Yadda Nagarta Za Ta Yi Nasara Bisa Mugunta
Sarki Dauda mutum ne nagari. Ya ƙaunaci Allah ƙwarai, ya ƙaunaci adalci, kuma yana ƙaunar matalauta. Duk da haka, wannan nagarin sarki ya yi zina da matar amintaccen bawansa. Kuma bayan ya fahimci cewa ya yi wa matar, Bathsheba, ciki, sai ya ƙulla mutuwar mijinta. Kuma ya auri Bathsheba domin ya rufe zunubinsa.—2 Samuila 11:1-27.
ABAYYANE yake cewa mutane suna iya yin nagarta ƙwarai. Amma to me ya sa suke da alhakin mugunta da yawa? Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai masu yawa game da wannan. Kuma ya bayyana yadda Allah ta wurin Yesu Kristi zai kawar da mugunta har abada.
Muradin Yin Mugunta
Sarki Dauda da kansa ya nuna dalili ɗaya na yin miyagun ayyuka. Bayan an fallasa muguntarsa, ya ɗauki alhakin abin da ya yi. Sai ya rubuta cikin nadama: “Ga shi, cikin mugunta aka sifanta ni; cikin zunubi kuma uwata ta ɗauki cikina.” (Zabura 51:5) Ba nufin Allah ba ne mata su haifi ’ya’ya da za su yi zunubi. Amma, sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka zaɓi su yi wa Allah tawaye, sun yi rashin iyawarsu na haifan ’ya’ya marasa zunubi. (Romawa 5:12) Sa’ad da zuriyar ’yan adam ajizai ta ƙaru, ya bayyana cewa “tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.”—Farawa 8:21.
Idan ba tare da kame kai ba, wannan muradin na yin miyagun ayyuka zai kai ga yin “fasikanci . . . husuma, kishekishe, hasala, tsatsaguwa, rabuwa, hamiya, hasada, maye, nishatsi,” da kuma wasu halaye marasa kyau da Littafi Mai Tsarki ya kira “ayyukan jiki.” (Galatiyawa 5:19-21) Kamar yadda ya kasance da Sarki Dauda, ya kasa kame kansa hakan ya sa ya yi zina, da kuma husuma. (2 Samuila 12:1-12) Da ya tsayayya wa muradinsa na lalata. Maimakon haka, Dauda ya ci gaba da sha’awar Bathsheba, ya bi tafarkin da almajiri Yaƙub ya kwatanta haka: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacinda sha’awa ta habala, ta kan haifi zunubi: zunubi kuwa, sa’anda ya ƙasaita, ya kan fidda mutuwa.”—Yaƙub 1:14, 15.
Kisan kiyashi, fyaɗe, da kuma kwasan ganima da aka ambata a talifi da ya gabata misalai ne masu tsanani na abubuwa da suka faru sa’ad da mutane suka ƙyale muguwar sha’awarsu ta rinjayi ayyukansu.
Jahilci Yake Jawo Mugunta
Abin da manzo Bulus ya fuskanta ya bayyana dalili na biyu da ya sa mutane suke miyagun ayyuka. Sa’ad da Bulus ya mutu an san shi mutumin kirki ne mai ƙauna. Ya ba da kansa babu son kai ga hidima domin ’yan’uwansa Kiristoci maza da mata. (1 Tassalunikawa 2:7-9) Amma da farko a rayuwarsa, sa’ad da aka san shi da suna Shawulu, yana “yin numfashi da kashedi da kisa” ga wannan rukuni. (Ayukan Manzanni 9:1, 2) Me ya sa Bulus ya yarda ya saka hannu cikin mugun aiki da aka yi wa Kiristoci na farko? “Da rashin sani na yi shi,” in ji shi. (1 Timothawus 1:13) Hakika, da farko Bulus yana “da himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba.”—Romawa 10:2.
Kamar Bulus, mutane masu gaskiya da yawa suna saka hannu cikin miyagun ayyuka domin rashin cikakken sanin nufin Allah. Alal misali, Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Sa’a tana zuwa, inda dukan wanda za ya kashe ku, za ya zace yana yi ma Allah hidima.” (Yohanna 16:2) Shaidun Jehobah na zamani sun ga gaskiyar kalmomin Yesu. A ƙasashe masu yawa, an tsananta musu har ma mutanen da suke da’awar suna bauta wa Allah sun kashe su. A bayyane yake cewa irin wannan himma ba ta faranta wa Allah rai.—1 Tassalunikawa 1:6.
Tushen Mugunta
Yesu ya bayyana ainihin dalilin da ya sa mugunta ta wanzu. Da yake magana da shugabannin addini da suke da niyyar su kashe shi, ya ce: “Ku na ubanku Shaiɗan ne, ƙyashe ƙyashe na ubanku kuma kuna da nufi ku yi. Shi mai-kisan kai ne tun daga farko.” (Yohanna 8:44) Domin son kai Shaiɗan ya yaudari Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah tawaye. Wannan tawayen ne ya kawo zunubi, zunubi kuwa ya jawo mutuwa ga dukan mutane.
Muradin Shaiɗan na kisa ya sake bayyana a abin da ya yi wa Ayuba. Sa’ad da Jehobah ya ba shi izini ya gwada amincin Ayuba, Shaiɗan bai gamsu da halaka dukiyarsa ba. Ya kuma sa ’ya’yansa goma suka mutu. (Ayuba 1:9-19) A shekarun baya bayan nan, ’yan adam sun ga ƙarin yaɗuwar mugunta, ba kawai domin ajizanci na mutane da kuma jahilcinsu ba, amma kuma domin Shaiɗan ya ƙara saka hannu a ayyukan ’yan adam. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa an “jefarda shi [Shaiɗan] a duniya, aka jefarda mala’ikunsa kuma tare da shi.” Wannan annabci kuma ya nuna cewa wannan hani na Shaiɗan zai ƙara “kaiton duniya.” Ko da yake Shaiɗan ba zai tilasta wa mutane su yi miyagun abubuwa ba, gwani ne wajen “ruɗin dukan duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.
Kawar da Muradin Yin Mugunta
Domin a kawar da mugunta har abada tsakanin ’yan adam, dole ne a mai da hankali ga muradin mutum na yin mugun abu, da kuma jahilcinsa, da kuma rinjayar Shaiɗan. Na farko, ta yaya za a kawar da muradin mutum na yin mugunta daga zuciyarsa?
Babu wani likita mai fiɗa, ko kuma magani na ɗan adam da zai iya wannan aiki. Amma Jehobah Allah ya yi tanadin magani ga zunubi da ajizanci da muka gada ga dukan waɗanda suke bukatarsa. Manzo Yohanna ya rubuta: “Jinin Yesu Ɗansa yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka.” (1 Yohanna 1:7) Sa’ad da kamiltaccen mutum Yesu ya ba da ransa da son rai, ya “ɗauki zunubanmu ya kai su cikin jiki nasa bisa itacen, domin mu, matattu ga zunubai, mu rayu ga adalci.” (1 Bitrus 2:24) Mutuwar Yesu ta hadaya za ta kawar da sakamakon muguntar Adamu. Bulus ya faɗi cewa Yesu Kristi ya “bada kansa fansar dukan mutane.” (1 Timothawus 2:6) Hakika, mutuwar Kristi ta buɗe hanya ga dukan mutane su sami kamilta da Adamu ya yi hasara.
Kana iya tambaya, ‘Idan mutuwar Yesu shekaru 2,000 da suka shige ta sa ya yiwu mutane su sami kamilta, me ya sa mugunta da kuma mutuwa suke wanzuwa?’ Samun amsar wannan tambayar zai taimaka a kawar da dalili na biyu na mugunta, wato, rashin sanin nufin Allah.
Cikakken Sani Yana Ƙarfafa Nagarta
Samun cikakken sanin abin da Jehobah Allah da Yesu suke yi a yanzu domin su kawar da mugunta, zai hana mutane masu zuciyar kirki daga yarda da ayyukan mugunta, ko ma mafi muni, su zama masu yaƙi “har da Allah.” (Ayukan Manzanni 5:38, 39) Jehobah Allah yana shirye ya gafarta zunuban da aka yi cikin jahilci. Da yake magana a Atina, manzo Bulus ya ce: “Kwanakin jahilci fa Allah ya yi birin da su; amma yanzu yana umurtan mutane dukansu cikin kowane wuri su tuba: da shi ke ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara; wannan fa ya bada shaidarsa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.”—Ayukan Manzanni 17:30, 31.
Bulus ya shaida cewa an tashi Yesu daga matattu, domin Yesu kansa ya yi magana da Bulus kuma ya hana shi tsananta wa Kiristoci na fari. (Ayukan Manzanni 9:3-7) Da Bulus ya sami cikakken sani na nufin Allah, ya canja halinsa ya zama mutumin kirki wajen koyi da Kristi. (1 Korinthiyawa 11:1; Kolosiyawa 3:9, 10) Bugu da ƙari, Bulus ya yi biyayya da himma ga umurnin Yesu ya yi “wannan bishara kuwa ta Mulkin.” (Matta 24:14) A cikin shekaru 2,000 tun bayan mutuwarsa da tashinsa, Kristi yana zaɓan mutane waɗanda kamar Bulus, za su yi sarauta tare da shi a Mulkinsa.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.
Tun a ƙarnuka da suka shige har zuwa yanzu, Shaidun Jehobah sun cika wannan umurni da himma: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi masu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Matta 28:20) Waɗanda suka yi na’am da wannan saƙon suna da begen rayuwa har abada a duniya a ƙarƙashin sarautar samaniya na Kristi. Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Taimaka wa wani ya sami wannan sani shi ne abu mafi kyau da mutum zai iya yi wa ɗan’uwansa.
Ko da yake mugunta ta kewaye su, waɗanda suka karɓi wannan bisharar Mulki suna nuna irin waɗannan halaye “ƙauna . . . , farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.” (Galatiyawa 5:22, 23) Wajen koyi da Yesu, ba sa “sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.” (Romawa 12:17) Kowannensu, yana ƙoƙari ya “rinjayi mugunta da nagarta.”—Romawa 12:21; Matta 5:44.
Nasara na Ƙarshe Bisa Mugunta
’Yan adam da kansu ba za su iya yin nasara a kan Shaiɗan Iblis ba wanda shi ne tushen mugunta. Amma ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi amfani da Yesu ya “ƙuje Shaiɗan” a ƙarƙashin sawayensa. (Romawa 16:20) Jehobah kuma zai umurci Yesu Kristi ya “farfashe” dukan wannan zamani na siyasa, da yawa cikinsu kuwa sun yi ayyukan mugunta a cikin tarihi. (Daniel 2:44; Mai Wa’azi 8:9) A wannan lokaci mai zuwa na hukunci, dukan waɗanda suka “ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu . . . za su sha, madawwamiyar halaka.”—2 Tassalunikawa 1:8, 9; Zephaniah 1:14-18.
Da zarar an kawar da Shaiɗan da dukan waɗanda suka tallafa masa, daga sama Yesu zai taimaki waɗanda suka tsira su mai da duniya ta zama kamar yadda take can asali. Kristi kuma zai ta da dukan waɗanda suka cancanci su rayu a sabuwar duniya. (Luka 23:32, 39-43; Yohanna 5:26-29) Wajen yin haka, zai kawar da sakamakon mugunta da mutane suka fuskanta.
Jehobah ba zai tilasta wa mutane su yi biyayya ga bishara game da Yesu ba. Amma, yana ba wa mutane zarafin su sami sani da zai sa su sami rai. Yana da muhimmanci ka yi amfani da wannan zarafin yanzu! (Zephaniah 2:2, 3) Idan haka ne, za ka koyi ka jimre wa dukan mugunta da ta ɓata maka rayuwa a yanzu. Kuma za ka ga yadda Kristi zai yi nasara na ƙarshe bisa mugunta.—Ru’ya ta Yohanna 19:11-16; 20:1-3, 10; 21:3,4.
[Hoto a shafi na 5]
Shawulu ya yarda da mugunta domin ba shi da cikakken sani
[Hoto a shafi na 7]
Taimakon wani ya sami cikakken sani na Allah shi ne abu mafi kyau da mutum zai yi wa ɗan’uwansa