Jehobah Allah Ne Mai Godiya
“Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi.”—IBRANIYAWA 6:10.
1. Ta yaya Jehobah ya nuna godiyarsa ga Ruth ’yar Mowab?
JEHOBAH yana godiya sosai da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da waɗanda suke neman su yi nufinsa suke yi, kuma yana saka musu. (Ibraniyawa 11:6) Boaz mutum mai aminci ya san wannan fanni na musamman na mutuntakar Allah, domin ya gaya wa Ruth ’yar Mowab da take kula da surkuwarta gwauruwa cewa: “Ubangiji ya sāka miki aikinki, ki karɓi cikakkiyar lada daga wurin Ubangiji.” (Ruth 2:12) Allah ya albarkaci Ruth kuwa? Ƙwarai kuwa! Domin an rubuta labarinta a cikin Littafi Mai Tsarki! Ƙari ga haka, ta auri Boaz kuma ta zama kakar Sarki Dauda da kuma Yesu Kristi. (Ruth 4:13, 17; Matta 1:5, 6, 16) Wannan yana cikin misalai da yawa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa Jehobah yana godiya ga bayinsa.
2, 3. (a) Menene ya sa nuna godiyar Jehobah ke da ban mamaki? (b) Me ya sa Jehobah yake nuna godiya ta gaske? Ka ba da misali.
2 Rashin adalci ne a wurin Jehobah idan bai nuna godiya ba. Ibraniyawa 6:10 ta ce: “Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.” Abin da ya sa wannan furci ke da ban mamaki shi ne cewa Allah yana godiya ga mutane masu ibada duk da cewa su masu zunubi ne kuma sun kasa ga darajarsa.—Romawa 3:23.
3 Domin ajizancinmu, muna iya jin cewa ayyukanmu na ibada ba su da amfani kuma ba mu cancanci samun albarkar Allah ba. Amma Jehobah ya fahimci muradinmu da yanayinmu, kuma yana daraja hidimar da muka yi da zuciya ɗaya. (Matta 22:37) Alal misali: A ce wata yarinya ƙarama ta kashe dukan kuɗin da ta tara kuma ta sayo wa uwarta sarƙa mai araha. Ko da yake sarƙar mai araha ce, uwar ta ɗauke ta da tamani kuma ta yi godiya sosai domin yarinyarta ƙarama ce ta sayo mata.
4, 5. Ta yaya Yesu ya yi koyi da Jehobah wajen nuna godiya?
4 Da yake ya san muradinmu da kasawarmu, Jehobah yana godiya sa’ad da muka yi iyakar abin da za mu iya yi, ko kaɗan ne ko babba. Yesu ya nuna halin Ubansa sosai game da wannan. Ka tuna labarin Littafi Mai Tsarki game da kyautar da gwauruwa ta ba da. “[Yesu] ya tada ido, ya ga mawadata suna zuba sadakokinsu cikin ma’aji. Ya ga wata gwauruwa kuma matalauciya tana zuba anini biyu a ciki. Ya ce, Gaskiya ni ke faɗa muku, abin da wannan gwauruwa matalauciya ta zuba ciki ya fi nasu duka: gama waɗannan duka daga cikin falalarsu suka zuba zuwa cikin sadakoki: amma ita daga tsiyatta ta zuba dukan iyakar abin zaman gari da ta ke da shi.”—Luka 21:1-4.
5 Hakika, da yake ya san yanayin matar cewa ita gwauruwa ce kuma matalauciya, Yesu ya fahimci darajar kyautarta, kuma ya yi godiya. Haka Jehobah yake yi. (Yohanna 14:9) Ba abin ban ƙarfafa ba ce ka san cewa ko menene yanayinka, za ka iya samun tagomashi a gaban Allahnmu da Ɗansa masu yin godiya?
Jehobah Ya Saka wa Bahabashe Mai Jin Tsoronsa
6, 7. Me ya sa kuma ta yaya Jehobah ya nuna godiyarsa ga Ebed-melek?
6 An nuna a kai a kai a cikin Nassosi cewa Jehobah yana nuna godiya ga waɗanda suke yin nufinsa. Ka yi la’akari da sha’aninsa da Ebed-melek Bahabashe mai jin tsoron Allah, shi tsaran Irmiya ne kuma bawa ne a gidan Sarki marar aminci, Zadakiya na Yahuda. Ebed-melek ya ji cewa hakiman Yahuda sun zargi annabi Irmiya da ta da zaune tsaye kuma suka jefa shi cikin rami don yunwa ta kashe shi. (Irmiya 38:1-7) Da yake ya san cewa an tsane Irmiya sosai domin saƙon da yake wa’azinsa, Ebed-melek ya kasadar da ransa kuma ya roƙi sarki. Da gabagaɗi, Bahabashen ya ce: “Ya ubangijina sarki, waɗannan mutane sun yi mugun aiki cikin dukan abin da suka yi ma Irmiya annabi, da suka jefa shi cikin rami; yana kuwa mutuwa a wurin da ya ke, domin yunwa da a ke yi.” Da izinin sarkin, Ebed-melek ya ɗauki maza 30 kuma suka ceci annabin Allah.—Irmiya 38:8-13.
7 Jehobah ya ga cewa Ebed-melek yana da bangaskiya, kuma hakan ya taimake shi ya sha kan kowane tsoro da yake ji. Jehobah ya nuna godiyarsa kuma ya gaya wa Ebed-melek ta wurin Irmiya cewa: “Ga shi, batun da na faɗi a kan birnin nan na masifa, ba na alheri ba, zan tabbatadda shi . . . Amma zan cece ka kai a ran nan . . . ba kuwa za a bashe ka a cikin hannun mutanen da ka ke jin tsoronsu ba. Gama zan cece ka, . . . amma za ka tsira da ranka; tun da ka bada gaskiya gareni.” (Irmiya 39:16-18) Hakika Jehobah ya ceci Ebed-melek da kuma Irmiya daga hannun miyagun hakimai na Yahuda kuma bayan haka daga Babiloniyawa, da suka halaka Urushalima. Zabura 97:10 ta ce: “[Jehobah] mai-kiyayadda rayukan tsarkakansa ne; Yana fishe su daga hannun masu-mugunta.”
“Ubanka Kuwa Wanda Ya ke Gani Daga Cikin Ɓoye Za Ya Saka Maka”
8, 9. Kamar yadda Yesu ya nuna, wane irin addu’o’i ne Jehobah yake ji?
8 Mun ga wani tabbaci da ya nuna cewa Jehobah yana godiya kuma yana daraja furcinmu na ibada ta wajen abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da addu’a. “Addu’ar kamilai abin murnassa [Allah] ne,” in ji mutum mai hikima. (Misalai 15:8) A zamanin Yesu, shugabanan addinai da yawa sun yi addu’a a fili ba don suna da ibada ba amma don su burge mutane. Sun “karɓi ladassu,” in ji Yesu. Ya umurci mabiyansa: “Amma kai, lokacinda ka ke yin addu’a, shiga cikin lolokinka, bayanda ka rufe ƙofarka kuma, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ke cikin ɓoye, Ubanka kuwa wanda ya ke gani daga cikin ɓoye za ya sāka maka.”—Matta 6:5, 6.
9 Yesu bai ce kada a yi addu’a a fili ba, saboda shi da kansa ya yi addu’a a fili a wasu lokatai. (Luka 9:16) Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka yi masa addu’a da zuciya ɗaya, ba tare da son mu burge wasu ba. Hakika, addu’a ta kanmu tana nuna yadda muke ƙaunar Allah da kuma yadda muke dogara a gare shi. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne da Yesu sau da yawa ya nemi wuraren da ba kowa don ya yi addu’a. Sau ɗaya, ya yi hakan “da assussuba.” Wani lokaci, “ya hau dutse, shi ɗaya, garin yin addu’a.” Kuma kafin ya zaɓi manzanninsa 12, Yesu ya yi addu’a dukan dare shi kaɗai.—Markus 1:35; Matta 14:23; Luka 6:12, 13.
10. Idan addu’o’inmu suka nuna cewa muna da cikakken muradi na faranta wa Allah rai, wane tabbaci ne za mu kasance da shi?
10 Babu shakka, Jehobah ya saurari addu’o’in da Ɗansa ya yi da zuciya ɗaya! Hakika, a wani lokaci Yesu ya yi addu’a da “kuka mai-zafi da hawaye . . . da aka amsa masa kuma saboda tsoronsa mai-ibada.” (Ibraniyawa 5:7; Luka 22:41-44) Idan muka nuna a addu’o’inmu cewa muna da cikakken muradi na faranta wa Allah rai, mu tabbata cewa Ubanmu na samaniya na sauraronmu da kyau. Hakika, “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, . . . da gaskiya.”—Zabura 145:18.
11. Ta yaya Jehobah yake ji game da abin da muke yi a ɓoye?
11 Da yake Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka yi addu’a gare shi a ɓoye, zai yi farin ciki sosai sa’ad da muka yi masa biyayya a ɓoye! Hakika, Jehobah yana sane da abin da muke yi a ɓoye. (1 Bitrus 3:12) Idan muka kasance da aminci kuma muna yin biyayya sa’ad da muke mu kaɗai, wannan yana nuna cewa muna da “sahihiyar zuciya” wadda ke da cikakken muradi ga Jehobah, kuma tana bin abin da ke daidai. (1 Labarbaru 28:9) Irin wannan halin na faranta wa Jehobah rai!—Misalai 27:11; 1 Yohanna 3:22.
12, 13. Ta yaya za mu tsare zuciyarmu kuma mu zama kamar almajiri Natanayilu mai aminci?
12 Saboda haka, Kiristoci masu aminci suna guje wa yin zunubi a ɓoye da ke ɓata zuciya, kamar kallon batsa da kuma nuna ƙarfi. Ko da za a iya ɓoye wa ’yan adam wasu zunubai, mun fahimci cewa “abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibraniyawa 4:13; Luka 8:17) Ta yin ƙoƙarin guje wa abubuwa da ke ɓata wa Jehobah rai, muna da lamiri mai tsabta kuma muna farin ciki cewa muna da yardan Allah. Hakika, Jehobah yana farin ciki da mutumin “wanda ke tafiya sosai, yana aika adalci, yana kuwa faɗin gaskiya cikin zuciyarsa.”—Zabura 15:1, 2.
13 To, yaya za mu tsare zuciyarmu a cikin duniya da ke cike da mugunta? (Misalai 4:23; Afisawa 2:2) Ƙari ga yin amfani da dukan tanadi na ruhaniya, dole ne mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu ƙi abin da ke mugu kuma mu yi abin da ke nagari, mu aikata da sauri don kada sha’woyi da ba su dace ba su tsiro kuma su haifi zunubi. (1 Yaƙub:14, 15) Babu shakka, za ka yi farin ciki idan Yesu ya faɗi game da kai abin da ya ce game da Natanayilu: “Duba, ga mutumin Isra’ila na gaske, wanda ba shi da algus!” (Yohanna 1:47) Natanayilu wanda kuma ake kira Barthalamawus, daga baya ya samu gatar zama ɗaya daga cikin manzannin Yesu goma sha biyu.—Markus 3:16-19.
“Babban Priest Mai-Jinƙai Mai-Aminci”
14. Ta yaya yadda Yesu ya aikata ga abin da Maryamu ta yi ya bambanta da abin da wasu suka yi?
14 Da yake shi “surar Allah marar-ganuwa” ne, Yesu ya yi koyi da Ubansa sosai wajen nuna godiya ga waɗanda suke bauta wa Allah da zuciya mai tsabta. (Kolossiyawa 1:15) Alal misali, kwanaki biyar kafin ya ba da ransa, an gayyaci Yesu da wasu cikin almajiransa zuwa gidan Siman na Bait’anya. Da maraice, Maryamu, ’yar’uwar Li’azaru da Martha, “ta ɗauki tandun mai mai-ƙamshi, wanda ana ce da shi nard, mai-tsada dayawa” (ya yi kusan kuɗin aiki na shekara guda na lokacin) ta shafa a kan Yesu da ƙafafunsa. (Yohanna 12:3) Wasu suka ce “Ina dalilin wannan ɓarna?” Amma a gaban Yesu, Maryamu ta yi abu mai kyau. Ya ɗauka cewa ta yi karimci mai girma kuma yana da muhimmanci sosai domin mutuwarsa da jana’iza sun yi kusa. Shi ya sa maimakon ya zargi Maryamu, Yesu ya ɗaukaka ta. Ya ce, “dukan inda za a yi wa’azin wannan bishara cikin duniya duka, abin da macen nan ta aika kuma za a ambace shi domin tunawa da ita.”—Matta 26:6-13.
15, 16. Ta yaya muka amfana da yake Yesu ya yi rayuwa kuma ya bauta wa Allah kamar ɗan adam?
15 Muna da gatar samun Yesu mutum mai godiya ya zama Shugabanmu! Hakika, rayuwar Yesu na ɗan adam ta sa ya kasance a shirye don aikin da Jehobah yake son ya yi na hidimar Babban Firist da kuma Sarki, zai soma da ikilisiyar shafaffu bayan haka kuma duniya.—Kolossiyawa 1:13; Ibraniyawa 7:26; Ru’ya ta Yohanna 11:15.
16 Kafin ya zo duniya, daular Yesu tana wurin ’yan adam. (Misalai 8:31) Don ya yi rayuwa kamar ɗan adam, ya fahimci gwajin da muke fuskanta a hidimarmu ga Allah. Manzo Bulus ya rubuta: “Domin wannan fa ya wajabce shi shi kamantu ga ’yan’uwansa a cikin dukan abu, domin shi zama babban priest mai-jinƙai, mai-aminci . . . Gama yayinda shi da kansa ya sha wahala ana jarabtassa, yana da iko ya taimaki waɗanda a ke jarabtassu.” Yesu zai iya “tarayyar kumamancinmu” domin “an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai banda zunubi.”—Ibraniyawa 2:17, 18; 4:15, 16.
17, 18. (a) Menene wasiƙu zuwa ga ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama suka nuna game da yadda Yesu yake godiya? (b) Menene ake shirya shafaffu Kiristoci su yi?
17 A bayyane yake cewa Yesu ya fahimci gwaji da mabiyansa suke fuskanta bayan an ta da shi daga matattu. Ka yi la’akari da wasiƙu da ya aika wa ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama, waɗanda manzo Yohanna ya rubuta. Yesu ya gaya wa ikilisiyar da ke Samiruna: “Na san ƙuncinka da talaucinka.” Wato, a nan Yesu yana cewa, ‘Na fahimci matsalolinku; na san abin da kuke fuskanta.’ Domin shi ma ya sha wahala har mutuwa, ya daɗa cewa cikin juyayi da tabbaci: “Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.”—Ru’ya ta Yohanna 2:8-10.
18 Wasiƙun Yesu zuwa ga ikilisiyoyi bakwai suna cike da furcin da ya nuna cewa Yesu ya fahimci matsalolin almajiransa ya kuma yi godiya don hidimarsu na aminci. (Ru’ya ta Yohanna 2:1–3:22) Ka tuna cewa shafaffu Kiristoci ne Yesu yake wa magana da suke da begen yin sarauta da shi a sama. Kamar Ubangijinsu, ana shirya su don aikinsu mai girma na taimakawa wajen gudanar da amfanin hadayar fansa ta Kristi cikin juyayi ga ’yan adam masu zunubi.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 22:1-5.
19, 20. Ta yaya waɗanda suke cikin “taro mai-girma” suke nuna godiyarsu ga Jehobah da Ɗansa?
19 Hakika, kamar yadda Yesu yake ƙaunar mabiyansa shafaffu, yana ƙaunar miliyoyin “waɗansu tumaki” waɗanda sune ‘taro mai girma, daga al’ummai, da za su tsira daga “babban tsananin” da ke zuwa. (Yohanna 10:16; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Domin suna godiya don hadayarsa ta fansa da kuma begensu na rai madawwami, waɗansu tumaki suna jerin gwano zuwa wurin Yesu. Ta yaya suke nuna godiyarsu? Suna hakan ta wajen “yi masa [Allah] bauta kuma dare da rana.”—Ru’ya ta Yohanna 7:15-17.
20 Rahoto na dukan duniya ta shekarar hidima ta 2006 da ke shafofi na 27 zuwa 30 ya ba da tabbaci cewa waɗannan amintattu masu hidima suna bauta wa Jehobah da gaske “dare da rana.” Hakika, a shekarar hidimar da ta wuce, taro mai girma da sauran rukuni na shafaffun Kiristoci sun ba da sa’o’i 1,333,966,199 a hidimar fage wato daidai da na fiye da shekaru 150,000!
Ka Ci Gaba da Nuna Godiya!
21, 22. (a) Game da nuna godiya, me ya sa dole ne Kiristoci su mai da hankali a yau? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
21 A sha’aninsu da ’yan adam ajizai, Jehobah da Ɗansa sun nuna godiya mai ban mamaki. Amma, abin baƙin ciki shi ne, yawancin ’yan adam ba sa tunanin Allah, maimakon haka suna mai da hankali ga nasu damuwar. Da yake kwatanta mutanen da suke zaune a “kwanaki na ƙarshe,” Bulus ya rubuta: “Mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi . . . marasa-godiya, marasa-tsarki.” (2 Timothawus 3:1-5) Kiristoci na gaskiya ba sa haka, amma ta addu’arsu, da biyayyarsu, da kuma hidimarsu da dukan zuciya suna nuna godiyarsu don dukan abubuwan da Allah ya yi musu!—Zabura 62:8; Markus 12:30; 1 Yohanna 5:3.
22 A talifi na gaba, za mu maimaita wasu cikin tanadi masu yawa na ruhaniya da Jehobah ya yi mana. Yayin da muke tunanin waɗannan “kyakkyawar baiwa” bari mu ci gaba da ƙara yin godiya.—Yaƙub 1:17.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai godiya ne?
• Sa’ad da muke mu kaɗai, yaya za mu faranta wa Jehobah rai?
• Ta waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna godiya?
• Yaya rayuwa ta ɗan adam ta taimaki Yesu ya zama sarki mai juyayi kuma mai yin godiya?
[Hoto a shafi na 17]
Kamar yadda iyaye suke ƙaunar furcin yaransu, Jehobah yana godiya sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu