Abin Da Ya Sa Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba
“Fa ne shi, aikinsa cikakke ne.”—KUBAWAR SHARI’A 32:4.
1, 2. (a) Me ya sa kake ƙaunar begen rayuwa ta har abada? (b) Menene ya hana wasu su gaskata da Allahn da ya yi alkawarin abubuwa masu ban al’ajabi a nan gaba?
KANA farin cikin tunanin rayuwa a aljanna kuwa? Wataƙila kana tunanin yadda za ka yi bincike a wannan duniya mai ban sha’awa kuma ka koyi abubuwa dabam dabam game da abubuwa masu rai waɗanda ba su da iyaka. Ko kuma kana tunanin irin gamsarwa da za ka samu sa’ad da kake aiki da waɗansu don ku gyara duniya kuma ku mai da ta ta zama aljanna. Ko kuma ka yi tunanin irin aikin da za ka koya a ɓangaren fasaha, zane-zane, kaɗe-kaɗe, ko kuma waɗansu abubuwa da ba ka da lokacin su a wannan rayuwa. Ko yaya dai, kana ƙaunar begen yin rayuwar da Littafi Mai Tsarki yake kira “hakikanin rai” wato irin rayuwar da Jehobah yake so mu yi, har abada.—1 Timothawus 6:19.
2 Gata ce kuma abin farin ciki ne a gaya wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da bege, ko ba haka ba? Amma, mutane da yawa ba sa son irin wannan begen. Suna ganin ƙage ne ko kuma tatsuniya ce ga mutanen da ake saurin yaudararsu. Wataƙila zai yi musu wuya su gaskata da Allahn da ya yi alkawarin rayuwa ta har abada a aljanna. Me ya sa? Matsalar da ke damun waɗansu shi ne mugunta. Sun gaskata cewa babu dalilin mugunta da wahala da ke cikin wannan duniya, idan da gaske Allah yana wanzuwa kuma shi maɗaukaki ne mai ƙauna. Babu Allahn da ya ƙyale mugunta da ya kamata ya wanzu, sun yi tunani cewa idan yana wanzuwa, shi ba maɗaukaki ba ne ko kuma ba ya kula da su. Ga wasu, irin wannan tunanin tabbatacce ne. Hakika, Shaiɗan ya nuna cewa ya ƙware wajen makantar da hankalin ’yan adam.—2 Korinthiyawa 4:4.
3. Waɗanne tambayoyi masu wuya ne za mu iya taimaka wa mutane su fahimta, kuma me ya sa mun cancanci mu yi haka?
3 Da yake mu Shaidun Jehobah ne, mun cancanci mu taimaki mutanen da Shaiɗan da kuma hikimar duniyar nan suka ruɗe su. (1 Korinthiyawa 1:20; 3:19) Mun fahimci abin da ya sa yawancin mutane ba su gaskata da alkawura na Littafi Mai Tsarki ba. Gaskiyar ita ce ba su san Jehobah ba. Wataƙila ba su san sunansa ba ko kuma ma’anarsa, kuma ba su san kome ba game da halayensa ko kuma yadda yake cika alkawuransa. Muna da gatar samun irin wannan ilimin. A koyaushe yana da kyau mu riƙa tunanin yadda za mu iya taimakon mutane “masu-duhun hankali” su sami amsar tambayoyi masu wuya da ’yan adam suke yi, “Me ya sa Allah ya ƙyale mugunta da wahala? (Afisawa 4:18) Da farko za mu tattauna yadda za mu iya ba da tabbataciyar amsa. Bayan haka za mu tattauna yadda halayen Jehobah suka bayyana a yadda ya bi da matsalar mugunta.
Neman Hanyar ba da Amsa da ta Dace
4, 5. Menene ya kamata mu yi da farko idan wani ya yi tambaya game da abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala? Ka ba da bayani.
4 Idan wani ya yi tambaya, me ya sa Allah ya ƙyale wahala, yaya za mu amsa? Ba da ɓata lokaci ba za mu so mu ba da bayani dalla-dalla, daga abin da ya faru a lambun Adnin. A wani lokaci, hakan zai dace. Amma ya kamata mu kula. Muna bukatar mu yi shiri kafin mu amsa wasu tambayoyi. (Misalai 25:11; Kolossiyawa 4:6) Bari mu tattauna darrusa guda uku da za su sa mu taimaki mutum kafin mu amsa tambaya.
5 Na farko, idan mutum ya damu game da mugunta da ta yi yawa a duniya, wataƙila muguntar ta taɓa shafansa ne ko kuma waɗanda yake ƙauna. Zai yi kyau mu fara da nuna juyayi na gaskiya. Manzo Bulus ya shawarci Kiristoci: “Ku yi kuka tare da masu-kuka.” (Romawa 12:15) Idan muka nuna masa “juyayi,” wataƙila hakan zai motsa mutumin. (1 Bitrus 3:8) Idan ya fahimci cewa muna ƙaunarsa, zai so ya saurari abin da muke faɗa.
6, 7. Me ya sa ya kamata mu yabi mutumin da ya yi tambaya game da wasu batu na Littafi Mai Tsarki da suke damunsa?
6 Na biyu, ya kamata mu yaba wa mutumin don tambayar da ya yi. Wasu sun kammala cewa tun da sun damu da irin wannan tambayar, hakan ya nuna cewa ba su da bangaskiya ko kuma ba su daraja Allah ba. Wataƙila wani malamin addini ya taɓa gaya masu haka. Duk da haka, yin tambaya ba shi ba ne yake nuna rashin bangaskiya ba. Ballantana ma, mutane masu aminci a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki sun yi irin waɗannan tambayoyin. Alal misali, mai zabura Dauda ya yi tambaya: “Ya Ubangiji, don mi ka tsaya daga nesa? Don mi ka ɓuya cikin wokatan wahala?” (Zabura 10:1) Hakazalika, annabi Habakkuk ya yi tambaya: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina tada murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto. Don me ka ke nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma? gama ɓarna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso.”—Habakkuk 1:2, 3.
7 Waɗannan mutane masu aminci ne waɗanda suka yi wa Allah biyayya sosai. An tsauta musu ne don sun yi tambaya game da abin da ke damunsu? Maimakon haka, Jehobah ya ga ya cancanta a rubuta tambayoyinsu cikin Kalmarsa. A yau, wataƙila mutumin da ya damu saboda yawan mugunta, yana jin yunwa ta ruhaniya ne, yana neman amsoshin da Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya bayarwa. Ka tuna cewa, Yesu ya yaba wa waɗanda suke jin yunwa ta ruhaniya, ko kuma waɗanda suke “ladabi a ruhu.” (Matta 5:3) Gata ce mai girma mu taimaki waɗansu su sami farin cikin da Yesu ya yi alkawarinsa!
8. Wace koyarwa ce ta sa mutane suka gaskata cewa Allah ne yake da alhakin wahala, kuma ta yaya ne za mu iya taimaka musu?
8 Na uku, ya kamata mu taimaki mutumin ya fahimci cewa Allah ba shi da alhakin mugunta da yake faruwa a duniya. An koyar da mutane da yawa cewa Allah ne yake mulkin wannan duniya da muke ciki, cewa Allah ya san dukan abin da yake faruwa da mu, kuma wai ba za mu iya fahimta dalilin da ya sa ’yan adam suke wahala ba. Waɗannan koyarwan ba gaskiya ba ne. Hakan ba ya daraja Allah kuma yana nuna cewa shi ke da alhakin mugunta da wahala a duniya. Saboda haka ya kamata mu yi amfani da Kalmar Allah ta wurin daidaita al’amura. (2 Timothawus 3:16) Shaiɗan Iblis ne yake mulki a wannan lalatacen zamanin, ba Jehobah ba ne. (1 Yohanna 5:19) Jehobah bai ƙaddara halittunsa masu hankali ba; amma ya ba su ’yanci da kuma zarafi su zaɓa tsakanin nagarta da mugunta, da kuma abu mai kyau da marar kyau. (Kubawar Shari’a 30:19) Saboda haka, ba Jehobah ba ne tushen mugunta, ya ƙi jinin mugunta kuma yana kula da waɗanda suke wahala.—Ayuba 34:10; Misalai 6:16-19; 1 Bitrus 5:7.
9. Waɗanne littattafai ne “bawan nan mai-aminci mai-hikima” ya yi tanadinsu don ya taimaka wa mutane su fahimci abin da ya sa Jehobah Allah ya ƙyale wahala?
9 Bayan ka daidaita wannan batu, za ka ga cewa mai sauraronka yana so ya san abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala ta ci gaba. Don ya taimaka maka, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadin littatafai da za su amfane ka. (Matta 24:45-47) Alal misali, a taron gunduma ta “Ibada ta Allah” ta shekara ta 2005 zuwa 2006, an fito da wata warƙa mai jigo Dukan Wahala za ta Ƙare ba da Daɗewa ba! Idan da wannan waƙar a yarenku, ka karanta abin da waƙar take ɗauke da shi. Hakazalika, littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, wanda a yanzu ana iya samunsa a harsuna 157, yana ɗauke da wani babi da ya tattauna wannan tambaya. Ka yi amfani da irin waɗannan littattafai. Sun yi bayani sarai game da tushen batun ikon mallaka na Nassi da aka yi a Adnin da kuma abin da ya sa Jehobah ya bi da batun yadda ya yi. Ka tuna cewa, sa’ad da kake tattauna wannan batu, kana koya wa mai sauraronka ilimi na musamman. Wannan ilimi na Jehobah ne da kuma halayensa masu ban al’ajabi.
Ka Mai da Hankali ga Halayen Jehobah
10. Menene wasu suka kasa fahimta game da abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, kuma menene zai taimake su?
10 Sa’ad da kuke taimaka wa mutane su fahimci abin da ya sa Jehobah ya ƙyale ’yan adam su yi mulkin kansu a ƙarƙashin rinjayar Shaiɗan, ka yi ƙoƙari ka jawo hankalinsu ga halayen Jehobah masu ban al’ajabi. Yawancin mutane sun sani cewa Allah yana da iko; suna ji ana kiransa Allah Maɗaukaki. Duk da haka, sun kasa fahimtar abin da ya sa bai yi amfani da ikonsa ya kawar da rashin adalci da wahala nan da nan ba. Wataƙila ba su fahimci waɗansu halayen Jehobah ba, kamar su tsarkaka, adalci, hikima da kuma ƙauna. Jehobah yana amfani da waɗannan halaye a hanya da ta dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aikinsa cikakke ne.” (Kubawar Shari’a 32:4) Ta yaya za ka nanata waɗannan halayen sa’ad da kake amsa tambayoyin da ake yi game da wannan batu? Bari mu tattauna wasu misalai.
11, 12. (a) Me ya sa gafartawa ba za ta yiwu ba sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi? (b) Me ya sa Jehobah ba zai ƙyale zunubi har abada ba?
11 Me ya sa Jehobah bai gafarta wa Adamu da Hauwa’u ba? Gafartawa ba za ta yiwu ba a wannan batu. Da yake su kamiltattu ne, da gangan Adamu da Hauwa’u suka ƙi ikon mallaka na Jehobah, suka bi ja-gorar Shaiɗan. Babu shakka, ’yan tawayen ba su nuna sun tuba ba. Duk da haka, idan mutane suka ce, me ya sa Jehobah bai gafarta masu ba, wataƙila suna tunani abin da ya sa Jehobah bai yi watsi da mizaninsa ba don ya ƙyale zunubi da tawaye. Amsar ta dangana ne bisa halin Jehobah na musamman wato tsarkakarsa.—Fitowa 28:36; 39:30.
12 Littafi Mai Tsarki ya nanata tsarkakar Jehobah sau da yawa. Abin baƙin ciki, mutane kaɗan ne a cikin wannan lalataciyar duniya suka fahimci wannan halin. Jehobah yana da tsarki da tsabta, kuma yana keɓe kansa daga kowane zunubi. (Ishaya 6:3; 59:2) Game da zunubi, ya yi tanadin kafara, kuma zai kawar da shi, ba zai ƙyale shi har abada ba. Idan Jehobah yana son ya ƙyale zunubi har abada, ba za mu sami bege na nan gaba ba. (Misalai 14:12) A lokacin da ya zaɓa, Jehobah zai tsarkake dukan mutane. Hakika, nufin Mai Tsarki ne ke nan.
13, 14. Me ya sa Jehobah bai halaka ’yan tawaye a Adnin ba?
13 Me ya sa Jehobah bai halakar da ’yan tawayen a Adnin ba, ya halicci waɗansu? Hakika yana da ikon da zai yi haka; ba da daɗewa ba zai yi amfani da ikonsa ya halaka miyagu. Wasu za su yi tunani, ‘me ya sa bai yi haka ba sa’ad da miyagu uku ne kawai a sararin samaniya? Da hakan ya hana zunubi da dukan abubuwa da muke gani suna faruwa a duniya.’ Me ya sa Jehobah bai yi haka ba? Kubawar Shari’a 32:4 ta ce: “Dukan tafarkunsa shari’a ne.” Jehobah ya ɗauki adalci da muhimmanci. Hakika, “Ubangiji yana son shari’a.” (Zabura 37:28) Saboda irin ƙaunar adalci da yake yi ne, ya sa Jehobah ya ƙi ya halaka ’yan tawaye a Adnin. Me ya sa?
14 Tawayen da Shaiɗan ya yi ya ta da tambaya game da gaskiyar ikon mallaka ta Allah. Azancin Jehobah yana bukatar a amsa zargin Shaiɗan a cikin adalci. Idan aka halaka ’yan tawayen da sauri, zai kasance abin da ya dace da su ke nan, amma ba zai ba da amsar da ta dace ba. Hakan zai nuna ikon mallaka na Jehobah ne, amma ba ikon Jehobah ba ne ake zargi. Bugu da ƙari, Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u nufinsa. Nufinsa shi ne su haifi ’ya’ya, su cika duniya, su mallake ta, kuma su yi mulkin dukan halitta na duniya. (Farawa 1:28) Da a ce Jehobah ya halaka Adamu da Hauwa’u, nufinsa game da ’yan adam ba za ta cika ba. Adalcin Jehobah ba zai taɓa ƙyale irin wannan abu ba, saboda koyaushe yana cika nufinsa.—Ishaya 55:10, 11.
15, 16. Idan mutane suka ba da nasu “amsa” game da zargin da aka yi a Adnin, ta yaya za mu taimake su?
15 Shin akwai wanda zai iya bi da wannan tawaye da hikima fiye da Jehobah ne? Wasu mutane za su iya tsara nasu hanyar “magance” tawayen da aka yi a Adnin. Ta wurin yin haka, ba za su nuna cewa sun fi Jehobah hikima ba ne. Ba za su yi haka don suna da mugun ra’ayi ba ne, amma gaskiya ita ce domin ba su fahimci Jehobah da kuma hikimarsa mai ban al’ajabi ba. Sa’ad da yake rubuta wasiƙa ga Kiristoci a Roma, manzo Bulus ya yi bincike game da hikimar Allah da kuma “asirin da ke ɓoye,” da kuma nufin Jehobah na yin amfani da Mulkin Almasihu ya ceci amintattu ’yan adam kuma ya tsarkake sunansa mai tsarki. Yaya ne Bulus ya ji game da hikimar Allah wanda yake da irin wannan nufin? Manzon ya kammala wasiƙarsa da waɗannan kalaman: “Ga Allah kaɗai mai-hikima, ta wurin Yesu Kristi; a gareshi daraja har abada. Amin.”—Romawa 11:25; 16:25-27.
16 Bulus ya fahimci cewa Jehobah ‘kaɗai ne mai-hikima’ shi ya fi kowa hikima a dukan sararin samaniya. Wanene a cikin mutane ajizai zai yi tunanin hanya mafi kyau na magance wata matsala, balle ma wannan matsala mai wuya da ta ƙalubalanci hikimar Allah? Ya kamata mu taimaki mutane su dogara ga Allah da yake da “hikima a zuciya.” (Ayuba 9:4) Idan muka fahimci hikimar Jehobah, za mu gaskata cewa hanyar da ya bi da abubuwa ne ya fi kyau.—Misalai 3:5, 6.
Fahimtar Halin Jehobah na Musamman
17. Ta yaya ne fahimtar ƙaunar Jehobah za ta taimaki waɗanda suke damuwa da abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala?
17 “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Da waɗannan kalaman, Littafi Mai Tsarki ya nuna halin Jehobah na musamman, wato halin da ya fi dukan halayensa kuma shi ne yake ƙarfafa waɗanda suke damuwa saboda yawan mugunta. Jehobah ya nuna ƙauna ta yadda ya bi da zunubi da yake halaka halittunsa. Ƙauna ce ta motsa Jehobah ya yi tanadin bege ga ’ya’yan Adamu da Hauwa’u, ya yi musu tanadin komawa gare shi kuma su kafa dangantaka da shi. Ƙauna ce ta motsa Allah ya yi tanadin fansa da zai buɗe hanyar gafarta zunubai da kuma maido da kamiltacciyar rayuwa ta har abada. (Yohanna 3:16) Kuma ƙauna ce ta motsa shi ya jimre da ’yan adam, ya ba mutane da yawa ’yancin ƙin Shaiɗan kuma su zaɓi Jehobah ya zama Maɗaukakinsu.—2 Bitrus 3:9.
18. Wane gata ne muke da shi, kuma menene za mu tattauna a talifi na gaba?
18 Sa’ad da wani fasto yake magana da mutane da suka taru don su tuna da ranar da aka yi wani ta’addanci mai ɓarna, ya ce: “Ba mu san dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala ta ci gaba ba.” Wannan abin baƙin ciki ne! Bai kamata mu yi farin ciki saboda mun fahimci wannan batu ba? (Kubawar Shari’a 29:29) Tun da yake Jehobah mai hikima ne, mai adalci, kuma mai ƙauna, mun sani cewa ba da daɗewa ba zai kawo ƙarshen dukan wahala. Hakika, ya yi alkawari zai yi haka. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Akwai bege ga dukan waɗanda suka mutu a dukan ƙarnuka kuwa? Yadda Jehobah ya bi da batun a Adnin ya bar su babu bege ne? A’a. Ƙauna ta motsa shi ya yi musu tanadin tashin matattu. Abin da za mu tattauna ke nan a talifi na gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za ka amsa wa mutumin da ya yi tambaya game da abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala?
• Ta yaya ne Jehobah ya nuna tsarkakarsa da adalci ta yadda ya bi da ’yan tawaye a Adnin?
• Me ya sa ya kamata mu taimaki mutane su fahimci ƙaunar Jehobah?
[Hoto a shafi na 11]
Ka taimaki waɗanda suke damuwa da wahala a duniya
[Hotuna a shafi na 13]
Amintattu Dauda da Habakkuk sun yi wa Allah tambayoyi