ratayen. Alal misali, idan ɗalibi ya ce bai gane ba ko kuma yana da tambayoyi a kan wasu abubuwa saboda bangaskiyarsa ta dā, zai fi kyau ka yi amfani da ratayen da ya dace, kuma ka tattauna batun da kanka. A wani ɓangare kuma, za ku iya gama babi ɗaya bisa ga bukatar ɗalibin. Ratayen yana ɗauke da batutuwa na musamman daga cikin Nassosi, kamar “ ‘Kurwa’ da kuma ‘Ruhu’—Menene Ainihi Ma’anar Waɗannan Kalmomi?” da kuma “Gano ‘Babila Babba.’ ” Za ka so ka tattauna waɗannan batutuwan da ɗalibinka. Tun da yake ba a yi tanadin tambayoyi ba a wannan ratayen, ya kamata ka fahimci batutuwan sosai don ka ƙera tambayoyi masu muhimmanci.
13. Ta yaya ne addu’a take ƙarfafa bangaskiya?
13 Zabura 127:1 ta ce: “Idan ba Ubangiji ya gina gidan ba, Banza magina su ke aiki.” Saboda haka, sa’ad da kake shirin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani, ka roƙi Jehobah ya taimake ka. Ka bari addu’o’in da za ka yi a farko da kuma ƙarshe a kowane nazarin ya nuna dangantakarka da Jehobah. Ka ƙarfafa ɗalibinka ya yi addu’a ga Jehobah don ya samu hikimar fahimtar Kalmarsa da kuma ƙarfin yin amfani da umurninta. (Yaƙub 1:5) Idan ya yi haka, wannan zai ƙarfafa ɗalibin ya jimre wa gwaji kuma ya ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarsa.
Ka Taimaka wa Ɗalibai na Littafi Mai Tsarki su Zama Masu Koyarwa
14. Wane irin ci gaba ne ya kamata ɗalibai na Littafi Mai Tsarki su yi?
14 Idan ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki za su yi biyayya da “iyakar abin” da Yesu ya umurce almajiransa, ya kamata su sami ci gaba daga ɗaliban Kalmar Allah zuwa masu koyar da ita. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 1:6-8) Menene za ka yi don ka taimaka wa ɗalibi ya sami irin wannan ci gaba na ruhaniya?
15. Me ya sa ya kamata mu ƙarfafa ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki su halarci taron Kirista?
15 Ka gayyaci ɗalibin zuwa taro na ikilisiya a nazarinku na farko. Ka bayyana ma shi cewa a taron ne kake samun koyarwa a matsayinka na malamin Kalmar Allah. A cikin ’yan makonni na soma nazarin, ka ɗauki mintoci kaɗan a ƙarshen nazarin ka kwatanta masa umurnin da kake samu a taro da kuma manyan taro. Ka gaya masa albarkar da kake samu a waɗannan taro. (Ibraniyawa 10:24, 25) Idan ɗalibin ya soma halartar taro a kai a kai, zai iya zama malamin Kalmar Allah.
16, 17. Waɗanne makasudai ne ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai kafa kuma ya cim ma?
16 Ka taimaki ɗalibin ya ƙafa makasudai da zai iya cim ma. Alal misali, ka ƙarfafa shi ya gaya wa abokinsa ko kuma wani danginsa abin da yake koya. Kuma ka shawarce shi ya ƙafa makasudin karanta duka Littafi Mai Tsarki. Idan ka taimake shi ya manne wa irin wannan hali na karanta Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci, wannan zai taimake shi bayan ya yi baftisma. Bugu da ƙari, me ya sa ba za ka shawarci ɗalibinka ya ƙudurta cewa zai tuna da aƙalla nassin da ta amsa wata tambaya mai muhimmanci a kowane babi na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Idan ya yi haka, zai zama ‘wanda babu dalilin kunya gareshi, yana rarrabe kalmar gaskiya sosai.’—2 Timothawus 2:15.
17 Maimakon ka koya wa ɗalibin ya maimaita nassi ko kuma ya taƙaita abin da nassi yake cewa, ka ƙarfafa shi ya bayyana duka abin da surar take cewa sa’ad da yake ba da amsa ga waɗanda suka tambaye shi game da bangaskiyarsa. Ɗan gajeren gwaji zai amfane shi, kana iya zama danginsa ko kuma abokin aikinsa da ya tambaye shi ya ba da bayanin bangaskiyarsa. Bayan ɗalibin ya ba da amsa, ka nuna masa yadda zai ba da amsa cikin ‘tawali’u da ladabi.’—1 Bitrus 3:15.
18. Wane ƙarin taimako ne za ka iya ba ɗalibin Littafi Mai Tsarki, sa’ad da ya zama mai shela marar baftisma?
18 Bayan wani ɗan lokaci, ɗalibin zai iya cancanci zuwa hidimar fage. Ka sanar da shi cewa ba ƙaramin gata ba ne a ƙyale mutum ya saka hannu a wannan aikin. (2 Korinthiyawa 4:1, 7) Sa’ad da dattawa suka yarda cewa ya cancanci ya zama mai shela marar baftisma, ka taimake shi ya shirya gabatarwa mai sauƙi kuma ka bi shi zuwa hidimar fage. Ka ci gaba da kasance tare da shi a kowane sashe na hidima, kuma ka koya masa yadda zai shirya don ya koma ya ziyarci mutanen da ya yi wa wa’azi. Halinka mai kyau zai taimake shi sosai.—Luka 6:40.
“Za Ka Ceci Kanka duk da Masu-Jinka”
19, 20. Wane makasudi ne ya kamata mu kafa, kuma me ya sa?
19 Babu shakka, ana bukatar a yi aiki tuƙuru don a taimaka wa wani ya kai “ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Abubuwa kaɗan ne a rayuwa za su sa mu farin ciki da za a iya gwadawa da taimaka wa wani ya yi biyayya da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. (1 Tassalunikawa 2:19, 20) Hakika, muna da gata na zama “abokan aiki na Allah” a wannan aiki na koyarwa da ake yi a dukan duniya!—1 Korinthiyawa 3:9.
20 Jehobah zai yi amfani da Yesu Kristi da kuma mala’iku ya hukunta waɗanda “ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tassalunikawa 1:6-8) Rayuwa tana cikin haɗari. Za ka iya ƙudurta soma nazari aƙalla ɗaya da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Yayin da kake ci gaba da yin wannan aikin, kana da damar ‘ceton kanka duk da masu-jinka.’ (1 Timothawus 4:16) Fiye da dā, ya kamata mu kasance da gaggawa a wajen taimakawa wasu su yi biyayya da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Menene Ka Koya?
• Me ya sa aka tsara littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
• Ta yaya za ka iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
• Waɗanne hanyoyin koyarwa ne suka fi kyau?
• Ta yaya za ka iya taimaka wa ɗalibi ya zama malamin Kalmar Allah?
[Hoto a shafi na 12]
Kana amfani da wannan littafin kuwa?
[Hoto a shafi na 13]
Ɗan tattaunawa zai iya motsa mutum ya ƙosa ya samu sanin Littafi Mai Tsarki
[Hoto a shafi na 15]
Menene za ka iya yi don ka jawo hankalin ɗalibi zuwa Littafi Mai Tsarki?
[Hoto a shafi na 16]
Ka taimaka wa ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya samu ci gaba