Cikakken Sani Game da Allah na Yi Mana Ta’aziyya
GA WASU mutane, abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙaunar Allah da jinƙai na ta da tambayoyi. Sun yi tambaya: Idan Allah yana son ya kawar da mugunta, kuma ya san yadda zai yi haka, kuma yana da iko ya yi haka, me ya sa mugunta ta ci gaba da ƙaruwa? A gare su matsalar ita ce a warware abubuwa uku da ba daidai ba: na (1) Allah mai iko duka ne; na (2) Allah mai ƙauna ne kuma nagari; na (3) abubuwa na mugunta ta ci gaba da faruwa. Sun yi tunani cewa idan na uku gaskiya ne, aƙalla ɗaya cikin sauran biyu ba zai zama gaskiya ba. A gare su, Allah ba zai iya hana mugunta ba ko kuma bai damu ba.
’Yan kwanaki bayan halaka Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a New York, (World Trade Center) sanannen shugaban addini a Amirka ya ce: “A rayuwata an tambaye ni sau da yawa abin da ya sa Allah ya ƙyale masifa da wahala. Hakika, ban san dalilin ba gabaki ɗaya, kamar yadda nake so.”
Wajen mai da martani ga wannan kalami, wani farfesa na tauhidi ya rubuta cewa “tauhidi mai kyau” da wannan shugaban addini ya yi wa’azinsa ya burge shi. Ya kuma yarda da ra’ayin wani ɗalibi da ya rubuta: “Rashin yiwuwar fahimtar wahala ɓangare ne na rashin yiwuwar fahimtar Allah.” Amma da gaske ba zai yiwu ba a fahimci abin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta?
Tushen Mugunta
Akasin abin da shugabanan addinai suka ce, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za a iya fahimtar abin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta. Abu na farko ga fahimtar batun mugunta fahimtar cewa Jehovah bai halicce duniya ta mugunta ba. Ya halicce ma’aurata na farko kamiltattu, babu zunubi. Jehovah ya dubi aikinsa na halitta ya ga “yana da kyau.” (Farawa 1:26, 31) Nufinsa ne Adamu da Hauwa’u su faɗaɗa Aljanna na Adnin zuwa dukan duniya kuma mutane masu farin ciki su zauna a ciki a ƙarƙashin kāriya na ikon mallakarsa na ƙauna.—Ishaya 45:18.
Mugunta ta soma da wata halitta ta ruhu, wadda dā tana da aminci ga Allah, amma ta so a bauta mata. (Yaƙub 1:14, 15) An ga tawayenta a duniya sa’ad da ta rinjayi ma’aurata na farko su bi ta wajen yi wa Allah rashin biyayya. Maimakon su yi biyayya ga umurnin Allah da ke a bayyane kada su ci ko taɓa ’ya’yan itace na sanin nagarta da mugunta, Adamu da Hauwa’u suka tsinke wasu suka ci. (Farawa 3:1-6) A yin haka, sun yi wa Allah rashin biyayya kuma sun nuna cewa sun fi son ’yancin kansu.
An Tayar da Mahawwara
Wannan tawayen a Adnin ya tayar da mahawwara, ƙalubale da yake da muhimmanci a dukan duniya. ’Yan tawayen sun yi shakkar ko Jehovah yana nuna iko yadda ya dace bisa halittarsa. Mahaliccin yana da ikon ya bukaci cikakkiyar biyayya daga mutane? Zai fi kyau ne idan mutane suka bi ’yancin kansu?
Jehovah ya bi da wannan zargi ga sarautarsa a hanyar da ta nuna cikakkiyar ƙauna, shari’a, hikima, da iko. Zai iya amfani da ikonsa ya halaka ’yan tawayen babu ɓata lokaci. Da wannan ya zama kamar daidai, tun da yake yana da iko ya yi haka. Amma yin haka ba zai amsa tambayoyin da aka yi ba. A wata sassa, da Allah sai ya ƙyale zunubin kawai. Ga wasu mutane a yau da irin wannan tafarki zai fi kyau. Duk da haka, wannan ma ba zai amsa da’awar Shaiɗan ba cewa zai fi kyau ’yan Adam su yi sarautar kansu. Bugu da ƙari, irin wannan tafarki ba zai ƙarfafa wasu su ratse daga hanyar Jehovah ba? Sakamakon zai zama wahala da ba za ta ƙare ba.
A cikin hikimarsa, Jehovah ya ƙyale mutane su mallaki kansu na ɗan lokaci. Ko da wannan yana nufin ƙyale mugunta na ɗan lokaci, da haka mutane sun samu zarafin nuna ko za su iya sarautar kansu da ’yanci daga Allah, su yi rayuwa ta mizanan kansu na abin da ke nagari da mugunta. Menene sakamakon haka? Tarihin ’yan Adam ya cika da yaƙi, rashin gaskiya, zalunci, da wahala. Kasawar tawaye ga Jehovah zai warware mahawarar da aka tayar a Adnin dindindin.
Yayin nan, Allah ya nuna ƙaunarsa ta ba da Ɗansa, Yesu Kristi, wanda ya ba da ransa hadayar fansa. Wannan ya sa mutane masu biyayya su ’yantu daga hukuncin zunubi da mutuwa da rashin biyayyar Adamu ya kawo. Fansar ta buɗe hanyar rai madawwami ga duka da suka ba da gaskiya cikin Yesu.—Yohanna 3:16.
Muna da tabbaci mai ta’azantarwa cewa wahalar ’yan Adam na ɗan lokaci ne. Mai Zabura ya rubuta: “In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: hakika, da aniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:10, 11.
Kwanciyar Rai da Farin Ciki a Nan Gaba
Cikar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokacin da Allah zai kawo ƙarshen ciwo, baƙin ciki, da mutuwa ya yi kusa. An ba manzo Yohanna a wahayi hoton abubuwa masu ban al’ajabi da za su zo. Ya rubuta: “Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma: gama sama ta fari da duniya ta fari sun shuɗe; teku kuma ba shi. . . . Allah kuma da kansa za ya zauna tare da [mutane], ya zama Allahnsu: Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” A furci da ya nanata gaskiyar wannan alkawari, an gaya wa Yohanna: “Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.”—Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.
Mutane biliyoyi marasa laifi da suka mutu tun lokacin tawayen a Adnin fa? Jehovah ya yi alkawari cewa zai mayar da mutane da yanzu suna barci a mutuwa zuwa rai. Manzo Bulus ya ce: “Ina da bege ga Allah, . . . za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Waɗannan za su sami begen rayuwa a duniya inda “adalci ya ke zaune.”—2 Bitrus 3:13.
Kamar yadda uba mai ƙauna zai bari a yi wa ɗansa aiki mai zafi idan ya san zai amfana dindindin, haka Jehovah ya bar mutane su wahala na ɗan lokaci daga mugunta a duniya. Duk da haka, albarka ta har abada na jiran duka da suke neman su yi nufin Allah. Bulus ya yi bayani: “Aka ƙasƙantadda talikai zuwa banza, ba da yardar kansu ba, amma sanadin shi wanda ya sanya su, ana bege talikai da kansu kuma za su tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.”—Romawa 8:20, 21.
Hakika wannan labari ne—ba irin wanda muke gani a telibijin ba ko kuma wanda muke karantawa a jarida amma labari ne mai kyau. Labari ne mafi kyau daga “Allah na dukan ta’aziyya” Wanda lallai yake ƙaunarmu.—2 Korinthiyawa 1:3.
[Hotuna a shafi na 6]
Lokaci ya nuna cewa mutane ba za su yi sarautar kansu da kyau ba tare da taimakon Allah ba
[Inda aka Daukos]
Iyalin Somaliya: UN PHOTO 159849/M. GRANT; bom na atam: hoton USAF; sansani: hoton U.S. National Archives