Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 8-12
  • Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Koyon “Iya Koyarwa”
  • Ka Koyar da Abin da ke Cikin Kalmar Allah
  • Ka Yi Amfani da Tambayoyi Masu Amfani
  • Ka sa ya Kasance Mai Sauƙi
  • Ka Taimaka wa Ɗalibai Su Ɗauki Abin da Suke Koya da Tamani
  • Nuna Ƙauna
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Taimaka wa Dalibinka Ya Cancanci Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Taimaka Wa Mutane Su Yi Biyayya Da Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 8-12

Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’

“Ka yi wa’azin kalma . . . ka tsautar, ka kwaɓa, ka gargaɗar, da iyakacin jimrewa da iya koyarwa.”—2 TIM. 4:2, NW.

1. Wane umurni ne Yesu ya ba almajiransa, kuma wane misali ne ya kafa?

DUK da ayyuka masu ban al’ajabi na warkarwa da Yesu ya yi a lokacin hidimarsa a duniya, mutane sun san shi ne a matsayin malami, ba mai warkarwa ko mai yin mu’ujiza ba. (Mar. 12:19; 13:1) Sanar da saƙon Mulkin Allah shi ne abin da ya fi muhimmanci a rayuwar Yesu, kuma hakan yake ga mabiyansa a yau. Kiristoci suna da aikin ci gaba da yin almajirantarwa ta wajen koyar da mutane su bi dukan abubuwan da Yesu ya ce.—Mat. 28:19, 20.

2. Menene muke bukatar mu yi domin mu cika aikinmu na wa’azi?

2 Don mu cika aikin da aka ba mu na almajirantarwa, a kowane lokaci muna ƙoƙarin kyautata iya koyarwarmu. Manzo Bulus ya nanata muhimmancin wannan iyawar sa’ad da yake yin wasiƙa ga abokin wa’azinsa Timothawus. Ya ce: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.” (1 Tim. 4:16) Irin koyarwar da Bulus yake magana a nan ba koyar da mutum ba ne ba kawai. Ƙwararrun Kiristoci suna motsa zuciyar mutane kuma hakan na sa su canja rayuwarsu. Wannan ita ce iyawa. Saboda haka, ta yaya za mu iya nuna “iya koyarwa” sa’ad da muke gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah?—2 Tim. 4:2.

Koyon “Iya Koyarwa”

3, 4. (a) Ta yaya za mu iya koyon “iya koyarwa”? (b) Ta yaya ne Makarantar Hidima ta Allah take taimaka mana mu zama ƙwararrun malamai?

3 Wani ƙamus ya ce “iyawa” “ƙwarewa ce da ake samu daga nazari, aikatawa, ko kuwa ta wajen kallo.” Muna bukatar mu mai da hankali ga waɗannan abubuwan guda uku don mu zama ƙwararrun malaman bishara. Muna iya samun cikakken fahimi na batun da muke dubawa ne kawai ta wajen yin nazari da addu’a. (Ka karanta Zabura 119:27, 34.) Kallon ƙwararrun malamai sa’ad da suke koyarwa zai taimaka mana mu koyi hanyoyin da suke amfani da shi kuma mu yi koyi da su. Kuma ta wajen yin amfani da abin da muke koya a kowane lokaci hakan zai taimaka mana mu kyautata iyawarmu.—Luk. 6:40; 1 Tim. 4:13-15.

4 Jehobah shi ne Mai Koyar da mu. Ta sashen ƙungiyarsa ta duniya, yana yi wa bayinsa da ke duniya ja-gora game da yadda za su cika aikinsu na wa’azi. (Isha. 30:20, 21) Don haka, a kowane mako ana yin Makarantar Hidima ta Allah a kowace ikilisiya, don a taimaka wa dukan waɗanda suke wannan makarantar su zama ƙwararrun masu sanar da Mulkin Allah. Ainihin littafin da ake amfani da shi a wannan makarantar shi ne Littafi Mai Tsarki. Hurarriyar Kalmar Jehobah ta gaya mana abin da za mu koyar. Bugu da ƙari, ta nuna irin hanyoyin koyarwar da suke da amfani kuma waɗanda suka dace. A kowane lokaci Makarantar Hidima ta Allah tana tunasar da mu cewa za mu zama ƙwararrun malamai idan muka koyar da abin da ke cikin Kalmar Allah, muka yi amfani da tambayoyin da suka dace, muka koyar a hanya mai sauƙi, kuma muka nuna mun damu da mutane. Bari mu bincika waɗannan batutuwan dabam dabam. Bayan haka, za mu tattauna yadda za mu motsa zuciyar ɗalibi.

Ka Koyar da Abin da ke Cikin Kalmar Allah

5. Menene ya kamata ya zama tushen koyarwarmu, kuma me ya sa?

5 Yesu, wanda shi ne babban malami, ya koyar da abin da ke cikin Nassosi. (Mat. 21:13; Yoh. 6:45; 8:17) Bai faɗi ra’ayoyinsa ba sai dai na Wanda ya aiko shi. (Yoh. 7:16-18) Wannan shi ne misalin da muke bi. Saboda haka, abin da muke tattaunawa a hidima ta kofa-kofa ko kuwa a nazarin Littafi Mai Tsarki na gida ya kamata ya fito ne daga Kalmar Allah. (2 Tim. 3:16, 17) Babu wani irin tunanin da za mu yi da zai yi daidai da amfani da kuma ikon hurarrun Nassosi. Littafi Mai Tsarki yana da iko. Duk irin bayanin da muke ƙoƙarin taimaka wa ɗalibi ya fahimta, hanya mafi kyau da ya kamata mu bi ita ce mu sa shi ko ita ya ko ta karanta abin da Nassosi suka ce game da batun.—Ka karanta Ibraniyawa 4:12.

6. Ta yaya ne malami zai tabbata cewa ɗalibi ya fahimci batun da suke tattaunawa?

6 Wannan ba ya nufin cewa Kirista da ke koyarwa ba ya bukatar ya shirya nazarin Littafi Mai Tsarki. Akasin haka, ya kamata a yi tunani sosai a kan nassosin da ba a yi ƙaulinsu ba da malamin ko ɗalibin zai karanta daga cikin Littafi Mai Tsarki a lokacin nazari. Gabaki ɗaya, zai dace a karanta nassosin da su ne tushen imaninmu. Zai kuma dace a taimaka wa ɗalibin ya fahimci kowane nassin da aka karanta.—1 Kor. 14:8, 9.

Ka Yi Amfani da Tambayoyi Masu Amfani

7. Me ya sa yin amfani da tambayoyi hanya ce mai kyau na koyarwa?

7 Iya yin amfani da tambayoyi yana sa tunani kuma yana taimaka wa malami ya motsa zuciyar ɗalibi. Saboda haka, maimakon ka bayyana wa ɗalibinka nassosi, ka ce masa ya bayyana maka su. A wasu lokatai za ka bukaci ka yi amfani da ƙarin tambayoyi ko jerin tambayoyi don ka taimaka wa ɗalibinka ya fahimce ka. Sa’ad da ka yi amfani da tambayoyi ta wannan hanyar koyarwa ba kawai kana taimakon ɗalibinka ya ga dalilin da ya sa zai gaskata da abin da yake koya ba amma kuma kana taimakonsa ne ya gaskata da kansa cewa abin da yake koya gaskiya ne.—Mat. 17:24-26; Luk 10:36, 37.

8. Ta yaya za mu iya sanin abin da ke cikin zuciyar ɗalibi?

8 Salon yin nazarin da ake amfani da shi a cikin littattafanmu shi ne tambayoyi da amsoshi. Babu shakka, yawancin mutanen da ka ke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su za su iya amsa tambayoyi da ke cikin littafin da wuri ta wajen yin amfani da bayanan da ke cikin sakin layin da ya amsa tambayar. Duk da haka, waɗannan amsoshin waɗanda daidai ne ba za su ishe malamin da ke son ya motsa zuciyar ɗalibinsa ba. Alal misali, ɗalibi zai iya yin bayani dalla-dalla a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da fasikanci. (1 Kor. 6:18) Ta wajen yin amfani da tambayoyin bincika ra’ayi, hakan zai iya nuna ainihin ra’ayin ɗalibin game da abin da yake koya. Malamin yana iya tambayarsa: “Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya haramta yin jima’i da wadda ba abokiyar aurenka ba? Menene ra’ayinka game da wannan hanin da Allah ya yi? Kana ganin cewa akwai amfanin bin mizanan Allah game da ɗabi’a?” Amsoshin da ya bayar a kan waɗannan tambayoyin za su iya bayyana abin da ke cikin zuciyar ɗalibin.—Ka karanta Matta 16:13-17.

Ka sa ya Kasance Mai Sauƙi

9. Menene ya kamata mu tuna sa’ad da muke bayyana abubuwan da ke cikin Nassi?

9 Yawancin gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna da ɗan sauƙi. Wataƙila an ruɗe mutanen da muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su da koyarwar addinin ƙarya. A matsayinmu na malamai muna bukatar mu sa Littafi Mai Tsarki ya kasance abin da ke da sauƙin fahimta. Ƙwararrun malamai suna yin bayani cikin sauƙi, dalla-dalla, kuma daidai wa daida. Idan muka bi wannan ja-gorar, ba za mu sa gaskiya ya zama abin da ke da wuyar fahimta ba. Ka guje wa yin bayanan da ba su dace ba. Ba ma bukatar mu yi kalami a kan dukan nassosin da muka karanta. Ka mai da hankali kawai a kan abubuwan da suka fi muhimmanci don bayyana batun da ake tattaunawa. Hakan zai sa ɗalibin ya fahimci gaskiya masu zurfi da ke cikin Nassi yayin da yake ci gaba da fahimtar abin da yake koya.—Ibran. 5:13, 14.

10. Waɗanne abubuwa ne za su sa mu san yawan batun da za mu tattauna a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki?

10 Menene yawan batun da ya kamata mu tattauna a zama ɗaya na nazari? A wannan, ana bukatar a yi amfani da fahimi. Iyawa da kuma yanayin ɗalibi da kuma malaminsa za su bambanta, amma ya kamata mu dinga tunawa a kowane lokaci cewa ainihin abin da muke son mu cim ma a matsayin malami shi ne mu taimaka wa ɗalibinmu ya kasance da cikakkiyar bangaskiya. Saboda haka ya kamata mu ba shi isashen lokaci ya karanta, ya fahimci, kuma ya yi na’am da gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. Ba zai dace mu tattauna batutuwa masu yawa da ba zai iya riƙewa ba. Kuma ya kamata mu ci gaba da yin nazarin a kai a kai. Da ɗalibinmu ya fahimci bayanin, sai mu ci gaba kawai.—Kol. 2:6, 7.

11. Wane darassi game da koyarwa ne za mu iya koya daga manzo Bulus?

11 Manzo Bulus ya faɗi saƙon Mulki a hanya mai sauƙi sa’ad da yake tattaunawa da sababbin ɗalibai. Ko da yake yana da ilimi sosai, ya guji yin amfani da kalmomi masu wuyan fahimta. (Ka karanta 1 Korinthiyawa 2:1, 2.) Gaskiya mai sauƙi da ke cikin Nassi yana jawo mutanen da suke son gaskiya kuma yana gamsar da su. Mutum ba ya bukatar ya kasance mafi ilimi kafin ya fahince su.—Mat. 11:25; A. M. 4:13; 1 Kor. 1:26, 27.

Ka Taimaka wa Ɗalibai Su Ɗauki Abin da Suke Koya da Tamani

12, 13. Menene ya kamata ya motsa ɗalibi ya bi abin da yake koya? Ka kwatanta.

12 Don ya zama mai amfani, koyarwarmu na bukatar ya motsa zuciyar ɗalibinmu. Ɗalibin yana bukatar ya fahimci yadda bayanin ya shafe shi, yadda zai amfane shi, da kuma yadda rayuwarsa za ta ƙara gyaruwa idan ya bi umurnin da ke cikin Nassi.—Isha. 48:17, 18.

13 Alal misali, wataƙila muna tattauna Ibraniyawa 10:24, 25, wadda ta ƙarfafa Kiristoci su taru da ’yan’uwansu masu bi don samun ƙarfafa daga Nassi da kuma tarayya mai kyau. Idan ɗalibin bai soma halartar taron ikilisiya ba, muna iya ɗan kwatanta masa yadda ake tafiyar da taron da kuma abin da za a tattauna. Muna iya gaya masa cewa taro na ikilisiya sashe ne na bautarmu kuma ka nuna masa cewa muna amfana sosai. Bayan haka, muna iya gayyatar ɗalibin ya halarci taro. Abin da ya kamata ya motsa shi ya bi umurnin da ke cikin Nassi shi ne muradinsa na son yin biyayya ga Jehobah, ba don ya faranta ran wanda yake nazari da shi ba.—Gal. 6:4, 5.

14, 15. (a) Menene ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai iya koya game da Jehobah? (b) Ta yaya ne sanin halin Allah zai amfane ɗalibin Littafi Mai Tsarki?

14 Ainihin amfanin da ɗalibai suke samu a nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma bin mizanansa shi ne, yana sa su san Jehobah sosai kuma su ƙaunace shi. (Isha. 42:8) Shi Uba mai ƙauna ne da Mahalicci kuma Mai sama da ƙasa kuma ya bayyana halinsa da iyawarsa ga waɗanda suke ƙaunarsa da kuma bauta masa. (Ka karanta Fitowa 34:6, 7.) Sa’ad da Musa yake gab da yi wa al’ummar Isra’ila ja-gora daga bauta a ƙasar Masar, Jehobah ya bayyana kansa ta wajen yin amfani da wannan furcin: “Zan zama duk abin da nike son in zama.” (Fit. 3:13-15, NW) Hakan ya nuna cewa Jehobah zai ci gaba da kasancewa abin da ya kamata ya zama don ya cika nufe-nufensa game da zaɓaɓɓun mutanensa. Shi ya sa Isra’ilawa suka san Jehobah a matsayin Mai Ceto, Jarumi, Mai Tanadi, Mai Cika alkawura da kuma wanda ya taimaka musu a wasu hanyoyin.—Fit. 15:2, 3; 16:2-5; Josh. 23:14.

15 Wataƙila ɗalibanmu ba za su iya samun taimako ta wurin mu’ujiza daga Jehobah yadda Musa ya samu ba. Duk da haka, sa’ad da ɗalibanmu suka ci gaba da yin imani da kuma ƙara daraja abin da suke koya kuma suna amfani da su, babu shakka, za su ga cewa suna bukatar su dogara ga Jehobah don samun gaba gaɗi, hikima, da kuma ja-gora. Sa’ad da suka yi hakan, su ma za su san Jehobah a matsayin Mai hikima kuma Mai ba da shawara mai kyau da za su iya dogara da shi, Mai kāriya, kuma Mai tanadin dukan abubuwan da suke bukata.—Zab. 55:22; 63:7; Mis. 3:5, 6.

Nuna Ƙauna

16. Me ya sa ba iyawa ba ne abu mafi muhimmanci da zai sa mu zama ƙwararrun malamai?

16 Idan ka ga cewa ba ka ƙware sosai ba yadda ka ke so a wajen koyarwa ba, kada ka karaya. Jehobah da Yesu ne suke ja-gorar tsarin koyarwa da ake tafiyar da shi a dukan duniya a yau. (A. M. 1:7, 8; R. Yoh. 14:6) Suna iya kyautata ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu saboda kalamanmu ta motsa masu zukatan kirki. (Yoh. 6:44) Ƙauna ta gaskiya da malami yake nuna wa ɗalibinsa zai sauya duk wani rashin iyawarsa. Manzo Bulus ya nuna cewa ya fahimci muhimmancin nuna ƙauna ga ɗalibai.—Ka Karanta 1 Tassalunikawa 2:7, 8.

17. Ta yaya za mu iya nuna ƙauna ta gaskiya ga kowane ɗalibi na Littafi Mai Tsarki?

17 Hakazalika, muna iya nuna ƙauna ga kowane ɗalibinmu na Littafi Mai Tsarki ta wajen saninsa sosai. Yayin da muke tattauna mizanan da ke cikin Nassi da shi, wataƙila za mu iya sanin yanayinsa. Muna iya ganin cewa ya soma yin rayuwar da ta jitu da wasu abubuwan da ya koya daga Littafi Mai Tsarki. Wataƙila har ila yana bukatar ya yi gyare-gyare a wasu wuraren. Ta wajen taimaka wa ɗalibin ya ga yadda bayanin da aka tattauna a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki suka shafe shi, za mu iya taimaka masa ya zama almajiran Kristi na gaskiya.

18. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi addu’a tare da ɗalibinmu kuma mu sa shi a addu’armu?

18 Abin da ya fi muhimmanci, shi ne muna iya yin addu’a tare da ɗalibinmu kuma muna iya sa shi a namu addu’ar. Ya kamata ya fahimci cewa muna son mu taimaka masa ne ya san Mahaliccinsa sosai, ya kusance Shi, kuma ya amfana daga ja-gorarsa. (Ka karanta Zabura 25:4, 5.) Sa’ad da muka roƙi Jehobah ya taimaka wa ɗalibin da yake ƙoƙarin yin amfani da abin da yake koya, ɗalibin zai ga muhimmancin zama ‘mai-aika magana.’ (Yaƙ. 1:22) Sa’ad da ɗalibin ya saurari addu’armu, shi ma zai koyi yadda ake yin addu’a. Abin farin ciki ne a taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su soma dangantaka da Jehobah!

19. Menene za a tattauna a talifi na gaba?

19 Abin farin ciki ne mu san cewa Shaidu fiye da miliyan shida da rabi a dukan duniya ne suke aiki tuƙuru wajen nuna “iya koyarwa” domin su taimaka wa masu zukatan kirki su bi dukan abin da Yesu ya umurta. Waɗanne sakamako ne ake samu a ayyukanmu na wa’azi? Za a tattauna amsar wannan tambayar a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• Me ya sa Kiristoci suke bukatar su koyi “iya koyarwa”?

• Ta yaya za mu iya sa koyarwarmu ta kasance mai amfani sosai?

• Menene zai iya sauya duk wani rashin iya koyarwarmu?

[Hoto a shafi na 9]

Ka shiga Makarantar Hidima ta Allah?

[Hoto a shafi na 10]

Me ya sa yake da muhimmanci mu gaya wa ɗalibinmu ya karanta Littafi Mai Tsarki?

[Hoto a shafi na 12]

Ka yi addu’a tare da ɗalibinka kuma ka sa shi a naka addu’ar

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba